Showing 57001 words to 60000 words out of 69263 words

Chapter 20 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB

Aisha JB   

22 Aug 2025

313

ta sa yake yi, kafin ya yatsar da idonshi kan Hisham ganin haka ya sa Hisham ɗin ɗauke kan shi, mayar da kallon shi ya yi kan Balaraba aikuwa ta yi mishi murmushi tare da gyaɗa kai.
“Umma ai da kin kira ni sai in so gida in same ki...”


“Sai ga shi na zo da kaina ba, daman na zo in gargaɗeski ne, ashe ke mutuniyar banza ce ban sani ba? Ke har kin yi bakin da za ki kalli Balaraba kina mata rashin kunya? Saboda na aura mishi ke ba yana nufin ita ba na sonta ba ne, ban aura mishi ke don ki raba min kan ahali ba, Balaraba 'yata ce, ba za ki wargaza zumuncin mu ba, kuma ki ba ta haƙuri ban so in sake jin irin wannan maganar ina miki kallon mutuniyar arziki ashe ba haka ba ne” Haɗiye kukan da ke ƙoƙarin zuwa min na yi da sauri ina faɗin “Dan Allah Umma ki yi haƙuri hakan ba za ta sake faruwa ba, Hajiya ki yi haƙuri dan Allah” Cike da raunin murya ta ƙarasa maganar “Amma Umma da kin san abin da ya faru da ba za ki ce wa Amnoor..” Da sauri na kalle shi tare girgiza mi shi kai alamar kar ya yi magana.


“Da na san me? Ok kana goyon bayan matarka ta ci gaba da yi wa uwar 'ya'yanka rashin kunya tana juya Hisham kamar ƙaramin yaro, a girme Hisham ya girme mata don meye za ta yi mishi rashin kunya don ya tambaye ta abinci? To kar in kuma jin irin haka in ba haka ba zan saɓa maka daga kai har ita, abinci kuwa dole ki girka ki ba su tun da gidan uban su ne, kema ki yi ciki ki haihu mana in ya so sai ki juya baki ɗan...” Da sauri na ɗago ina kallonta hawaye cike taf idanuwana kuka ne yake ƙoƙarin ƙwace min amma ina ta dannewa. “Ki yi haƙuri Umma”


Iya kalmar da nake iya furta mata kenan domin ba zan taɓa yin musu da ita ba, Suhaima ma kuka take ganin yanayin da Amnoor ɗin ta shiga, ga shi babu halin ta yi magana dan Mommy da Hisham sun gargaɗeta sosai. Alhaji Aminu ma haƙurin ya shiga ba ta sai da ta gama yi wa Amnoor faɗa sosai sannan ta bar gidan. Miƙewa na yi tsaye, sai a yanzun na samu damar tsiyayar da hawayena. Hanyar ɗaki zan yi, ya yi sauri kamo hannuna tare da faɗin. “Balaraba kin kyauta! Ya yi kyau Allah kuma yana kallon ki, ki ci gaba da ɓata min tarbiyyan yara akwai Allah shi za sakawa Amnoor bisa sharrin da kika yi mata”


Yana gama faɗar haka ya fito riƙe da hannunta har wurin mota ya buɗe ya sakata sannan shi ma ya shiga, sai da ya fita a gidan sannan ya juyo gareta tare da kamo tafukan hannunawanta “Ban san kalaman da zan yi amfani da shi wurin ba ki haƙuri ba, dan Allah ki yi haƙuri kar ki ƙullace mahaifiyata duk Balaraba ce ta shirya mata wannan ƙariyar, dan Allah ki bar kukan nan haka”


“Ni ba maganar nake yi wa kuka ba, Daddy ban ga lafin Umma ba, kawai magana ɗaya ne ya taɓa zuciyata. Amma babu komai akwai Allah”


“Amnoor ba zan iya zuwa da ke gida a wannan yanayin ba...”


