Showing 57001 words to 60000 words out of 77913 words

Chapter 20 - 'Yar Mahaukaciya

10 Oct 2024

15846

hana shi,

Ya damki hannun mamansa ya kafe ta da ido saï ga hawaye wasu na korar wasu

hajiya Fadimatu ta kasa jurar ganin hawayen yaronta Bata san sanda ta jawo shi jikinta ba du da tsananin sanyin ruwan nan ta ce" Hasbunnalahu Wa ni'imal wakim, Ya Salam, shin yaushe dan Fadimatu zai daina daukan bacin rai da zapi haka ? Shin yaushe zai lazumci fadin Inalilahi Wa'ina ilaihir'raj'une à duk lokacin da yaji ransa ba Daidai ba ? Dan Fadimatu irin wannan zuciya ba'asan musulmi da ita, Tunda ka yarda da kalmar La'ila ha ilalahu MUHAMMADU'rasululah salalahu alaihi Wa Salam ka gama komai, Tunda ka yarda da shi kadai ya Isa yayi kuma shi kadai ya Isa ya hana mai yasa zaka kuma saka damuwar wani à ranka ? haba dan Fadimatu yanzu fa girma ya hau kanka, Dan mai bazaka gyara shi ba ?

Kalaman mahaifiyarsa na sauka à kunan sa tamkar warware masa kalmomin bakinsa ake cikin ikon ALLAH ya fashe da kuka mai tsanani ya kara rike mahaifiyarsa yana tunanin da mugun nufin su sahala ya kasance da an halaka masa mahaifiyarsa dan kuwa bazata juri hakan ba,

yana kuka tana hamdallar Jin muryar sa domin Bata sakawa ranta zata ji muryar sa a kusa kusan nan ba, hakan yasa ta barshi yayi mai isarsa sannan ya shiga ajiyar zuciya, du wannan abin bai lura da Idriss da Yar Mahaukaciya dake zaune dirshen à cikin bayi suna nasu hawayen ba

Cikin yanayin tausayi ta ce" fada min Wanda ya bata maka haka ?

AA ya lumshe Idannuwansa, da ace zai iya da ya boyewa mamarsa wannan lamarin, saï dai Ina bashida sama da ita, damuwarsa damuwarta ce, Dan haka ya bude bakinsa yana hawaye yana fada mata gaba daya abinda kunuwansa suka jiyo masa à gidan sa wato tataunawar Matarsa ta suna da Sirikarsa

Idriss dake saurare yafi kowa firgita inda ya rushe da kuka tamkar mace ya hada kansa da garun bayin ya shiga buga kansa da garun yana tir da halayen mahaifiyarsa da Kanwar sa

sai à lokacin AA ya lura da mutane à bayin bayan mahaifiyarsa, da sauri ya Mike ya nufi Idriss ya jawo shi da hanu guda ya ce " Idriss, baka da hankali ne ?

Idriss cikin kuka ya ce" banga anfanin rayuwata ba Mubasshir, Ba yau ba nake yiwa su mama à kan duniya aman abin har ya tsalake baiwar ALLAH (Hajiya hawau) ya fito kai ? Shin Mamana Bata kaunar saduwarta da rahamar ubangiji ne ? Ta raba d'a da mahaifiyarsa, ta kyamaci nakasasu, ta wulakanci talaka, yanzu tana kokarin halaka rayuwar jama'a da dama dan kudi?

why ?
Hajiya Fadimatu ta karaso gabansu ta ce" ya ku yayana ku saurara, ku kasance masu yiwa iyayen ku adu'ar alkhairi à duk halin da kuka tsince su, Idriss tsananin ka da mahaifiyarka adu'ar shiriya da ita da kanwar ka,

Ta juyo wajen AA ta ce" ka Sani da 1 ALLAH ya kawo ka har ka tsinci wannan tataunawar ya saka da Rahama, abinda nake SO da kai shine kayi ta adu'a ba dare ba rana à duk halin da ka tsinci kanka à ciki kan ALLAH yayi maka jagora, sannan idan ta baka karka sha, ta kali Idriss ta ce" Kayi hakuri Idriss kayi hakuri Haka Taka Kadarar take, yanzu Baban abinda ya dace muyi shine mu kwatanta musu cikin nutsuwa idan da halin kubutar su cikin ikon ALLAH zaku ga sun kubuta

Idriss ya sada kansa, shi yanzu wata irin kunyar su yake ji ya zaiyi da iyayen sa ne ? Ina zai saka ransa ?

