Showing 21001 words to 24000 words out of 69263 words

Chapter 8 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB

Aisha JB   

22 Aug 2025

305

abin da aka danganta shi da Allah yana jin lallai lamarin ya girmama. Cike da sanyin jiki ya biyo ta ɗakinta yana rarrashinta tare da bata haƙuri haka yai kiɗinsa yai rawarsa ba tare da ta kulashi ba. Ƙarshe ma fita ta yi a gidan ta nufi gidan Honourable Sa’id da niyar sauke masa kwandon bala’i harda matar tasa domin duk da haɗin bakinsu aka munafurce ta. Suna sane da yadda ta tsani maganar kishiya amma babu wanda ya sanar mata kowa ya yi gum da bakinsa aikuwa sai ta tashin kan kowa har ita me ɗaure mishi ƙugu (Hajiya Umma).


Nuriyya zaune kusa da Amrah yayin da Zaliha take nunawa Momy Salamatu turarukan da suka kawo mata wadda Honourable Sa’id ya saya. Kallon Amrah Momy ta yi tana faɗin "Ku shiga daga ciki mana tun da taƙi sakewa a nan ɗin, ina ga can zata sake" Ta faɗa tare da kallon yadda Nuriyya take ta sunkuyar da kai tamkar wacce take gaban surukanta. Hannunta Amrah ta kama suka nufi ɗakinta "Dalla malama ki saki jikinki duk kin bi kin takura kanki haka za ki je kina yi wa Dad ɗin mu?" Murmushi kawai ta yi tare da kwanciya saman katifar "Wai Noor wani irin wulaƙanci ne haka, mutum yai ta miki magana ba za ki ce komai ba sai murmushi.." Zaune na miƙe ina mamakin abin da ta ce "Uhm ai kin fi kowa sanin yadda nake" Ɓata rai Amrah ta yi tare da faɗin "Bari in kira Dady ya zo wataƙila za ki yi magana.." Ai da sauri ta ce "Dan Allah ƙyale ni da wannan maganar ni bana so ya dinga zuwa inda nake"
"Akan wani dalili? Mijinki ne fa" Amrah ta faɗa tare da zaro ido "Ni dai dan Allah ki bari kada ki kira shi" Miƙewa Amrah ta yi tare da jan glass ɗin window tana kallon motar da ya shigo "Taɓɗijam! Lallai akwai daru Momy Larai ta dawo kenan" Ta faɗa cikin ranta tare da rufe Window kiran Alh. Aminu ta yi domin shi ya ce ta ɗauko mishi Nuriyya.


"To munafukai shi ne aka munafurce ni Salamatu ashe har da ke za a haɗa baki a yi mini kishiya? Wallahi tun da Aminu ya yi aure Sa’idu ma zai yi aure Allah ya isa tsakani na da ke.." Da sauri Momy Salamatu ta ce "Zaliha shiga ɗakin su Khadijah ina zuwa" Tana barin wurin ta ce "Haba Larai me ye haka? Ya za ki shigo ba sallama sannan kina kirana da munafuka yaushe na san an yi haka? Hajiya Umma ita ta yi wa mijinki aure dan Allah karki tada hayaniya da yara a gidan..."
"Eh ai dole za ki ce haka tun da an haɗa baki da ke wallahi ki faɗawa Sa’idu za mu gamu Allah sai na ci masa mutunci munafuki dan na san duk da sa hannunsa" Rufe baki momyn Amrah ta yi tana ƙoƙarin danne dariyar da ke son ƙwace mata "Dan Allah Aminiyar zauna mu yi magana duk ba abin tashin hankali ba ne.." Dakatar da ita ta yi da faɗin.
"Babu wani zaman da zan yi a gidan munafukai" Cike da zolaya Maman Amrah ta ce "Haba uwargidan Aminu.." Fuuu Hajiya Larai ta yi wucewarta tare da jan tsaki me Maman Amrah za ta yi ban da dariya ai gwara ma da Nuriyya bata falon domin wallahi zata raina mata dan wannan hauka ne take yi ba kishi ba, Allah ya sa ma ɗakin Amrah akwai tazara ba za su ji wannan ɓaɓatun nata ba. "Allah ya kyau" Abin da ta ce kenan sannan ta kira Zaliha suka ci gaba da lissafin turaren kasancewar ita ma yanzu ta shiga business ɗin turarukan tana bawa Maman Nafisa kuɗi a kan ta dinga yi mata masu kyau aikuwa jama'a na saya sosai dan harda haɗi na musamman take siyarwa.
Kallon Amrah da ke ƙoƙarin fita ta yi tana faɗin "Ina za ki je?" "Yanzu zan dawo" Abin da ta ce mata kenan sannan ta fita a ɗakin. Tana dariya saƙo ta turawa Dady sannan ta koma falo ta samu Mamanta har yanzu suna lissafin turaren.


