Showing 18001 words to 21000 words out of 69263 words

Chapter 7 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB

Aisha JB   

22 Aug 2025

304

ki shirya kawai ki je wurin mijinki ba inda za ni"
Juyowa ta yi tana kallon Mamansu da ke zuba turare a kwalba, "Ayya Mamanmu dan Allah ki ce mata muje tare" Ba tare da ta ɗago kanta daga abinda take yi ba ta ce "Ku je tare da Zaliha" Zaliha da ke taya ta zuba turaren ta zunɓuro baki tana mita ita tana aiki za a ɗaga ta. "Ai ko na je wallahi ba zama zan yi wurin mata da miji ba" Ta faɗa tana share hannunta a jikin hijjabin da za ta saka, kallon yadda Nuriyya ke shirin fita ba tare da ta shafa mai ko turare ba "Eyye! Dama haka ake zuwa wurin miji bagajan-bagajan ba shafa mai bare hoda ko turare? Kuma da wannan uban hijjabin za ki tafi sai ka ce matar malam?" Dakatawa Nuriyya ta yi tare da juyowa tana kallon yanda take hijjabin da take Sallah ne, ba shi da wani ainu. Bata aune ba ta ji Fiddoh ta buɗe turare tana zuba mata. Cikin faɗa Maman su ta ce "Wai Firdausi lafiyar ki ? Turaren nan fa an riga da an biya na gama musu haɗin kayan amare ne fa.."
"To ai ita ma amariyar ce" Fiddoh ta faɗa tana dariya tare da kallon yanda Mamansu ta haɗe fuska "Yi haƙuri Mamanmu ni zan biya sai a musu wani shi ke nan? Ku kuma tsayuwar me kuke? Ko se Baba ya dawo ne za ku tafi?" Hannun Zaliha ta riƙe suka fita Zalihar ce ta yi Sallama sai da aka amsa musu sannan suka shiga.
Zama suka yi kan ledar da ke malale ƙasan ɗakin cike da ladabi Zaliha ta gaishe su da murmushi suka amsa domin yabawa da nutsuwa tare da tarbiyyanta abin ya burgesu ƙwarai. Nuriyya kam har yanzun kanta na ƙasa da murmushi Baban Amrah ya kalli Nuriyya tare da taɓa Aminin nasa nan shima ya ɗago yana duban inda take, mutuwar zaune yai yana sake kallonta "Ita ce fa!" Ya faɗa yana kallon Baban Amrah wanda ya miƙe tare da yafito Zaliha suka fto tare da nufar wurin mota yana tambayarta sunan ta.
"Suna na Zaliha Hamisu Saleh"
"Ni ce name amma kina mace na ji ki da turaren maza kuma haɗi na musamman" Turo baki ta yi tana faɗin "To ba aiki ɗurawa nake yi ba, shi ne Mamanmu ta ce se na rako Aunty Nuriyya"
Dariya domin yanayin da yarinyar take magana ya burge shi sosai haka suka ci gaba da hira tana zuba mishi surutu da shirme shi kuwa yana biye mata can dai ya tambaye ta game da karatu shuru ta yi masa ba tare da ta ba shi amsar ba.
"Turaren na siyarwa kuke yi?"
"Eh kuma harda haɗin amare Mamanmu ta iya da na maza ma duka ana yi"
"Je ki kawo min su na gani" Da gudu ta shiga gida ta ɗauko mishi kwandon da take zuwa talla da shi.
"Lallai Mamanmu ta iya turare masu kyau zan so mu yi magana da ita domin haɗin ya yi min kyau, kodayake zan turo Amrah sai su yi magana.."
"Amrah? Aunty Amrah dai da na sani ƙawar Auntyna?"
Murmushi yai mata gwalo ido ta yi tana faɗin "Taɓ! Abun da mamaki wallahi to shi wancan mijin Aunty na ya alaƙarku yake da shi?"
"Alh Aminu shi ɗin Amini na ne tun yarinta komai namu tare muke yin sa" Daga haka hira ya ɓarke tsakaninsu Zaliha nata zuba mishi shirme yana murmushi.


