Showing 48001 words to 51000 words out of 69263 words
Chapter 17 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB
na da Suhaima kin ƙi yarda ya zan yi miki gaisuwar sallah fa kawai ta zo min wallahi bayan shi ba mu yi wani abun ba, kuma wallahi ba mu taɓa yin komai ba...”
Buɗar bakin Suhaima sai cewa ta yi “Ke kariya mun yi sai me? Kuma cewa ya yi na fiki daɗi da aji, saboda ke ko wani kare da biri binsu kike yi ko ba ka faɗa ba?” Suhaima ta ƙarasa maganar tana kallon shi , cikin zare ido Fiddoh ta ce “Haka ka ce ko?” A rikice ya ce “Suhaima ba mu yi haka da ke ba fa...” Wani irin cakumar junansu suka yi nan suka shiga naushe-naushe cikin haka Fiddoh ta buga kan Suhaima ya fashe. Jama'ar da suka taru ne wani daga cikin su ya kira 'yan sanda haka aka kwashe su gabaɗaya zuwa police station har shi Dalil ɗin. Wanda zuciyar shi ke harbawa domin Alhaji Aminu ba ƙaramin jan kunne ya yi mishi wancan lokacin ba.
Ina kwance a falo su Zaliha kuwa suna cikin gida suna ɗaukar hotuna a wayana daman ni na san abin da ya kawota kenan hoto. Daddy ne ya shigo direct ya yi wucewar shi wurin abinci yana faɗin “Madam a zo a ba ni abincin mana” Da ƙyar na miƙe saboda jikina da ke min mugun ciwo ga shi a hakan wai zan yi wani girkin saboda baƙin shi da za su zo. Kwanukan wanke-wanken ma na tattara su wuri guda ne ina jiran shigowar Zaliha dan haka zan sa ta dole sai sun wanke min dan ba iya wa zan yi ba. Jikin a kasalance nake zuba mishi abincin “Kina lafiya?” Yamutsa fuska na yi tare da faɗin “Wallahi na gaji ne sosai bayana kaman zai ɓalle” Cokali ya ɗauka yana faɗin “Allah Ya ƙara sauƙi sai ki sha magani ai” Abinci ya fara ci ni kuwa komawa na yi na kwanta a kujera, kallon wayarshi dake haske yai tare da ɗauka. Ai ban san lokacin da na miƙe da sauri ba jin ya yi mugun ƙwarewa da sauri na nufi wurin tare da kai kofin ruwa bakin shi ina shafa kan shi. “Sannu Daddy” Buɗe idanunsa da suka canza launi ya yi tare da miƙewa yana ƙwalawa Hajiya Laraba kira. Kallona yai tare da faɗin “Yi sauri ki kira min Hisham” To kawai na ce masa sannan na nufi hanyar fita. “Na manta dawo bai jin daɗi” Ajiyan zuciya na sauke domin haka kawai ban son ma raɓan inda Hisham ɗin yake, wanda tun zuwan na shi ba mu haɗu ba, “Wannan yarinyar? Hmmm! Sai na yi wa abun tufkar hanci wallahi, me raba ni da Suhaima ko...” Hajiya Laraba da ke fitowa ta ce “Me Suhaiman ta yi kuma? Oh! Ni Balaraba wannan yarinyar dai ba za ta bar ni in huta da ƙananun magana ba” Cikin ɓacin rai ya ce “Yanzu fa Hon. Sa’id ya kira yana sanar min da cewar an kamata suna station”
#Ayshajb.
#Amnoor.
#Sadstory
#Lovestory
#Sexstory
#Sisterslove
#Paidbook
₦500.
2389596965 A'isha Jubreel Zenithbank. A tura wa wannan Number shedar biya. 09079740079
[5/9, 11:46 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
Romance Story.
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. J.W. A★
Page 36.