Kwanciyar rub da ciki ta yi tana duba hotunan su na makaranta wadda ta gani a ɗakin bata ji motsin shigowarsa ba duk da yai sallama ciki-ciki hakan bai sa ta farga ba, kasancewar hankalinta yai nisa tsaye yai yana bin bayanta da ido ganin yadda ta ko'ina ta cika mace kasancewar ta cire hijjabinta lokacin da ta idar da Sallar la'asar tana da diri me kyau da ɗaukan hankali babu abin da ya fi mayar da hankali kamar bayanta mazaunanta sun fisgeshi sosai wani irin lumshe ido yai domin doguwar rigan yadin material ne a jikinta dalilin da ya sa ya kwanta a jikinta har ya fitar da mazaunanta kenan. Motsin da ta ji ne ya sa ta faɗin "Lallai Amrah kin iya ajiyar hoto yanzu harda wanda muka ɗauka a waya kika wanko su..." Ɗif ta ɗauke maganar tata sakamon jin saukan numfashin sa gab da ita yana faɗin "Muga hoton.." A zabure ta watsar da su tana ƙoƙarin neman abin da zata kare jikinta da shi. Sai dai hijjabin na ƙasa nesa da su, ƙoƙarin sauka a gadon ta fara yi domin ɗauko hijjabin yadda take motsi da ƙoƙarin sauka ne ya sa shi ƙura mata ido ganin yadda jikinta ke rawa komai Tabarakallah Ma Sha Allah. Hannunta ya riƙe tare da mayar da ita ya zaunar da ita a jikinshi da sauri ta fara ƙoƙarin janye wa daga jikinshi lumshe ido yai jin yanda hannunta ke da mugun laushi tamkar auduga, tsam ya rumgumeta a ƙirjinshi yana shaƙar ƙamshin jikinta wanda yake sake birkita mishi lissafi. "Dan Allah ka yi haƙuri ban san ka shigo ba ne.." Ɗif maganar tata ya ɗauke jin saukan numfashinsa bisa wuyanta wani irin dirirr jikinta yai kamar wacce aka tsikara da allura sai zamewa da rawar jiki take a ƙoƙarinta na son ƙwacewa daga riƙon da yai mata sai dai bata san sake rikita shi take ba kasancewar yadda jikinta ke gugan nashi ga tafin hannayenta da ke taɓa cinyarshi wanda ya sa shi sake susucewa yana sauke mata wani irin zazzafan kiss me rikitarwa gabaɗaya sai kai shi ya kwance jin yanda ko'ina na jikinta ke ɗauke da ƙamshi me fisgar hankali.
Wani irin numfashi yake saukewa tare da ni man bakinta wanda yake tsuke yayin da idanuwanta ke rufe tana fitar da wani irin numfashi na firgicewa da ƙyar ya iya kai bakin shi saitin kunnenta tare da yin magana cikin wani irin yanayi da sanyi ya ce "Yi haƙuri to" Buɗe idanuwanta ta yi tare da ture shi gefe tana mayar da numfashi bayan ta rarumo hijjabin ta saka nan ta sake duƙunƙune jikinta tare da fashewa da wani gigitaccen kuka tana jin kanta na juyawa. Da sauri ya matso yana shirin taɓa ta cikin tashin hankali ganin yadda take rawar jiki "Ki yi haƙuri ni kaina ban san na aikata miki hakan ba.."
Zubur ta miƙe tana neman hanyar fita, ganin yadda take a birkice ne ya sa shi saurin kamo ta domin muddin ta fita cikin wannan yanayin za a iya samun matsala. "Ki nutsu mana bai da ce ki fita cikin wannan yanayin ba.."
"Dan Allah ka daina bana so! Ka daina kusanto inda nake ba zan iya maka komai ba, ba ni da wannan ƙarfin da zan maka abin da kake.."
"Ban nema wani abu ba, kuma ba zan ƙara miki irin hakan ba I'm sorry..." Ya yi maganar cikin sanyi bayan ya zaunar da ita, Miƙewa yai yana kallon yadda har yanzu taƙi ta kalleshi wayarta ya ɗauka ba tare da ta sani ba sannan ya fita a ɗakin. Tana zaune shuru har Amrah ta shigo tana mata magana ba tare da ta sani ba dafata ta yi tana faɗin "Noor wai lafiyar ki lau kuwa? Tun ɗazu nake magana kin yi shuru me ke faruwa?" Wani irin numfashi ta sauke tare da miƙewa tana faɗin "Zan tafi gida yamma ya yi.." Ba tare da ta ji ƙarshen zancen nata ba tari numfashinta gurin faɗin "Ok Daddy na jiranki gurin mota and ni ma zan zo after saboda maganar tafiyar da za ku yi.."
