Showing 48001 words to 51000 words out of 77913 words

Chapter 17 - 'Yar Mahaukaciya

10 Oct 2024

15921

ya ce " No ba jikarta bace, hasalima bata hada komai da ita ba , ranar da na fara yin tiyata a rasun nan ranar da bazan taba mantawa da ita ba a ranan na hadu da ita , sanan a ranar hajiya ta ganta , yaron da ya rasun danta ne ,,,..............''''''''''''',,,,,,,,,,,,,nan ya kwashe duka yanda akayi har daukanta da sukayi shi da Hajiya Hawau ya fadawa Mubasshir Wanda yake sauraronsa kamar ana kara yi masa bita ne kan abinda aka karanta masa



Mubasshir ya ce " kuma haka kuka dauki yarinyar da baku san KO wacece ba , wada ta shigo maka asibiti da yaro jiki a farfashe? Shin idan fa wata muguwa ce KO sato dan tayi?


Abdul ya kawar da kansa ya ce" she is innocent, tabas Rahma ba muguwa bace, sanan kamila ce, kuma nitsatsiya ce, domin da muguwa ce a zaman mu da ita da KO ta yaya sai halinta ya fito



Mubasshir ya kuma jefo masa tambayar " kana sonta ne?


Abdul ya gyara zama yace" ina sonta tamkar yar uwata ta jini, ina jinta a jinin jikina,


Mubasshir ya ce" ya akayi ka gane cewar kana sonta? Mai kake ji har ka gane cewar sonta ne kake?


Abdul ya dago ya kuma kalon Mubasshir Wanda daman shi yake kalo, da alamar mamakin tambayoyinsa ya ce" kafi kowa sani domin kai har kayi aure KO?



Mubasshir ya koma ya jongina da kujerar da yake zaune ya lumshe idanuwansa ya ce" kafi kowa sanin KO auren mai nayi,kafi kowa sanin amintaka ta ci karfina har na kasa yin musu da abinda ya zamto tamkar a cikin duhu nake, ya kuma dago kansa ya ce " freind tell me dan Allah mai ake ji? May be na dade da fara son matata rashin sanin inda so din soyaya ya nufa ya hana ni ganewa



Abdul ya ja ajiyar zuciya ya ce" tabas kai namiji ne mai kokari, jarumta, na yarda da jarumtar ka , sanan na gode da abinda kayi domin ni, nima Allah ya bani ikon yi maka abin alkhairi , ya nisa ya dora da cewa" idan kaga abin sonka kafin ka furta masa kalmar so zakana ji gabanka na faduwa, koya ka nisanta da shi burinka ka dawo ka gansa, koda mumuna ne tofa zaka Ganshi ba Wanda ya kaishi kyau, da zarar kun hada idanuwa sai gabanka ya fadi, baka gajiya da kalonsa, ka tsani wani ya rabe sa balatana namiji, ka tsani wani ya kale shi, ka tsani....



Cikin Sauri Mubasshir ya furta wait wait wait yana daga hanunsa sanan dayan hanun yana laluba gashin kansa ya mike da sauri ya debi ruwa ya rufe ido ya shanye tas sanan ya ajiye kofin ya juyo yana kalon Abdul Wanda yayi tsamanin KO kwaruwa yayi ya ce" aman ai idan amanarka ne ma kana iya jin irin haka KO?



Abdul ya ce" koda kanwarka ce bazaka ji irin hakan ba , ina tsaka da zana maka ka katse ni , naci gaba ne?


Mubasshir ya shiga girgiza kai uwa karamin yaro ya ce" No barshi haka is OK



Abdul ya ce" gaba daya abinda na zana maka ba Wanda bana ji a tatare da yarinyarnan , dan haka ya hade hanayensa ya ce" ka taimakeni ka taya ni ta fada min inda take




Mubasshir ya rintse idanuwansa ya bude ya ce" zanyi kiranka zanje na ganta karka damu



Abdul ya taso cikin jin dadi ya rungume Mubasshir yana yi masa godiya sanan yayi masa salama ya fita


