Showing 69001 words to 72000 words out of 77913 words
murnar hakan
Elhaj Muhammad ya ce" Alhamdulilah, barni da ita, ni nasan yanda zan bilowa al'amarin da yardar ALLAH,
Bayan wani dan lokacin Elhaj Idriss ya kali Mubasshir ya ce" yarona tashi ku tafi gidanku kaji,
Mubasshir ya dan sada kansa ya ce" ai aba Bazan iya barinsa haka shi kadai ba
Idriss yayi murmushi ya ce" broth tashi ka tafi da sister baiwar ALLAH ta gaji da yawa, ai nima yanzu zan tashi mu koma gidan
Mubasshir ya ce" tohm sai munyi waya, suka Mike suka yi musu salama
Tafiyar minti talatin da dan dori ne suka yi kafin su Isa gidan su, kowanen su da abinda yake sakawa à ransa, ita dai Yar mahaukaciya tana fatan auren nan ya tabata domin Idriss mutunan kirki ne, shi kuwa yana tunanin gaskiya an shiga hakinsa da yawa,
Tsayar da motar yayi ta bude ta fice, ya bita da kalo à ransa yana tunanin Bata san tafiyar kawarta fati ba,
Yar mahaukaciya ta tura falonta ta shiga da ada'a à bakinta, karo tayi da farar takarda ta buda ta karanta sakon fati ne na ta tafi gida sai an kwana biyu zata dawo da yardar ALLAH
Yar mahaukaciya tayi murmushi ta ce" My fati,
Dakin ya sha gyara sai kanshi yake ta shige dakinta tana ta murnar yanda fati ta gyara mata dakin kafin ta tafi
Wanka ta fada, kafin tayi sai da ta shiga ruwan dumi ta fito ta sala Wanka ta dauro alwallah ta fito daure da tawul, ta zumbula doguwar Riga ta kabarta sallar magariba, bayan ta gama ta cire ta bude cikin kayanta ta saka wasu Riga da wando masu shegen kyau ta daure gashin kanta Bata tsaya yin Wata kwaliya ba ta nufi dan karamin frij dinta ta bude ta dauko jikon kabewa da madara no sugar da mamanta ta dadafa ta cicika biduduna aka jera mata à frij, guda ta dauko ta girgiza ta shanye tana tande baki, haka ta bude zumuwar da aka yi mata Hadin amarya aka ce ta ringa sha kadan kadan, ta kuwa zauna ta aniya sha sai da taji ta koshi ta rufe sauran ta Mike ta ajiye, sannan ta fito ta nufi Baban falonta ta kuna TV,
Kalonta take hankali konce ba abinda yake damunta, ta jawo wayarta ta danawa fati Kira, suka shiga labari sai kyakyata dariya suke
Cikin farar jalabiyarsa ya turo kofar ya shigo da salama aman Bata ji ba dalilin hankalinta ya dauku wajen wayar da take,
Ajiye ledar hanunsa yayi ya zuba mata ido yanda take labari tana dariya, ita Sam ba abinda ya dameta, ya lumshe Idannuwansa yana tunanin first night dinsa da ita du da yana cikin halin bacin rai aman abin nan yaki fita à ransa, ya sada kansa à ransa ya ce" anya kuwa zan iya hakura har sai ta yarda dan kanta,
Ya girgiza kai à hankali ya furta " Islam
Dago kanta tayi da sauri sai à lokacin wata kunya ta dirar mata, to yaushe ya shigo dakin ma ? Da sauri ta kali kayan jikinta ai kuwa ta diro da gudu zata nufi dakinta
Mubasshir ya saka hannunsa ya kamota ya janyota jikinsa ya rungumeta
Yar mahaukaciya ta shiga sisine kanta, aman kanshin turarensa na mugun birgeta, haka kawai ta shiga cusa kanta à jikinsa tana shakar kanshin turaran
Hakan ba karamin rikita shi ba yayi, domin sai yake Jin hakan tamkar tafiyar tsutsa take yi masa à kirji, à hankali ya dago da kanta ya zuba mata ido,
Yar mahaukaciya ta bude idannuwanta Jin an rabata da kanshin nan mai dadi ta kale sa, gabanta ne ya fadi wata irin soyayar mijinta ta kara tsarga mata jikinta, da sauri ta sada kanta kasa
Mubasshir ya saki murmushi ya kuma rungumeta, à hankali ya ce" kaunar Mubasshir ne nake hange à kwayar idanuwan islam ???
