Showing 27001 words to 30000 words out of 69263 words

Chapter 10 - Amnoor Complete book Romantic Hausa Novels by Aysha JB

Aisha JB   

22 Aug 2025

302

yana murmushi, lokacin da ta farga da abin da yai mata kamar zata fasa ihu ga shi kayan da ke jikinta ba za ta so ya ganta a haka ba domin rashin ɗa'a ne duguwan riga me hannu shimi ne a jikinta wanda bai sauka gwiwarta ba, ga shi ya ɗame jikinta sosai ya fitar da shep ɗinta, kwanciya ta yi a gadon tare da rufe jikinta. Turo ƙofar yai tare da sallama murya can ciki ta amsa mishi tare ɓata fuska ɗauke kanshi yai ganin yadda take cika tana batsewa wayarshi ya kara a kunne bayan ya zauna kan kujera, satan kallonta yai tare da faɗin. “Ki zo ga Mamanmu...” Ai da sauri ta wuntsilo har da ɗan guduta, ta manta da yanayin da take ciki jin ya ambaci sunan Maman su. Wani irin haɗiye miyau ya yi yana gyara zaman shi ganin yadda kayan yai bala’in amsar jikinta, gefen shi take shirin zama ya jawota ta faɗo jikinshi, ajiye wayar yai a gefe tare da ƙura wa ƙirjinta ido yana sake haɗiyan miyau cikin marerecewa ta fara magana da ’yar siririyar muryanta “Kuma ka ajiye wayar? Dan Allah ba ni mu yi magana da ita...” Tsit maganar nata ya tsaya jin yana shafa fuskarta zuwa leɓen bakinta.
“Uhm ashe ba ki da wayo farat ɗaya kin taso kina juya min wannan ƙananun abun..”
“Wayyo Allah! Ni ka barni dan Allah ba na so!” Numfashi ya sauke sannan ya ɗagata tare da miƙa mata wayar ya nufi bayi. Hira sosai muka yi da Zaliha domin Mamamu bata kusa wai sun je bikin 'yar maƙofciyarsu ina gama magana da ita na fara binciken Number Amrah bugu ɗaya ta ɗauka “Mara kirki” Cikin ihu ta ce “Matar Daddyna afuwan! Ya abubuwa ya amarci? Ina fatan ana kula min da Daddy?” Juyowa na yi ina satar kallon shi ganin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa ɗauke kaina na yi ina faɗi cikin raina _(Shi dai ba ya gajiya da wanka sai ka ce agwagwa bini-bini yai wanka)_ “Alhamdulillah Ya Mama da Abba ki gaishesu” Karɓan wayar yai tare da kashewa sannan ya min nuni da nawa ɓata fuska nai ina kallon wayar domin har yau ban iya amfani da shi ba. “Ayya Daddy ban iya amfani da wayar ba ne ai” Ido ya zuba mata yana so ta sake magana da shegen muryan nan nata mai tsayawa a zuciyar mai sauraro “Kika ce?” Ya faɗa tare da ɗaukar wayar ya zauna kusa da ita zubur ta miƙe domin kunyar ganinsa a haka take yi. Suna sallar Isha ya ɗauketa suka sake fita yau ma sun yi yawo dare sosai suka dawo gida yau kan ko wanka ba ta yi ba haka ta faɗa gadon saboda barcin da ya cika idanunta. Shi kam ba zai iya kwanciya haka ba, sai da ya watsa ruwa washegari suka kamo hanya direct ya nufo gida da ita inda ta ga an sauya komai na gidan harda fenti aka yi musu daga cikin motar take kallon gidan tana mamakin wadda yai wannan aiki domin ta san mai gidan de ba yi zai yi ba, dan gyaran bayin gidan ma da ƙyar ya yi sa. Ajiyan zuciya ta sauke jin ya kamo hannunta yana faɗin “Sai na zo kenan? Ko kuma mu wuce can gidan?” Da sauri ta kalleshi tare da kai hannu za ta buɗe motar “Ba zan samu wani abun ba?”