Hajiya Fadimatu ta juya jikinta à matukar mace ta nufi waje tana mamakin wannan lamari

Yar mahaukaciya ma ta juya da sauri zata fita AA ya ce" Islam dakata

Cak ta tsaya tana kalon kasa inda Idriss ya juya à nitse ya silale daga bayin ya fito matatakalar benen ya zauna yana kalon kasa

Aunty Habiba Y'ar sokoto ta kali Hajiya Rafi'at ta ce " sister banga fitowar amarya ba fa, kar aikina ya koma baya, ta karashe tana murmushi

Hajiya Fadimatu da gaba daya jikinta yayi mata nauyi ta ce" au ai mantawa Nayi na barota à dakin, please sister tashi maza ki sauko min da ita domin yaron nan sai adu'a

Hajiya Rafi'at ta Mike tana murmushi ta nufi matatakalar benen tana hawa kunuwanta na jiyo mata sheshekar numfashi inda tayi tsai gabanta na faduwa tana son gane kukan waye ?


😳 Amarya à dakin ango😳, Idriss ma yana wajen, shin kukan waye ????????????? 😄😄😄😄😄😄😄🤒

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*Na*
*Sajida*

71

*Wannan page Ina rokon duk wani mai rauni karya karantawo 🤷🏻‍♀*

Cikin sasarfa ta karasa daga kusan mai kukan gaba daya jikinta ya mutu cikin wata irin murya ta ce" komai yayi zapi ka barwa sarki ALLAH, shi zai sanyaya maka Idriss, kadarar ka mai sauki ce Idriss domin da ranka da lafiyarka to sai ka barwa ALLAH komai shi zai warware maka damuwar ka

Tunda ta fara magana ya tsayar da kukan da ya Zo masa yana sauraron duk wata Kalma da zata furta Har ta dasa Aya, ji yayi inama Bata rufe bakinta ba domin wata iriyar nutsuwa da take sauko masa lokacin da Take maganar, dago kansa yayi ya zuba mata ido, tana maganar ashe Bama shi take kalo ba, tana kalon kasa, saurin kawar da kansa yayi daga kalon kurular da ya kafeta da shi yana furta a'uzubillah haka kawai ya kare matar mutane da kalo, cikin yanayin sauri ya Mike yana gagawar magana ya ce " na na na gode,
Da sauri ya raba ta gefenta ya fice tamkar tana biye da shi dan ta kama shi,

Hajiya Rafi'at ta lumshe idannuwanta maimakun ta nufi dakin AA sai ta shige dakin Hajiya Fadimatu ta Konta à gefen bed ta rufe idannuwanta tana tunanin irin rudanin wannan family da kuma shi Idriss Da Allah ya tsame daga halayen mahaifiyarsa

Kalon bayanta yake yana takowa à hankali har ya ISO Daidai inda take tsaye Tunda ya kama sunan ta, a nitse ya dan rage tsawon sa ya dora kansa à wuyanta yana sinsinawa

Yar Mahaukaciya tayi saurin juyowa tana kikifta ido cikin inda inda ta ce" Yaya Lafiya ? Mainene kuma hakan ?