"Wacce tafiya kuma?" Cike da mamaki Nuriyya ta dakatar da ita kallonta Amrah ta yi sannan ta ce "Au na manta fa, Maman bata sanar da ke Daddy ya ce jibi za ku wuce tare ba?.."
"Dan Allah ki yi mini magana yadda zan fahimta ya ce za mu je ina?.."
"Zai je Ghana shi ne ya ce ki shirya daga nan sai ku je asibiti domin a duba lafiyar.."
Jagwab! Ta koma ta zauna tare da zare ido tana faɗin "Please dan Allah babu fa inda za ni tare da shi, koma waye ya shirya wannan tafiyar bafa zanje ba" Daga haka ta fito a ɗakin sannan ta je ta yi wa Maman Amrah Sallama koda ta je wurin motar gidan baya ta nufa sai dai tun kafin ta buɗe ta ji sautin muryansa inda yake faɗin ta shigo gidan gaba.
Ba dan ranta ya so ba ta shiga haka ya kawo su gida Zaliha na fita ya ƙulle motar tana ta kiciniyar buɗewa amma shuru ɗan juyowa ta yi ta kalleshi ganin yana danna wayarsa ne ya sa ta faɗin "Uhm motar a ƙulle fa yake.."
Ɗagowa yai yana kallonta tare da faɗin "Uhm ina sane da hakan" Yana gama faɗar hakan ya ci gaba da amsa waya inda suke tattaunawa kan tafiyar da zai yi, yanayin yadda yake maganar ta lura tafiyar me muhimmanci ne domin ya nutsu yana zuwa jawabi cikin nutsuwa da kyakkyawan turanci kamar baturen Faransa. Ya ɗauki a ƙalla minti talatin kafin ya sauke wayar zuwa lokacin kam ta gaji da zama ta yi kicin-kicin da fuska ga shi taƙi yi masa magana shi kuwa so yake lallai ta yi masa magana ganin bata da niyar maganar ne ya sa shi kwantar da kujeran motar yana lumshe ido ganin haka ya sa ta juyowa kamar zata fashe da kuka ta ce "Hmm zan tafi ana sallah fa" Wani irin murmushin gefen baki yai tare da faɗin "Ki shirya jibi za mu wuce.." Bata tsaya sauraron zancen nasa ba ta yi shigewarta cikin gida, a anguwar yai Sallar magariba tare da Baban su inda yake sake jaddada masa maganar tafiyar tasu sun taɓa hira kafin ya ba shi kuɗi, ya so ya sake ganinta sai dai lura da tana cikin fushi ne ya sa shi shiga mota leƙowa Baban su yai ganin bai tafi ba yana faɗin "Ba ku yi sallama ita ba ne a turo ta?" Ɗan murmushi kawai yai tare da girgiza masa kai sannan ya bar Area ɗin.
Zama ta yi jikin Maman su tana sauke ajiyan zuciya, zame jiki Maman Nafisa ta yi tana faɗin "Mene ne haka? Sai ka ce wata jinjira kin zo kin wani danne min jiki" Ɓata fuska ta yi tana faɗin "Mamanmu idan ban zauna jikinki ba a ina zan zauna? Ai gwara na ji ɗumin uwata"
"Mijinki ya ce ki shirya za ku tafi jibi"
Sunkuyar da kanta ta yi tana jin hawaye na shirin zubo mata "Mamanmu ni ɗaya haka zan bi shi?" Ta yi maganar tana kallonta miƙewa Maman su ta yi domin bata cika son dogon magana dangane da maganar mijin ɗiyar tata ba, domin kunya take ji. Wani irin murmushi Fiddoh da ke kwance ta yi domin kunya irin na Maman tasu ba ƙaramin dariya yake bata ba.
"To sai a shiryawa ɗiya abin da ya da ce, domin da miji zata tafi, gwara tun yanzu a fara koya mata dabarun riƙe mijin tun da an ce kishiya gareta kuma..." Dakuwa Maman su ta yi mata tana faɗin "Ungo nan na ce haba! Wai Firdausi wannan bakin naki ba ya shuru ne kam?" Ya mutsa fuska ta yi tare da nufar gurin kayanta dan zaman gidan ya gundureta haka, duk da zuwa take yi bata cika kwanan gidan ba, zuwan Amrah ne ya dakatar da ita inda suka shiga tattaunawa domin Daddy ya bata kuɗi akan ta yi wa Nuriyya siyayya nan fa suka fita tare dan Nuriyya tana can tana ihun babu inda za ta bishi. Kasuwa suka shiga inda suka shiga mata siyayyan wasu 'yan iskan kayan da da su da babu duk ɗaya, su kansu suna dariya ganin irin kayan da suke zaƙulo mata duk babu na arziki gefen underwear ma ba'a magana, haka suka jido mata kaya sosai sannan suka dawo gida ko kallon su Nuriyya ba ta yi ba, domin duk haushin su take ji.


