Showing 51001 words to 54000 words out of 69263 words

Chapter 18 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB

Aisha JB   

22 Aug 2025

298

haka Ashraf zai yi ta kawo min rubutu ni kuwa sai in ƙi sha, dan ina tunanin wani mugun abu ne yake kawo min sai da ya yi min rantsuwar shi ba wani mugun nufi a zuciyarsa kafin na yarda na fara sha, haihuwar kuwa ya zo min cikin sauƙi lokacin da na haifi Nuriyya.


“Daman Ba baba ba ne baban mu duka? Suka haɗa baki wurin tambayarta. Gyaɗa musu kai ta yi sannan ta cigaba.


Bayan arba'in aka ɗaura aure na da baban ku, auren da har gobe nake da-na-sanin yin sa saboda sam halayyarss ba shi da kyau. Na sha wahala da shi domin tun da aka ɗaura auren ya ɗauke ni daga cikin gidan su zuwa wani wajen, ɗan aiken da nake samu daga yaya Ashraf duk babu, na san bai ji daɗi ba, domin sau da dama yakan zo ya ɗauki Nuriyya saboda tsananin ƙaunar da yake mata yana kashe mata kuɗi sosai. Baban ku kuwa ya ɗaura karan tsana a kan Nuriyya a cewarsa duk ta silarta ne bai sameni a cikakkiyar mace ba.


Bayan aure na da baban ku, ya auri mata uku duk kuma ya sake su, a waje zai nuna musu kuɗi, yana musu faɗi ga shi da iya ɗaukar wanka Uwa Uba kashe mace da kalamai, matan sun ɗauka shi wani me arziki ne ganin irin suturan da yake sawa, sai sun shigo sun ga ba haka ba ne domin ko abinci bai ajiyewa lokuta da dama Uwar riƙon shi ke ciyar da ni. Idan suka ga haka nan fa aure yake ƙare wa. Ni kuwa na zama 'yar kallo domin haka nake zama ina kallon diraman shi da matan shi, lokacin da na yi cikin Firdausi a lokacin Uwar goyon shi ta rasu. Na yi kuka sosai domin ita ce me temaka min da abinci, ana gama hidimar mutuwa ya ce shi fa Najeriya zai zo dan an ce ana samun harka sosai, nan ma na ji baƙin ciki sosai, saƙo kawai na aikawa yaya Ashraf cewar za mu komo Najeriya daga nan ban sake jin su ba.
Na sha wahalar rayuwa a hannun babanku domin zuwar mu nan komai ya sake lalacewa nan ya shiga harkan caca sace-sace ke duk wani harkan banza da shi ake yi zan ce neman mata ne kawai ba ya yi, amma shi ma ba ni da tabbacin yana yi ko baya yi, nan ma sai da ya auri mata biyu Maman su Audu ce Allah ya yi zaman zai ɗore da ke ita ma ba ta barshi haka ba ya sha tafiya ya yi sati ba tare da na san inda ya je ba, kuma ba ya ajiye min ko ƙwayar hatsi haka zan yi aikatau in samo abin da za mu ci.


“Tab! Lallai sannu da ƙoƙari Maman mu! Ai haƙuri kan kin yi da babanmu har yanzu kuma kina kai to amma kina jin labarin 'yan'uwan naki?” Cewar Fiddoh.


Maman Nafisa ta ce “Duk suna nan lafiya.." Caraf Zaliha ta ce “To yaushe za mu je?” Kallon Zaliha Fiddoh ta yi tare da faɗin “Ai baban ta ya ce kar ta koma ga ahalinsa. Sunkuyar da kai Maman Nafisa ta yi tare da faɗin. “Hmm! Ai ya rasu tun dawowar mu ba jimawa, da ke lokacin ina samun magana da Saliha ta wayar baban ku ita take sanar min da rasuwar” Duk sai suka yi shuru suna jin babu daɗi a ransu. “Amma ya kamata ki je gida tsawon shekaru fa ba ki je ba, izuwa wannan lokaci mun samu cigaba tun da mijin Noor yana iya ƙoƙarinsa a kanmu” Cewar Fiddoh tana ƙoƙarin shiga bayi jin ana kiran sallar magariba.