“Dan girman Allah Daddy kar ka ce haka, ni dai ka kaini gida kawai dan Allah!” Ta yi maganar tare da fashewa da wani irin mugun kuka. “To in ba ki daina kukan nan ba, ba zan kai ki ba...” Da sauri ta fara share fuskanta tana faɗin “Na daina to ka gani na share hawayen” Kwantar da kanta ya yi saman kafaɗarshi har suka ƙaraso gidan ɗagowa ta yi tana kallon shi sannan ta ce “Da wane lokaci za ka dawo?” sumbatar bakinta ya yi tare da faɗin. “Zuwa Isha dai zan dawo, dan Allah kar ki bari kowa ya san halin da ake ciki, ki yi mini wannan alfarman dan Allah Amnoor” Girgiza mishi kai ta yi tare da riƙo hannunshi “Daddy ka daina damuwa babu wanda zan faɗawa wannan maganar In Sha Allah”


“Na gode sosai Amnoor, sai na dawo ko?” Gyaɗa mishi kai na yi tare da faɗin “Allah Ya tsare min kai, Allah ya dawo min da kai lafiya, Allah ya kauda idon sauran mata a kanka” Da murmushi ya amsa yana cewa ta isar mishi da gaisuwa wurin Maman Nafisa. Tana ɗaga mishi hannu har ya motar shi ya tashi sannan ta nufi cikin gidan tana amsa kiran Amrah “Amnoor kina ina? Yanzu na fito gidanki Suhaima take sanar min da ya faru”


“Ga ni a gidanmu” Amrah ta ce “Ok ga ni zuwa” Zaliha ce ta taso da gudu tana faɗin “Oyoyo Aunty Noor!” Rumgumeta ta yi tare da Karɓan jakarta tana dubawa. “Auntyn mu ba ki kawo min komai ba?” Ɗan murmushi ta yi kawai ba tare da ta ce mata komai ba, “Assalmau Alaikum!”


“Waalaikumussalam Nurriya ke ce tafe da safiyar nan?” Zama na yi tare da faɗin “Eh wallahi Maman mu, yanzu ya kawo ni zuwa yamma zai dawo ya ce yana miƙo gaisuwa kafin ya dawo” Maman Nafisa ta ce “To Madalla ina amsawa ya gidan naku duk lafiya dai ko?”


“Alhamdulillah” Na ce mata sannan na zauna tare da faɗin “Mama kina da magani anan? Ƙwanƙwaso na ke ciwo wallahi duk jikina ya sake..” Wani kallo Maman Nafisa ta auna mata kafin ta miƙa ma Zaliha ɗari biyu ta ce a je a sayo mata maganin. “Wani abu na faruwa ne? Duk naga kin yi wani yanayi fuskarki na nuna damuwa, in da wata matsala ki faɗa min” Murmushi kawai na yi tare da faɗin “Maman mu babu komai”


“To yaya zaman ku da matar gidan?” Kafin na ba ta amsa Amrah ta shigo ɗakin “Barka da safiya Maman mu, Amnoor yanzu Suhaima take cewa in ba ki haƙuri ta so yin magana amma tana tsoron abin da mahaifiyarta za ta yi mata”


Kallon Maman Nafisa na yi ina jin takaicin maganar Amrah dan ban so ta yi maganar a gaban Maman mu ba.


“Mai ya faru?”


Ta yi maganar tana kallon Amrah bayan ta wurga min harara “Wannan mugun halin naki na ƙin yin magana watarana sai ya ja miki abin da ba daɗi, kin zo ina tambayar ki ko da damuwa amma kika ce min bakomai, na fi kowa sanin wacece ke tun da ni na haifeki, daman na yi shuru ki huta zuwa jimawa in sake tuntuɓar Ashe dai da komai ɗin, ina jinki Amrah faɗa min mene ne domin wannan shashashar me nauyin baki ba magana za ta yi ba, idan suka kashe ki shi kenan Allah ya sa ina da wasu yaran..” Wannan furucin nata shi ya sa ni sakin sauran hawayen da ban samu damar tsiyayar da su ba, wani mugun tsaki ta ja bayan ta gama jin abin da ya faru. “Kuma kin yi mata rashin kunyar da gaske?” Girgiza mata kai na yi tare da faɗin “Wallahi ban yi mata komai ba Maman mu” Maman Nafisa ta ce “To mai ya haddasa muku wannan fitinar da safiyar nan? Yau juma'a ma ba za bar masifa ba?” Kunyar sanar da ita yanda Hajiya ta sake mu a kitchen nake ji, cikin daka tsawa ta ce “Za ki buɗe ba ki ki yi magana ko sai na saɓa miki?” Zabura na yi tare da mannewa jikin Amrah ina faɗin “Tun jiya ta fara min wani yanayi ba daban, yau kuma dan ta ganmu uhm-uhm..”