*Domin ki ƙanwaty, Maryam Usman Turare much luv dear. Wannan page naki ne.*
Subscriber My YouTube channel Muna ɗora littafanmu a can. https://youtube.com/@farinjinihausatv.5609?si=4jZwznZJHugMg4VU
Saboda tsananin takaicin abin da Suhaima ta yi kasa tuƙa motar ya yi. Abban Amrah shi ya amsa yana tausar shi a kan ya yi haƙuri, “Ka san ɗan yau, ka haifeshi ne ba ka haifi halinsa ba, dan Allah ka danne wannan fushin naka...” Dakatar da shi Alhaji Aminu yai zuciyar shi na wani irin ƙuna “Kamar ni da girmana, da mutuncina, a ce kullum ina hanyar karɓo Suhaima a police station? Wannan yarinyar ta isheni! Karatu taƙi ta mayar da hankali ta yi shi, ba damuwa ba dai aure take so ba? Zan yi mata tun kafin ta ɗauko min abin kunya, tun kafin ta watsar min da mutuncina a idon jama'a zan aurar da ita” Hon Sa’id dai shuru yai mishi domin idan Aminin nasa ya ɗau zafi ba ya jin lallashi. Haka suka isa station ɗin. Cikin girmamawa 'yan sandan suka shiga kawo gaisuwa tare da musu jagora wurin mai gidan nasu. Suna fitowa Abban Amrah ya ce a sake su duka. Haka aka buɗe su suka fito, kallo Dalil ya yi rai a haɗe ya ce “Ka zo gida ka same ni” Sunkuyar da kai Dalil ya yi zuciyar shi na bugawa da jin furincin Alhaji Aminu. Fiddoh kuwa ba abin da take sai kallon Alhajin tana zabga uban murmushi. Ko zafin bakinta da ke a fashe ba ta ji domin ganin Alhaji Aminu da jin muryan na shi ya tafi mata da raɗaɗin komai farinciki take ji a ranta tare da wani irin shauƙi. Kallon Suhaima ta yi tare da lashe baki harda lumshe ido ta yi kana ta ce “Sexy guy...” Naushi Suhaima ta kaiwa bakinta sai dai kafin hnanun nata ya isa Fiddoh ta riƙe tana mata wani irin banzan kallo, “Ki shiga nutsuwarki domin na kusan zama Maminki, zan auri mahaifinki dan shi ne murdin raina, shi ne mafarki na, kuma farincikin rayuwata” Cikin ihu da jin zafin furucinta Suhaima ta ce “Shashasha ki ma daina wannan tunanin domin fasiƙa ƙazama mara asali irin ka ba ta da gurbi a gidanmu, Uban ki ma ɓarawo ne an gaya miki ban da labarin ki ne? wallahi tallahi kika sake irin wannan maganar saina illata ki!” Riƙe haɓa Hon. Sa’id ya yi yana kallon ikon Allah, Alhj Aminu kuwa wani ƙazamin kallo ya watsawa Fiddoh tare da jan dogon tsaki ya fisgi hannun Suhaima suka fita. Da sauri ta biyo bayansu tana faɗin “Koma dai mene ne saina mallake...” Ba ta ƙara sa maganarta ta ba Abban Amrah ya tari numfashinta da faɗin “Hauka kike yi domin ba abin da zai yi da ballagazar karuwa irin ki, matar shi ta farko naushi ɗaya za ta miki ta ɓalla ƙasussuwan jikinki, ita kuwa Amariyarsa ba ta bar ƙofar da wata mace za ta burge mijinta ba, idan za ki je ki nema ɗan' iska irin ki gwara tun wuri ki kama hanya domin kuwa a nan kin makaro, ba ki da gurbi, kariya kawai. Kuma wallahi idan na sake samun labarin kina bibiyar shi ba za ki ji da daɗi ba” Sai da Abban Amrah ya yi mata tas sannan ya shiga mota suka baɗe ta da ƙura. Wani irin ihu Fiddoh ta saka tare da zubewa bisa guiwowinta tana sakin wani azababben kukan da tun da take ba ta taɓa yin sa a rayuwarta ba, domin ba'a