..........Abban Amrah yana faka mota Suhaima ta yi saurin fita dan ta san Daddy a cike yake da ita, aikuwa shi ma ya fita da sauri da zummar cin ƙaniyarta sai dai Aminin nasa ya dakatar da shi tare da lallashinsa kan ya ƙyaleta har yanzu giyar ƙuruciya ke ɗaiwaniya da ita Alhj Aminu bai ce komai ba har Abban Amrah ya yi masa sallama yana faɗin “Sai mun zo diner anjima dan kasan ban taɓa cin girkin Amariya ba, yau da ni da za a yi wannan bushashan” Suhaima kuwa tana shi falon ta fara ƙoƙarin shigewa ɗakin Amnoor miƙewa Hajiya Laraba ta yi tare da faɗin. “Ina kike shirin zuwa?” Tsayawa ta yi zuciyarta na bugawa dan ba ta tsammaci maganar mahaifiyarta ba. Ba ta aune ba taji ta sauke mata yatsu biyar bisa kuncinta hagu da dama. “Kina ƙoƙarin zubar mana da mutunci ke har kin yi wayon bin namiji gida? Oya muje in duba ki dan wallahi ban yarda da ke ba Suhaima” Cikin kiɗimewa Suhaima ta ce “Wallahi tallahi Momy ƙalau nake....” Saukar bulala ta ji da jikinta nan take ta saka ihu tare da ƙwalawa Amnoor kira. “Wayyo Allahna! Dan Allah Aunty Noor ki zo ki ceceni, wallahi tallahi Daddy ba zan sake ba Momy ki ba shi haƙuri, wayyo yaya Hisham..” A zuciya ya dinga sauke mata bulalan a jikinta. “Kar ka kashe min 'ya, wannan wane irin baƙin zuciya ne? Ka daina dukanta!” Nunata ya yi da ɗan yatsa yana faɗin “Ba ga irinta nan ba, to wallahi idan Suhaima ta ɗebo abin kunya sai dai ki tattara da ke da ita ku barmin gida shashasha mara lissafi, bari ki ji in gaya miki wannan ba soyayya bace! Ba tarbiyya bace! Wallahi kin ji na rantse miki kika sake min magana a kan hukuncin da nake yi wa Suhaima sai na saɓa miki.... Cikin ɓacin rai ta ce. “Sai me? Ka fito fili ka yi magana ka ce za ka sake ni ai tun da ka yi aure ka ɗauke hankalinka daga gare mu ƙarshe ba tura min 'ya ka yi wani wurin don a barka da matarka.... “Ya isa! Ya isa, kar ki yarda ki sake kirin gidan mahaifiyata da wani gun” Ya yi cikin muguwar tsawa, matsowa ta yi tana mishi kallon raini tare da kai hannu za ta janye Suhaima aikuwa cikin fushi ya zuba musu bulalan daga ita har Suhaiman. “Wallahi na faɗa maka ka daina duka min 'ya! Ka bar dukan Suhaima Aminu!” Bai saurara mata ba daga ita har Suhaiman. Sallame sallar na yi ba shiri jin irin kururuwan da Suhaima take yi tana k'wala min kira. Da sauri na fito wanda ku san a tare muka ƙaraso ni da Hisham, tare Suhaima na yi tare da faɗin. “Ka yi haƙuri Daddy...”
“Matsa a nan!” Cikin tsawa ya yi min maganar tare da min nuni da gefe. Girgiza mishi kai na yi tare da riƙe Suhaima wacce ta ƙanƙameni tana kuka. Hisham kuwa cak ya tsaya yana kallon Suhaima tare da Amariyar mahaifin nasa wacce tun da ya zo gidan bai ganta ba sai yau. Ƙuru ya yi mata da ido yana sake jin sautin muryanta inda take ba wa Daddy haƙuri. Lumshe ido ya yi yana jin zuciyarshi na wani iri da sauri kuma ya buɗe ido jin Suhaima ta saka ihu tana kiran sunan Amnoor. Da sauri Amnoor ta ja Suhaima zuwa ɗakinta Hajiya Laraba ta ce “Ki dawo mishi da ita ya kasheta! Ai wallahi Aminu ni da kai ne, ba dai ka haɗa ɗi da Suhaima ka daka ba?Shuru Amnoor ta yi tare da faɗin “Haba Hajiya! Ta yaya zai dinga mata irin wannan dukan? Ai sai ya ji mata rauni maimakon ki rarrashe shi ya ƙyaleta duk irin kururuwan da take yi na ɗauka ma kina ɗaki ne, a she duk kina kallonsu gaskiya irin wannan dukan bai dace ba, duk da ba ta kyauta ba, amma ai ta ba da haƙuri..” Nuna Amnoor ta yi da yatsa tare da faɗin “Kar ki sake min magana irin haka, ina magana a kan 'yata ne da mijina dan wallahi zan ɓata ranki, Aminun ne zan lallashe shi? Shi yarone? Ko shi jariri ne? Ki je ki ɗauko Suhaima ki dawo mishi da ita, ba duka ba, ƙarshen duka ya kasheta, kai kuma na dawo gare ka, da ke 'yar gwal matar so, ta fito ta yi magana dole ka dakata da dukan ko? To na rantse da Allah ka sake taɓa lafiyar Suhaima ko, abin da zan maka sai ya ba ka mamaki” Da wani irin mutuwar jiki Hisham ya fita a falon yana jin wani irin abu ya toƙare shi a ƙirji, domin Amnoor kawai yake kallo zuciyar shi kuwa na wani irin yanayin da ya kasa fahimta, wayar shi ya ɗauka tare da kiran Munir ko sun ƙara so dan ya je ya ɗauko su a filin jirgi, tun yau yake son sanin inda take ba zai iya jira mai tsayi ba.


