Showing 39001 words to 42000 words out of 69263 words
Chapter 14 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB
dan ya lura tambayar renin hankali take mishi “A'ah Alhaji ba ka ba ni amsar tambaya ta ba”
Riƙe mishi hannu na yi tare da matsewa ina mishi alamar rarrashi domin na lura ya fusata da maganar likitar. “Idan na faɗa miki adadin da nake yi a rana tsorata za ki yi, domin tun ba ta saba ba haka har ta saba tana nema da kanta, shi ne yanzu za ki faɗa min wani zancen banza ina ga ba ku san aikin ku ba ba zan iya zuba ido ina kallo mace ba tare da na juye mata abin da...” Riƙo shi na yi tare da faɗin “Ki yi haƙuri Dr tun da aka ce mafitsarar shi ya samu matsala yake a fusace, musamman ma idan aka ce ba zai iya tarawa da iyali ba” Na faɗa ina kallon ƙwayar idonshi “Ni na ce miki ba na jin ƙarfin da zan..”
“Mu je gida lokacin shan maganinka ya yi” Dariya kawai Dr ɗin ta yi domin daga shi har matar tashi dariya suke ba ta ganin yadda ta ɓata rai tana cewa su je ya sha magani shi kuwa sai faɗin “Ni na ce miki ba ni da ƙarfin da zan yi wani abu? Wato kin raina ni yanzu saboda kin ga ba ni da lafiya ko? Ya yi kyau!”
“Dan Allah duk wannan rigimar ka ajiye shi har mu ƙarasa gida tukun na lokacin ne zan kulaka amma ban da nan domin idon jama'a na kanmu” Suna ƙarasawa gida ya fisgota da ƙarfi kamar zai ɓalla mata hannu “Saboda ba ni da lafiya shi ne kike min haka? Kin gaji da ni ko kina son rabuwa da ni dan ba na biya miki buƙatar ki...” Hannunshi ta riƙe har cikin falonta Zaliha ta iske zaune. “Aunty Noor kun dawo? Daddy ya jikin ka? Na zo Maman Suhaima take cewa kun je asibiti” Da sakin fuska ya amsa mata sannan ya fita zuwa nashi ɗakin. Zama Nuriyya ta yi tana faɗin “Ai na manta yau za ki zo ga shi ban girka mana komai ba ko za ki shiga ki mana girkin?” Miƙewa ta yi tana faɗin “To” Kayanta Amnoor ta adana mata sannan ta nufi ɗakinsa yana kwance ta ɗauko magani da ruwa tana miƙa mishi karɓa ya yi tare da ƙure ta da ido, ɗauke kanta ta yi sannan ta miƙe ta fita a ɗakin.
Da yamma suka haɗu dukkansu a falo suna cin abinci suna kammalawa Laraba ta yi ɗakinta domin tun da Amnoor ta tare ta sallama mata shi tun da ta san abin da ta ƙulla musu. Kwana biyu Zaliha ta yi ta tattara ta ce za ta koma gida dan masifar da suke yi kullum dare ya ishe ta ɗan kullum da dare sai sun yi faɗa yau da wuri ma suka fara rigimar ta su. “Daddy mai ya sa kake min irin haka? Kana ganin ƙanwata na nan amma kullum sai ka ta da rigima ka bari ta koma mana in ya so koma mene ne sai ka yi tun da ka zama mafaɗaci..”
“Ni kike faɗawa wannan maganar? Amnoor zan mare ki...” Da mamaki ta matso tana faɗin “Daddy ai ba sai ka faɗa ba, daman na daɗe da fahimtar kana son kai hannu jikina wallahi na gaji da wannan fitinar naka haba dan Allah sai ka ce wani ƙaramin yaro kullum sai an jiyo muryan mu...”