“Kamar me fa?” Cike da mamaki ta yi maganar. Matsowa yai tare da kai hannunta bakinsa “Irin haka..” Da sauri ta fara waige-waige tana jin wani bala’in kunya na rufe ta. Buɗe mata motar ya yi suka fito tare nan ya sa yara suka kwashe kayan zuwa cikin gida da sauri Zaliha ta fito ganin Nuriyya ce ya sa ta daka tsalle tare da rumgumeta “Wayyo Allah Aunty shi ne ba ku faɗa kuna hanya ba? Ina wuni Daddy barka da hanya” Da murmushi ya amsa mata yana kallon yadda Nuriyya take ƙasa-ƙasa da kai ita ala dole kunya take ji. Wannan yanayin nata ba ƙaramin burgeshi yake yi ba. “Hmmm! Alhaji da ma ina jiran wannan ranar ya kamata in faɗa maka gaskiya dangane da wanna yarinyar da aka liƙa maka, yanzu kai ba ka yi bincike ba ka amince da auren wannan 'yar iskar..” Runtsa idonta ta yi da ƙarfi tare da ƙanƙame hannun Zaliha idanunta na kawo ruwa.
“Ya Subhanallah bawan Allah me kake faɗa ne? Ban fahimce ka ba fa?” Ya faɗa yana kallonta yana son gasgasta zancen nasa duba da yanayi da ta shiga. “Eh Alhaji abin da ka ji na faɗa maka yarinyar nan karuwa ce! Maza uku suka gama hawa da sauka kanta, da farko ni zan aureta amma da na fuskanci halayyarta sai na janye dan ba mace-ta-gari ba ce, burin kowane uba ya samar wa 'ya'yansa uwa-ta-gari sai aka yi rashin dace domin da na fahimci ɓoyayyun halayyarta sai na ga ba zan iya auren fanɗararriya..”
“Innalillahi wainna ilaihir rajiun! Wallahi Daddy ƙariya yake min sharri yake min! Ban san...” Dakatar da ita yai ta hanyar faɗin. “Ya isa haka! Ku shiga gida!” Cikin ɗaga sauti yai maganar muryanshi na nuna zallar ɓacin rai. Baban su ne ya shaƙe wuyar mutumin yana faɗin. “Munafuki la'ananne me haddasa fitina tsakanin ma'aurata sai Allah ya la'ance ka..” Dukan shi yake yana faɗa mishi mugayen kalamai motar shi ya shiga da sauri yana jin yadda kanshi ke juyawa yana ji kamar ba a duniyar yake ba. “Taka mota mu tafi!” Da sauri ta buga motar tana kira sunan shi cikin muryan kuka “Dan Allah Daddy ka tsaya ka saurare ni wallahi sharri yake mun ka tsaya na yi maka bayani ba haka ba ne karka kalle zancen sa. Daddy dan Allah ka saurare ni...” Hannunta Amrah da ƙarasowarta kenan ta riƙe suka nufi cikin gidan tana gunjin kuka “Me ya sa ba ki faɗa ma sa komai ba? Na ɗauka duk ya san abinda ya faru ashe bai san komai ba? Ɗan farincikin da na fara samu aka daƙushe min? Shi kenan ni ba zan ji daɗi ba a rayuwa? Amrah na dawo da niyar karɓan sa a matsayin miji duba da halayyarsa masu kyau da nagarta, Amrah mai ya sa ƙaddara ta zaɓe ni? Sai ni? Komai sai ni ce? Whay Amrah! Me ya sa komai yake zuwa mun a cukurkuɗe? Sai yaushe ne zan yi dariya kamar kowa? Sai yaushe zan samu sukuni na daina fuskantar matsalolin rayuwa? Ni kenan daga wannan sai wannan...”
“Yi haƙuri Noor komai da lokacinsa duk abin da yai farko zai yi ƙarshe wallahi na ɗauka Hajiya Umma ta sanar da shi komai ashe ba haka ba..”
Cikin kuka Nuriyya ta dakatar da ita da faɗin “Ya zan yi? Ban san yadda zan yi mishi bayani ya fahimta ba na san yana can yana saƙa zancen zuci..”
“In Sha Allahu komai zai zo da sauƙi muje ki yi sallah sai mu ƙarasa maganar daga ba ya”
Janta ta yi har ƙuryar ɗaki Nuriyya kam ta yi shuru tana kallon ikon Allah domin an canza fasali da tsarin gidan an ware part ɗin Maman Nafisa da ban haka ma nasu kowane da toilte an gyara tare da zuba kayan alatu “Duk cikin sati biyu aka yi wannan aiki? Waye ya yi?”
