Showing 27001 words to 30000 words out of 77913 words

Chapter 10 - 'Yar Mahaukaciya

10 Oct 2024

15869

shi yasa , da baki da kyan nan da garin kalon mai kyau har sai kin fadi , sis dan AA yayanki ne shi yasa kyansa baya baki tsoro


Yar Mahaukaciya a ranta ta ce na fiki tsoron kyan bawan Allahn nan domin ina daya daga cikin wa'inda suka Ganshi yana zubawa mahaifiyarsa shagwaba , da a lokacin kika Ganshi da sai kin suma ma ina jin , aman a fili ta ce" idan kin gama ki zo mu kimtsa plz


Suna tsaka da kimtsawa Fati ta dage ta gyara zama tana tsantsarawa Yar Mahaukaciya kwaliya mai shegen kyau da tsari ta caje mata girar ta domin girar kalar gashin kanta , ta dauko tana kokarin zabar mata jan bakin da zata shafa Hajiya Fadimatu ta shigo fuskarta dauke da murmushi


Tayi musu salama


Suka amsa suna gaishe da ita

Ta amsa su tana ta zuba murmushi ta ce" kuyi hakuri yayana na barku ku kadai, kunsan bakin ne da yawa sai yanzu na samu na kufce


Yar Mahaukaciya ta ce" lah ba komai mama

Hajiya Fadimatu ta karasa tana fadin zaku tafi ne wajen dîner?


Fati ta ce" No mama ba zamu je ba


Hajiya fadimatu ta ce ohk ba damuwa , daidai nan wata mata tayi salama da wata jaka a hanunta ta tsuguna har kasa tana gaishe da su fati , suka amsa suna kalonta


Ta juya cikin murmushi ta ce" ma'am wacece kanwar ogan?


Hajiya Fadimatu ta nuna Yar Mahaukaciya ta ce" kin ganta nan baki ga kama ba?


Wace aka nunawa mai aikin bangaren Hajiya Fadimatu ce ta ce" kai masha Allah , Ashe ta warware ma , Allah ya raya mana ita ( uwa wata beby? )


Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin Ya Allah sanan ta karbi jakar ita kuwa ta juya ta bar dakin


Hajiya Fadimatu ta bude jakar wasu abayoyi ne a ciki da kuma wasu mahaukatan less farare tas anyi dogayen riguna da su gwanin ban sha'awa da ribon na less din ta ce" kunga wajen ango ga abinda zasu saka nan wanan less din , tunda bazaku tafi ba sai kuyi shigan arabian ku fito dan saboda hotuna da za'ayi mana da ango kafin ya tafi diner


Yar Mahaukaciya ta ce" An gode mama,,,,,.....kafin ta karasa Hajiya Fadimatu ta rufe mata bakinta tana fadin no kar naji godiyar nan , dan mamanki tayi miki kyauta sai ki kama gode mata? No kiyi hamdallah ya wadatas sanan ta Mika hanu ta dauko wani Jan baki kalar pink ta Mika mata ta ce" wanan shine daidai da kwaliyarki


Yar Mahaukaciya tana murmushi ta karba ta dan goga pink ne Wanda bai ciza ba sanan bashida man lebe a hade da shi ta fito tsaf da ita

Hajiya Fadimatu a ranta ta ce" Allah yayi halita a nan , Allah ya kade hau da bakin duniya , a fili kuwa ta ce" Yar Fadimatu kinyi kyau har kin gaji masha Allah


Yar Mahaukaciya tayi murmushi sanan ta sada kanta , Hajiya Fadimatu ta kali Fati ta ce" takwara kuyi Sauri ku fito fa kunsan al'adar mu da banbanci


Fati ta ce " toh mama i'a gamu nan fitowa


Ta juya ta fita , tana FITA Yar Mahaukaciya ta cire tawul din dake nanade da gashinta ta saka macaji baba ta caje kanta sanan ta dauko ribom ta daidaita gashin tsakiyar kanta ta daure ta warware abayar bata san lokacin da ta furta masha Allah ba ta juyo dan nunawa Fati sai taga ita har ta saka