“Ta ganku me? Ki buɗe baki ki yi mini magana, ko a cikin madafin ta ga kuna auratayya?” (Tabɗijam! Wa ya ga mai gabaɗaya, tun da tana jin kunya gwara a yi mata kai-tsaye😃)


“Ku san hakan ne” Na faɗa hawaye na zubo min sannan na ba ta labarin yadda rigimar ya fara.


Cikin zubar da hawaye na ce “Maman mu har gorin haihuwa sai da Hajiyar shi ta yi min, dan Allah iya shekara biyu kawai dan ban yi ciki ba shi ne za a goranta min yara”


“Sai ki yi ƙoƙarin haihuwar ai” Maman Nafisa ta ce tana juya maganar cikin ranta “Ke bari in faɗa miki tun yanzu ba za ki koma gidan shi ba, bare matar shi da ɗan shi su ci gaba da miki sharri abin da ba ki aikata ba” Rarrafawa na yi zuwa wurinta da sauri hankali na ya tashi da jin wannan furincin nata “Dan Allah Maman mu kar ki yanke wannan hukuncin wallahi ni zan yi haƙuri da koma mene ne za su min, ni dai kar ki rabani da Daddy ina son shi sosai shi ma kuma yana sona dan Allah Maman mu” Miƙewa Maman Nafisa ta yi tare da barin ɗakin tana faɗin “Koma dai mene ne na gama magana”


“Amrah duk ke kika jawo min wannan damuwar da kin yi shuru ai da ba ta san maganar ba, amma daga zuwa kika ɗauko maganar ni fa a yanzu ba zan iya jure rashin mijina ba gaskiya ba zan iya zama ba tare da na ji ni cikin jikinshi ba, ya riga da ya sabar min da jikinshi shi ma kuma ya saba zama jikina ta yaya zan iya.. ”


“To fitsararriya ai sai ki zo ki tare ne da cewar ke kin san daɗin miji ba za ki iya kwanciya ke kaɗai ba sai a cikin jikinshi ko? To in ba canza miki gida ya yi ba wannan gidan kam, ba za ki koma ba”


Kuka na saka tare da ɗaukar jakata da mayafi na zan fita “Saboda ina shirin kankaro miki mutunci da ƙima shi ne kike jin haushi na? In dai namiji ne Bisimillah da ƙafar ki za ki zo kina min kuka da ƙorafi”


“A'a Maman Nafisa, Daddy ba haka yake ba, ba ya daga cikin irin wannan mazajen”


“Ke Amnoor kina hauka ne? Mahaifiyarki na miki magana kina magana saboda kin yi aure kin san daɗin namiji, in kin so ki fi ruwa tafiya shashasha, ba ka nunawa namiji so ba ma ya wulaƙanta ka bare ka nuna mishi kana mutuwar shi” Cewar Mahaifiyar Amrah wacce shigowar ta kenan ta tarar da wannan rigimar.


Maman Nafisa ta kalli Amnoor ta yi wani murmushi tana faɗin “Ni ma lokacin da nake son baban ku haka na yi ta hauka a kanshi, ƙarshe ba ga shi ya kawo ni inda ban sa kowa ba ya jefa ni? Ke kin san taurin kan da nayi lokacin da nake matashiyata? In za ki ga hanya nan ban hanaki ba, amma wallahi ki sani kar ki yarda ki tako nan da sunan kin zo kawo min ƙorafi”




“Haba ke kuwa bai dace ki ce mata haka ba, har yanzun yarinya ce fa... “Hajiya Salma ban katse ki ba, ana maganar shekara ashirin da huɗu kin ga ba maganar yarinta anan, giyar soyayace kawai ke ɗi banta” Zubewa na yi a ƙasa tare da fashewa da kuka. Amrah ce ta zo ta kama ni muka koma ɗaki. Kallon Zaliha wacce ke zaune shuru na yi tare da faɗin “Ina baban mu?”