****
Tana zaune a falo yai Sallama ya shigo "Barka da dawowa" Fuska a sake ya amsa mata tare da faɗin "Barkanmu dai" sannan ya nufi ɗakinsa bin bayanshi ta yi tana ƙoƙarin taya shi cire kayan shi dakatawa ta yi jin baƙon turare a jikinsa ƙoƙarin daurewa ta yi sannan ta je ta haɗa mishi ruwan wanka yana shiga ɗaki ta fara binciken wayarsa ko zata samu Number yarinyar sai dai ko'ina na wayar tasa a ƙulle yake, tsaki ta yi tare da fita a ɗakin tana cin alwashin tarwatsa duk wani abin da ya danganci wannan kishiyar da aka yi mata koda za ta yi yawo tsirara sai ta hanata shigowa rayuwar mijinta uban 'ya'yanta , domin Aminu nata ne ita ɗaya babu macen da ta isa ta taɓa shi muddin kuwa ta yi gigin hakan sunanta 'GAWA' domin tana matuƙar son mijinta tana kuma kishin sa.
Abinci ta haɗo ta kawo mishi ɗaki abin da aka jima ba'a yi masa ba, aikuwa ya ji daɗin hakan sosai ganin yadda lokaci ɗaya ta watsar da mahaukacin kishin nan nata tana tarairayarsa tare da janshi da hira, duk wannan abin da take tana so lallai ta ji labarin Amariyar tasa ne sai dai ko kusa bai ɗauko zancen Nuriyya ba, duk yadda ta kai ga son jin wacece ita bai bata wannan damar ba, ƙarshe ma shuru ta yi tana tunanin yadda za ta yi ta gano inda yarinyar take nan yake sanar mata maganar tafiyar da zai yi, fatan alkairi da samun nasara ta yi masa sannan ta fita a ɗakin koma nata da niyar yana tafiya za ta je ta ɗauko Suhaima ta dawo gida. Yana gama kimtsawa ya kwanta zuciyarshi fal tunaninta shi kaɗai yake murmushi tare da shafa ɗan sajensa wanda suke kwance luf-luf, ga shi ya ɗauke mata waya bare ya kira ya ji muryanta duk da idan ya kira ma ba magana take mishi ba, se dai ta manna wayar a kunne tana jinsa har bacci ya ɗauke ta kafin yake ƙyaleta.




