Showing 72001 words to 75000 words out of 120090 words
yana kunna redio'n ƙaramar wayarsa,babu jimawa aka fara labaran kamar yadda aka gaya masa,da sauri Lamir ya miƙe yace "what..? ubanwa ya faɗi wannan abun?" da mamaki suke kallonsa kafin Governor Mubarak Yahya cibo yace "kai mene naka?koma waya faɗa ai ya ƙara taimakon mune" cikin ɓacin rai Lamir yace "waya fada wannan labarin a cikinku?idan kun san kuna da hannu ko faɗa min wanene?" Hon Faisal Lawan yace "haba Lamir,babu wanda yabar a cikinmu gaba ɗaya muna tare,sannan dukkan abinda ake shiryawa ai dakai ake komai,munsan cewa munyi niyyar watsa photo nan,amma kuma ba'a samu ba,banda haka ai babu abinda muka tsara wanda kai baka sanshi ba" da kallo kawai ya bisu kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice daga cikin gidan.
Mama kam tana zaune ita ɗaya sai mai aiki Laure wacce tace tazo ta zauna wajanta kafin masu gidan su dawo,tana dai zaune amma minti kaɗan zata miƙe ta leƙa waiko sun shigo, ɓangaren Aryan bawai haka nan yaƙi zuwa wajan zaɓe ba, tunda safe ya tashi da kasala da faɗuwar gaba yanzu ma yana ƙwance saman bed sai juyi yake kamar wanda bai da lfy,Imran Irfan da Jafar duk suna waje guda wajan zaɓen,ga dai alamomi nasara suna gani amma fuskokin su gaba ɗaya babu walwala,gudanar da aikin zaɓen suke babu kuzari a tare da su, Ambulance ɗin na parking a harabar asibitin nurses suka ƙarasu wajan da gadon marasa lfy, ɗaya bayan ɗaya aka dinga ɗura su akai, Nihila da Mameey banda kuka babu abinda suke, Abbou kuwa yana baka taɓa gane halin da yake ciki, lokaci zuwa lokaci yake danne saitin zcyarsa, manyan likitoci suka rufo akansu.
Lokaci kaɗan Labarin accident ɗin Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo da iyalansa suka karaɗe Garin Ibadan da kewayanta, cikin tashin hankali Jafar da Imran da Irfan suka ƙarasu wajan,kallo guda zakai masu su baka tausayi,babu jimawa shima Lamir ya ƙarasu wajan,har yanzu babu wani labari gane da halin da suke ciki domin babu likitan daya fito,Wajan 1:40 Alhaji khamal mahaifin Nusaibat shida matarsa Hajia Atine suka ƙarasu wajan domin ko Nusaibat basu faɗawa ba, lokacin guda asibitin ya cika da mutane,sai da securities ɗin Jalal suka fara kurar mutane ya rage family ne kawai a wajan,misalin 3 dai-dai likitocin suka fito daga cikin emergency room ɗin sai share zufa suke,da sauri Abbou dasu Jafar suka miƙe tare da faɗin "Dr wanne hali suke ciki?"goge glass ɗin hannunsa babban likitan yay kafin yace "muje office tukunna" gaba ɗaya suka mara masa baya banda Alhaji khamal da Irfan wanda ya kasa mutsi dan fargaba,kujera Dr yaja ya zauna tare da nunawa Abbou waje ya zauna,amma sam Abbou bai san me Dr yake cewa ba hankalinsa yana wani wajan daban,ga wani sarawa da kansa yake yana runtsa idanunsa sai yaga abubuwa da yawa suna maza gizo a cikin idanunsa, Jafar ne ya kama hannun Abbou ya zaunar da shi a kan kujera kana yace "Dr yaya ake ciki ne Please,ka faɗa mana halin da suke ciki ka riga kasan ko waye shi a wannan garin,so Please ka faɗa mana muma hankali ya kwanta" jinjina kai Dr yay kafin yace "Allhamdulillah,da farko wajan shi Ur excellence ɗin da sauƙi,ya samu tension ne,wanda shine yaja masa ɗaukewar numfashi tun kafin faruwar accident ɗin,sannan ita yarinyar tsoro ne yay mata yawa sai kuma ɗaukewar numfashi data samu wanda yaja mata ta shiga duguwar suma,to duk su biyun nan da wani lokaci zasu farko..,"shuru yyi yana sauke numfashi ba tare da kuma da yace komai ba,Imran ne yaja numfashi yace "Mummy fa?" Kallon Dr Abbou yay