Yana tafiya Mubasshir ya shiga zaro ido tamkar sabon kamu ya fada saman kujera jagob ya tatara gashin kansa ya cakula ya rufe ido yana furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une , inalilahi wa'ina ilaihi raj'une , ya buga hanunsa saman table ji kake taratsatsa domin kolba ce ta fashe

Zumbur ya kuma mikewa ya dauki ky din motarsa hanunsa na digar jini aman bai damu ba ya fito ya shiga motarsa ma'aikatan sai kalonsa suke kowa na mamakinsa aman ba Wanda ya nufe shi dan ba fuskar hakan ,


Tuki yake na ganganci kansa ba hula sanan ba Babar rigarsa a jikinsa farar Riga ce kawa ta ciki, sai dogon wandonsa na shada , idanuwansa sunyi jajajir haka fuskarsa a murtuke , bai san inda zai nufa ba hasalima burin sa ya ganta a gabansa ya kali fuskarta sanan ya furta mata cewar shi fa sam baya sonta yana kokarin kare mutuncinta ne ,


Wani irin burki ya taka aman ina sai da ya bigi Babar motar da ta kwaso kaya take gabansa ji kake piiiiiiiiit karar oda inda kansa ya fada , jama'a duk suka fifito hanu a saman kai suna furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Da Sauri direban babar motar ya taka birki duk suka firfito suka nufe shi





Zaune suke suna cin abinci wayar dakin ta dauki kara , haka kawai ta ji gabanta ya fadi ta mike da Sauri ta nufi wayar ta daga , sakin wayar tayi sanan ta tafi luuu zata fadi tana fadin inalilahi wa'ina ilaihi raj'une


Da Gudu Yar Mahaukaciya ta tareta tana fadin mama lafiya??????????????????????????????????????????????????????????????????











😱😱😱😱😱😱
πŸ‡³πŸ‡ͺBelles Γ©crivaines du Niger



*'YAR πŸ‘§πŸ»*

*MAHAUKACIYAπŸ‘Ή*

*_Na SAJIDA_*







53
Da gudu Yar Mahaukaciya ta tareta tana faman fadin " Mama lafiya? Aman ina sai da suka kai kasa dan kuwa karfin ba daya ba, cikin Sauri ta rarumo wayar ta kanga a kunanta tayi salama


Daga dayan bangaran likitar take shaida mata anga numberta da kuma ta gida a cikin wani litafi a motarsa yana asibitin Jarumai aman bai ji ciwo sosai ba


Yar Mahaukaciya cikin sarkewar harshe ta ce" wa .....wane yayi hatsarin?"


Matar ta ce" *AA MUBASHIR* "



Yar Mahaukaciya ta furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une sanan ta FITA da sauri tayi Kiran direban gidan kafin ya fitar da motar ta haye sama ta dauko hijabin Hajiya Fadimatu da nata sanan ta sauko cikin gudu gudu ta tsuguna kusan Hajiya Fadimatu ta ce" Mamana yaya bai ji ciwo sosai ba , please ki tashi mu tafi wajensa plz mamana"


Hajiya Fadimatu da sai a lokacin ta dawo daga sumar tsoratar da tayi na jin gidan jininta a asibiti ta mike da kyar ta zura hijabin suka fito suka kama hanyar asibitin




Suna isa aka kaisu dakin da aka kontar da shi cikin girmamawa


Tsayuwa tayi tana kalonsa tana tofa masa adu'a tana yiwa Allah godiya da hatsarin nasa bai zo da tsanani ba , waigowa tayi ta kali doctern ta ce" docter bacin nan na lafiya ne?"


Docter ya ce" eh ma'am alurar baci muka yi masa dan ya huta domin da alama tinani yayi masa yawa dan kuwa shi kadai ya zo ya bigi motar sanan an duba motar lafiyarta lau, kuma shi ba shan wani abin maye yayi ba, ba earpice a kunan sa, kuma kwakwaluwarsa lafiyarta lau kawai dai cikin biyu ne KO wani abin ya taba masa ransa KO yana Sauri ya je wani wajen ne hakan yasa ya kasa control din kansa"


Hajiya Fadimatu ta shafa fuskarsa ta ce" Ya jima yana barcin ne?"