“Ɗazun nan ya shigo ya fita” Gyaɗa mata kai na yi sannan na ce “Firdausi fa?” Zaliha ta ce “Tun daren jiya da ta fita ba ta dawo ba” Daga haka ba ta sake cewa uffan ba sai ma kwanciyar da ta yi tare da lumshe ido tana jin kaman Maman Nafisa ba ta mata adalci ba, domin a yanzu ne take tsananin ƙaunar mijinta, har wuraren ƙarfe ɗaya Amrah na zaune kusa da ni tana danne-dannen waya ba ta ce min komai ba, miƙewa na yi tare da nufar bayi na kama ruwa tare da alola ina fitowa Amrah ta miƙe tana faɗin “Ni zan wuce gida sai mun yi waya, dan Allah Amnoor ki nutsu ki yi abin da Maman Nafisa ta ce, domin ta fiki gaskiya, ko ni ba na goyon bayan ki ci gaba da zama tare da mommy dan wallahi ba ta da kirki” Gyaɗa mata kai kawai sannan na ta da kabbaran sallah. Ina idar da sallah sai ga Maman mu ta shigo min da abinci Zaliha na biye da ita. Ajiye try ɗin Zaliha ta yi tare da fita a ɗakin. “Ga abinci ki ci” Ban ce mata komai ba na fara cin tuwon sai da na kammala sannan ta ce “Ga wannan romon ki ci ki shanye romon a cikin haɗin da nake yi wa amare na ɗibar miki” Kallonta na yi tare da ɗauke kai ina faɗin “Tun da nan zan zauna ba tare da miji ba, ai babu amfanin wani abun..” Ƙura mata ido Maman Nafisa ta yi sannan ta ce “Soyayya ya canza min ku, gwara Fiddoh daman tana iya magana, ke kam sam ba haka kike ba, duk Alhaji Aminu ne ya mayar min da ke haka? To ni dai ki daina jin zafina dan ban yi haka don na ɓata miki rai ba, kwana biyu nake so yi wanda a cikin kwanakin nan nake son shirya jikin ki ta yanda koda officer yake ya dinga tuna ki cikin ransa idan hakan ya yi miki to in kuma kina jin rashin kyautawa ta za ki iya tafiya Hajiya Laraba tana jiran ki” Tana gama faɗar haka ta fita a ɗakin. Sai da na gama cin abin da ta kawo sannan na ɗauke kwanukan zuwa waje. Kamar yanda ya ce zai zo da sallar Isha'i haka kuwa aka yi, lokacin na yi wanka na saka doguwan me ɗan fasali daga cikin kayan Fiddoh dan sai da na yi ta bincike ma kafin na samun rigan, ina zaune na ji ƙaran wayata kallon Zaliha na yi tare da faɗin. “Ki je ki shigo da shi ɗayan ɗakin da aka ware na baƙi” Miƙewa ta yi ta fita. Ba jimawa sai gata ta dawo tana faɗin “Maman mu ya ce wai za ku gaisa” Mayafi Maman Nafisa ta ɗauka ta fita. Sunkuyar da kai ya yi yana gaisheta “Barka da wannan lokacin mama da fatan an yi sallah lafiya? Allah Ya maimaita mana”


Maman Nafisa ta ce “Lafiya lau Alhamdulillah ya ayyuka? Allah Ya taimaka, daman na ce in da hali a sauya mata gida dan Nuriyya ba mai hayaniya ba ce, ban mance abin da likita ya faɗa dangane da maganar ciwonta na kwanaki ba, hayaniya da tashin hankali zai iya komawa da ita cikin wancan halin na ƙunci da razana dan Allah kafin ta koma zan so komai ya kafa tukun na”


“To-to ba damuwa na gode, kuma ina mai ba da haƙuri da hakan ba zai kuma faruwa ba” Miƙewa ta yi tana faɗin “Allah Ya sa” Sannan ta dawo ta barshi cike da zulumi.