abinda yake ta son cewa kenan sai kuma Allah ya taimake sa,baya Dr yayi yana sauke ajjiyar zcya kafin yace "ban san yaya zance maku ba,amma dai ita sai dai mu bita da addu'a" zcyar Abbou ce ta buga da ƙarfi kafin ya tattara nutsuwar yace "kamarya?" Jafar yace "kai mana maganar da zamu fahimta Dr kasa zuƙatanmu cikin zullumi da kuma fargaba" Dr ya fesar da numfashi kafin yace "Ta samu buguwa a kanta, ma'ana kanta ya fashe,sannan ancire mata wani ƙarfe a cikin wata sanadiyar cakarta da ƙarfan yay ya tsinka mata hanjin cikinta,abu mara daɗin kuma glasses ɗin daya caki wuyanta harya taɓa maƙoshinta"Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"kafin Jafar yace "yanzu Dr mene condition ɗin da take ciki?" Fesar da numfashi Dr yayi kafin yace "she's critical condition,amma in sha Allah everything will be fine ok"da ƙyar ya sauke ajjiyar zcya kafin ya saita numfashinsa yace "zamu iya ganinsu yanzu?"miƙewa Dr yay yace "of course"gaba ɗaya suka miƙe tare da bin bayan Dr kowa da abinda yake tunani a ransa,wani ward suka nufa kai tsaye Dr ya shiga wani special side,wajan part biyar ne a side ɗin,room ɗin farko suka tarar da Mummy ƙwance an juna mata Oxcygen ta cikin bakinta gefen kanta an naɗeshi da bandeji haka ma wuyanta, cikinta ba an sanya anduga da filasta,kana an rufe jikinta da wani green ɗin abu, ɗakin sai ƙarar na'urori gefen hannunta an maƙala mata drip yana shiga a hankali, ƙirjinta dake ɗagawa shine kawai yake nuna tana raye,da sauri Abbou ya juya domin bazai jure ganin halin da matar tasa take ciki a halin yanzu ba,cikin zallar tausayin halin da take ciki Jafar yake kallonta yana jin ƙwalla na tarar masa a idanunsa, juyawa yay ya fita a room ɗin, Imran na fita yay ya rufe ƙofar,daga nan wajan Jalilerh suka shiga itama tana ƙwance an saka mata Oxcygen sai drip,hucin numfashin dake fita ta hancinta shike nuna tana raye,amma babu kurjewa ko ɗaya a jikinta,daga nan suka nufi room ɗin da aka saka Jalal a ciki,tun daga nesa suka hango farar fatar jikinsa data ƙarayin jaaa,ga wani haske data ƙara tai fresh,da sauri Abbou ya ƙara wajan Jalal yana zuwa ya zauna tare da kama hannunsa sai a lokacin wata ƙwalla ta sauka daga cikin idanunsa, ƙwance yake flat ko riga babu jikinsa sbd wani gumi da yake haɗawa duk da sanyin a.c dake kaɗawa a ɗakin,cikin nutsuwa yake fidda numfashi,fuskarsa ta faɗa lokaci guda kamar wanda ya shekara yana jinya,ga yadda sumar kansa ta hargitse,babu abinda aka juna masa sai drip da injection da ake masa,cikin ƙasa da Murya Abbou yace "am so sorry Muhammad,nina ja maka laifi nane,dana san wanene ni da tuni na bai yana gsky,bana da ikon faɗin komai akai na sbd sa gske ban san yaya nake ba,ina da asali bana dashi ban san komai a kaina ba Muhammad,ka yafemin kada kalleni da laifin da banawa ba,ban taɓa dana sani irin na yau ba,ban taɓa ƙunci da shiga damuwa irin na yau ba, Tabbas ni me laifi ne,bansan da wanne baki zanyi maka bayani akan wanene kai ko kuma wacece mahaifiyarka,dan Allah ka gafarta min Muhammad" ya faɗa yana ƙara ƙanƙame hannunsa,wasu siraran hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Jalal,cikin rawar jiki kuma ya riƙe hannun Abbou'nsa nasa still hawaye na kwarara a idanunsa, Jafar tuni yabar room ɗin sbd bazai iya kallon abin tausayin nan ba,lura da halin da Jalal ke ciki yasa likitoci suka rufu akan,cikin zafin nama ya miƙe tsaye tare da fisge drip ɗin da yake hannunsa,wasu likitoci ne suka nufu inda yake suna zuwa yasa hannu ya hankaɗesu cikin sauri haɗi da gudu ya fice daga room ɗin.