Mubasshir ya rintse Idannuwansa ya kuma budewa gaba daya jikinta wani irin santsi da wani shegen kanshi yake, kara janyota yayi ba tare da ya Bata amsar tambayoyinta ba ya hadata da jikinsa,

Gaba daya jikinta Bari yake domin har à lokacin jikin AA banda gajeran Wandan nan ba komai, Yar Mahaukaciya ta dimauce ta rasa mai yasa yake sha'awar hada jikinta da nasa,

Katse mata tinaninta yayi sanadiyar jan dan kwalin kanta Wanda à dole aunty Habiba ta konce mata shi dan al'adarta ta dauke dole ta wanke mata shi tayi wankan sallar Azahar, hakan ne ma ya saka aunty habiba sakawa a kirawo Yar Mahaukaciyar dan tana gudun kilu ta jawo bam,

Yana jan dan kwalin ya fadi kasa gashin ya zubo da dan danyatar sa ta mayukan wankin kan da aka yi anfani da su wajen wanke kan, Hancinsa ya kai à hankali ya sisina ya lumshe Idannuwansa cikin nutsuwa ya shiga cusa hannunsa à cikin gashin yana kara lumshe ido

yar mahaukaciya ta zaro ido da sauri ta dago idannuwanta tayi arba da fafadan kirjin sa Wanda à Yau ne ta fara ganinsa à fili haka, gabanta ya fadi ganin irin baiwar ni'imar da Allah yayi masa gashine konce yayi sidik da shi s kyalin ruwa yake, dago da kanta tayi dan Jin bugawar zuciyarsa ya tsananta kan na da,

Tana dago da kanta tamkar Jira yake ya hade bakinsa da nata ya shiga kissing,

Yar Mahaukaciya ta zaro idonta ta shiga kokarin kwacewa, aman Ina karfin ba daya ba, ganin zata Bata masa lokaci ya saka shi yayi sama da ita ya fito daga bayin yayi saman bed da ita

wutar dakin ya mika Hannu ya kashe sannan ya ci gaba da kissing din Fadimatul islam wace daidai wannan lokacin tana kokarin fita daga hayacinta dan ita kanta à Yau tana Jin dadin tabatan da yake sakamakon tsumin Aunty Habiba Mai Abin Mamaki Y'ar sokoto,

Zuwa wani lokaci AA yayi fatali da Rigar Yar Mahaukaciya wace ita kadai ce à jikinta sai zani da ta Daura,

Arba yayi da yan biyu sunai masa hello, bai san sanda ya kai bakinsa domin kawo musu agaji ba,

Su duka nunfashin wahala suke saukewa Daidai nan AA ya ce fa yana bukatar isar da sakonsa banban birnin,

Saï à wannan lokacin Y'ar Mahaukaciya ta bude idannuwanta ta zuba masa ido inda ta lura da gaske fa yake,
Tura shi ta shiga yi tana Kiran sunansa aman Ina aikinsa yake ba sasautawa, kukan wahala ta saki tana tura shi tun karfinta aman Ina baya Jin duniyarta bale ya saurara mata,
Kuka take tana yakushinsa domin ji take tamkar zata bar duniyar, tun tana yi da karfinta har ya kasance KO hannunta ta kasa dagawa tana ta zubar da hawaye saï da bukatarsa ta biya dan kansa sannan ya kyaleta ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya( 😳 Leila ba ruwana)

Ganin shirun yayi yawa gashi wayarsa saï ringin take Sahla na kiransa mai yiwuwa dan taga dare yayi ne bai dawo ba take kiransa ya saka Hajiya Fadimatu ta Mike ta haura sama dan ganin tataunawar mai suke haka da yar aiken, da Fadimatul islam din, da kuma Oga AA din da suka shantake suka kasa fitowa har magariba ta kawo kai ( Jama'a ku mu taro Maman Mubasshir karta sume mana🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻😄😄😄😄😄😄?

🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*





73


*Manzan Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce wanda ya karanta subhanallahi wabi hamdihi subhanallahil azim,,, sau dari a rana za'a yafe masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi*




Yana karasowa ya tsareta da ido ya ce" Sahla mai kike à nan gidan da tsohon daren nan ?



