Showing 69001 words to 69263 words out of 69263 words
Chapter 24 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB
Nafisa ta yi tare da faɗin “Ai ki kwantar da hankalin ki, kamar yanda a baya ba ta yi nasara a kan ki ba, ta je ta jiggata haka ma yanzun babu abin da za ta miki, dan duk sheɗancinta ba ta isa ta taɓa yara ba balle kuma ke, ki kwantar da hankali ba abin da zai taɓa ku ln Sha Allah” Amnoor na kashe wayar Maman Nafisa ta ce “Ina ga Hajiya Laraba na nema wa kanta mutuwa ne wallahi, dan in ta kuskura taɓa min 'ya da jikokina ko Ashraf bai yi mata komai ba ni zan mata”
Ba'a sauya musu sunan su ba, haka ake kiran su da Hassan da Hussaini duk da na yi tunanin zai mayar da sunan Haisam sai na ga ba haka ba, ni ma kuwa na ji daɗi da bai mayar da sunan ba. Wankan gida kan ya ƙi amincewa na tafi, duk yanda Maman Nafisa ta so na dawo gida haka bawan Allahan nan ya murzawa idanunshi toka a kan babu inda za ni. Haka na yi jego na a ɗakina a ranar da na yi kwana arba'in Amnoor ya ce shi haƙurin shi ya ƙare a daren ranar ba mu runtsa ba saboda shagalin da muka kwana yi dan an ci uwar sabada.
Ƙarshe. END
ALHAMDULILLAH! A nan na kawo karshen littafin AMNOOR kuskuren dake ciki Allah ya yafe min, da ni daku masu karatu Allah. Ina muku fatan alkairi masoyana jama'ar Wattpad Arewabooks WhatsApp ina sonku domin Allah. Sai mun haɗu a sabo A'isha JB ke muku fatan alkairi sai mun haɗu a sabo.
08062715485