MANAGE🌚naje hospital ne.
UNCLE NE pay before you read 08119237616
NIMCYLUV
7/5/21, 7:31 AM - Buhainat: Uncle ne
78-79
Wata zabura Abbou yay jikinsa duk rawa yake,cikin ɗaga murya yace "what...kin san mene kike cewa kowa?noo!! Nasan zafin ciwo yake sakin wannan zantukan,komai zaiyi dai-dai Please Oum Jalal ki daina wannan maganar na roƙeƙi kada ki sanya zcyta bugawa"ya ƙare maganar a lokaci na farko da wasu hawaye Masu zafi suke sakkowa daga cikin idanunsa, Jalal kasa da idanu Yake kallon iyayen nasa ba tare daya iya cewa komai kuma, Nihila kam saurin miƙewa tayi tana jin maganar kamar a mafarki, Lamir kam tuni yabar room ɗin yana zcyarsa nata fasa,sbd ganin komai yana shirin ruguje masa ba tare da yakai ƙarshe ba, murmushin takaice Mummy tayi kafin wasu hawaye ya fara saukowa daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta,cikin rawar murya tace "wannan ranar nake jin tsoran zuwanta, ranar da zan fallasa asirin zcyata,na cuci kaina da nabiye ruɗin shaiɗan,zata iya yiwuwa kuga laifina,amma banyi hakan da son raina ba,nayi haka ne domin ceton rai" Aryan ne yace "Mummy kinata bayani a rufe,yana da ƙyau koma mene kika aikata ace kin faɗa domin ki ciremu daga cikin ruɗu" ɗan yunƙurawa tayi zata miƙe zaune Jalal ya kama ta tare da jinginar da ita a jikinsa,wasu sabbin hawayen ne suka wanke fuskarta kafin tace "tabbas Jalal ni ba haifiyar ka bace kamar yadda kake tunani,dani da mahaifiyarka ƴar wa da ƴar ƙanwa ce, Mama itace ta haifi mahaifiyarka Zulfa,ni kuma Mama Yayar mahafiyata ce dani da yaya Lamir, sanadiyar rasuwar iyayen mu yasa muka dawo wajanta da zama, Allah ya jarabci Lamir da son mahaifiyarka Zulfa so bana wasa ba,kafin ya bai yana abinda yake ransa mahaifinka yaga Zulfa yace yana SO,nan Lamir yace sam bazai taɓa yiwuwa ba,a nan ya faɗa mata cewa yana sonta,ita kuma lokacin soyayyar Alhaji Kabeer tayi nisa a ranta,don haka tace bata son Lamir Alhaji Kabeer takeso,sosai tashin hankali ya gama bai yana akan fuskar Lamir ya rasa wanne mataki zai ɗauka,gashi bashi da tunun dafawa,ana haka aka fara shirye-shiryen aure,ana saura ƙwana guda aure Lamir yazo da labarin mahaifinka Alhaji Kabeer bashi da asali domin babu wanda yasan wanene shi da kuma iyayensa, Mama tace babu komai ita dai ta yarda da shi,sosai Lamir yay baƙin ciki domin a tunaninsa Mama za tace an fasa auran shi kuma a bashi auranta,haka akai aure cikin mutunci da kamala,domin Alhaji Kabeer yana da dukiya da kuma rufin asiri,bayan an kai Zulfa ɗakinta,wata rana ina zaune a cikin uwar ɗaka kamar mai bacci naji Lamir yana faɗin _ya fison data haihuwa aje har gida a kasheta sannan a kashe mijin,idan kuma hakan zai basu wahala kawai su kasheta subar gidan,idan har suka kasheta shi kuma zai nemi auren wata yarinyar sai yace a bashi riƙon abinda ta haifa daga nan duk dukiyar da mahaifin Zulfa ya bari ɗan ta zai kajeta shi kuma zai riƙe ɗan kaga dukiya ta dawo wajansa_ wannan dalili yasa na fahimci manufarsa ta son auran Zulfa da yace zai yi,dalilin guda ɗaya ne akan dukiyar da mahaifinta ya mutu ya bar mata kasan cewarta ƴa ɗaya tilo garesa,sosai na shiga tashin hankali,kullum cikin tunani nake har na rasa wa zan faɗawa abinda yake damuna,kwanci tashi aka wayi gari Zulfa nada ciki sai tashin hankali na ya nunku fiye dako wanne lokaci,wata rana na shirya naje gidanta,a zaune na sameta cikin shigar duguwar riga abaya mai kalar milk sai touchs ɗin