Showing 6001 words to 9000 words out of 77913 words

Chapter 3 - 'Yar Mahaukaciya

10 Oct 2024

15849

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









7
Na sadaukar da wanan gareki yar uwa masoyiya Maman manal matar oga lolz Allah ya barmin ke

Baba ta zaro ido tace" yar nan bana son neman magana wani irin yar mahaukaciya kuma? Ina babarki take ne?

Yar mahaukaciya tayi tsai ta tuna lokacin idan tana daka a gidan su Larai yayansu suna cewa babata babata nan ta gane Babar mutun tamkar uwa Wace ta haifi mutun hakan yasa ta watsa hanayanta irin bata sani ba


Baba ta ce " mu je kiyi wanka ki ci abinci sai ki bani labari ,

Baba ta shige gaba yar Mahaukaciya na biye a bayanta ta buda bayin ta tara mata ruwa sai da ta nununa mata komai domin a yanda tayi mata tsaye da alama bata iya ba , ta juya ta dauki yaron harda pampos dinsa tun na jiya da suka saka masa ba'a cire ba , hasalima ita bata san menene ba tana tsaka da yiwa yaron wanka yana tsala kukansa Yar Mahaukaciya ta fito ta dauki rigar da Baba ta Nuna mata ta saka tayi tsaye tana kalon yanda Baba ke juya Dan Mahaukaciya tana yi masa wanka , a hankali ta zauna tana kalon fatar hanunta ta zama wata kala wai daman haka take? Tana tsaka da tunanin irin rayuwar nan mai dadi ta ji baba tsohuwa na cewa to bude ki bashi ya sha


Yar Mahaukaciya a ranta ta ce " wai meye ake cewa ta bude ta bashi ya sha ne? Ita fa bata san mai ake nufi da hakan,


Baba ta ce " ke yarinya ki dena yawon tunani kar ciwon nan mai suna totion ya kama ki , ai ina fada miki haka mukayi da sale ya shirishiri ya dankara min saki uku bayan ya dala min mari a gaban sabuwar amaryar sa kuma ya tunkudo ni waje aka yi mana taro jama'a na tambayar mai ya hadamu wai kinsan mai yace?

Yar Mahaukaciya ta girgiza kai tana sauraron baba

Baba ta ci gaba da cewa wai wani cewa yayi fa na saci kudinsa murtala fa

Yar Mahaukaciya ta ce " kai har Murtala ? To wa ya dauka ?

Baba ta karkace ta gyara zama tace" yar nan nera sha biyar ne na dauka aradu ni ba duka na dauka ba kuma wata hudu yayi bai bani kudin cefane ba shine fa na dauka kuma ai ba sata bace KO?

Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana mamakin wai dauka ne tayi ba sata bane tayi murmushi

Baba ta ce " ke yarnan ai dukan da yayi min da kuma sakin ya saka na kumbure uwa hulawa ni kadai nake kara girma babar uban gidana ta kaini ganin likita a can ne yace min wai totion ( tension ) ce ta kamani kuma har kisa take kinga ki dena tunani dan miji ya sakeki kiyi hakuri Allah zai baki wani cikin ruwan sanyi balatana ke din nan mai kyan aljanu

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce " toh , domin ta lura Babar nan ba dai surutu ba

Baba ta kama rigar Yar Mahaukaciya ta zuge zup din , ita dai kalonta take tana son ganin abinda zata aikata tana zugewa Yar Mahaukaciya ta saka hanayenta biyu ta rufe mamarta

Baba ta ce " ke kuji mini yarinya da iyayi kunyar shayar da yaron ne kike a gaban idona na FITA?


Yar mahaukaciya ta ce " kunu yake sha

Baba tayi tsai ta ce " dadina da yan gayu Kenan wai baza'a shayar da yaro ba kar nono ya fadi ,hum to Allah shi kyauta ta dauki yaron tayi kicin da shi sai wake take rera masa ta dora kunu ta kada domin shima mai gidan ma'abotin shan kunu ne hakan yasa ta hada ta baiwa yaron ya sha ya koshi sai baci ( bawon Allah )



Wasa wasa yau har sun cika kwana uku a gidan Idriss bata aikin fari bale na baki aman duk da hakan tana fitowa tana kalon yanda baba ke kula da harkokin gidan da irin kulawar da take basu ita da Dan Mahaukaciya , har mamaki take wani abin ,


Zaune take tana kalon TV baba ta zo ta zauna kusa da ita ta ce " yarinya baki fada min inda babarki take da kuma abanki ba fa abun da mamaki har yanzu basu neme ki ba lafiya kuwa?