Fati ta ce" kawai ki rage mamaki yan Mata dan kuwa haduwa mun hadu saka nayi miki roling mu tafi ,


Yar Mahaukaciya ta saka tata Fati ta nada mata mayafin Abayar ta fito tamkar balaraba ga hasken da idanuwanta ke bayarwa idan ta kaleka abin ba'a cewa komai ,suka dauki takalmansu mai shegen kyau suka saka , Fati ta dauko wayarta ita kuwa ta kama hanyar fita cikin takunta na nutsuwa da daukan hankali


Fitowa suka yi suka tarar da matar nan ta dazu tana tsaye tana jiran su , ta ce " Hajiya mu je na kaiku falon da ake salamar angon


Yar Mahaukaciya ta ce" salamar ango kamar yaya?


Amina ta waigo ta ce" Eh ai haka al'adarsu take yanzu angon ya fito tun dazu ana ta hotuna tamkar baza'a daina ba , idan aka gama sai a barku ku uku tunda Hajiya ce yar uwarsa ta jini da Mahaifiyarsa , Mahaifiyarsa tayi masa nasiha sosai da sosai shi Kenan sai ya tafi daga wajen dinern gidansa zai fice da matarsa shi Kenan sai jibi da auren zamu ganshi shima gasuwa zata kawo shi idan ya koma sai bayan sati guda kuma shikenan ya zama magidanci shima


Fati ta ce " waouh wanan tsarin ya tsaru ya birge ni sosai tsarin nan , ta juya kan Yar Mahaukaciya ta ce " sister al'adar ku tana birge ni



Yar Mahaukaciya tayi murmushi tamkar wata sakara ta dan juya kanta a ranta ta ce " nima yanzu na ji ,

Daidai nan suka karaso wani falo Wanda fadin haduwarsa bata lokaci ne , ya hadu ya hadu yayi karshen haduwa , cikin nutsuwa Yar Mahaukaciya ta saka hanunta ta bude tana kalon Fati dake yi mata magana , sai gani tayi Fati ta zama tamkar robo kikam tana kalon ciki


Cikin faduwar gaba ta juyo a hankali idanuwanta sukayi arba da jama'ar dakin ta furta ya salam ta lumshe idanuwanta dan faduwar da gabanta yayi

Hajiya Fadimatu ta mike cike da murmushi ta tarota ta kamo hanun Yar Mahaukaciya da Fati ta ISO har tsakiyar jama'ar dake hahakimce ana ta daukan hoto domin Mubasshir a zaune yake saman wata kujera mai ruwan ash da baki baba gaba daya idanu aka zuba mata ganin wanan yarinyar mai shegen kyau a tare da ita ,


Hajiya Fadimatu cikin Murmushi ta ce" Asalamu alaikum

Gaba dayansu suka amsa mata salamarta kanan ta ce " Ina mai gabatar muku da Yarinyata Rahma , da kuma kawarta mai sunana , Kanwar Mubasshir ce she is my daughter my lovely Girl ta karashe tana sakarwa Yar Mahaukaciya Murmushi



Gaba daya dakin suka kwashi dan surutu suna fadin waouh,

Hajiya Halima ta taso ta karaso gaban kawarta tana murmushi ta Mika hanayenta ta kamo na Yar Mahaukaciya tana murmushi ta jata jikinta suka yi irin gaisuwar nan ta larabawa sanan ta jata gaban sauran kawayen Hajiya Fadimatu suna gaisawa cikin raha kowa yana mamakin daman yayanta biyu?