Sahla ta yatsina fuska ta ce" wajen Mom na Zo,
Ta raba ta gefensa tayi shigewarta

Idriss ya sauke ajiyar zuciya ya ce akoy ALLAH,


Tana shiga ta ce" Mom Ina ta Kiran wayarsa tana ringin baya dagawa


Daidai zata yi magana Mubasshir ya Kira ta, cikin rawar jiki ta daga ta kara à kunenta

Mubasshir bisa umarnin elhaj Muhammad da ya tsare shi da ido ya ce" Wifey, kiyi hakuri Ina wajen aiki wata gagarumar kongila ce ta sameni daga wajen sarki, so ki kular min da kanki, sannan ki tanadar min Abu mai dadi ki tsumayi tukuicin ki


Sahla da tayi Shiru tana sauraron zazakar muryar mijinta ta rausayar da kai ta ce" i miss u my man sai ka sauko


Mubasshir yayi murmushin yake ya ce" miss u too wife, bye-bye, kit ya kashe Kiran ya dora kansa saman kujerar da yake zaune


Elhaj Muhammad ya yunkura ya ce" Saki, Saki ? No saki ba shine solution ba, ka tsunduma matar ka à tsananin kaunarka, idan har da rabon ta tsira da ita da mahaifiyarta to zasu daina mumunan nufin su, idan kuwa basu da rabo ne, To ka Sani ALLAH baya baci, shi ya san yanda zaiyi da su,


Mubasshir ya Gyada kansa irin ya gamsu da bayanan mahaifin matar sa,


Elhaj Muhammad ya ce" ka huta son bara na leko madame


Mubasshir ya yi murrmushi, yanayin soyayar Sirikan nasa yana matukar birge shi, yana son yin koyi da su, à hankali ya lumshe Idannuwansa yana tuna moment dinsa da Islam, islam cikakiyar budurwa ce, yarinyar da tayi rayuwa à bola, gardawan maza suka sauketa, lale ya yarda Allahn nan shi ne mai karewa, domin ita Yar gatan ta shigo à bude ita kuwa Yar bolar ta shigo à rufe, à hankali ya furta da banbanci tsananin ku à zuciyata, Zanyi iya yini dan ki ringa jina à jinin jikin ki my Islam


Maman Mubasshir ce zaune tana Jiran Aunty Habiba ta gama hada ruwan dumin da zata kuma gasa Yar mahaukaciya, gefe guda su Hajiya Rafi'at ne zaune suna labarin tafiyar su,


Maman Mubasshir ta juya ta kale su ta ce" na kula ba mai kama min y'a ta KO ?


Hajiya Rafi'at da ta san ita ce da Laifi tayi saurin tasowa ta ce" Eyah maman islam ai na Zo na kama miki kika kiya kuna fushi kan dan Aljannah,


Hajiya Fadimatu ta kawar da kai ta ce " lale fa dan Alhannah, Ai yau KO Aljani yake idan ya shigo sai na hadu da shi


aunty habiba ta fito ta ce" Aunty na hada aman kiyi hakuri mu yi mata aikin ni da Rafi'at


Hajiya Fadimatu ta dago ta kan Yar mahaukaciya wace du tana Jin su, su basu san abinda ya sameta bane zasu ci gaba da sakata à ruwan tiraren nan ? (Wa ya fada miki ?)


Da sauri ta Mike tana kakawar da kanta ta ce" Mama zan iya fa,
Ta juya tana kokarin yin sauri idannuwanta sai rufe su take tana cije lebenta, har ta shige bayin suka Mara mata baya


hajiya Fadimatu ta zauna Kusa da Hajiya hafsat ta ce " sister ya zakina nunawa y'ata halin KO in kula ne haka ? Kin ga fa irin wahalar da ta sha na rashin ki aman sai Ina ga bakya Bata kulawar da ya dace da ita


hajiya hafsat ta zaro ido ta ce" Lah aunty, wace kulawa kuma zan baiwa islam wace ta fice Wada kike Bata ? Kin tarbeta à lokacin da kowa yake hantarar ta, kin zauna da ita ba tare da kyama ba, kin sakata à hanyar samun ilimi, kin koyar da ita girki, kin koyar da ita tsaya, kin aurar da ita ga miji mafi daukaka à rayuwarta mai kuma zanyi mata ? Aunty ki Sani wly wly islam kece mahaifiyarta domin ni haihuwarta kawai Nayi, har kunyarta nake ji a zuciyata, Ina Jin dacin irin rayuwar da na gana mata,
Ta karashe zancen tana kokarin mayar da hawayenta