Yar Mahaukaciya ta juyo tana kalon baba a hankali ta furta nima nemanta nake , Mahaukaciya ta bata ban san inda ta nufa ba , na rasa inda ta tafi ta barmu da Dan Mahaukaciya


Baba ta gyara zama ta ce " ban gane ba

Yar mahaukaciya ta gyara zamanta ta baiwa baba labarin rayuwarta har Wanda bata san sunanta ba bata san kowa ba hasalima bata san sunan garin nan ba wai jos ita kuwa a tinaninta a kano take domin tana ji a bakin mutane


Mai baba zatayi in ba kuka ba harda face majina tana karkata kai ta ce " kai duniya kai duniya ina zaki da mu ? Oh ni habiba ya ga murja jikar saude wayo duniya kana tunanin a kunci kake sai ka tsinci Wanda ya fika oh Allahna , ta juyo ta kali Yar Mahaukaciya ta ce " yarinya Ashe shi yasa da na tambayeki sunan ki kika ce min Yar Mahaukaciya?


Yar Mahaukaciya ta gyada kanta

Baba ta ce " to ni zan ringa kiranki da Rahamu sunan yayi miki?

Yar Mahaukaciya tayi dariya ta ce " eh yayi min baba

Suna tsaka da zance sai ji suka yi an banko kofar dakin an shigo , Baba ta mike tana dafe kirji ta ce " salalahu alaihi wasalam Tawa ta sameni ,


Kafin Yar Mahaukaciya ta fahimci inda baba ta dosa sai jin saukan duka tayi ta ko'ina dukanta ake ba kakautawa , mai dukan ta warto Dan Mahaukaciya ta jefa shi kasa ya rufe da kukan jarirai da gudu Yar Mahaukaciya ta nufi wajen da yake yashe ta rungume shi suna rusa kuka a tatare ,

Mai dukan ta nuna su da yatsa ta ce " """"' """""""" """""


Love u
🇳🇪 Belles écrivaines du Niger


*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









8
Mai dukan ta nuna su da yatsa tana kunfar baki tace" ke karamar yar bariki shegiya mai shige da zabaya ( albinos ) a gidan ubanwa ma ya hadu da ke har ya dirka miki cikin nan kika haifo yaro mai kama da ke? Kaga yayan shegu sai dai suyi kama da uwar su to bara kiji na fada miki Idriss nawa ne ni kadai babu ubanda ya isa ya hada shi da wata matar sai dai bayan raina dan haka ki dauki shegen danki da ke ku bace min a gidan mijin da zan aura tun kafin na kontar da ku nayi muku yankan rago


Yar Mahaukaciya dake goge jinin dake zuba a kan Dan Mahaukaciya ta dago idanuwanta ta sauke su a fuskar wanan matar wada da gani ta girmi idriss nesa ba kusa ba kuma tana ambatan mijin da zata aura cikin rashin kuzari ta dauki dan Mahaukaciya ta juya tana share hawayenta daidai zata bude kofa Idriss ya turo ya shigo ta dan ja da baya da sauri ya matso yana tambayar lafiya?


Hajiya Mariya ta taso tana fadin : my man ai na koreta ne kana ganin irin yanda ake zaginka a cikin family dina ana fadin ka ajiye karuwa yar bariki harda danku a cikin gidan ka ?

Idriss yayi gagawar daga mata hanu cikin daga murya yace ubanwa ya baki izinin korar a gidana? KO gidanki ne? An fada miki itama irinki ce? An fada miki itama ta samu yayane a waje irinki?


Hajiya Mariya tace" kai dakata Malan yayan ba da kai na samesu ba? KO an fada maka KO wani jaki nake mu'amala da shi ne? To wly KO ka kori yarinyar nan KO na kirayi mahaifiyarka na fada mata sanan na yada ka har a wajen uban gidan naka na samu na ganshi na fada masa irin abinda kake aikatawa ya koreka banza kawai , ta ficeshi ta ja rigar yar Mahaukaciya tayi waje da ita ta baiwa mudi mai tebur kudin mashin tace ya kaita inda yaga dama ,

Baba tsohuwa ta zauna tana ta hawaye ta fadawa idriss gaba daya abinda Yarinyar nan ta fada mata , harda sunan da tayi mata wato Rahamu ,

Idriss ya nisa ya ce" ban taba tinanin cewar watarana zan hadu da mace lokaci guda naji ta shige min a rai irin wanan yarinyar ya lumshe idanuwansa ya ce na kamu da sonta baba kuma insha Allah KO ina take zan nemota na aureta koda kuwa zan rabu da aikina ne , aman gaskiya ni bazan raka mata sunan Rahamu ba , bakya ganin yanayinta yanayin yayan larabawa ne ina wa laifin sunan Manal?

Baba tsohuwa ta washe hakora tace ai kuwa kaga sunan yayi min dadi sosai wato Manil

Yace aa Manal take baba ya Mike yayi dakinsa yana neman layin yaronsa ya kwatanta masa kamaninta da nufin maza ya zo anguwar su zai ganta da beby a hanunta ya dauketa kafin ya fito ( baka sans cewar a mashin aka dauketa ba ?)