Sake bulalan ya yi tare da zubewa kan kujera yana kallon Laraba, tsaki Hajiya Laraba ta yi tare da barin falon, ruwan sanyi Amnoor ta ɗauko tare da zama kusa da shi ta kai ruwan bakin shi. “Ka yi haƙuri Daddy” Ta faɗa tare da riƙe hannunshi tana murzawa cikin nata. Bayan kalmar haƙuri ba ta san abin da za ta ce mishi ba. Wayarshi da ya yi ƙara ne ya ɗauka yana magana ya ce mata “Ina abincin da na ce a yi wa baƙi na?” Ya fad'i haka tare da miƙewa tsaye. “Na kammala komai ai” Yana ƙoƙarin fita ya ce “Ki shirya komai ina dawowa”


“Allah Ya tsare hanya” Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta sunkuyar da kai na yi ƙasa ina murza 'yan yatsu na. Ji kawai na yi ya ɗago fuskata tare manna min kiss a goshi yana faɗin “Amin” Sannan ya fita a gidan. Ɗakina na nufa a falo na ci karo da Suhaima kallona ta yi tare da faɗin “Auntynmu irin wannan love haka? Naga Daddyna ai” Kame fuska na yi tare da faɗin “Allah Ya shiryar da ke Suhaima”


“To Amin, amma ai gaskiya na faɗa. Ni kam ki lallaɓa Daddy idan Dalil ya zo a yi maganar aure kawai, dan wallahi ina son shi da yawa, ba zan iya barin shi da wancan karuwar tana zuwa mishi ba” Juyowa na yi ina kallonta kafin na ce “Suhaima wani abu ya taɓa shiga tsakanin ku?” A tsorace ta zare ido tare da faɗin. “Wallahi tallahi a'a Aunty, babu abin da ya taɓa haɗa mu, ko kiss komai bai taɓa min ba” Ajiyan zuciya na yi tare da faɗin “Allah Ya tsare gaba. Tun da karsashi soyayya ya goge zafin duka oya sai muje a tayani shirya abincin baƙi ko?” Suhaima ta ce “Ok mu gama sai na yi miki makeup dan ban ga kina irin kwalliyar nan ba” Share batun na yi muka nufi kitchen, sai da muka jera komai a daining sannan na koma ɗaki. Wanka na yi tare da yin alola na gabatar da sallar magariba ina cikin yin azkhar Suhaima ta yi sallama ta shigo zama ta yi tana faɗin “To in kin gama sai in miki” Kallonta na yi sannan na ce “Wai ke da gaske kike? Ni fa ban damu da wannan fenti da ake yi wa fuska ba” Gyara zama Suhaima ta yi tana faɗin “Tabɗi! Manyan baƙi Daddy zai yi kuma ma ba ki ga kwalliyar da Momy ta yi ba, Auntynmu ki zo kawai in gwangwaje ki da kwalliya dan in wanke fushin da Daddy yake yi da ni Please” Ganin lallai da gasken gaske take yi ya sa na ce mata “Bari na yi sallar lsha'i to” Ina idar da sallah kuwa ta sani gaba da fente-fenten fuska kusan minti goma sha biyar muna abu ɗaya dirin motar shi ya sa ni faɗin “Wai har yanzu?” Cikin sauri Suhaima ta ce “Sorry yanzu zan ƙarasa miki..” Ai bata rufe baki ba sai ga kiran wayarshi “Kin gani ko? Kwalliyar ya isa haka Please ban so ya zo yana jirana gwara ni na jira shi” Suhaima ta ce “Ai na gama ma ɗaurin ɗankwali