hajiya Fadimatu ta ce " karki ringa tuna baya, abinda kika aikata ba à cikin hankalinki ba kike yiwa nadama ? Haba sister ai bai dace irin haka ba, na Sani sarai islam Ina bata kulawa aman ki Sani ya zama wajibi kema ki ringa sakata à jikinki domin ba komai zata iya fada min ba, KO daman can islam akoy zurfin ciki bale yanzu da yaron nan ya yi mana haka, kina gani fa irin saurin da ta kwasa du dan kar à gane baiwar ALLAH, Dan haka muna barar hakan


hajiya hafsat ta kawar da kanta tana murmushi à fili ta ce" korafinku ya karbu






à gaskiya na san Ina jinkiri wajen posting, aman Ina neman afuwarku kun san yau da gobe sai ALLAH, abubuwan ne sai à slow, thanx à lot

🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*





74



*Uwa Tana Iya Kula Da 'ya'ya Sama Da Goma Amma A Wasu Lokutan Sai Ka Tara 'ya'ya Goma Sun Kasa Kulawa Da Uwarsu Guda Daya!!! Yakamata Musan Cewa Abubuwa Masu Mahimmanci Da Daraja Basu Cika Maimaituwa A Rayuwar Mutum Ba... Shi Yasa Kowanne Mutun Uwa Daya Kacal Gareshi!!!
Kuma Watarana Zamu Wayi Gari Babu Ita A Duniyar Nan... Dan ALLAH Mu Kara Kulawa Da Mahaifanmu Musamman Ma Uwa Wacce Babu Kamarta A Duniyan Nan!!!
Ya ALLAH Ka Bamu Ikon Yiwa Mahaifan Mu Biyayya Ka Jikan Iyayenmu, Ka Basu Aljannatul Firdausi, Allah Ya Sakawa Iyayenmu Da Mafificin Alkhairinsa Duniya Da Lahira*




bayan ta ajiye wayar ta shaidawa mahaifiyarta aiki ne ya rike shi ashe


Hajiya Marhaba ta ce" jibi ne tsinaniyar yarinyar zata tare KO ?


Sahla ta ce"Eh mama


Hajiya Marhaba ta ce" toh duk yanda zanyi zanyi na kawo miki hadin maganin kinji ?

Sahla ta amsa mata ta Mike tana fadin bara ta juya kar aje yayi safiyar dawowa gidan Bata nan


Hakan kuwa hajiya Marhaba ta barta cikin tsohon daren nan ta juya ta koma gidanta tare da dumbin muguwar hudubar mahaifiyarta



Tunda ya juya ya fita bai sake saka Islam à Idannuwansa ba, domin Hajiya Fadimatu ta kasa ta tsare ta hana shi hawa saman balatana ya ganta, duk irin yanda yake fakewa da Bara ya dauko wani abin sai ta tare shi ta ce lala ba zai hau ba, hakan na matukar mahalar da shi,

Da kansa ya je gidan su Fati kawar islam ya shaida mata Auren islam aman ya boye mata mijin domin ya fi son ya zame mata surprise, auren kansa tayi mamakin sa domin Bata taba kawowa à ranta rashin zuwan islam school na kwana biyun nan haka ne ba, kuma ai suna waya Bata taba Shaida mata ba, Jin ya ce à washe gari zata tare ya sanya ta shirya da yama ta nufi gidan su AA Mubasshir,



Konce take tana baci, wannan bacin ya zame mata tamkar na rashin Lafiya, ta fiya baci à yan kwanakin nan,

Hajiya Hafsat ta shigo dakin ta Nemi gefen gadon ta zauna ta rasa ta Ina zata fara, à hankali ta saka Hannu tana dadaba bayanta

Firgigit Yar mahaukaciya ta farka tana adu'ar tashi daga baci, idannuwanta ta sauke à fuskar mahaifiyarta, da sauri ta zauna tana kalonta


Hajiya hafsat ta kawar da kanta à ranta tace " wannan ido na mahaifinki ai sai mutun ya tsorata,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login