Tafe suke yana papara gudu tun karfinsa ya ce " ke wace unguwa zan kaiki?


Yar Mahaukaciya tayi shiru can tace " Dan Allah ka kaini wajen magani kaga dan Mahaukaciya duk yayi wani iri


Mudi ya juyo kadan yaga yaron duk ya wani banbankare a ransa ya ce " kan uba kar aje ya mace min a rufe ni hakan yasa ya ja ya tsaya daidai wata katuwar asibitin kudi ta Yaron nan mai tashe wato Ibrahim Y Nazir ya ce " ke sauka ki shiga nan zasu warkar da ke kinji?


Yar Mahaukaciya ta sauka da sauri mayafinta har yana dan zamewa ta shige asibitin , tana zuwa ta nufi wajen da taga kamar nan ne wajen maganin , ta shiga layi , tun abin karfe goma sha daya har karfe 12 da yan mintuna sanan layinta ya ISO tana zuwa sai taga wata taga taji ance katin yan me kike so?

Ta dago dan Mahaukaciya ta nuna ta ce " dan Allah kiyi masa magani kina ganin jikinsa?

Matar ta dan bude windows din ta leko ta ce " ke dauke min jini mana karki bata min wajen aiki ki bayar da kudi a yanka miki katin ganin likitan yara


Yar mahaukaciya ta ce " nawa ne kudin?

Matar ta ce " dubu hudu

Yar Mahaukaciya ta ce " dan Allah ki yanka min a bashi zan kawo miki

Matar nan na jin haka ta dana Kiran securitie yana zuwa ta ce masa yayi waje da wanan tana neman tsayar musu da aiki


Sécuriti din ya ce " madame mu je

Haka tana ji tana gani yayi kokarin tura keyarta tana ta magiyar su saurareta , har ya kusan turota waje wata mata da wani a gefenta da alama sun zo dubiya ne ta tsayar da direban dake Jan su ta fito tana tambayar lafiya?

Securitie din ya fada mata abinda yake faruwa ,

Ta girgiza kai ta bude motar ta zaro kudi ta mikawa Yar Mahaukaciya tana fadin take kiyi maza ki kewaya urgence domin wanan ai urgence ne daga baya kwayi katin Allah ya bashi lafiya


Yar Mahaukaciya tayi Saurin tsugunawa da dan Mahaukaciya a hanunta tana hawaye ta shiga godewa wanan mata har ta shige mota direba ya jasu sai cikin asibitin ita kuwa da gudu ta mike tayi inda aka nuna mata , tana isa aka tarota aka dorashi saman wani gado na yara suka tura shi

Suna shiga akace wanan ai tamkar accident dan haka a kirawo Wanda ya kawoshi idan ba haka ba baza'a taba shi ba ( kuji fa )

Wata nurse da gudu ta fito ta yafito Yar Mahaukaciya ta biyo bayanta cikin Sauri

Suna zuwa
Docter mai sunan Abdallah ya ce " mai ya samu yaron ?

Yar Mahaukaciya ta ce " ban sani ba

Ya dan dago idanuwansa ya sauke a samanta domin muryarta mai dadin gaske , a ransa ya ce yarinya ce hakan yasa yace" ina Mahaifiyar sa?

Yar Mahaukaciya ta nuna kanta ta ce " nice Mahaifiyar sa faduwa yayi dan Allah Malan kayi masa magani kar ya mutu

Docter Abdallah ya ce " Malan ? Sai kuma ya basar ya mike domin gaba daya ji yayi ya kasa musa mata , ya nufi dakin da aka shinfidar da yaron ya ce a shiga dakin tiyata da shi ,

Nan da nan aka shirya shi akayi dakin tiyata da shi cikin gagawa domin yaron har wani shidewa yake , suna shiga docter Abdallah da sauran ma'aikatan suka dukufa don ceto rayuwar Dan Mahaukaciya Bawan Allah

Gani nayi Docter Abdallah da Sauri ya cewa nurse ta bashi irin abin nan da idan mutun yayi doguwar suma ake dana masa a kirjinsa , da gudu ta dauko ta daidaita ya kara yage rigar Dan Mahaukaciya ya murza abin ya dora masa saman kirjin sa , aman shiru kake gani ya kara murzawa ya dora masa cikin karaji ya ce " no ,no boy ka tashi mana kar ka yi min haka please ba'a taba mutuwa a hanuna ba ya kara murzawa ya dora masa yana kokarin kara murzawar da Sauri wata nurse ta rike hanunsa suka kama suka duba lokacin mutuwarsa 12h da minti 47

Docter Abdallah ya yi shiru gaba daya jikinsa ya mutu maganar matar nan wato yar mahaukaciya ta fado masa a rai inda take cewa dan Allah ka yi masa magani kar ya mutu , a hankali ya furta i'm sorry ,

Ya fito yana layi yana fitowa Yar Mahaukaciya tayi kuri tana kalon kofar dakin tiyatar sai da gabansa ya fadi ta iso da Sauri tana fadin " Likita ya jikin Dan Mahaukaciya ?