Kallon hannun shi ta yi tare da faɗin “Shi kenan ka mare ni ko wutar da ke cin zuciyarka zai ragu” Fitowa ta yi a ɗakin zuwa nata ɗakin dan kusan sati basu kwnaciya tare tun da ya tsiro da faɗar dare. Kallon Zaliha ta yi tare da faɗin “Ke lafiya na ganki da jaka?” Zaliha ta ce “Aunty Noor gaskiya ni gida zan ta fi wallahi ba zan iya da diraman ku ba” Ɗauke hawayen da ke zubo mata ta yi sannan ta ce “Shi kenan ki gaishe da Mamanmu ki ce mata ina kewarta” A haka suka yi sallama. Zama ta yi tare da fashewa da kuka dan ta rasa abin da ke jawo musu wannan fitinar kullum dare babu kwanciyar hankali sai sun yi faɗa sun koma tamkar karnuka tun ba ta kula shi har ya fara kaita maƙura.
#Paidbook 500
09079740079
[5/9, 11:45 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
Wattpad: ayshajb
Arewabooks:ayshajb
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
★F. J. W. A★
Free page 33_34
Ku je YouTube ku yi Subscriber Channel ɗi na FARIN JINI HAUSA TV. Domin samun ƙayatattun littafanmu.
H-P Place Group.
“Ya Nuriyya suke.?” Maman Nafisa ta yi mata tambayar bayan ta ajiye jakar Zaliha da ta karɓa. “Gaskiya babu lafiya Maman mu, dan kullum Aunty faɗa suke yi da mijinta...” Dakatar da ita Maman Nafisa ta yi da faɗin “Hajiya Laraba ke haɗa su faɗar ko? Dan na san za ta aikata fiye ma da hakan in dai a kan mijinta ne..” Cikin sauri Zalihar ta katse ta da faɗin “Ko ɗaya Mama mu, ai Maman Suhaima tana da kirki kuma suna zaune lafiya sai ma kinga yadda suke komai tare tamkar ma ba kishiyoyi ba tsakaninta da Daddy ne ban san me ke faruwa wanda kullum yake haddasa musu rigima ba” Shuru Maman Nafisa ta yi tana juya zancen a ranta ta san muddin Nuriyya ta ce ta yi kewarta tabbas tana cike da damuwa mai tarin yawa ne. Yinin ranar haka ta yi shi zuciyarta cike da tunanin ɗiyar tata, da a ce Fiddoh za ta amince da ta kaiwa Noor ɗin ziyara amma ta san da kamar wuya. Aikuwa Fiddoh na dawowa ta tare ta da maganar buɗar bakinta sai cewa ta yi “Ni in je gidanta? To in yi mata mene?” Da ga haka ba ta sake cewa uffan ba, domin zancen ma ɓacin rai yake saka ta.
Amnoor kuwa shuru ta zauna a ɗakinta tana tunanin abin da ke haddasa rigima tsakaninta da mijinta sai dai duk iya bincike da ta yi ba ta gano komai ba, ƙarshe haka ta kwana da matsanancin ciwon kai, ko da ta farka da Asuba da ƙyar ta iyayin sallah ba ta samu damar yin azkhar ɗin da take yi kullum ba haka ta kwanta tana riƙe da kanta. Rashin jin motsinta ba ƙaramin damunsa yai ba, domin ta saba zuwa duba shi ko da ba su kwana wuri ɗaya ba. Ga shi ko abincin kari bai ga alamar za ta kawo mishi ba, an ya ma ba fushi ta yi da shi ba? Tambayar da ya yi wa kanshi wanda ba shi da mai ba shi amsar kenan. Haka ya yi wanka ya shirya ya fito ɗakin Laraba ya leƙa nan ya ga ba ta nan, tun da ya doso ɗakin yake jin yadda take nishi tare da sheshsheƙan kukanta, da sauri ya ƙarasa ganinta yai dafe da kai tana juyi ga hawaye da ke zariya bisa kuncinta “Ya Subahanallah Amnoor!” Ya kira sunanta cikin rikicewa yana ɗagota “Mene ne? Ina ke miki ciwo? Daman ba ki da lafiya shi ne ba ki kira ni ba?” Duk wannan tambayar ya jero mata lokaci ɗaya. Da sauri ya ɗauki waya tare da kiran likita yana faɗin ta zo cikin gaggawa. Babu ɓata lokaci kuwa likitar ta ƙaraso kafin zuwan likitar ya yi ƙoƙarin ba ta tea. Nan ta yi mata allura domin jikinta har da zazzaɓi magunguna ta ajiye tare da faɗa mishi yadda za ta sha su sannan ta ƙara da faɗin “Damuwa ya yi wa Madam yawa, ya kamata a kiyaye abin da zai dinga haddasa mata wannan damuwar” Tana gama abin da za ta yi ta yi tafiyarta.