taɓa yi mata ƙazamin zagi da cin fuska irin wanda Abokin Alhaji Aminu ya yi mata ba. Ta yi kukan da tun da take a duniya ba ta taɓa yin irinsa ba, sannan ta kama hanyar gida tana shiga gidan ta faɗa jikin Maman su da ke zaune tana aiki “Subahanallahi Firdausi! Me ya samu fuskar ki? Wa ya taɓa min ke? Wa ya saka ki kuka?” Lokaci ɗaya Maman su ta jero mata wannan tambayoyin, cikin wani irin sheshsheƙan kuka me shiga jiki ta ce “Maman mu faɗa muka yi da yarinyar Alhaji na, Maman mu yau an ci mutuncina an yi mini zagin da tun da kika haifeni ba'a taɓa yi mini irinsa ba, Maman mu a gaban Alhaji na, amininsa ya zage ni, ya kirani da karuwa, ballagaza, ɗiyar sa ta yi min gorin dangi Maman mu wai ba mu da asali... Da sauri Maman Nafisa ta rufe bakin Firdausi hawaye na zubo mata. Cire hannun Maman tasu ta yi tare da faɗin “Akwai wanda ya isa ya kaucewa ƙaddarar sa ne Maman mu? Ba yin kaina ba ne! Zuciyata ce take son shi, ko laifin ne dan na so shi? Wallahi Maman mu ina son Alhaji sosai ban taɓa jin zafi da ƙunci irin na yau ba, kuma wallahi ko dan na baƙanta zuciyar Suhaima saina auri mahaifinta, ni suka kira da karuwa! Wallahi saina addabi rayuwarsu hatta uwar ta ba zan sararawa ba” Runtsa ido Maman Nafisa ta yi tana jin zafin abin a zuciyarta musamman ma kalmar *Karuwa*. “Ki yi haƙuri Firdausi, ki fita rayuwar... Miƙewa Fiddoh ta yi zaune tare da harɗe ƙafafunta tana faɗin “Wallahi tallahi ba zan barsu ba, muddin da rai a jikina saina addabi rayuwar Alhaji kuma saina aure shi” Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata. Matsowa Zaliha ta yi jikin Maman Nafisa tana sauke ajiyan zuciya domin ita ma abin da aka yi wa 'yar'uwatata ya taɓa zuciyarta tagumi ta yi tare da faɗin “Ina danginmu suke? Mu 'yan asalin ina ne? Domin ni ma an sha goranta min kuma har gobe ana yi mini gorin dangi dan Allah Maman mu ki faɗa mana” Juyar da kai Maman Nafisa ta yi tare da faɗin. “Na so a ce Nuriyya na daga cikin waɗanda za su saurari wannan labarin”.
****
Mutanen Bangaran ( Makiyayan shanu ) ko Larabawan Chadi rukuni ne na ƙabilun Afirka a yankin Larabawa da ke zaune a yankin Sahel na Afirka musamman tsakanin tafkin Chadi da kudancin Kordofan, wanda suke da mutane sama da miliyan shida. Ana kiran su Bangare a Sudan, Abbala, da Har ila yau, an san shi a gabashin Chadi da iyal DJINED da kuma Shuwa Arab a Kamaru, Najeriya da yammacin Chadi. Kalmar Shuwa ance ta samo asalin ne daga yaren Kanuri.
Bangaran suna magana da harsuna dabam dabam, wanda aka sani da Larabcin Chadi. Duk da haka Bangāran na Kudancin Kordofan, saboda tuntuɓar masu zaman kansu da kuma Larabawan ƙasar Sudan makiyayan raƙuma ne na Kordofan, ya haifar da tasirin Larabci na Sudan a cikin yare na wannan yanki. Har ila yau, suna da salon rayuwa na yau da kullum na al'ada, kiwon shanu, kodayake a zamanin yanzu da yawansu suna rayuwa irin na kowanne mutum. Amma duk da haka, a tare ba dole ba ne dukkansu su ɗauki kansu al'umma ɗaya, wato, ƙabila ɗaya. An gabatar da kalmar "al'adar bangaran a shekarar alif 1994 ta Braukämper.