Wannan Littafin na kuɗi ne domin kasancewa cikin group ɗin za a tura ₦500 ta wannan account 2389596965 Aisha jubreel Zenithbank. Sai a tura shedar biya ga wannan Number 09079740079


#Amnoor
#Sadstory
#Destiny
#Hotlove
#Romance
#Sexstory
[5/9, 11:44 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
Wattpad: ayshajb
Arewabooks:ayshajb
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. W. A★


Free page 25_26


Kuje YouTube ku yi Subscriber Channel ɗi na FARIN JINI HAUSA TV. Domin samun ƙayatattun littafanmu.


H-P Place Group.


Washegari yana idar da Sallar Asubahi ya nufi gidan Umma nan yake sanar mata tafiyar gaggawan da zai yi zuwa Ghana amma zai ɗauki Nuriyya su tafi tare domin yana son danganta ta da likita cikin jin daɗin kalamansa ganin ya sauko har ya karɓi aure kuma ga shi za su tafi tare da ita nan ta shiga sanya mishi albarka cike da jin daɗi shima ya dawo gida bayan ya kammala karin kumallo Laraba ta rako shi wurin mota inda drive ke jiranshi tana mishi addu'ar dacewa tare da buɗi mai amfani.
“Allah ya tsare min kai mijina uban ’ya’yana Ubangiji ya ba ka halal ɗinka Allah ya tsare ka da duk wani abun ƙi, Allah ya haɗa ka da alkairi zan yi kewar ka sosai” A bazata kalaman nata ya ratsa kunnuwansa da murmushi ya amsa tare da riƙe hannunta yana murzawa cikin nashi kana ya yi mata kiss sannan ya shiga motar yana ɗaga mata hannu ita ma bye bye ɗin take masa fuska cike da annuri. Motarshi ya ɓacewa taja wani dogon tsaki tare da shigewa cikin gidan Lagos zata koma wurin ƙawarta Fumi domin neman mafita dan ba za ta ƙyale shi da wannan matar da ya auro ba.
Tun jiya da dare Mamanmu ta hanani saƙat da wasu turarukan tsungunno tare da ciye-ciyen wasu abubuwan da ban san na mene ne ba, in zan yi magana sai ta dakatar da ni taƙi ba ni damar da zan tambayeta kayana kuwa tun daren jiya Fiddoh da Amrah wacce anan ta kwana suka gama kimtsa min suna dariya ba tare da na san tsiyar da suka tsuka mini ba, kasancewar na yi tsifa ya sa Zaliha ta tasa ni a gaba sai da ta yi min ƙananun kitso domin ita gwana ce wurin kitso Firdausi ce ta iya lalle Amma duk ta watsar kasancewar bata ba abin muhimmanci ba, ni kaina yadda ta zizara min kitson ya yi matuƙar burgeni, sai kusan ɗaya da rabi na dare muka kwanta da Asuba na fara neman wayata nan Amrah take sanar mun wai yana wurin Daddy shuru kawai na yi har gari ya waye ina ji suna magana da shi a waya inda yake sanar mata ga shi nan zuwa su fito. Kallo na ta yi ganin yadda na yi kicin-kicin da fuska domin wallahi ba ƙaunar tafiyar nan nake ba, dariya kawai Firdausi ta yi tare da gyara kwnaciyarta tana faɗin. “Mamanmu idan sun tafi Allah ya tsare wallahi na gaji ba zan iya wani rakiya ba, Aunty Nuriyya Allah ya kiyaye ya tsare hanya Please ki kula ki dinga sake mishi fuska kina yi mishi magana ki aje kurmancin nan a gefe ki lallaɓa mijinki domin kishiya gareki ki yi ƙoƙarin kame zuciyarsa a ɗan tafiyar nan da za ku yi..” Sai ta yi shuru tare da lumshe ido kana ta ci gaba da magana "A baya naji haushin Babanmu amma ganin yadda wannan mijin yake miki abin arziki harda ƙoƙarin samar miki da lafiya ya sa naji sanyi, domin ga dukkan alamu zai kula min da ’yar’uwata zai ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login