Yar mahaukaciya tayi shiru Bata bashi amsa ba, to mai zata ce masa ? Ita Kam lamarinsa ya girmimi tunaninta, gashi tun karfi ya koya mata kaunar kasancewa à kirjinsa
Mubasshir ya dauki ledar hannunsa ya ja hannunta suka nufi dakinta, ya ce " dauro alwallah muyi nafila
Jin yace nafila ta nufi bayi ta kuma yin Wata alwallar ta dawo, ta zumbula hijabinta na sallah, Mubasshir ya ja su suka yi raka'a biyu
Bayan sun gama ya dafa kanta da harshen larabci ya rufe Idannuwansa yana ta kwararo mata ada'a, sai da ya gama yayi mata yan tambayoyi bisa kan adinin musulunci Wanda cikin ikon ALLAH ta bashi amsoshi gamsasu, har zuwa wannan lokacin Yar mahaukaciya Bata dago inda Mubasshir ya nufa ba,
Mubasshir ya ce " AM dauko plate mu ci abinci KO ?
Yar mahaukaciya ta ce" ai na sha jus din nan bana Jin yunwa KO kadan bara na dauko maka dai, tana gama fada ta nufi kicin ta fito da Baban plato ta ajiye ta bude gasasun zabi har Hudu ta juye ta ajiye masa jus din biyu ta zuba sauran à frij ta fitar da ledodin ta dawo ta shige bayi tayi brosh, ta dawo ta bude kayanta ta dauki wata Yar rigar baci ta dauki hijabinta ta nufi bayi ta saka ta zumbula hijabinta ta dawo ta dauki turarukanta na humrar ne, na fesawar ne, har ta juya zata konta ta ga turaren da aunty habiba ta Bata ta ce mata ta tabatar da ta zama mata cikakiya à gidan mijinta ta shafa shi, ta bude ta bulbula à hanunta ta shashafa à kowani sashe na jikinta tana Jin dadinsa à ranta, ta juya tayi bismillah ta gyara shinfidar gadon duda ba wani abin tayi ba, ta Haye tayi konciyarta
Du abinda take yana kalonta, mamakinsa ne ya karu ganin ta Konta da wannan katon hijabin dan yana dakin KO ? Yayi mrmushi ya Mike ya dauki sabon tawul ya nufi bayinta dan yin wanka
Ya dauki lokaci kafin ya fito daure da tawul ya fita ya rurufo kofofin ya dawo ya rufe dakinta ya nufi gaban miroir ya fefesa tarare,
Yana gamawa ya kashe fitilar dakin ya Haye gadon
Yar mahaukaciya ta tashi da sauri tana zazaro ido ta ce" Yaya Mubasshir ka kuna fitilar nan mana, kana ganin duhu, Yaya Mubasshir mai zaka yi à dakina kuma bayan sun tafi su aunty ka koma naka dakin mana, y a ta y y y y y y y y y y y y y y y y y hadiye sauran maganarta tayi sakamakon janyota da yayi ya hade bakinsa da nata ya shiga aika mata zazafan kisssss
Cikin kankanin lokaci Mubasshir ya wular da hijabin Islam yayi mata runfa yana sarafa harshenta, sakin harshen yayi yayo kasa da kansa inda ya shinshino abinda ya fitar da shi daga hayacinsa bai san lokacin da ya cafke na................... Ya shiga sarafasu cikin kwarewa
Abinda da Wanda ta sha tsumi ta sha jiko ta bulbula tarare nan da nan ta maida hankali tana karbar sakon AA cikin na'am da sakon da yake Bata, Jin dadin hakan take, shi kuwa banda Bari ba abinda jikinsa yake, adu'ar saduwa da iyali ya yi hakan yasa Nayi baya Inaiwa Yar mahaukaciya adu'ar juriyar mijinta
I'm sorry iya hakan nake iya rubutawa☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹ sauran na samu mazga😄😄😄😄😄😄😜
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*Na*
*Sajida*
81
*Aunty Zainab kiyi ki gama min Docter deejart plz 😩*
*Sister Dee ya haka ? Gaskiya page daya yayi mana kadan, kawai ki karo mana page din bintalo domin ya dauko sugar😋*
wayarsa dake ajiye kasa ta kwashi ruri, à tare suka zabura, Mubasshir ya diro daga bed din Yar mahaukaciya tayi saurin mayar da kanta cikin bargon, yayi murmushi yana daga wayar
Idriss ya ce" kai wai ya haka Tunda safe Ina kiranka har karfe tara tayi mai kake ne ?