kawai za mu yi” Leshi wanda ake yi wa ɗinkin zamani riga da siket wanda ya ji adon stone na fito da shi na saka bayan na shafa turare masu sanyin ƙamshi “Gaskiya Auntynmu turaren ki suna min daɗi sosai” Ɗan murmushi na yi tare da faɗin “Bari mu gama hidimar baƙi sai na ware miki wasu” Cikin murna ta ce “Wow! Ina godiya sosai” Tana gama ɗaura min ɗankwalin ta ce “Haɗuwa! Tsakani da Allah kin fito cas! Kin yi acan-acan bari mu yi hoto yanzu na turawa Daddy” Ba laifi kam, dan ko ni ma na yaba da kwalliyar. Haka ta ɗauke mu hoto sannan ta yi min, nan take kuwa ta tura mishi.


Daidai lokacin da yake shirin sake kiran wayarta ya ga saƙon Suhaima buɗewa ya yi yana kallon hotunan ƙuri ya yi wa wayar sai yau ta fito fess a Amariya miƙewa ya yi tare da nufo ɗakin. “Assalmu Alaikum!” Kallon juna muka yi, aikuwa Suhaima me za ta yi bayan dariya. Amsa sallamar muka yi sannan Suhaima ta kama hanyar fita bayan ta yi mini raɗa a kunne, tana kallon Daddy da ya ɗauke kanshi daga kallonta domin har yanzu da saurin fushinta a ranshi bai huci ba. Harɗe hannuwa ya yi a ƙirji ya tsaya ƙare mata kallo “Alhamdu Lillah Ma Sha Allah! Very nice” Ya faɗa tare da haɗa 'yar manuniyar yatsarshi da babban yatsar alamar ta yi kyau sosai. Murmushi kawai na yi sannan na fara taku ɗaɗɗaya ina zuwa inda yake tsaye daidai kafaɗar shi na saka kaina tare da buɗe wayata na shiga Camera. Ji kake cat-cat na ɗauke mu hoto. Ina shirin barin jikinshi ya sake kamo ni tare da kai hannuwanshi ƙugunta yana zagayewa kanshi ya saka a wuyanta yana shinshinar ƙamshin jikinta kana ya dawo fuskarta, ɗan ƙaramin bakinta da ya sha man baki sai maiƙo yake nan ya dire ido tare da kai bakin nashi kan lips ɗinta yana wani irin sauke mata zazzafan numfashi runtsa ido ta yi tare da suke ajiyan zuciya daidai lokacin da ya fara tsotsar lips ɗinta.


_Shin ko burin Fiddoh zai cika na auren mahaifin Suhaima? Yaya batun furucin da Hajiya Laraba ta yi wa Alhaji Aminu? Suhaima za ta cika burinta na Auren Dalil? Shin Dalil ɗin zai amince da ita? Zai zo ya amsa kiran da Alhaji Aminu ya yi masa? Ina labarin Emanuel? Yaya Hisham zai yi idan ya binciko kuma ya gano yarinyar da ya ɓatawa rayuwa ce take matsayin matar mahaifinsa? Shin zai haƙura da soyayyar da yake mata? Koma dai mene ne ku biyoni don jin yadda labarin zai kasance._


_Na kammala free PAGE. Don samun cigaban akwai Number asusu da kuma inda za ku tura shedar biya._


#Ayshajb
#Amnoor
#Sexstory
#Lovestory
#Sister'slove
#Paidbook
₦500
2389596965 Aisha Jubreel Zenithbank.
A turawa wannan Number shedar biya 09079740079
[5/9, 11:46 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
Romance Story.