Bangaren Mubasshir Hajiya Fadimatu ta nufa tana nazartar yanayinsa , lokaci guda du ya wani dan daburce yana kalon kasa gashi Mubinna ta rumgume shi ana daukan su hoto aman sam hankalinsa baya kan daukan hoton


Hajiya Fadimatu na isa ita ma ta shiga aka dauke su da Mubinnat sanan ta yafito Yar Mahaukaciya , sai da gabanta ya fadi ta mike kamar wace Kwaï ya fashewa kaza a ciki ta nufe su , Allah ya taimaketa kafin ta isa Mubinnat ta daga waya tayi waje ,


Cikin nutsuwa ta isa abin mamaki kanshin tiraren da ta fesa shi ne a jikin Mubasshir , shima yana jin kanshin ya dago suka hada ido daidai ta ISO kusa da shi

Cikin Sauri ya kawar da kansa yana ajiyar zuciyar da bai san KO na mainene ba ,

Hajiya Fadimatu ta kara matsota sosai jikin kujerar kamar yanda itama take ta ce " Yar Fadimatu ki saki jikinki mana sanan kiyi murmushi ayi mana hotunan mu

Mubasshir ya dago kansa ya kali Mahaifiyarsa da alamar shagwaba a fuskarsa ya ce" Yar ?????🙁




Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce " yes

Mai hoton ya dauke su ya kai kala biyar sanan Hajiya Fadimatu ta ja Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita a gefen kujerar sanan ta dora hanunta na dama saman kafadarsa kasa kasa ta ce" wai ba zaku saki jikinku ba ana kalonku fa


Mubasshir da yayi sumar zaune ya kuma dago da kansa da cikin muguwar kasala ya bi dayan hanun nata da kalo Wanda ya sha kunshi yayi mugun kyau a ransa ya ce Au Ashe sai da tayi kunshin , a fili kuwa ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa inda mai hoto ya dauki abinsa tamkar itace amaryar yanda take wani annuri

Haka dai akayi ta hotunan nan har lokacin nasiha yayi , gaba daya mutanen suka bar dakin harda Fati kawar Yar Mahaukaciya ,

Hajiya Fatima ta nemi waje ta zauna ta kali Yar Mahaukaciya dake kalon kofa tana son fita kuma ta rasa ya zata yi

Hajiya Fadimatu ta ce" Yar Fadimatu zo nan ki zauna mu yiwa Yayanki gargadi KO?


Mubasshir ya zaro ido Yar Mahaukaciya ma ta zaro ido nima haka cos wanan gargadi harda abinda yaro ba zai ji ba , ita kuwa Mahaifiyar Mubasshir an fada mata Yar Mahaukaciya bazawara ce , shi yasa zatayi maganar ta a gabanta , shi kuwa gani yake sam bai dace ba karta raina shi dan kuwa KO da ta taba aure har ta haihu hakan ba yana nufin za'a yi masa galgadi a gabanta ba dan yarinya ce , ita kuwa mugun tsoron sa ne ya Sakata firgici jin za'a yi masa gargadi a gabanta



Hajiya Fadimatu ta ce"""""""""""''''"'''''"""""""""""""""'





Muah
🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




35



Hajiya Fadimatu ta kare musu kalo sunyi wani cirko cirko suna kalon ta ta ce " yar Fadimatu matso kusa da ni ki zauna KO kema kina jure tsayuwa ne?


Yar Mahaukaciya ta kifta ido tamkar ta juya ta fice take ji aman kuma bazata iya yin hakan ba , cikin nutsuwa ta karasa ta zauna a kasa daidai kafar Hajiya Fadimatu , inda shima ya karaso ya zaunan


Gyaran murya tayi sanan ta fara da adu'a , wato haka al'adar su take idan kayiwa yaron ka aure sai ka zaunar da shi ka tinatar da shi cewar da da yanzu ba daya bane , ka kara jadada masa irin nauyin dake kansa a yanzu Wanda idan yayi wasa da su tabas gobe kiyama yana cikin garari tsirar sa sai wani ikon Allah , hakan Hajiya Fadimatu ta dage wajen kawowa danta kwaya daya misalai da ayoyin da suka zo mana da mahinmancin iyali da yanda zaka kula da su , tana tsaka da yi masa wanan jawabin gaba daya ya nutsu maganganunta na ratsashi duk da ya san duk abinda take fada masa kamar ana kara yi masa bita ne aman kwarai yana ratsa shi kuma yana ji a jikinsa cewar dole ne ya kula da iyalinsa, jin mahaigiyarsa tayi shiru ne ya saka shi dago da kansa , aman mai zai gani *Hawaye* take sharewa daga idanuwanta


Cikin kidima ya mike tsaye ya dare saman kujerar da take zaune har hanunsa na rawa ya dan karkato fuskarta , kwarai hawaye Mamanda ke zubarwa , cikin wata irin murya ya ce " Kuka? Hawaye daga idanuwan Maman Mubasshir? Shin mai ya batawa Maman Mubsshir rai haka? Mai ya daga mata hankali haka?