Mubasshir ya zaro ido yana fadin " what karfe 9 fa ? Ya Salam abokina bara muyi sallah
Idriss ya zaro ido ya ce" Ina gidanka
Mubasshir ya ce" gidana fa ? Haba bawan ALLAH da safiyar nan ?
Idriss ya ce " kasan ALLAH ka bude min KO Nayi maka aika aika à cikin gida
Mubasshir ya ce" aa yi hakuri, Bara na wurgo maka ky din falon kafin na sauko
Hakan kuwa akayi Mubasshir ya wulowa Idriss ky din falonsa ya bude ya zauna ya kuna TV domin yayi niyar fa bazai bar gidan nan ba sai da shi
Cikin nutsuwa ya dauki matarsa yayi bayi da ita inda ta dan sake da shi domin ta lura idan da taci gaba da nonokewa Mubasshir sai ta rame irin yanda yakeda takuran nan da son komai sai yayi mata,gashi ya mayar da lips dinta filin saukarsa du motsinsa sai ya mana mata kis
Haka suka gama ya jasu sallar asuba à karfe 9🤔,
Bayan sun gama Yar mahaukaciya ta duka gabansa cikin muryarta uwa ta yara ta ce" morning yayana
Mubasshir ya zuba mata ido yana kalonta yaki amsa gaisuwar tata,
Dago da kanta tayi tana kalon sa, yanayin kalon da yake mata sai da taji kunya, hudubar aunty habiba ce ta fado mata cikin ranta inda take fadin" karki baiwa mijinki damar wata ta waje ta birge sa, kiyi iya yinki dan ganin kin Wadata mijinki da dukan abinda yake bukata idan dai bai kaucewa hanya ba, sannan ki Kula da yannayin fuskar mijinki, Idannuwansa lebensa komai nasa yana iya yi miki magana da su, ki kasance mai gane kurmancin mijinki,
Yar mahaukaciya ta Mike ta cire dogon hijabinta, ta kuma cire abayar da ta dora saman Yar karamar rigarta fara tasss, tana sane ta duka kamar zata cire wani Abu à akaifunta,
Mubasshir dake zaune ido ya zaro yana kalonta, kafin yayi wani yunkurin ta Mike,, ta juyo gabansa, cikin dabara ta dan ja rigar tata kasa, saman mamarta suka dan bayana à fili, nufo shi take, shi kuwa ya tsura mata ido yana son ganin abinda zata aikata
tana isowa daidai shi ta mika hannayenta biyu ta zagaye wuyansa da su, ta Haye saman cinyoyinsa ta hade idannuwanta da nasa tana kashe shi da wani Shu'umin kalo, à hankali take matso fuskarta da tasa har ta ISO Daidai lebensa, inda Idannuwansa ke rawa ya kali idannuwanta ya kuma kali lebenta, gaba daya ya kunce ya zama wani sususu, maimakun ta mana masa Kiss sai ta fitar da harshenta ta lashi gefen fuskarsa wajen sajensa sannan ta Isa Daidai kunnansa ta hura masa iska cikin wata murya wace ni kaina sai da na zaro ido domin ban san Islam da ita ba ta furta" *Morning My Blood*
Mubasshir bai san lokacin da ya rintse Idannuwansa yana Jin saukar leben islam à kunansa da kuma sunan da ta nada masa, gaba daya tsikar jikinsa tayi wani irin tashi, bai san sanda yayi saurin jawo ta gaba dayanta jikinsa, jikinsa na mugun Bari ya lalubi lips dinta ya shiga kissing dinsu cikin zafafan Kiss,
wayarsa ta Kuma kwasan ruru tamkar an kara mata sautin kidan