Docter ya ce" eh toh sai da muka daidaita komai ya samu kamar awa uku muna ta neman yanda zamu sanar muku, zuwa yanzu yaci ace ya farka ma sai dai da alama yana jin dadin bacin, Muje ma'am na baku takardun da ake bukatar a cike da kuma na maganin sa"




Hajiya Fadimatu ta kali Yar Mahaukaciya dake tsaye itama tana sauraron bayanan likitan ta ce" Yata bara na dawo" ta juya ta bi bayan doctern




Da tafiyarsu Yar Mahaukaciya tayi tsai tana kalonsa sai bacinsa yake gashin idon nan nasa yayi zagar zagar a konce baki yayi lufluf da shi , bakin nan nasa tamkar ya shafa man lebe sai sheki yake namiji da shekin lebe, a hankali ta jawo kujera ta zauna daf da shi ta dago hanayenta ta dora saman cinyoyinta ta tokare habarta ta zuba masa ido tana kare masa kalo a ranta tana matukar mamakin mumurdewar hanunsa shi kuwa ba karfe yake ci ba a saninta bata taba ganinsa yana irin daga karfen nan aman hanunsa yana yan dambe da ake nunowa a tashar TL9 ,


Tana haka har wani irin baci ya kama idanuwanta ta karewa dakin kalo ba wajen konciya hakan yasa ta dan dora kanta daga bakibakin gadon baci yayi awon gaba da ita ( toh fa ke da aka barwa marar lafiya?)




Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salamar ta , murmushi ne ya subuce mata ganin Mubasshir ya farka yana kalon Yar Mahaukaciya dake baci duk da bai ga fuskarta ba yana son sanin KO wacece ke konce kusan sa ,


Shima Murmushin ya sakar mata ya dago hanunsa irin ta karaso


Hajiya Fadimatu ta karasa suka gaisa da gudan jininta ta ce" Dan Fadimatu yaya saukin jikin?



Mubasshir yayi murmushi cikin muryar maran lafiya ya ce" maman Mubasshir i'm sorry"



Ta girgiza kai ta dora yatsarta a saman lebensa ta ce" no dan gidan Fadimatu dena bani hakuri yarona, Allah ya baka lafiya "


Yayi murmushi yana kalon hanunta magunguna ne ya dan yatsina fuska a ransa ya ce " tap gaskiya ni bazan sha maganin nan ba"



Bayan ta ajiye ledar maganin ta zo a nitse ta tana murmushi ta ce" oh Yar Fadimatu nasan bacin nan na jiya daman bai wani isheta ba , baiwar Allah gashi yanzu mun kado KO abinci bata ci ba




Gaban mubasshir ya fadi ya lumshe idanuwansa yana kalon mahaifiyarsa na kokarin cirewa Yar Mahaukaciya hijabinta dan ya shake mata wuya , yayi gagawar kawar da kansa yana kara rintse idanuwansa a ransa yana ta adu'o'i kan Allah ya kare masa idanuwansa da kalon banban muradin sa



Idanuwanta ta bude suka yi ido hudu da Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce" Mama kin dawo? Baci ne ke damuna



Hajiya Fadimatu ta ce" ai Dole yar Fadimatu, Konta ki hutawarki , ai likitan yace zai mabu salama aman sai dai mu tafi gida da yayanki dan nayi Kiran number matarsa ta yiwa mahaifiyarta rakiya bata nan shi kuwa baya son shan magani sai dai mu tafiyarmu gida da shi



Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana leken fuskarsa ta ce" Allah ya kara afuwa



Hajiya Fadimatu ta ce" Amin , sanan taci gaba da hada masa yan magungunan da likita ya ce ya sha idan ya farka sai a basu salama su je gida ya ci gaba da sha




Cikin ikon Allah likita ya salame su suka nufi gida da magungunan su, aman tunda ya farka bai yarda sun hada ido da Yar Mahaulaciya ba , koda tayi masa sanu da jiki hanunsa kawai ya daga mata a hakan har suka isa gida , inda Hajiya Fadimatu ta rasa dΓ©cision din da zata dauka domin shi dai ba lafiya ne da shi ba, bazata yarda ya kwana a dakunan kasa ba , kuma dakin nasa shine Yar Mahaukaciya ta zauna, sanan tana ganin lokacin ta fada musu gaskiya yayi KO dan su dan saba da juna









πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³
.