®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. J.W. A★


Page 37.


Ku je ku yi Subscriber YouTube channel ɗinmu, mu ɗora littafanmu a can. https://youtube.com/@farinjinihausatv.5609?si=4jZwznZJHugMg4VU


Lokacin ɗaya naji wani irin kasala na sauko min musamman yadda yake lashe laɓɓan bakina cikin nutsuwa yana shafo wuyana. Gabaɗaya sai jikina ya sake yanayin da yake tsotsar bakina shi ya tuna min da wani Romantic series ɗin da nake kallo, buɗe tsumammun idanunta ta yi wanda suka sake narkewa tana mishi wani irin tsumamen kallo, sannu a hankali suka fara kissing junansu ɗakin ya yi tsit sai k'arar fanka da sautin saukan numfashinsu da kuma sautin kiss ɗin da ke fita, murya can ciki ta kira sunan shi bayan ta zare bakinta a nashi “Amnoor lokaci na tafiya” Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da hura iska a fuskarta kana ya ce. “Idan ina cikin wannan yanayi na shauƙi tare da 'yar matata mantawa nake da kaina, bare kuma wani lokaci. Mu je kar su suji mu shuru” Gyaɗa mishi kai tayi tare da daidaita nutsuwarta jin hannuwanshi ta yi cikin nata, a haka suka nufi falon. Tun dosowar su Hajiya Laraba ta kafe su da ido, wacce ta jima zaune tana jirar fitowarsu ta tsinewa Amnoor ya fi biyar cikin ranta, dan ta tsani yarinyar Alhaji Aminu ya fi mayar da hankalinsa gareta. Ko a ɗakinta yake muddin yaje sallamar Amnoor sai ya ci fiye da minti goma. Da wani irin kallo take bin hannayensu wanda ke saƙale cikin na junansu, lura da hakan ya sa na yi saurin zare hannu na daga nashi. Abban Amrah kuwa hararan shi ya yi. Ƙara sa wa ya yi wurin baƙin shi tare da gabatar musu da ni, nan muka gaisa sannan na fara ƙoƙarin zuba musu abinci Suhaima ce ta yi ƙoƙarin taya ni domin sun zuwanmu wurin Hajiya Laraba ta yi tafiyarta. Komawa gefe muka yi domin basu wuri nan Suhaima ta ce “Uhm Auntynmu da alama an tashi kan Daddy na da wannan kwalliyar, bayan daɗewa yana yaba kwalliyar a ɗaki, yanzun ma dai idanuwanshi ya ƙi barin kanki” Murmushi na yi tare da kallon inda yake nan kuwa idanuwana ya faɗa cikin nashi, kashe mishi ido na yi sannan na ɗauke kaina ina faɗin “Kai Suhaima ban da sa ido fa” Dariya ta yi tana faɗin “Ai gaskiya na faɗa Auntynmu”. Nan muka cigaba da hira har suka kammala lokacin da ɓakin za su wuce muka musu rakiya har wurin mota daman su uku ne, ɗaya daga cikinsu ne ya ce “Amariya ga wannan a yi haƙuri ba yawa” Karɓa na yi ina godiya. “Ai Aminu ba shi da mutunci a ce aure ana tafiya shekara biyu amma ba labari sai dai kawai muka ji a bakin Sa’idu gaskiya ba ka kyauta mana ba. Madam ni ma ga nawa a yi haƙuri mijin naki ne bai sanar mana ba” Dukkan su sai da suka min kyautar banjinta sannan suka ba wa Suhaima barka da sallah. Ciki muka dawo muna tattara kayan kwanukan domin Daddy ya tafi ya kai su masaukin su. Sallama muka yi da Suhaima ta nufi ɗakin mahaifiyarta nuna mata sarƙa da kuɗin da aka ba ta ta yi. “Mommy baƙin Daddy ne suka ba ni goron sallah, Auntynmu ma an bata nata...” Kallon da Hajiya Laraba ke yi mata ya sa ta yin shuru “Abokan kasuwancin shi sun ba wa amariyarshi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login