yellow,zama nayi ina gaidata kafin tai Murmushi cikin fuskar mai cike da annuri wacce ta rabuwa da fara'a tace "Ina Mama? Taƙi zuwa ta ganni bata sani ba zan haife abin cikina lafiya ko akasin haka" gaba nane ya faɗi sbd jin abinda ta faɗa,sai kuma a wannan lokacin na tuna da maganar Lamir, Murmushi nai mata nace "haba Anuty ki daina faɗin haka,in sha Allah zaki haihu lfy" kallona tayi sannan ta kalli cikin nata tace "ai Ɗan da zan haifa bashi da wata damuwa indai kina raiye kamar ni ce,dan haka tun yanzu abinda na haifa mallakin ki ne"tsayawa kawai nayi ina kallonta sbd abin na keji kamar almara,daga haka mukai sallama na koma,ina zuwa naita tunanin yau shene E.D.D ɗinta zai cika?kawai sai na kirata a waya na tambaya babu musu ni kuma ta gayamin,ana saura ƙwana ɗaya zata haihu na buga sammako zuwa wajan wani malami sbd na aikata abinda nake gani shine kawai hanyar da zanbi na tseratar da rayuwarta,nan najewa malamin da buƙatar ina son ya haukata min Zulfa,amma ba haukan da zai cutar da ita ba,nai masa bayanin komai,zane yay a jikin ƙasa kana ya ɗago kai yace "za'ai maki abinda kikeso,amma tabbas abinda yake cikinta shima haukan zai taɓasa indai ba ta haihu kafin haukan ya risketa ba" shuru nayi ina nazarin maganarsa sai kuma nace "babu damuwa indai ba wani abu bane mai illa"ban baro wajan ba sai da aka tabbatar min da aiki ya kammalo,a ranar bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauke ni tunanin abinda na aikatawa ƴar uwar tawa ya dinga damuna,shin nayi dai-dai kowa? Shi ne abinda zcyata ke ta damuna da tambaya kenan,amma idan na tuna abinda Lamir ke shirin yi sai naji abinda na aikata shine dai-dai, washegari da safe kasa breakfast nayi nabi na damu kaina,ina wannan tunanin na tsinkayi Muryar Mama na sallati da sauri na fito ji kina yana rawa,kallonta nayi nace "Mama lfy?" Cikin damuwa ta shaidamin haihuwar Zulfa da kuma neman ta da akai aka rasa, ɗaki na koma naci kuka na ƙoshi domin duk abinda ya faru NICE SILA,lokacin da Lamir ya samu labari kasa cewa komai yay sai zirga-zirga da ya dinga yi a gidan,yafi kowa damuwa akan abin,bayan haka nice na buƙaci auran mahaifinka domin riƙonka ya dawo gareni, Lamir baiso haka ba,amma haka na rufe ido nace dole ya barni, tun daga nan rainonka ya dawo gareni,ni kuma kullum cikin fargaba nake bana iya bacci ga kuma mafarkan da nake marasa daɗi,ashe abinda naiwa Lamir yana nan ƙasan ransa kuma bokansa ya bashi Labarin ina da hannu wajan ɓatan Zulfa,nan ya ɗura min ƙiyayya sannan yaci alwashi akan abinda zan haifa nan gaba,tunda nazo gidan babu taɓa tarayya da Abbou Jalal ba naje an sauke masa sha'awata sbd wani dalili nawa"
Saurin yin shuru tayi sbd yadda numfashinta yake fisga da ƙarfi ga kuma yadda computer take ƙara ihu alamun rai ya kusa halinsa, Muryar Jalal can ƙasa kamar bai son magana yace "bani Oxcygen"da mmki Dr ya kallesa sbd yasan cewa Mummy ita sa rayuwa sai dai wani ikon Allah, Dr yace "Ur excellence Oxcygen kuma?"da ido kawai Jalal ya kalli Dr alamar "eh" bai gardama ba ya miƙa masa, tallafo kan Mummy yay zai sanya mata Oxcygen ɗin tayi saurin riƙe hannunsa tace "mene yay saura kuma?baka son na faɗa maka cikar muradina ne?ko kuma baka son na faɗa maka asalin uban Nihila?zuwa yanzu kaine garkuwanta kai kawai zan iya damƙawa amanar ta,kai kaɗan nake da tabbacin zaka kula da jini na ko bayan babu rai na"sbd ɓacin rai da tashin hankali idanun