Hajiya Fadimatu tayi lalausan murmushi a ranta ta ce' ina kaico da rashin sa'ar mata da kayi shi ya saka ni kuka aman a fili ta ce" Ina mamakin girman Mubasshir ne , yau da gobe sai Allah


Yar Mahaukaciya ma da ta mike tana kalonta sai taji hawayen maman Mubasshir na shigar mata zuciya tamkar Mahaukaciyarta , haka kawai taji zuciyarta ta tsinke wani irin kuka yana kokarin zuwar mata tayi iya yinta ta dane shi aman sai da hawaye ya zubo mata tayi saurin sharewa

Hajiya Fadimatu ta Mika mata hanu ta matso itama ta zauna suka Sakata a tsakiya a hankali taci gaba da jawabinta Wanda wani har kunya yake baiwa Yar Mahaukaciya , wasu abubuwan sai yau ta taba jin wai a aure akoy su kuma Dole a kiyaye , ita kam tata ta sameta koda yake Wanda ya nuna yana son nata ya fasa son nata kenan bata da wata damuwar tinanin idan fa bata yi biyaya ba itama zata hadu da fushin ubangijinta

Sosai ta kwashe lokaci tana ta kara jadadawa har abokan Mubasshir suka fara dana masa kira ba kakautawa domin can wajen diner an taru sosai har amarya ta zo tana jiran karasowar ango su shige tare , nan Mahaifiyarsa ta salame shi ya mike suma suka mike dan su yi masa rakiya ta kama hanun Yar Mahaukaciya da hanunta na dama shima ta kama hanunsa da na hagu suka Sakata a tsakiya suna dan taba hira suna dan murmushi idan har ba saninsu kayi ba to lale zaka rantse cewar su duka yayanta



Sai da suka rakoshi har daidai motar da tarin mutanen gidan da jama'ar sa suka cicika , daidai wata yar madaidaiciya fara mai shegen kyau Hajiya Fadimatu ta Bude masa gidan baya dan kuwa a yau ta hane shi tuki da kansa ,

Ya rungume ta suka yi irin gaisuwar larabawa ya juyo kan Yar Mahaukaciya suka kali juna tayi dan murmushi ta daga masa hanu alamar byby ya juya ya shige cikin motar tare da faduwar gabar da baisan KO ta meye ba




Wajen diner ,casu ake sosai kowa yana kwasar gara inda Mubasshir yayi shiru yana kalon mutane hankalinsa a rabe yake wajen gida da yawa daman shi ba ma'abocin son kida ba ga kuma abinda ke nukurkusar sa Wanda yake matukar jin haushin kansa da kuma kunyar kansa dan kuwa wanan tabas abin kunya ne a gareshi ( to kaji )


Sahla ta juyo tana kalonsa taga hankalinsa a wani wajen cikin kisa ta matso daidai kunansa ta ce" Mijina tunanin mai kake?