Zaliha da ke ƙoƙarin girka mata taliya ne ta amsa da faɗin “Aikin mijinki ne duk shi ya yi mana wannan abun arzikin” Shuru tayi tare da ajiye handbag ɗinta ta nufi bayi wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala tana fitowa sai ga Fiddoh ta shigo da ihun murna ta rumgumi Nuriyya “Su amare an yi fresh kinga yadda jikinki yake wani glowing kuwa? Kin yi kyau kin cicciko lallai an ji...”
“Ke kam Allah ya shirya mana wannan bakin naki” Dariya ta yi tare da kwanciya saman Bed tana faɗin “Ina zanga Alhaji na? Taɓ! Wallahi na yarta aure ni’imomi gareshi tun da ga shi na gani da idona..” Tsaki Nuriyya ta yi don ta lura magana take son saka ta. Zaliha ce ta faɗa wa Firdausi abin da ya faru.. Tun kafin ta dire zancen nata Fiddoh ta wuntsilo tare da faɗin “Kan babban buran uba! Ai kuwa zai na ci kan uwar..”
Riƙe ta Nuriyya ta yi ganin yadda ta zaburo tana shirin fita ta san kuma muddin ta fita maganar ba zai tsaya iya nan ba sai an kai ga 'yan sanda dan kaɗan ne daga halin Fiddoh abu in dai ya shafe ta ko Maman su ba ta wasa da shi. “Mene ne haka? Dalla malama cika ni saina koya mishi hankali wallahi da sojoji zan haɗa shi su ci uban ɗan shegiya”
“Eh na san haka za ki yi shi ya sa ba na so ki fita Baba ma kaɗai ya ishe shi ba sai an kai ga hukuma ba..”
“Kina nufin kenan na ƙyale shi?” Cike da takaici ta miƙe tana jan tsaki sannan ta sake faɗin “Wannan shegen zuciyar naki ba ya faɗa miki gaskiya” Fita ta yi tana ashar domin dai ba ta cikin hayyacinta shi ya sa ma ta yi saurin dakatar da ita. “Ai da kin ƙyaleta wallahi..” Da sauri Nuriyya ta ce “A'a Amrah ba ki ganin halin da take ciki ne? Ta yaya zan barta ta je ta yi abin da za a dawo ana da-na-sani?”
Amrah ta ce “Kuma haka ne fa Allah ya kyauta, ina wayarki?” Kallon Zaliha da ke ajiye musu abinci ta yi tare da faɗin “Ɗauko min waya yana cikin jakar can” Juya wayar Zaliha ta yi tana faɗin “Wow! iPhone 14 pro max! Aunty Nuriyya wayyo Allah! zan kashe selfi..” Karɓan wayar na yi ina faɗin “Damuwarki ragagge ne”
“Noor ai gaskiya ce koni na yaba lallai an tsuma Daddyna dole kema ya gwangwajoki da wannan wayar da ake ya yi” Ta faɗa tana jujjuya wayar ita ma kana ta kira layin shi sai dai har kiran ya katse ba a ɗaga ba, sake kira ta yi amma still no answer sai da ta jera mishi five miss call bai ɗaga ba kallonta na yi domin tuni zuciyata ta sake karyewa murya na rawa na ce “Kin gani ko? Ya ƙi ɗaukar kiran...” Na ƙarasa maganar hawaye na zubo min “Tura mishi saƙo" Karɓan wayar na yi hannuna na rawa na rasa ma me zan rubuta kallon ta na yi tare da yin shuru “Noor ki nutsu! Mijinki ne a wannan ɗan tafiyar da kuka yi, ya ci a ce kin fahimci wa kike aure sati biyu ba wasa ba..”
“Wallahi Amrah na kasa tuno komai ban san abin da zan rubuta mishi ba, kuma ma ba zama yake ba, bare har na karanci halayyarsa..” Amrah ta katse ta da faɗin “Ki tuna dai!” Runtsa idona na yi da ƙarfi nan sauran hawayen suka zubo a hankali na fara rubuta mishi kalamai har na gama sannan na tura mishi muna zaune har 10 domin ta ce a nan za ta kwana tun da Mamanmu sun je biki ƙauye ne. Abinci ma sai da ta takura min kafin na ci kaɗan.