Da kyar ya tataro nutsuwar sa ya ce " Madame i'm sorry Allah ya amshi abinsa


Yar Mahaukaciya ta ce " ban gane ba mai kake nufi?

Docter ya hadiyi wani yawu ya ce " ya rasu ,

Yar Magaukaciya gaba daya taji tana kokowa da nunfashinta da kyar ta iya furta ya mutu? Sai luuuuuuuu ta tafiiiiiiiii

😭😭😭😭😭😭😭😭😭
🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









9


Luuuuuuuu ta tafi kafin ta fadi Docter Abdallah ya tarota ya dagata cimak yayi wani daki da ita ya shiga bata taimakon gagawa cikin kankanin lokaci ta dawo hayacinta tana farkawa ta shiga rusa kuka har muryarta na dishewa , shi kuwa yana zaune yana kalonta yana share zufa domin ji yayi kwatakwata baya iya wata magana ,

Tana tsakar kukanta ta daga kanta sama tana kalon pankar dake juyawa a dakin asibitin tana tunanin ya zatayi da rayuwarta ? Tana kalon Dan Mahaukaciya tamkar Tana tare da mahaukaciyarta , Yanzu ta sanadiyarta aka kashe mata dan Mahaukaciyarta? Ta nisa bata san cewar a fili taci gaba da fadin " shin ya zanyi? Wa gareni? Ina zan kai Dan Mahaukaciyana ayi masa sitira? Wayo Allah gani gareka


Docter Abdallah ya dago kansa yana kalonta ga dukan alamu zancen zuci ne ya fito fili ya lura tana boye wani abu a ranta da alama ta fiya zurfin ciki, to aman mai take nufi da ina zata kai Dan Mahaukaciya? Mai yiwuwa yaron nata ne mai suna hakanan domin da ya tambayeta sunan yaron hakan ta fada, to aman ina babansa?

Cikin karfin hali ya ce " ina babansa yake ne?

Ta juyo idanuwanta wa'inda suka koma kalar ja tana kikifta ido ta ce " babansa ya mutu , bamu da kowa a garin nan kuma ban san hanyar bola ba

Ya budi baki zaiyi magana sai yaji karar bude kofa yana juyawa yaga kakarsa ta shigo cikin shigarta ta alfarma ta sha glas na karin gani tana shigowa ta juya ta cewa direban da ya kawota " yaro Kagan shi a nan ai ka juya kawai idan na gama yi masa fadan ya maidani gida KO ya dorani mashin 😌


Shi dai dan ladi direba ya juya yana dariya domin lamarin hajiya Hawaou sai ita , ta shigo cikin nutsuwa ta tsaya ta ce" kai Abdallah ka kiyayeni yanzu dan nayi maka maganar aure shine zaka fice yau baka gaisheni ba? Ai Allah ya taimakeni nasan wajen aikin naka , to ka sani aure ba fashi au ka kawo KO na zabo maka yaro 😏

Docter Abdallah ya taso da sauri a ransa yana fadin wani dan duniyan ya gaya mata yau ga asibitin da yake ? A ransa ya ja dan karamin tsaki haka kawai iyayensa basu takura shi kan yayi aure ba ita tana faman shiga rayuwarsa , ya kamo hanunta ya zaunar saman kujerar da ya tashi sai a sanan taga Yar Mahaukaciya na kuka ta zaro ido ta ce " Ikon Allah yarinya mai akayi miki? KO alurar ce bakya so? Ko dai yaci zalin dinki yayi miki biyu irin yanda yayi min?


Docter Abdallah ya ce " iya dan Allah ki saurara kadan kinga nan fa asibiti ne yama akayi suka barki kika shigo?


Hajiya Hawaou ta ce " gidanku akayi suka barni na shigo, kuma na fada maka ka dena kirana da iya sai kace uwar kaji

Ya girgiza kai ya ce " kinga wanan yarinyar marainiya ce batada kowa kuma yanzu ta kawo yaronta nan ya rasu shine take kuka domin bata san kowa a garin nan ba ,

Ai hajiya Hawaou na jin haka ta shiga salalami tana kuka ta Mike ta rungume Yar Mahaukaciya tana fadin" kiyi hakuri yarinya dukan mai rai mamacine , ai nima dan makociyata tana haihuwar shi ya rasu kai nayi kukan mutuwar yaron nan domin suna mugun neman haihuwa Allah ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login