"Bisimillah ta so ki zauna a nan" Ya faɗa tare da nuna mata gefen sa. Girgiza kai ta yi tare da ƙara takurewa da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce "Ina yini.."
Maƙalewa sauran maganar tata yai jin ya zauna gab da ita, ɗagowa ta yi da sauri tare da watsa mishi Lulu Eyes ɗinta da ya tara ruwa, murmushi ya sakar mata tare da riƙe fuskarsa da hannun biyu yana kallon kyakkyawan siririn fuskanta. "Kina mamaki ko? A baya na sha neman ki kamar zan yi hauka, domin an ƙidaya min lokaci na fito da matar aure har wa'adi ya cika ba tare da na ganki ba, lokacin da muka haɗu sai na ga gabaɗaya tsoro ne ke ɗawainiya da ke, da na tuntuɓi ɗiyata 'yar wajen Aminina Amratullah ita take sheɗamin cewar ke matar aure ce domin an ɗaura miki aure watanni baya, na ji babu daɗi nan na yanke shawarar zan amshi zaɓin da mahaifiyata ta yi mini sai gashi a she ke ce, ina ta cika ki da surutu ba tare da na sanar da ke waye ni ba. Sunana Alh Aminu ni haifaffen nan garin Abuja ne, ina da mata ɗaya wacce ta kasance 'yar'uwata ce, yaranmu biyu Hisham shi ne Babba wanda a yanzu yana ci gaba da karatunsa a ƙasar waje, se Suhaima. Matata tana matuƙar so na kuma tana da kishi sosai bana wasa da duk wani abun da ya shafi iyalina musamman Ummata ina son su.
Ni ɗan kasuwane ina ƙasuwanci har ƙasashen ƙetare, anan ina da shagunan sarƙoƙi, ni kaɗai nake ta magana ba tare da kin ce min komai ba"
Ɗan matsawa ta yi ganin yadda suke gab da juna, sake ƙanƙame jikinta take yi domin gabaɗaya a takure take "Babu abinda zan yi miki" Ya faɗa tare da matsowa ya kamo hannunta ƙara ta saka tana ƙoƙarin fisgewa nan da nan ta shiga rawar jiki "Subhanallahi!" Ya faɗa tare da riƙe ta sosai a jikinshi yana mamakin wannan lamarin nata. Wayarshi ya ɗauka tare da kiran Baban Amrah yana faɗin ya tura mishi Zaliha. Kallon Zalihar yai tare da faɗin "Har ka gama shan love ɗin ne da wuri haka?" Tsaki Alh Aminu yai tare da kashe wayar sannan ya ɗauketa ya ɗorata akan kujera kana ya zauna kusa da ita.
Kuɗi masu yawa Baban Amrah ya miƙa mata tare da faɗin "Ki bawa Auntyn ki, domin zuwan gaggawa ne bamu samu munyi tsaraba ba" Maƙe kafaɗa ta yi tare da ƙin karɓa "Wallahi idan na amsa duka Mamanmu za ta yi min" Cike da yabawa da tarbiyyanta ya ce "Idan kika ce mata mijin Auntyn ki ne ba za ta yi komai ba, in kuma taƙi ki ajiye min" Da ƙyar dai ta amshi kuɗin sannan ta nufi ɗakin.
Kallonta yai tare da faɗin "Zan tafi amma zan dawo dole zan kaiki asibiti domin a duba lafiyar ki, ki kula da kanki" Ya faɗa tare da kai bakin shi goshinta yai mata kiss yana gyara gaban rigar tasa. Shigowar Zaliha ya ba shi damar fita kanta har yanzun a sunkuye yake sai da ya kusan fita sannan ya juyo ya yi daidai da ɗagowar da ta yi, nan idanunsu ya faɗa cikin na juna, da sauri ta ɗauke kanta daga kallon shi sannan ta miƙe ita ma jiki a sanyaye ba ta san ya ajiye mata kuɗi ba sai da taga Zaliha ta ɗauko tana miƙa mata. "Laa Aunty ga kuɗin ki manta da su" Juyowa ta yi tare da kallon kuɗin wanda ya kusan talatin. Haka suka shigo cikin gida nan Maman su ta dinga faɗa ganin kuɗi har dubu hamsin "Mamanmu wallahi ban san ya aje min kuɗin ba.."
"Ke ba ni kuɗin tun da ba ta so.." Baban su ya faɗa tare da kai hannu zai amshe, da sauri Zaliha ta faɗa kan Maman su tana faɗin "Wallahi ba zan bayar ba, ai ina kallo Baban Amrah ya ba ka kaima" Fita yai a ɗaki yana faɗin yara duk babu me tarbiyya da zai dinga faɗar magana cikin ladabi da biyayya.