****
Kiran wayar Laraba ya yi yana tambayarta ina ta tafi nan take sanar masa tana Lagos amma jibi za ta dawo bai tsaya jin ƙarshen maganarta ba ya kashe wayar tare da jan dogon tsaki wanka ya yi yana jin wani azaban ciwon kai gefe ɗaya yana ganin kiran Amininsa amma ya ka sa ɗauka sai da ya yi wanka tare da sallah sannan ya kira shi suka gaisa “Ya na ji muryan ka haka? Wani abu ya faru ne?” Murya can ciki ya ce “Mu haɗu a gidan Hajiya Umma sai mu yi maganar gabaɗaya a can” Da ƙyar ya yi driving zuwa gidan yana isa ya zube a kan kujera yana mayar da numfashi tare da runtsa ido yana mai dafe kanshi gefe guda “Oyoyo Daddyna!” Suhaima ta faɗa tare da zama kusa da shi. Buɗe daurewa ya yi suka yi ɗan hira domin ba ya so ta fahimci halin da yake ciki, sai da Abban Amrah ya ƙaraso kafin ta shiga ciki ganin Hajiya Umma ta fito ga dukkan alamu magana mai muhimmanci za su yi.
“Lafiya naga duk ka yi wani irin?” Murya can ciki ya ce “Umma akwai abin da ya dace na sani a kanta ne? Akwai wani abin da ya kamata in sani ne?” Haɗa baki Umma da Hon. Sa’id suka yi wurin faɗin “Kamar ya fa?”
Furzar da iska me zafi yai daga bakinsa tare da cije leɓe yana faɗin “Ina magana ne a kan Nuriyya domin na ji abin da bai min daɗi ba..”
“A ina? Wa ya faɗa maka?” Umma ta faɗa tana kallon shi. “Kenan da gaske ne? Shi ne ba ki sanar da ni...”
“Dakata min haka! Akwai wadda ya isa tsallake ƙaddararsa ne? Ba na son dogon magana Aminu! Ka shirya maganar tarewa ka gyara ɗayan gidanka domin ban yarda da tuban da Laraba ta yi ba”
Ɗagowa ya yi da jajayen idanunsa yana kallon yadda take masa magana “Tarewa yanzu?” Miƙewa ta yi tare da nufan hanyar ɗakinta ta barsu a wurin. Bin bayanta yai da ido yana jin kanshi tamkar zai faɗo ƙasa saboda tsananin sarawar da yake yi, domin maganar tata ya sake dilmiyar da shi zuwa ga wani irin tunani na daban nan take zuciyarshi ya shiga kitsa mishi abubuwa a kanta.
“Wai me ke faruwa?”
“Komai ma ya faru” Nan ya kwashe komai ya faɗa masa “Yaa Subhanallah! Kai! Wannan batun ba gaskiya ba ne..” Kallon sa Alhj Aminu yai tare da faɗin “To yaya ne? Kana ji dai Umma da bakinta ta tabbatar mun..” Wani irin kallo yai masa tare da faɗin “Ban ji inda Umma ta ce maka 'yar isaka ba ce, ban ji ta ce maka komai dangane da wancan zancen ba. Kai Aminu! In ka ce za ka bi maganar mutane wallahi kashe maka aure za su yi gwara tun wuri ka kawar da wannan mugun tunanin a ranka Nuriyya ba za ta taɓa aikata haka ba” Shuru kawai ya yi masa. Koda ya dawo gida tunani ya shiga yi a haka kiranta ya shigo wayarshi bai ɗauka ba, hatta saƙonta ma bai kula ba, haka aka shafe kwana biyar tana kiran wayarshi tare da tura mishi saƙo duk ta kasa nutsuwa tun tana kukan ɓoye har ya zo ta kasa daurewa Amrah ma ta yi ƙoƙarin kiran shi amma wayar ba ta shiga koda ta samu Abbanta da maganar ya yi matuƙar mamaki jin har yanzu bai bar wancan maganar ba, nan take sanar da shi ainihin abin da ya faru da ita. Ya ji matuƙar tausayinta sosai jin wannan mugun ta'asar da aka yi mata.