Amfani da kalmar bangāran a siyasance a Sudan yana nuni da gungun ƙabilu masu magana da harshen Larabci masu alaka ta kud da kud da ke zaune a yankunan kudancin Darfur da Kordofan wadanda suka yi cudanya da 'yan asalin mutanen dake zaune da su a yankin, a cikin musamman mutanen Fur, mutanen Nuba da fula . Da yawa dai kawai zuriyar ƙabilun 'yan asalin da aka riga aka yi su ne kawai. [11] Mafi yawa daga cikin "Larabawa Bangaran" suna zaune a Chadi da Sudan, tare da 'yan tsiraru a Najeriya, Kamaru, Nijar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Sudan ta Kudu . Wadanda har yanzu makiyaya ke yin hijira a kan lokaci tsakanin wuraren kiwo a lokacin damina da wuraren koguna a lokacin rani.
Harshensu na asali dangane da masana ilimi na da sunaye daban-daban, kamar Larabci na Chadi, waɗanda aka ɗauko daga yankunan da ake magana da harshen. A mafi yawancin karni na 20, wannan yare da masana ilimi suka san shi da "Shuwa Arab", amma "Shuwa" kalma ce ta yanki da kuma zamantakewar al'umma da ta fada cikin rashin amfani a tsakanin masana ilimin harshe da suka kware a cikin harshen, wanda maimakon haka suna kiransa "Larabcin Chadi" ya danganta da asalin masu magana da harshen da ake tuntubar su don wani aikin ilimi.
Zuriyar gidanmu sun aminta da auren zumunta wanda suka taso suka taso tun iyaye da kakani. Sun cigaba da wannan auratayyan tsakanin 'ya'yensu har jikoki a haka suka fara yawa har suka zama babban zuri'a a garin Sudan. Asalin sunana Hamnah kamar a lokacin da na taso kowa so na yake yi saboda tsananin kyau da nutsuwar da nake da shi, sai dai ban cika kula mutane ba duk da sukan biyoni har gidanmu kasancewar na san gidanmu ba'a ba wa bare sai ban mayar da hankali kan maneman da suke min tururuwa ba, ilimi daidai gwargwado muna da shi amma ni karatuna ba mai zurfi ba ne. Ina da yayye mata da maza wanda suma duk cikin gida aka bayar da auren su muna da wayewa kasancewar dayawa daga cikinmu sun yi ilimin boko akwai masu aikin gwamnati, da masu kiyon shanu a cikin mu, gidan mu ya kasu sashi daban-daban kuma dukkan 'yammatan gidan kowacce tana da sana'ar yi, kamar ni da nake aikin turare kasancewar ina son ƙamshi sosai, akwai yayata Saliha wacce a wurinta na koya turaren kasancewar ita shago ma take da shi na turare da na koyar da abubuwa da dama tana gyaran amare, dan mijinta ya rasu wanda shi ma ɗan nan cikin gidanmu ne, yaron yayan mahaifinmu ne, ya rasu ya barta da ɗa, yanzu zaune kawai take tana sana'arta duk da a cikin 'yan'uwa akwai masu sonta sai dai taƙi yarda ta yi wani auren tana harkan kasuwnacinta tare da rainon ɗanta. Ashraf shi ne yayan mijin Saliha wanda ya rasu, shi ne wanda aka yi mana baiko duk da babu wata shaƙuwa ta soyayya tsakaninmu saboda ba nan ya yi karatunsa da rayuwarsa ba, domin ya tsallake ƙasa har Najeriya ya zo garin Barno nan ya yi karatunsa inda ya samu sani daga Akur'ani sosai, amma akwai fahimtar juna sosai a tsakaninmu, sannu a hankali lokaci ya fara tafiya har aka sanya bikina da Ashraf wanda ya tattaro ya dawo gida inda yake da garken shanu yana kiwon su, sai da biki ya zo daf kwatsam na haɗu da Saleh duk kyau da haɗu war da ake cewa ina da shi sai na rena kaina, domin shi Saleh babu macen da ba za ta so ya kasance matsayin mijinta ba, ta ko'ina ya haɗu ne matsalar shi talaka ne futuk, domin mu kan gidanmu akwai rufin asiri sosai, amma ba wai masu kuɗi