Mubasshir yayi murmushi ya kaleta ya ce" ba komai wifey


Ta ce " taso muyi rawa manan

Yayi dan murmushi ya ce" kinsan su Maman Mubasshir suna kalo daga can fa

Tayi far da ido ta dora kanta a kafadarsa ta wani lumshe ido , su kuwa masu daukan hoto da yan uwa sai yi suke


Mubinnat dake hakimce tana kalo a ranta ta ce , wai a kan wanan skelet din ce zaka kasa zama a can , lale zaku dandana kudarku , tayi murmushi


Zaune suke su uku da dan abin ciye ciye a gefen su suna kalon abinda ke faruwa sai suna ta yabawa haskowar da za'ayi aka hasko Sahla ta manawa Mubasshir kis a kuncinsa su Yar Mahaukaciya suka zaro ido a tare nan da nan wata kunya ta kama Yar Mahaukaciya ta rufe idanuwanta

Hajiya Fadimatu dake zaune itama ta lura da yanayin Yar Mahaukaciya a ranta ta ce " BIYU Kenan domin tana wani wasi wasi a ranta aman ba komai lokaci

[11/7, 07:51] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




36



Haka dai ta kawar da tinanin suka ci gaba da kalonsu har wani lokacin inda baci ya fara kama idanuwan su

Hajiya Fadimatu ta ce " Baci KO?


Yar Mahaukaciya tayi murmushi tana murza ido


Hajiya Fadimatu ta ce " ai sun gyara miki dakin naki ( wato dakin na wajen Mubasshir ita ta zaune shi dan kuwa yafi kusa da dakin Hajiya Fafimatun )


Yar Mahaukaciya a ranta ta ce " dakina? Waouh , a fili kuwa ta ce " an gode mamana


Hajiya Fadimatu na matukar jin dadin sunan da Yar Mahaukaciya ke kiranta da shi wato *Mamana*

Suka mike da niyar zuwa yin bacin suka yi mata sai da safe suka haura saman benen

Suna shiga suka tarar an canza zanin gadon , an saka tirare mai kanshi an gogoge ko'ina sanan kayansu an jere su tsaf


Fati ta kali Yar Mahaukaciya ta ce " ke princess ce ashe shi yasa kike luwai luwai da ke


Yar mahaukaciya tayi murmushi tana cire kayanta ta zaro na baci ta saka tayi konciyarta


Fati ma ta saka ta haura saman gadon ta lumshe ido can ta ce " yau za'a kwashi gara , duk da kashi ce Zala


Yar Mahaukaciya ta bude idanuwanta ta ce " gara ? Ta me fa?


Fati ta karkato ta ce " ta angoncewa mana yau su AA za'a fada wata duniyar


Yar Mahaukaciya ta zaro ido ta cije lebenta ta daga filo ta kwalawa Fati suka shiga kokowa uwa wasu kananun yara sai kyakyata dariya suke , can Yar Mahaukaciya ta nisa ta ce " Allah ya shirye ki


Fati ta ce " ya shirye mu baki daya



Washe gari tunda asuba Yar Mahaukaciya ta farka , ta saba gidan Hajiya Hawau idan suka Farka sai aikace aikacen su Hakan Yasa ta kasa hantsewa tana baci sanan zaman dakin ya ishe ta , cikin nutsuwa ta bude dakin ta fito daure da Zani na atampa da rigarta daidai ita da dan kwalin atampar ta sauko kasa ba kowa a falon duk da ba wata dauda gare shi ba ta zage ta shiga aiki kakabe can goge nan share can gaba daya har inda Yan Aikin basa tabawa dan wani abin sai mutun da kansa dan kuwa dan aiki bazai tsaya ya yi maka aikinka yanda ya kamata ba , kafin karfe takwas Yar Mahaukaciya ta gama gyare falon nan , sanan ta je bangaren masu aikin ta tambaye su ina tiraren gidan

Cikin rawar jiki hanne ta fito tana mamakin Hajiyar ce da kanta take shara , lale wanan ta daban ce , ta fito ta buda wani dan daki Yar Mahaukaciya ta shiga , haba zo laga kalo tamkar dan shago ne aka Buda na tiraruka kanshi ta ko'ina tashi yake kai kace kasuwar tiraruka ta shiga , wangalau tayi da baki tana kama sunayen Allah tana mamakin rayuwa , bolarsu ta fado mata a rai da Mahaifiyarta ta lumshe ido tana adu'ar Allah ya sa bata cikin wata bolar , ganin zata fara sana'ar tata yasa ta shiga bubudawa can

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login