Bai saki bakinta ba ya lalubo wayar sannan ya saki cikin kasalaliyar murya ya ce" Haba Idriss, haba Idriss ya zaka yi min haka, haba mana, shin mai Nayi maka da farar safiyar nan kazo kana shigar min haki haka ? Ka tausaya min mana kana katseni
Idriss ya ce" la la la, lale ma Mubasshir jarabarka tafi karfinka, toh wly au ka bude kofar nan ka fito ka raka ni zance au na hanaka koma meye kake bazaka yi shi ba wly
Yar mahaukaciya banda dariya kasa kasa ba abinda take, ta Mike a hankali daga jikinsa tayi gaba abinta
Mubasshir ya ce " baby plz karki tafi
Idriss d'à bai katse wayar ba ya ce" tafi ke karki kula shi
haka dai à dole ba dan ya SO ba ya bude kofar bayan ya saka shadarsa maroon ya sauko inda ya bar Yar mahaukaciya tana shafa mai
yana saukowa ya nufe Idriss d'à maseefar taya zai adabi rayuwar amare, ba'a yiwa ango sauko haka
Idriss yayi murmushi ya ce" nawan wly ban rintsa ba, dama na samu Nayi hajiya traitement dinta na dawo dakina dan yin baci abin ya gagara, dole na tashi na shiga fadawa ALLAH kan ya kwata min zuciyar Rafi'at
Mubasshir ya ce " abokina baka da dama, yanzu dan iya shege ka tsalake ka diro kan auntyna ?
Idriss ya ce" au yaushe kuma ka yarda da auntynka ce ?
Mubasshir ya ce" Tunda ta haifi My Islam
Idriss yayi dariya ya ce" ai kuwa nima na zama uncle dinka daga yau
zaiyi magana wayar Idriss ta kwashi kara, ya daga da sauri yana salama
Elhaj Ilyass ya ce" kaga fa abin arziki Idriss insha ALLAH yau za'a daura aurenka, yanzu haka zancen da nake maka muna gidan à zaune, ga su elhaj da mamana, da su hajiyar, Elhaj ya ce Tunda yau juma'a ne kawai mu je gidan liman mu shaida masa sai à daura idan an gama sallah
Idriss ya Mike da sauri yana ta wara ido murna ta cika masa ciki ya rasa ma mai zai ce hakan yasa ya mikawa Mubasshir wayar yana ta hamdallah,
Mubasshir yayi godiya ya ce" su din ma gasu nan tafe gidan
hakan kuwa akayi islam banda murna ba abinda take
Suna Isa ta bude ta fice da gudu inda Mubasshir ya zaro ido ya ce" ya Salam, islam no karkiyi ki fadi
Ina bata ma jinsa ta tura kofar ta shige tana ta murna sai dai Bata kai ga karasawa ba ta ja ta tsaya tana kalon ikon ALLAH, Aunty Rafi'at ce sai kuka take shekawa an kewaye ta
Turo kofar suka yi suka shigo inda suma suka ja suka tsaya suna kalon ikon ALLAH
Rafi'at ta ce" haba aunty, haba hajiya, kawai dan yaro ya ce " ga abinda yake SO sai à biye masa, haba dan Allah yanzu da girmana à hada ni Aure da yaro karami ? Nafa girme masa fa kuma wly tausayina ne yake ba wani sona ba
hajiya hafsat ta ce " sister wai meye haka ne ? Haba taya za'a zauna ana nuna miki gabas kina kalon yama ? Sunar ce bakya SO ? Idan har baki godewa ALLAH kan ni'imar da yayi miki à yanzu mai zaki yi ? Taya zaki fasara kyautar da Allah yayi miki adu'arki da ya amsa da wata fasarar ? Rafi'at à da inai miki kalon kinyi hankali ashe dai da sauran ki,
hajiya hawau ta ce " aa hajiya ku tashi ku barni da y'ata mu zanta kun ji ?
Hakan kuwa akayi sai da suka tashi suka ga su Mubasshir sunyi cirko cirko da hanu suka yi musu nunin su fice karta gansu
hakan kuwa suka shige inda hajiya hawau ta dage wajen kontarwa da hajiya Rafi'at hankalinta kan auren ta da idriss
ya kasa tsaye ya kasa zaune, du labarin da suke yana dai jinsu ne aman baya fahimtar abinda suke fada,
Hajiya hafsat ce ta fito da faranti da abinci à ciki, ta ajiye ta dauko ta shiga zubawa kuskus ce ta sha muryar jan nama sai kanshin kayan yaji ke tashi, ta mimika musu,, har ta kai kan Idriss ta mika masa ta ce" Idriss ka dawo cikin hayacin ka mana,
Idriss ya juya à hankali ya shiga cacakar abincin
Yar mahaukaciya ta shigo da jus jus ta ajiyewa kowa à gabansa, ta juya ta dauko nata farantin ta zauna Kusa da hajiya Fadimatu tayi bismillah ta debo ta kai bakinta
Wani irin Abu taji ya bigeta à hancinta na kanshin kayan yajin nan da tafarnuwa, kafin ta Ankara tayi wani abin sai kawai taji cikinta ya fara hautsina mata sai ga amai
da gudu ta mike zata nufi Bayi aman Ina dole ta duka à nan tana kwara amai tun karfinta, dan kwalin kanta ya fadi kasa haka mayafinta domin wani irin tukota aman yake
da gudu Mubasshir ya rigayi kowa isawa wajenta ya kamata yana tambayarta Lafiya ? Mai ya sameta ? Wani abin ta hadiye ?
Da kyar ta samu ta gama aman du ta galabaita ya dauketa yayi bayi da ita dan ya wanke mata wajen da ya baci à jikinta, ita kuwa hajiya Fadimatu sai sintiri take tana tambayar ta shigo ne bayin ? inda hajiya hafsat ta shiga gyara wajen
Idriss ya Mike ya fice dan dauko kayan aikinsa domin yana Docter gida har uku hakan ya sa baya tafiya ba malet dinsa mai dauke da yan abubuwan da ya dace domin aikinsa
Daidai zai fita suka yi karo da Hajiya Rafi'at, da sauri ta zaro ido tana yi masa kalon mamaki domin Bata san shigowarsu ba, ido Hudu suka yi inda gabanta ya fadi, tayi saurin sada kanta kasa shi kuwa yaki dakin hanyar balatana ta fice,
Hajiya hawau ta taho tana fadin lafiyarku kuwa yayanan ? Naga kun tsare hanyar ficewa
hajiya Rafi'at ta ce " hajiya shine ai ya tsare hanyar fa
Idriss ya ce" to hajiya ta shige mana ?
Hajiya hawau tayi murmushi ta juya tama daina shigan balatana su fake da ita
Rafi'at ta juya itama zata bar wajen da saurinsa ya riko hannunta ya jawota tamkar wata beby ya hadeta da garun dakin
Idannuwanta ta rintse tana mutsukmutsuk da baki, Idriss ya tsurawa bakin nata ido Yana kalonta
Jin yayi shiru ne t'a bude idannuwanta ta sauke su à cikin Idannuwansa, ta kasa janye idonta daga NASA
Idriss ya saki murmushi à hankali ya ce" hei *I Love u*
Aunty Rafi'at ta zaro ido ta kasa dauke idannuwanta daga fuskarsa gabanta na dukan uku uku
Idriss ya kashe mata ido daya ya ce" Yaya dai madame, kalon fa ?????
Da sauri ta sada kanta tabi ta kasa hannun NASA tayi dakin da gudu tana ajiyar zuciya
Yayi murmushi y'a ce " she love me too, yayi gaba abinsa
Yana dawowa dauke da kayan aikinsa ya shiga aune aunensa inda ya bukaci fitsarinta, bayan tayi ta bayar ya kuma daukan