Jalal har wani ruwa yake,ga fuskar tayi jajir, pouting lips ɗinsa yay cikin dauriya yace "wanna maganar duk babu amfanin ta,abu guda nake nema wajanki wanda nakeso kiyi min alfarmar sa"cikin sauri Mummy tace "babu abinda bazan iya yi maka ba Jalal,sai wanda Ubangiji ya sanya bazan iya yi maka shi ba" ajjiyar zcya ya sauke tare da jan numfashi kana ya lumshe idanunsa yace "yaya kamin Ammina take?"Murmushi Mummy tayi kafin ta kalli Irfan tai masa nuni da madubin data gani a jingine,da sauri ya dauko madubin ya kawo mata, karɓar tayi da hannu ɗaya kana ta sai tashi a fuskarsa tace "buɗe idanunka" a hankali ya buɗe idanunsa tare da sauke ganinsa a kan madubi,cikin sarƙewar numfashi tace "kaga kamannin mahaifiyarka,aduk sanda nake tare dakai inaji kamar da ita nake tare ne,komai nata ka kwashe sa,hatta dimples ɗinka irin nata ne...Ware idanunsa ya ƙara yi yana mai ƙara kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubin,wayar Jafar ce tayi ƙara da sauri yay picking ganin sunan Prince Hassan,daga can ɓangaren Prince Hassan yace "an kammala zaɓe gamu yanzu mun ɗauki hanyar zuwa hukumar inec domin tabbatar da wanda ya samu nasara a zaɓan,amma in sha Allah Ur excellence Jalal shine da nasara domin muna ganin alama" jinjina kai kawai Jafar yay kafin yace "on mah way in sha Allah"yana faɗin haka ya kashe wayar kana ya juya yabar cikin room ɗin domin bazai iya ƙarasa jin wannan labarin ba,da idanu kawai Jalal yabi Jafar, Jalal ne ya kalli Mummy wacce take ta fama da jan numfashi kafin yay magana tace "bayan na ɗauki hukunci ɗaukewa Oum Jalal sha'awarsa akai na,saina fara tunanin tayaya zan haifi ƴar wacce zata zama na a gurbina ko bayan babu raina,hakan tasa wata rana naje har office ɗin Alhaji khamal na nemi alfarma a wajansa,kallo na yay yace "haba Oum Jalal wanne abin naki gsky aƙwai hatsari a cikinsa,bazan iya cin amanar amini na ba,wannan ai shi ake kira da CIN AMANR RUHI,tayaya zanyi mu'amala da matar aminina,gsky bazan iya ba"cikin kuka na kalli Alhaji khamal nace "ka taimakin dan Allah, wallahi banyi da wata manufa amma ina dalili na faɗin hakan kuma kasan komai na faɗa maka" cikin wani hali Alhaji khamal yace "yanzu idan na yarda kika samu ciki kika haihu mene sunan yaro ko yarinyar da kika haifa? Shege fa kenan..
MANAGE dan Allah Wlh bana gida😇
Uncle ne isn't free is for sale just pay before you read 08119237616
By
NIMCYLUV
7/6/21, 8:52 AM - Buhainat: UCL NE
_80-81_
A gsky lamarin aƙwai abun dubawa,ina yare na haifi ɗa a kirasa da shege,nikam ba zan iya wannan ɗan yan aikin ba,cin amana ido biyu"zubewa nayi a ƙasa tare da dafa ƙafafunsa ina kuka kamar raina zai fita nace "ka taimake ni,kayi min rai babu wanda zan iya tunkara da buƙata ta sai kai,kai ne ka cancanta da kazama uba ga ɗan da zan haifa,bana da wani ƙata kuma burina bai huce ɗan da zan haifa ya samu kyakkyawar mu'amala a wajan Jalal ba,a yanzu burina bai huce na sama yarinya mace ma wacce zan haɗa ta Jalal domin ya zama garkuwa gareta,ina da tabbacin bazai taɓa bari jinina ya hulaƙanta ba sai iya rasa komai akan ya rasa ɗan dana haifa,kaga idan har Jalal na raye Lamir bazai taɓa samun nasarar cutar da ita ko shi ba,dan Allah ka taimaka min Please" na ƙare maganar ina ƙara sautin kuka na,shuru Alhaji khamal yay,ban san mene yake tunani ba sai kawai naji yace ya "amince amma bisa sharaɗi guda"da sauri nace masa "sharaɗin mene?" Kallonta yaga da gaske