"Ji nai kana ƙamshi da alama dai sai da ka angwance.." Taka burki yai da ƙarfi yana kallon shi tare da faɗin "Allah zanci abu kazan ka.. Haba! Duk ka isheni da surutu da ke ni na rako jaraba duniya dole daga zuwa na hmm" Sai kuma yai shuru domin idan ya biye masa haka zai yi ta zolayar tasa a haka suka nufi gidan Aminu suna tattauna yanda tariyar zai kasance anan ne yake sanar mishi halin da take ciki wanda ya rasa gane mene ne, sun tsayar da maganar akan zai samu Amrah su tattauna yayin da Hon. Sa’id ya ce ya sanar da Larai halin da ake ciki.
A gefen guda kuwa ɗaya daga cikin 'yan group ɗin su ne ta samu labarin Alh Aminu ya yi aure ba tare da sanin matarshi ba nan fa aka kafa mitin tare da laluɓo number Hajiya Larai wacce take can Legas tana duba shagon kayan ta Fiddoh ce ta yi kiran a ɗaya daga cikin wayar da suke amfani da shi. Ganin baƙuwar number ya sa ta ɗauka tare da kara wayar a kunnenta tana faɗin "Hello!" Daga ɓangaren Fiddoh ta ce "Ki duba mun tura miki account ɗin mu ki turo da miliyan ɗaya mu kuma za mu faɗa miki abinda ke shirin faruwa daga ɓangaren mijinki" Tana gama faɗar haka ta kashe wayar jiki na rawa ta tura musu kuɗin murmushi Fiddoh ta yi tare da miƙawa Na'ilah wayar don ita ta gama aikin ta. "Ki yi gaggawar barin Legas ki dawo gida domin mijinki na shirin angwancewa domin tuni an ɗaura aure" Tana kawowa nan a zancen nata ta datse wayar tare da kashewa bayan ta ajiye layin a ƙasa. Zubur Hajiya Larai ta miƙe tana faɗin "Jar uban can! Ni ce za a yi wa kishiya? Duk yaushe aka yi wannan ban sani ba?" Jiki na rawa ta ɗauki waya tare da kiran layin shi sai dai baya shiga, haka ta siyi tikiti ba shiri ta kamo hanyar Abuja.


***
Yana ɗaya daga cikin ɗalibai masu hazaƙa da malaman ke ji da shi, nutsuwa haɗe da tarbiyya gami da biyayyarsa ne ya ƙara mishi ɗaukaka da farin jini, duk inda ya gifta nuna shi ake tare da yabon ƙwazo da hazaƙar sa. Mata da yawa suna bin sa daga fararen fata zuwa ga 'yan'uwansa 'yan Nigeria da suke tare a wurin sai dai ko ɗaga kai ba ya yi balle ya kulasu. Mace ɗaya ce ta tsaya masa wacce a kullum cikin mafarkinta yake kuma kullum cikin da-na-sani abin da ya aikata mata yake, kusan kullum suna waya da abokansa wanda su ma tun faruwar lamarin iyayensu suka ɗaga su a ƙasar kasancewar ta'asar da suke yi wa 'ya'yan mutane sai gaba yake yi, duk da haka ba su daina ba, domin sex ya zame musu tamkar ruwan shan su wadda in har ba su sha shi ba ba su jin daɗi iskancin na su ya shahara ne ya yi da suka samu gurbin karatu a jami'ar London inda suka haɗu da gogaggun tatattun 'yan iska wanda suka yi ƙaurin suna a harkan 'SEX GAME' idanunsu ya Buɗe fiyye da baya dan suna iya kwanciya da mace fiye da ɗaya a lokaci ɗaya duk da haka ma maneji suke yi dan har yanzu ba su samu mace kamar yarinyar can ba. Juyi yai a gadon da yake tare da runtsa idanunshi hoton abinda ya faru yana sake dawo masa tamkar yanzu aka yi sa ihu da magiyar da take mishi ne ya sake cika dodon kunnen shi.


Saura ƙiris free page zai ƙare.


Wannan Littafin na kuɗi ne domin kasancewa cikin group za a tura ₦500 ta wannan account ɗin 2389596965 Aisha jubreel Zenithbank. Sai a tura shedar biya ga wannan Number 09079740079


#Amnoor
#Sadstory
#Destiny
#Hotlove
#Romance
[5/9, 11:43 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_


®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. W. A★


H-P Place Group.


Free page 23_24


Kuje ku yi Subscriber Channel ɗi na a YouTube. FARIN JINI HAUSA TV. Domin sauraron ƙyatattun littafanmu.


*Following me on Wattpad: ayshajb*
*Arewabooks: ayshajb*


Kuje Arewabooks za ku samu littafaina a can.




A kasalance ya sake buɗe idanun nasa wanda ya fara sauya launi saboda yanayin da yake ciki, wayarshi ya laluɓo tare da kiran Hajiya Larai wacce take ƙoƙarin saukowa daga matakalan jirgi ƙarar wayar tata ba ƙaramin kiɗimata ya yi ba, nan take zuciyarta ya fara dukan tara-tara buɗe jakarta ta yi sannan ta ɗauko wayar hannunta na rawa a hankali kuma ta sauke gwauron numfashi ganin Hisham ne me kiran nata zama ta yi a kujeran da ke kusa da ita kana ta kara wayar a kunnenta ba tare da ta ce masa komai ba, dan ta san maganar tasa ba zai wuce wannan yarinyar da suka hake mata ba, ita ta rasa wane irin masifa ne yake bibiyarta ɗanta yana neman haukacewa a kan yarinyar da bata san wace ce ba, shi ma kanshi bai san wace ce ita ba, amma duk ya damu a kan lallai sai ta binciko mishi ita, bari yau za ta yi maganin abun. "Barka da warhaka Mome ya gida da su Hajiya?" Amsa mishi ta yi da faɗin "Kowa lafiya ya karantun naka ina fatan kana mayar da hankali?" Tamkar yana gabanta ya gyaɗa mata kai kafin ya ce "Mome wai har yanzu ba a samo inda yarinyar nan take ba ne.." Miƙewa ta yi daga zaunen da take ganin drive ya ƙaraso tare da faɗin "Zan ci mutuncin ka muddin ka sake min wannan maganar! Hisham ka fita idona na rufe daga kai har uban nan naka kun saka ni gaba da fitina to wallahi ba za ku kashe ni da raina ba karka sake kirana muddin wannan maganar za ka yi mun" Tana kawowa nan ta kashe wayar tana jan tsaki tare da da ka ma driven tsawa "Dalla taka mota mu tafi ka wani tsare ni da ƙananun idanu kaman fincen ƙuma!" A gefen Hisham kuwa bin wayar ya yi da ido yana jin wani abu ya tokare masa ƙahon zuciyarsa.
Hamdala ta yi a ranta ganin motar tasa a gida da sauri ta fito ta nufi cikin gidan a falo ta jefar da jakarta kana ta nufi ɗakin sa. Daidai ya fito toilte ɗaure da towel a ƙugunsa kenan ta shigo kamar wacce aka jeho ta ba tare da ta yi sallama ba, ɗauke kanshi yai daga kallonta ita kuwa ganinsa a haka ya sa ta ji wani yanayi matsowa ta yi kusa da shi ba tare da ta ce komai ba bayan idanunta da ke yawo a jikinsa kaucewa yai domin ya lura so da abin da take son yi, sai dai duk yanda ya so ƙin abin sai da ta samo kanshi domin ta yi matuƙar kewarsa da ma shima a 'yan kwanakin nan haƙuri yake musamman ma idan ya je gurin Nuriyya duk sai ya ji shi a takure nan fa suka lula duniyar sama sai da ta fara mishi ƙananun mita kafin ya ƙyaleta tare suka shiga wanka sai da ya sake kimtsawa sannan ya zauna yana kallon yanda take ta murmushin yaƙe ga dukkan alamu kuma akwai abin da take son faɗa masa sai dai yanda ya yake ɗauke kai tare da sake tamke fuskarsa ne ya hanata yin magana. Abinci ta zuba mishi tana kallon yadda yake komai a nutse wannan yanayin nasa ba ƙaramin burgeta yake yi ba. Wani murmushi ne ya suɓuce mata wadda ita kanta bata san na mene ne ba, ɗagowa yai yana kallon yadda take murmushi har sautin sa yana fita wanda rabon da ya ga irin haka a ɗau shekaru masu yawa "To fa! Wannan murmushin fa?" Ya tambaye ta tare da ajiye cokalin gyara zama ta yi tare da faɗin "Ina kallon kyakkyawan fuskar mijina mana, gani na yi ka ƙara kyau da cikar haiba, nutsuwarka ya sake ƙaruwa fiyye da na baya gaskiya ba ƙaramin dace na yi ba.."
"Dacen me?" Ya katse ta da faɗin haka "Samun gwarzon kamar ka mana" Wani murmushi yai tare da ture abincin gefe yana fuskantar ta ganin haka ya sa ta nutsu sosai tare da ƙura masa ido.
"Tun kwanaki na so in faɗa miki abin da ke faruwa sai dai kika ƙi ba ni damar hakan duk yanda na so mu yi maganar sai ki kauce da kawo min uzirin kina busy" Ɗan dakatawa ya yi tare da fesar da numfashi dan ya san halin abar tasa akwai ta da birkicewa musanman ma a kan batun kishiya. "Hmmm! Ina sauraron ka" Ta faɗa tana jin hawaye na cika mata idanu ya tabbata dai maganar aurensa da gaske ne kenan?
"Wata takwas kenan da Umma ta yi mini.." Ganin yadda ta zaro idanu tana kallon shi ne ya sa shi yin shuru "Ka yi shuru ka ci gaba da maganar ka" Murya a karye ta ƙarasa maganar tare da runtsa ido "Ta yi min aure" Buɗe idanuwanta ta yi da sauri nan hawaye suka zubo mata "Aure fa ka ce? Kai ƙaramin yaro ne da Umma za ta yi maka aure ba tare da akincewarka ba? Shi ya sa kake ta inda inda kana kauce min , kwana biyu ba ka kirana bare ka ji ya nake ashe aure ka yi kana can kana shagali da amariyarka wallahi sai Allah ya saka min zalunta ta da ka yi munafuki wai an maka aure ai ko yaro ba zai ɗauki wannan maganar taka ba bare ni da girmana da hankali na ka dinga faɗa min zancen da hankali ba zai ɗauka ba.."
"Ya isa haka! Ban son wani dogon magana dan Allah aure na ce miki an yi min ni ma ban sani ba sai da ta gama komai take sanar mun.." Cike da ɓacin rai ta dakatar da shi tana faɗin "Ka ce dai sai da kuka gama komai naku kake sanar min, munafuki ai dama haka halinku yake ba za ku taɓa iya canzawa ba, ba de aure ka yi ba? Hmm! Wallahi ka kuskura ka kawo wata 'yar isa gidan nan se na ƙona ku daga kai har ita in ba munafurci ba me ya sa ba a bari an yi auren a gaban idona ba sai da ba na nan shi ne za a rufe ni saboda ba a sona? Allah ya fiku kuma zai saka min wallahi ba zan ya fe ba!" Duk sai ya ji babu daɗi ganin yadda take ta ihu tana faɗin Allah zai saka mata kenan zalunci ne dan ya yi aure? Me ya yi mata da zafi take haɗa shi da Allah, shi ba mutum ba ne me son hayaniya da maimaita magana duk

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login