“Noor!” Buɗe shanyayyun idanunta ta yi tana kallon Amrah “Ki shirya muje ki duba Daddy ba ya Jin daɗi”
“Ni ba zan iya zuwa gidan matarshi ba..” Hararanta Amrah ta yi sannan ta ce “Dalla can malama ki tashi muje matarshi ba ta nan” miƙewa ta yi tana ƙoƙarin saka hijjabinta “Dan Allah je ki yi wanka bari na dafa mishi wani abun ba haka ake zuwa dubiya ba” Dan dole ta shiga ta yi wanka doguwan rigan material ta saka sannan suka fito bayan ta shafa turarukan da ta ajiye mata, cikin gida ta bayar da makulli a ajiye wa Zaliha dan ta tafi islamiyya.
Zama suka yi tana ƙare wa falon kallo ganin yadda aka narka dukiya, nuni Amrah ta yi mata da ɗakinsa sannan ta fita tare da faɗin “Noor ki shiga ki duba shi ina zuwa” Kiran wayarshi na yi ina tunanin ko zai ɗauka amma har kiran ya tsinke bai ɗaga ba. Saƙo na tura mishi _Daddy ga ni a falon na zo duba jikinka._ Kusan minti shida ba reply nan take jikinta ya ƙara yin sanyi miƙewa ta yi a sanyaye ta nufi hanyar ɗaki daidai ya fito toilte ɗaure da baban towel a ƙugunsa wurin wayarshi ya nufa domin tun yana wanka ya ji ana kira ɗaukar wayar ke da wuya ya ji sallama juyowa yai ganin ita ɗin ce ya sa shi ɗauke kanshi yana duba kiran da ta yi masa tare da saƙon “Daddy ya jikin?” Murya na rawa ta yi maganar shuru yai mata tare da ajiye wayar ya nufi gaban mirror yana ƙoƙarin shafa mai da turare, matsowa ta yi tare da ajiye wayarta gefen sofa ɗin sannan ta kai hannu ita ma kan mai ɗin da yake ƙoƙarin shafawa da sauri ya kalleta ganin hannunta ya kan nashi marerecewa ta yi kamar za ta fashe da kuka ganin yanayin da take yi mishi ya sa shi ɗauke kai daga kallonta a hankali ta ɗiba mai ɗin tare da kallon shi kaɗan kafin ta kai hannunta ƙirjinshi jin tattausan lallausan hannunta cikin fatar jikinshi ya sa tsigar jikinshi miƙewa da ma ga shi kwana biyun nan daurewa kawai yake, lumshe idanunshi yai tare da sauke ɓoyayyen ajiyar zuciya. Yanayin da take tafiyar da hannunta a jikinshi ba ƙaramin gigitashi take yi ba.
“Dan Allah ka yi min magana mana..” Buɗe tsumammun idanunsa yai tare da watsawa cikin nata murya a shaƙe ya ce “In ce miki mene?”
“Dan girman Allah ka yi haƙuri wallahi Allah ban taɓa aikata wani abu na alfasha ba, namiji bai taɓa riƙe koda yatsata ba, duk maganar da aka faɗa ba haka ba ne Daddy fyaɗe aka min wallahi bayan wannan ƙaddara sai kuma Aurenmu..” Da wani irin kuka me karya zuciya ta ƙarasa maganar. Tun da ta furta kalman fyaɗe ya runtsa idanunsa yana jin wani abu ya tokare masa ƙahon zuciyarsa share fuskarta ta yi ganin har yanzu ya ƙi yi mata magana “Shi kenan zan tafi tun da ba ka yarda da ni ba Allah ya ƙara lafiya” Juyawa ta yi sauri duk yadda ta so tsayar da hawayenta kasawa ta yi domin haka ya ci gaba da tsiyaya tamkar a buɗe famfo buɗe idanunshi yai tare da saukewa a bayan ta taku biyu yai tare da riƙo hannunta cak ta tsaya tana sauraron numfashinsa da yake sauke mata a bayan ta, juyowa da ita ya yi tare da faɗin. “Ba wai ina fushi ba ne, ina jin zafin abin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login