“Ki je ku gaisa” Miƙewa na yi tare da nufar ɗakin “Assalamu Alaikum” Murya a sanyaea na yi salllamar amsawa ya yi tare da kafe ta da ido duk ya yi wani yanayi yana jin babu daɗi. Zama ta yi bisa cinyarshi tare da kwantar da kanta saman kafaɗarshi, nan suka sauke ajiyan zuciya a tare lumshe ido ya yi yana faɗin “Whay Amnoor? Mai ya sa kika bari har aka fahimci abin da ke faruwa bayan mun yi da ke a kan ba za ki bari kowa ya san halin da ake ciki ba?” Ya yi maganar murya can ƙasa, ɗagowa ta yi tana kallon yanayin shi wanda ya sa ta yin narai-narai da idanuwa hawaye na cikowa...


_Ai na biya ba shi ko? Long page fa. Ga shi ba ku Comments bare sharhi_


#Ayshajb
#Amnoor
#Lovestory
#Sexstory
#Sister'slove
#Paidbook
#500Naira
2389596965 Aisha Jubreel Zenithbank, a tura shedar biya ga wannan Number 09079740079
[5/9, 11:46 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
Romance Story.








®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. J.W. A★


Ku je ku yi Subscriber YouTube channel ɗinmu, muna ɗora littafanmu a can. https://youtube.com/@farinjinihausatv.5609?si=4jZwznZJHugMg4VU


Page 38.


Hannuwanshi ta kamo a hankali cikin rawan murya ta shiga magana hawaye na tsiyayo mata “Allah Daddy ba ni ce na faɗa ba, zuwan Amrah ne ya sa Maman mu ta ji maganar shi ne ta ce wai na zauna sai bayan kwana biyu in koma” Matse hannunta ya yi tare da yin mana cikin sanyi da taushin murya. “Amnoor ya isa haka, ba na son wannan kukan Please a daina shi” Ya yi maganar tare da ɗago fuskanta tana kallon ƙwayar idonta. “Zan yi kewarki na tsayin kwanaki biyu, ba zan iya sake wa ina can kina nan ba, amma babu komai Allah ya kaimu lokacin” Ya faɗa tare da sakin fuskan ya miƙe “Ki riƙe wannan kuɗin ko da za ki buƙaci wani abun, ni zan wuce” Rumgumeshi ta yi ta baya tare da sakin sauran kukan, “Ka yi haƙuri dan Allah my love, ni ma zan yi kewarka sosai”Juyowa ya yi da ita yana share mata hawayen “Wai ba na ce a bar kukan ba?” Turo ba ki ta yi gaba cike da shagwaɓa ta ce “To ba kaine ba, za ka tafi ba ka ce min komai ba” Ta yi maganar har da buga ƙafa a ƙasa. Jawota ya yi jikinshi suka koma suka zauna “Ba na son na shiga wani yanayi ne, kin ga ba tare muke ba, amma sanin kanki ne ni ma ina sonki sosai” Da wani irin yanayi ta kalleshi tare da lumshe idanunta wannan yanayin da take yi mishi ne ya fara kashe mishi jiki, shafo fuskanta ya yi tare da cire mata himar ɗin da ta saka yana kallon yanda take ƙara shige mishi, bakinta ta kai saman na shi tana shirin kissing ɗin shi ya dakatar da ita, nan take ta buɗe idanuwanta da suka fara sauya launi “Dan Allah Daddy iya kiss ɗaya ka ji” Murya a narke ta yi mishi maganar tare da kamo fuskarshi bakinta ta kai ta fara lasan lips ɗin sa cike da zalama tana jin wani irin sha'awa yana taso mata da ƙarfi, laluɓo harshen shi ta yi ta shigo tsotsa tana sauke ajiyan zuciya, shi kuwa ji ya yi gabaɗaya tana shirin birkita mishi lissafi ne, jin ya yi shuru bai motsa ba ne ya sa ta kamo hannunshi zuwa Breast ɗinta. Matsosu ya yi tare da sauke numfashi yana jin laushin su, wasa-wasa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login