πŸ‡³πŸ‡ͺBelles Γ©crivaines du Niger



*'YAR πŸ‘§πŸ»*

*MAHAUKACIYAπŸ‘Ή*

*_Na SAJIDA_*







54

Tana zaunen nan falon tana waya da Hajiya Hawau Yar Mahaukaciya ta fito da kwaryar fura a hanunta ta sha damu sai kanshin kayan daka da cikwui take, cikin nutsuwa ta dan zauna har Hajiya fadimatu ta gama wayar



Ganinta ta karaso ya saka Hajiya Fadimatu fadin "toh Hajiya sai kin zo zuwa yamar, sanan kar fa ki daga hankalinki da sauki jikin"


Tana gamawa ta juyo da murmushin nan nata mai tsada ta kali Yar Mahaukaciya


Yar Mahaukaciya ta taso ta nufota ta ce" Mamana ga furar yayan nan na dama nasan zai sha"


Hajiya Fadimatu ta ce" Sanu da kokari Yar Fadimatu, aman tafi ki kai masa furar yana dakina"


Yar Mahaukaciya ta juya ba dan taso hakan ba dan kuwa tunda yayi hatsarin nan tamkar ya wani tsaneta ne KO baya ji idan tayi magana dan kuwa sai dai kawai ta ga yana hararanta



Cikin nutsuwa da faduwar gaban da bata san KO ta maicece ba ta tura dakin bakinta dauke da sallama ,



Idanuwa ta zaro ganin AA Mubasshir jingine da bed ya dafe zuciyarsa ya mike kafafuwansa yana kallon kasa sanan ga wani hawaye na bin fuskarsa , bata san lokacin da ta yar da kwaryar furar ta nufe shi har tana harde kafa


Tana isa ta dire gwuiwoyinta a kasa ta saka yatsarta ta lakato hawayen kuncinsa dan tabatarwa kanta kuka yake, cikin sarkakiyar murya ta ce" Yaya Mubasshir jikin ne? Ina ke yi maka ciwo? Ka sha maganinka? Dan Allah ka dena kuka, bara na kirawo Mamana"


Ta mike da niyar FITA ta kirawo Hajiya Fadimatu sai taji an riko mata hannunta riko ba na wasa ba , riko na keta da zafi sannan aka fisgota


Dabash ta zauna domin sauran kadan ta kifo a kansa Allah ya sota, ta shiga zazare ido tana tsoron abinda ya saka ya rike mata hanu haka sanan irin yanda ya hada fuska ka rantse cewar ba AA bane , gaba daya ya zama wani abin tsoro





Nunfashi ya ja ya sauke ya zuba mata ido yana ayana abubuwa da dama a ransa sannan ya bude bakinsa yayi iya kokarinsa wajen furtawa mai raya tinaninsa mugayen kalamai inda ya ce" *I hate you* "



Da Sauri Yar Mahaukaciya ta dago idanuwanta wa'inda suka fara canza launi sai hasken mai kama da na magen da ya fara fitowa ta zuba masa su



Hakan ba karamin karayar da shi yayi ba amman sam baya jin zai iya lamuncewa zuciyarsa abinda take so ya ci gaba da fadin" *Yes i hate you, na tsani na hadu da ke, na tsani na zauna tinaninki sanan rashin lafiyata ta dalilinki ne, ke ke din nan dai ke ba zawara ba aman kinfi zawara sanin hanunki dan har kin iya yanda zakiyi ki rikitar da maza, Abdul na sonki, Abdallah na sonki, jama'a da yawa na harin cewar suna sonki , Ni....ya ja nunfashi yaci gaba karyarki ta sha karya a kaina, Ni nafi karfin nace wai ina sonki abin ba dadin ji dan haka ina mai umartar ki da kiyi gagawar tsayar da daya a cikinsu wa'inda suka zubar da girman nasu na aura miki ki kara gaba dan kuwa bana son na ringa cin karo da ke a cikin gidan nan* "




Yar Mahaukaciya dake kalonsa cikin matsanancin faduwar gaba da tarin hawayen dake zuba daga idanuwanta ta ce" *Mai yasa ka tsaneni? Shin wani laifi na aikata?* "



Mubasshir ya kawar da kansa dan kuwa hawayen nan nata ji yake tamkar ya jawota jikinsa ya saka harshen sa ya lashe su sanan ya rukunkumeta dan kar Wanda ya kalan masa ita, yayi gagawar watsar da tinanin ya ce" *kwarai kuwa kina da laifi, kin fi kowa laifi ke laifinki yafi karfin na kawar da kaina kansa dan haka ki kiyayi abinda na fada miki* "



Yar Mahaukaciya ta Mike da kyar ta juya tana tafiya , har ta kusa fita ta juyo ta dawo inda duk takun tafiyarta bugawar zuciyar Mubasshir ne,


Tana dawowa ta tsuguna kanta a kasa ta ce" *shin tsanar da kayi min ta yan'uwantakar ce KO mai?*


Kwarai tambayar ta zo masa a bazata kuma sai a sanan y'a gane ilimi ne da ita , ya kawar da kansa cikin kame kame ya ce" *ai musulmi baya tsanar musulmi banza haka, ina yi miki son yan'uwantaka wanda koda Maman Mubasshir bata yarda da ke ba dalilinki na musulma zan taimaka miki aman banda wanan son ba wani* "


Yar Mahaukaciya ta kuma cewa " *Son soyaya ne na aure baka yi min?* "




Mubasshir ya gyada kansa da alamar gajiyawa da tambayoyinta



Da mamakinsa sai gani yayi ta saki murmushi ta ce" *Har ka bani tsoro yaya, daman ni? Wacece ni? Ilimin me gare ni? Mahaifiyata Mahaukaciya ni yar bola har nayi tsamanin soyaya daga namiji kamarka? Ta yi dariya irin da mamaki ta ci gaba" ai dan gata sai Yar Gata, i'a zan fadawa Abdallah idan da gaske yake ya fito inji yayana* "

Tana gama fadar haka ta mike tayi waje da gudu da alamar jin kunyar nan ,


Mubashir yayi gagawar rike daidai zuciyarsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya tamkar yayi tsere, ya silale nan ya konta yana kalmar shahada domin a yanda zuciyarsa ke bugawa shi yasan kawai lokacinsa ne yayi, yasan kawai shi tashi ta kare domin bai san ciwon *So* ba, ta kafa masa wuka ta barshi da tsiyayar jini a kahon zuciya,







Toh fa AA ai gwara karka bige plz ku tayani da adu'ar kar ya tafiπŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»


πŸ‡³πŸ‡ͺBelles Γ©crivaines du Niger



*'YAR πŸ‘§πŸ»*

*MAHAUKACIYAπŸ‘Ή*

*_Na SAJIDA_*







55

Tana fita d'akinta ta fad'a, ta ja ta rufe ta silale jikin kofar tana mai da numfashi, a hankali ta furta" *Ya Allah , kai kayi talaka kayi mai kud'i, kai kayi mai gata da marar gata, ALLAH da kai na dogara domin kaine gatana, Allah kayi min zab'i ba zabina ba, ALLAH ka zaba mini abinda yafi zama alkhairi a rayuwata, Ya Allah* " ta rintse idanuwanta hoton Bakin AA na furta mata kalmar *I HATE YOU* tayi Saurin bude idanuwanta ta mik'e tana fadin A'uzubilahi mina shaidanin'rajim ta fada bayi ta sakarwa kanta ruwa




Bayan sallar Magarib Yar Mahaukaciya ta sauko amsa Kiran Hajiya Fadimatu a falo, ta sha Riga da Zani na atamfa ta zaya mayafi ja tayi kyau tamkar Yar Tsana duk da ba wata kwaliya ta zana ba , tana isowa ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Fadimatu



Hajiya Fadimatu ta amsa cikin sakin fuska sanan ta ce" Yar Fadimatu ana salama da ke ina jin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login