Yana zaune jikinta har ta farka “Sannu Amnoor yaya kike jin jikin yanzu?” Ɗan murmushi ta sakar masa tare da daurewa ta ce “Ya yi sauƙi, ya naka jikin? Ka sha magani yau?” Ta yi maganar tana ƙoƙarin ta shi zaune. “Na sha kuma na ji sauƙi sosai” Miƙewa ta yi ta gyara ɗakin sannan ta nufi toilte ta wanke duk inda ta gifta yana binta da ido cikin zuciyarshi yana jinjina ƙarfin hali irin nata har ɗakinsa sai da ta je ta gyara ko’ina sannan ta shiga kitchen ta yi musu girki. Haka ta dinga daure ciwon kan da yanzu yake takura mata tana aikinta izuwa yanzu rigimar tasu yai sauƙi batun kwana gado ɗaya ne dai har yanzu babu in ya fita aiki yana ƙoƙarin dawowa da wuri kasancewar tana cikin kaɗaici yanzu ita ɗaya a gida a hakan ma wani lokaci Amrah na kawo mata ziyara wacce ita ma yanzu karatu take gadan-gadan ba kama hannun yaro shi ya sa ba ta samun zuwa wurin Amnoor ɗin.
Cikin barci ta fara jin warin hayaƙi buɗe idanunta ta yi tana kallon yadda tsakiyar ɗakin ya turniƙe da hayaƙi babu jimawa ta fara jin sautin dariya na muryoyi daban-daban wani irin juyawa ta ji kanta na yi dafe kunnuwanta ta yi da duka hannayenta tare da runtsa ido. Gabaɗaya ta mance da addu'ar sai jujjuya kai take tana runtsa idanu. Kimanin mintuna talatin ana haka kafin ta ji komai ya ɗauke zubewa ta yi a ƙasa tana mayar da numfashi daga haka barci yai awon gaba da ita. Ko da gari ya waye ta kasa faɗa mishi abin da ya faru, shi kuwa kasa shuru ya yi ganin yanayinta kamar a firgice take, ya yi mata tambaya sai dai ta ce babu komai, haka ya ƙyaleta ba don ya yarda ba. Yana kammala shiryawa ya fita aiki. Tun bayan fitar shi al'amarin jiya ya dawo, na yau ma ya fi na jiya tsananta domin wuni aka yi ana firgitata duk inda ta juya sautin ihu da dariya ne ke kaiwa kunnuwanta farmaki ga shi ta kasa furta kalma ɗaya na addu'a sai gab da magariba ta ji gidan ya yi ɗif tamkar ba shi ne ya ke juyawa ba juyowan da za ta yi ne ta yi arba da shi yana tsaye, da gudu ta nufeshi ta rumgumeshi tana fashewa da wani irin kuka, sosai ta yi kukan shi ma bai hanata ba domin ya lura tana cikin damuwa sai da ya ga kukan ba mai ƙare wa ba ne ya shiga rarrashinta washegari ma yana fita gidan ya juye mata zuwa wani sansanin daji na daban. Kwana biyar tana cikin firgici da tashin hankali wanda ta rasa da wane yanayin za ta yi masa magana ya fahimce ta. Gabaɗaya ta rame ta susuce tare da fita a hayyacinta. Bata iya taɓuka komai yanzu hatta abinci ba ta iya girka musu sai dai ya sayo musu. Shi kanshi yanayin da take ciki na damunsa amma da zaran ya tambaye ta sai dai ta ce bakomai so biyu yana kaita gidan Hajiya Umma a nashi tunanin ko zama ita ɗaya ne ke sanyata cikin damuwa amma duk da hakan ba ta dawo yadda take da ba. Yana cikin shirin tafiya aiki ta kalleshi tare da faɗin “Daddy ina so inga Maman mu” Jakar shi ya ɗauka tare da faɗin “Bari in na dawo anjima sai mu je tare” Sunkuyar da kai kawai ta yi domin ta san muddin suka tafi tare ba wani daɗewa zai barta ta yi ba.
Ya fito daga Ofishin sa kenan sakataren shi ya kira shi yana sanar da shi baƙin su sun iso dole ya shi ne ya nufi filin jirgi domin tarban su, da ga nan ya je ya kama musu masauki a tsattsaye ma suka gaisa domin gabaɗaya tunaninsa ya yi gida ganin har bakwai saura yau bai je gida ba, ga shi ita ɗaya ce a gidan. Da hanzari ya fito yana kallon wayarshi da ke haske alamar shigowar saƙo kasancewar ya saka wayar a silent nan ya ga miss call haɗe da saƙonninta tana tambayar lafiyarshi da abin da ya hanashi dawowa gida. Mayar da wayar yai cikin aljuhunshi tare da buɗe motar yana ƙoƙarin shiga. Da ga bayan shi ya ji an dafa kafaɗar shi da mamaki ya juyo yana tunanin waye haka? Nan ya yi arba da ita wani dogon tsaki ya ja tare da sake tamke fuska cikin ɓacin rai ya cire hannunta a jikinshi yana binta da ƙasƙantaccen kallo ganin irin shigar da ke jikinta wanda gabaɗaya ya bayyana komai na jikinta kasancewar kayan ɗamammu da su. “Alhaji na...” Wani irin zubewa ta yi a jikinshi gabaɗaya tare da fashewa da wani mugun dariya da ga haka idanunta ya fara rufewa Emanuel ne ya ƙara so wurin da sauri tare da ɗaukar ta yana faɗin “Yi haƙuri Alhaji ta yi sama sosai” Saboda tsananin takaicin kwanciyar da ta yi cikin jikinsa kasa magana ya yi. Haka ya ja motar yana me jin ƙyanƙyamin jikin nasa har ya ƙara sa gida.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa da sauri ta taho ta amshi jakar da ke hannunsa “Barka da dawowa Amnoor” Lumshe mata ido ya yi tare da jinginuwa da ƙofar shi ma yana sauke numfashi “Ki yi haƙuri yau ban dawo da wuri ba” Ɗan murmushi kawai ta yi tare da riƙo hannunshi zuwa d'akinshi. Sai da ya yi wanka tare da yin sallah sannan ta kawo mishi abinci tare da magani, kaɗan ya ci sannan ya sha maganin, kwashe kayan ta yi ta mayar da su kitchen kana ta nufi ɗakinta, wanka ta yi ta fito ɗaure da zani ba ta san yana ɗakin ba sai da ta ji ya yi gyaran murya sannan ta waigo tana mamakin zuwan nasa kasancewar yanzu bai fiya shigowa da dare ba. Karɓan man da za ta shafa ya yi tare da jan zanin nata gefe kawa kawai ya ji yana son rage ma kanshi zafi da ita bayan tsawon lokaci da suka ɗauka ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, duk wanan sheɗaniyar yarinyar ce ta saka shi cikin wannan halin (Fiddoh) haka ya fara bin santala-santalan cinyoyinta yana shafa mata mai cikin wani irin yanayi kasa daurewa ta yi da sauri ta riƙe hannunsa tare da girgiza mishi kai. Wani irin kallo yai mata sannan ya kwance zanin gabaɗaya ya jawota cikin jikinshi sannan ya kashe hasken ɗakin, nan ya dinga birkita mata lissafi wanda har kuka sai da ta yi mishi domin ya kunnota da ga ƙarshe sai ya kasa yi mata komai takaicin wannan abin ya sa ta juya mishi baya, shi kuwa a rayuwa ya tsani irin haka wai su kwana gado ɗaya kuma mace ta juya mishi baya.
Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya zaman lafiya ya yi ƙaranci a tsakaninsu tamkar masu almatsutsai yanzu-yanzu za su yi magana cikin daɗin rai ba jimawa kuma za su fara faɗa. Wannan abin shi ya sake ƙara mata damuwa sosai, yau yana fita ta haɗa kayan da za ta buƙata ita ma ta nufo gida lokacin da ta zo Maman su na aikin turarenta ta yi sallama da ’yar siririyar muryanta tare da zama jikin Maman Nafisa tana sauke ajiyan zuciya nan da nan ta ji wani nutsuwa ya zo mata take ta fara barci shafa kanta Maman Nafisa ta yi tana ƙare mata kallo ganin yadda ta sukurkuce ta lalace duk ta rame, gyara mata kwanciya ta yi sannan ita ma ta ci gaba da aikinta sai zuwa ƙarfe biyun rana ta farka za ta yi magana Maman Nafisa ta ce “Yi addu'a tukun na” Lumshe ido ta yi tare da karanto addu'a. Ruwan rubutun da ta sa Zaliha ta amso mata wurin malamin makarantar su tun kwanaki ta ɗibo tare da miƙa mata. “Ki sha da Bisimillah” Haka kuwa aka yi tana gama sha ta dire kofin tana sauke ajiyan zuciya.
“Me ke faruwa?” Maman su ta yi mata tambayar tare da ƙura mata ido, sunkuyar da kai Amnoor ta yi domin ba za ta iya kallon maman tasu ba bare har ta faɗa mata abin da ke faruwa ba. Ganin yadda take matse 'yan yatsun hannunta ya sa Maman fahimtar ba faɗa mata za ta yi ba, daman ta san halin kayanta da ƙyar ta iya faɗar damuwarta. Cikin jin haushin halayyarta Maman su ta ce “Ki tashi ko koma ɗakin ki...” A sukwane ta d'ago idanunta cike da hawaye tana faɗin “Dan Allah..” Dakatar da ita Maman Nafisa ta yi da faɗin “Ba za ki zo ki tasa ni a ga ba kina min hawaye bayan na tambaye ki damuwarki kin ƙi faɗa min ba, gwara tun wuri ki tattara ki tafi, shin mijin naki ya san kin fito?” Girgiza mata kai ta yi alamar a'a shigowar Zaliha ya sa ta yin shuru tare da miƙewa “Wayyo Aunty Noor ke ce a gidan mu yau? Dan Allah Aunty ba ni wayarki in yi abu” Miƙa mata wayar ta yi tare da shegewa ƙuryar ɗaki tana kuka. Ita dai ba za ta koma gidan Alhj Aminu ba, gwara ta zauna gidan su wurin Maman Nafisa kawai.
A gajiya ya fito daga motar domin yau gabaɗaya bai huta ba saboda ayyuka da suka mishi yawa, da sallama ya turo ƙofar falon yana me kiran sunanta domin ya saba da in ya dawo tana zuwa karɓan jakarshi ko kuma ta rumgumeshi tana mishi oyoyo yau kuma sai ya ji shuru ɗakinta ya nufa yana tunanin ko dai sallah take nan ma bai ganta ba toilte ɗin ma shuru gaban madubin ya ga takardan da ta rubuta mishi saƙo. “Ka yi haƙuri na fita ba tare da izinin ka ba, Daddy na gaji ba zan iya ci gaba da zama da kai a haka ba. Rayuwa haka muna matsayin ma'aurata sam babu armashi a lokacin da ban saba ba kai ka sabar min, tun ba na jin daɗi har ka koya min jin daɗin, tun ina gajiyawa har na zama gwana. Ta yaya zan zauna bayan ina jin mararin abun? Akwai cutarwa sosai, na yi iya haƙurin da zan yi dan Allah ka fahimta. Ina mai roƙon ka da ka sawwaƙe min kawai dan ba zan iya zama kullum muna faɗa da junan mu ba” Lumshe ido yai yana jin wani zafi a ranshi da ƙyar ya iya yin wanka tare da