can ba ne. Tsautsayi ya sa muka fara soyayya ba tare da kowa ya sani a gidanmu ba, ga shi da farin jinin 'yammata kowa son shi yake yi saboda tsananin kyawunsa. Da tafiya yai tafiya ne Ashraf ya lura da sauyi domin gabaɗaya hankalina ya karkata ga waninsa aikuwa da ya yi bincike ya gano da Saleh nake soyayya ran shi ya ɓaci sosai nan aka sake matso da bikina, hankali na ya tashi sosai domin a lokacin ina ƙaunar Baban ku sosai, haka muka rabu ba dan muna so ba, aka yi aure na da Ashraf. Dan so kan Ashraf yana so na sai dai shi irin mutanen nan ne masu bauɗaɗɗen halin tsiya da shegen ra'ay wanda ba ka isa ka canza ra'ayinsu ba, lokacin da na fahimci yana amfanin da sanin da ya yi a Alkur'ani wurin yin wasu abubuwa na tsubbu na so dakatar da shi amma sai ya gaza fahimtata daga wannan lokaci zaman lafiya ya yi ƙaranci a tsakaninmu domin ko a shimfid'a ba na yarda da shi, shi kuwa baya samun nutsuwa muddin bai keɓance da ni ba, dan tun daren farkon mu yake nan-nan da ni. Bayan ƙaura ce masa da na yi sai na fara ƙyamatar shi saboda ya yi nisa a harkan tsubbun da yake yi. Zama dai ya ƙi yin daɗi sai da ya sake ni, lokacin ina da ƙaramin ciki wanda ni da shi duk ba mu sani ba, ba don ya so ba ya saka shi a gaba da fitina sai da ya sake ni daga baya ne na fahimci ina da ciki. Babana kuwa ran shi ya ɓaci sosai nan ya zuciya ya ce lallai in koma ɗakina ni kuwa na kafe ba zan koma gidan shi ba muddin ba zai bar wannan sana'ar da yake yi ba. Dan a lokacin ina ji da taurin kai ni ma ga kafiyar tsiya, dan in na ce zan yi abu to fa babu shakka sai na yi, kamar dai ke. Ta kalli Fiddoh wacce ita ma kallon Maman su take. Zaliha ta ce “To cikin kuma fa? Ya aka yi da shi?" Ajiyan zuciya Maman Nafisa ta yi sannan ta ci gaba da ba su labarin. Da Babana ya kafe kan na koma na yi rantsuwar ba zan sake zaman aure da Ashraf ba, bayan haka na je na samu Ashraf na ce mishi ko ya saka ba ki a barni na auri zaɓin raina ko kuma wallahi cikin da nake da shi in zubar da shi. Nan hankalin shi ya tashi sosai ya dinga lallashina da in yi haƙuri kar ina zubar mishi da ciki, ya yarda a kan zai saka baki Babana ya ƙyale ni amma na bari sai na haihu sai na ba shi abin da na haifa tukun, nan ma na ce ba zan ba wa matsafi jaririna ba, ya buga ya raya na ce ban san zancen ba da jariri ba. Haka dai ya yi magana da ke shi idan ya yi wa baban mu magana ya na jin maganarsa sosai. Amma baban mu ƙarshe korata ya yi ya ce in je in samu Saleh shi babu ruwan shi da ni, kuma bai yarda in zauna cikinsu ba, in je in yi auren tun da shi na zaɓarwa kaina. Nan fa hankalina ya tashi na rasa inda zan saka raina, dan ya ce kar kowa ya yarda in zauna a gidan shi. Ƙarshe gidan su baban ku na tafi, yaya Ashraf shi ya ce in je can a nan na samu Uwar goyon shi kasancewar shi maraya ne. Nan muka zauna tare lokaci-lokaci yaya Ashraf yakan kawo min kayan abinci duk don na kwantar da hankali na haifi cikin jikina lafiya domin ya ƙwallafa rai a kan ciki, ni kuwa in ya zo, kullum da baƙar maganar da nake faɗa mishi dan ta silar shi mahaifina ya kore ni, saboda mahaifiyata ba ta raye, domin tun ina ƙarama Maman mu ta rasu. Duk dai bai damu ba, shi dai yana hidimtawa cikin, Saleh kuwa tun da na zo gidan ba mu haɗu da shi ba. Domin Uwar riƙon na shi ta ce har sai na haihu an ɗaura mana aure kafin muga juna. Lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa