Showing 30001 words to 33000 words out of 120090 words

Chapter 11 - UNCLE NE Complete

Unknown   

11 Nov 2024

5846

ba kamar yadda Abbou bai ƙara cewa komai ba.
da daddare bayan ya dawo gida daga meeting ɗin da sukai ya shige part ɗinsa yyi wanka ya sauya kaya zuwa wani farin yadi mai manyan zane,Black cap ya saka tare da sanya Black cover shoe ya fesa turare,yana gamawa ya fito,yana zuwa main parlour Mama tace "yawwa irin albarka,wanda ya sha Nonon albarka, daure ka siyomin tsire wlh yau tun safe nake sha'awar cinsa kamar mai yaron ciki, zcyata sai tashi take" kai ya ɗauke daga kallon Jalilerh wacce take sanye da riga da wando gashinta an rabashi gida biyu ansaya masa stone,ya sakko har wuyanta ta zama kamar wata ƴar baby, yace "da sauranki tunda zucyar har yanzu tana jikinki" miƙewa tayi tace "daman na sani bana da wani gata a gidan nan,da Lamir yana nan babu abinda zan nema wajansa yaƙi,kai amma dai bakai halin ƙwarai ba,atooo rowa dai babu ƙyau kuma wanda kaba yar shine rabonka wanda kaci kuma kashinsa zakai" ta ƙare maganar tana sauya fuska tace "nina san da wasa kakemin domin kana da zcyar tausayi ba kamar waccen yaron da yake tafiya kamar zai kifa,kai aini jiya naga daɗin ƙiba a talabijin kana jin na baka lbr...," da sauri ya miƙe yace "a'a zan siyo maki riƙe labarinki" da sauri Jalilerh ta sakko daga saman sofa ta karaso wajansa tace "uncle zani"baice mata komai yyi tafiyar,daga saman upstrais Abbou yace "my dear bisa mana"tana jin haka tabi bayansa da sauri yana ƙoƙarin shigewa cikin motarsa yaji ta kama hannunsa,zame hannun yyi tare da sakar mata ranƙwashi a kanta da sauri tayi ƙasa ta durƙoshe a wajan tana kukan,kafin yyi wani yunƙuri Aryan ya ƙarasu wajan tare da sanya hannu zai taɓa Jalal ya sanya hannunsa gaba ɗaya ya ɗauketa zuwa cikin motar yana zuwa ya cilla ta a side ɗin gaba shima ya shige mazaunin drever,baiko kalli inda Aryan yake ba sai da Aryan ɗin yace "yaya daman wasu matasa ne sukeson ganawa dakai gobe,amma ban basu dama ba sbd naga kana busy,sannan wasu ƴan jarida ma sun turo katin gayyatar ka zuwa gidan t.v ɗinsu domin su tattauna dakai akan takarar daka fito" lumshe idanu yyi yace "matasa san kace gobe suje gida gona ina can,su koma gidan t.v kace sai week end" yana faɗin hakan yaja motarsa ya fice daga cikin gidan,kai tsaye wani restaurant ya nufa mai suna vip restaurant yana zuwa yyi parking a parking space ya fito,hannu tasa zata fito taji ya kulle ƙofar,dole ta zauna ciki tana kumbure-kumbure,kai tsaye cikin restaurant ɗin ya shige yana shiga ma'aikatan wajan sukai masa barka da zuwa tare da bashi kujera"no ba zama zanyi ba" oder ya basu yana bayarwa yace akai masa mota yana faɗin hakan yyi gaba abunsa,yana gaf da shiga cikin motar yaji ana faɗin "Assalamu alaika"


juyawa yyi a hankali ganin macace yasa ya ɗauke kansa gefe guda kafin a hankali kuma yace "Wasalamu alaiki" yana faɗin hakan ya shige cikin motar yana jiran a kawo masa oder da yyi, ƙara ƙarasuwa jikin motar tayi tare da sunkuyar da kanta dai-dai saitin Kofar motar tace.


"Allah yasa ban katse maka hanzari ba,nayi tunanin rabuwa dakai ganin kamar sauri kake amma zcyta taƙi amincewa da hakan,ina fatan zaka fahimce ni"

Jalilerh take motar ta ɗago kanta a hankali kuma tayi ƙasa da muryarta tace "who is she?" kafin ya bata amsa Hibba tace.


"i"m Hibbatullah Mubarak Yahya cibo,kuma ina sha Allah am going to be ur Aunty soon"

ɗauke kai Jalilerh tayi bata sake magana ba,sai wayar bobo ta taci gaba da dannawa tana game.

numfashi ya sauke kafin yace "ok thanks,the You want me to help you?" ya ƙare maganar yana ƙwace wayarsa daga hannun Jalilerh sbd kada tayi masa restore, murmushi Hibba tayi kafin tace.

"Kawai ka birgeni ne tun a wajan siyan mota,nai ta binciken inda zan sameka sai gashi yanzu Allah ya haɗamu,idan babu damuwa ina son sanin sunanka?"


horn ya danna a motarsa wajan 10 seconds ya kalleta yace "Muhammad Jalal bobo" ɗan waro idanu tayi haka nan taji kamar ta taɓa jin sunan but at where? shine abin tambayar amma ta manta, murmushi tayi tana juya fararan idanunta tace.


"wow!! nice name bobo, please can u give me ur contact? sai mu dinga gaisawa as frnds,kallon Jalilerh yyi yaga gaba ɗaya ta ɗauke kanta tana kallon waje,hannu yasa ya ɗaukota gaba ɗaya ya ajjiye ta saman cinyarsa kafin yace.

"ina da mata"da mamaki take kallonsa sai taji duk zcyarta babu daɗi ranta ya ɓaci,saita kanta tayi tace "mata kuma..?wace?" rungome Jalilerh yyi wacce tai ƙwance a jikinsa ta fara bacci sbd sanyin a.cn ɗaya shigeta yace "gata" saurin riƙe ƙofar motar tayi sbd jirin da taji yana neman ka da ita,cikin nuna itama idanunta a buɗe yake tace "haba wannan yarinyar,ai sai dai ƴarka badai mata ba,idanma matarce ka rasa wacce zata aura sai kwaila mara jiki sosai" kallon gefen idanu yyi mata sannan ya kalli Jalilerh wacce ta ɗan ware idanunta tana sauraran maganar tasu sama-sama,wani smile yyi sbd shi gare shi bai ga wani banbanci ba,shekaru kawai zata nunawa Jalilerh da kuma girman jiki,amma duk halittun da zai nuna Jalilerh macace ya gama bai yana sai Abinda ba za'a rasa ba, ƙasa yyi da kansa dai-dai fuskarsa Jalilerh yace "haaa ba kinki na baki sweet kinji Noor" cikin magagin bacci ta buɗe bakinta,a hankali shi kuma ya sanya bakinsa cikin nata tare da bata wani lafiyayyan kiss,kafin tayi wani yunƙuri ya zoba mata yawon bakinsa cikin bakinta, lumshe ido tayi tai lamo jikinsa a hankali kuma baccin yyi gaba da ita.

baya Hibba tayi cikin ƙaramin lkc mood ɗinta ya sauya,kafin tayi ƙarfin halin faɗin "na yarda,amma kada kayi tunanin shkkn komai na iya sauya" tana faɗin hakan ta shige cikin motar ta,sai a lkcn aka kawo masa oder da yyi shima ba tare daya tashi Jalilerh ba ya gyara mata ƙwanciyar tare dayin revers yywa motar key pouting lips ɗinsa yyi tare dayin bisimillah ya fara dreving.


basu isa gida ba sai wajan ƙarfe 9 na dare sbd wani waje daya tsaya sukai wani ɗan ƙaramin meeting aƙan zaɓan cikin gida,yana shiga Mama tayi saurin miƙewa tsaye tace "ina nan zaune,ka ganni sau goma kenan ina sheƙa amai,duk yadda akai ƙwantaccen cikina keson tashi"waro idanu yyi kafin ya miƙa mata leda ɗaya acikin ledojin guda biyar ɗin daya shigo dasu, kafin yace komai ta yaga leda tayi zaman dirshen a ƙasan carpet tace "ma sha Allah gashi kowa ya sha kayan haɗi wannan ɓoye shi zanyi sbd ɓerakun gidan nan" baice mata ƙala ba ya haura saman upstrais hannunsa riƙe da Jalilerh wacce take ta bacci abinta,cikin nutsuwa ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama,shuru Nihila tayi harya ƙarasu cikin bedroom ɗin ya ƙwantar da Jalilerh yaja mata duvet ya rufe mata jikinta dashi,kallon Nihila yyi yace "zo nan" miƙewa tayi taga ita sai ƙaramin wando da rigar bacci mara nauyi, hannu yasa ya murɗe mata kunne yace "baki amsa sallama ba ko?ko baki san muhimmancin ta bane?" turo baki tayi hawaye na zuba a saman fuskar ta tace "shine kuka tafi kuka barni, tun ka dawo baka taɓa fita dani ba,ko kafi sonta akaina"baki ya ƙara murɗe mata kafin yasa hannu ya jata zuwa jikinsa yace "ban son irin wannan kalaman,ke jinina ce,ita kuma ƴar uwata ce kowa da matsayinsa" ya faɗi hakan yana share mata hawayen fuskarta yace "babyn Mummy ta girma bata san ta girma ba eyeee" ya faɗi hakan yana sumbatar goshinta yace "make sure kinyi maku addu'a keda ita" kaita gyaɗa masa ya fita yaja masu Ƙofar da sallama ya shiga part ɗin Mameey ya sameta tana shirin fita kasan cewar itace da girki, "Mameey Barka da dare" murmushi tayi tace "yawwa babban yaya" ledan hannunsa guda biyu ya miƙa mata yace "ke da Abbou" gdy tayi masa tare da addu'a kana ta nufi part ɗin Abbou,shima wajan Mummy ya shiga ya sameta zaune tana kallon wani abu,tana ganinsa ta ɓoye a bayan pillow,zama yyi yace "sannu Mummy na" sumar kansa ta shafa tace "yawwa yarona,sannu kaji bobo kaga abinda banso kenan harkar siyasa ya fara saka gaba" miƙewa yyi yace "kai Mom" ya faɗa yana bata ledan hannunsa yace "goodnight" ok "take care" yana sauka dwonstrais ya samu duka samarin gidan gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin "sannu yaya" zama yyi yace "yawwa darling" kallonsa Aryan yyi yace "tun ɗazo nake saka ran ganin dawowarku ashe sai yanzu,bari naje naga beb ko batai bacci ba" fuska babu yabo babu fallasa yace "sunyi bacci" ba dan ran Aryan yasu ba ya zauna, Irfan ne yyi dry yace "da dukkan alamu anyi gaba da zcyar wani" da sauri Imran yace "koba Aryan ba..?aina kula tunda ya sanu bbyn yaya ya faɗa" murmushi yyi yace "wlh ina sonta,kuma ina da burin auranta" miƙewa Jalal yyi tare da basu ledan hannunsa guda ɗaya wacce ta kasance babbar ciki,yana basu yyi shigewarsa part ɗinsa.

zaune president Mubarak Yahya cibo yake yana kallon matarsa Haj Ayshert yace "bana barin dukkan wanda yace zai yi takara dani akan abinda na keso,na ɗauki alwashi wulaƙanta dukkan wanda yace zai hakan,kuma zan tabbatar masa da magana ta gsky ce,badai na tura masa da saƙo ta email ɗinsa akan ya janye takarar ba yaƙi,shi ɗan miskilin tsiya ko..?" ya faɗa yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa,cikin girmamawa Haj Ayshert tace "your Excellency you don't need to worry about this issue,shekararka 4 kana mulki ya kamata ka hqr haka tunda babu abinda muka nema a rayuwa muka rasa,daman ita siyasa ai ba'ar dugaro bace,kuma ba gado bace bare ace dole mutum yyi sorry I don't mean to hurt u" miƙewa yyi yace "ban shiryar barin siyasa a yanzu ba,kamar yadda nayi al'ƙawari sai nayi shekara 8 cif akan mulki, shima da ina da iko sai na ƙara juyawa,dan haka dukkan abinda za kice kin daɗe baki faɗa ba,ruwanki ki maramin baya kisa a zaɓeni ruwanki kiƙi,kuma zuwa yamma Lamir zai dawo kuma nan zai fara zuwa domin nike da buƙatar ganinsa,dukkan hanyar da za'a bi a kawar da wannan mutumin a duniya sai nayi kuma ta hanyar Lamir zan iya hakan..




#Team Zulfa a ƙara hqr,ko daina tambaya Please kana kusa na taɓo inda ban shirya zuwa ba,ko bini sannu a hankali.
6/10/21, 1:06 PM - Buhainat: _Littafin *UNCLE NE* na kuɗi ne bisa farashi mai sauƙi wanda zan kammala rubutasa cikin ƙwana 30, mai buƙata zai biya 300 masu son vip posting sau biya zasu biya 600 ta wannan asusun 0116886423 sulaiman naima s unioun bank, send ur evidence of payement to 08119237616_


*#Something is over doesn't means ur life is over*



_30-31_


Da yamma Lamir ya sauka gidan president Mubarak Yahya cibo,motoci ne sama da goma sukai parking a parking space,ga wasu securities wajan ashirin duk riƙe da guns,kowa ka gani fuska babu walwala,a haka aka buɗewa President Mubarak Yahya cibo,yana tafe wasu masu tsaronsa suka rufa masa baya,da sassarfa ya shige parlour'n da yake meeting mai muhimmanci wanda ba kowa yasan dashi ba,yana zuwa parlour'n wasu manyan mutane su biyar suka miƙe tsaye alamar girmamawa,farin ciki fal fuskarsa ya kalli Lamir wanda ya ƙara girma shekarunsa suka jaa,sai dai yana nan fresh bawai ya tsofa bane, zama yyi akan wata lafiyayyiyar kujera a hankali kuma ya ɗauki coffee da aka ajjiyewa ko wannansu ya ɗan kurɓa kaɗan, Lamir ne yace "ur excellency sai naji kira daga sama,naji tsoro sbd tunda ka turani Istanbul domin kula da Company medicine ɗinka baka taɓa kirana ba,shiyasa wannan kiran ya ɗagamin hankali" Gwamna Faisal Lawan yace "ai Lamir abunda ba muyi tunanin zai faru damu ba shine yake shirin faruwa,babu wanda ya taɓa tsayawa takara shugaban ƙasa tun takarar da Khalil ya tsaya shima kafin zaɓe ya mutu,to yanzu an waye gari wani ɗan ƙaramin alhaki na neman tayar mana da hankali, tabbas idan mukai sanya za'a samu matsala" ya ƙare maganar yana kallon president Mubarak, miƙewa tsaye Lamir yyi ya Fara zagaye parlour'n kafin yace "duk wannan ba shine ba,bamu da matsala dashi idan duk sauran gwamnonin da muke dashi basu mara masa baya ba,kaga da zarar anyi zaɓen cikin gida bamu da wata matsala dashi,idan zaɓe yazo a nan zamu tara talakawan gari da matasa mu raba Musa ƴar shinkafa suger da ƴar dubu biyu haka,matasa kuma zamu basu ofer ta aiki amma ta ƙarya,sannan ƴan bangar siyasarmu zamu haɗasu da manyan drugs wacce zata har gitsa masu brain ɗinsu,kaga a nan zasu rage mana wani aikin ranar zaɓe sukaiwa ƴan kungiyar hamaiya farmaki,hakan zai saka magoya bayan jam'iyyar jin tsoro kowa yaƙi fitowa zaɓe sbd yana jin tsoron kada a kashesa ko a yanke sa, shine kawai" murmushi president yyi domin har yaji wani sanyi a ransa, Faisal Lwan shima ya mike tsaye yace "matsalar duk ba'a nan take ba,tashin hankalin da muke ciki a yanzu shine dukkan gwamnonin da muke dasu guda 39 sama da 30 suna bayan sabon ɗan takarar shugaban jam'iyyar D.R.P ɗin" cikin tashin hankali Lamir yace "wai waye wannan sabon ɗan takarar da yake wasa da rayuwarsa data danginsa?" ya ƙare maganar yana fesar da numfashi sai a lokacin President yace "his name is Muhammad Jalal Kabeer bobo" da saurin Lamir yace "what!!!?.

da wajan yamma akai parking da wata sabuwar mota black colour, wasu manyan securities ne majiya karfk sama da 20 suka zagaye motar kafin wani babba yazo ya buɗe murfin motar bayan motar, ajjiye jaridar hannunsa yyi ta daily truts kafin ya ɗauki farin glass ɗinsa ya manna a idanunsa,wayarsa dake gefensa tana ringing ya ɗauka tare da katse kiran ya zuro da fararan ƙafafunsa zuwa waje,cikin a zaba securities ɗin suka zagayeshi,yana sanye da wata light blue ɗin shaddar ɗinkin riga da wando da kuma babbar riga sai zabga ƙamshi yake,fuskarsa ta cika da haiba, kwarjini,annori da kuma cikar zati, wayoyin hannunsa aka amsa wani ya ajjiyesu wajansa,cikin nutsuwa ya fara tafiya har zuwa cikin gidan gonar tasa wacce yake jiyo ihun matasa da kuma ambatan sunansa da suke,yana zuwa aka ja masa kujera ya zauna,yana zama ya lumshe idanunsa kafin a hankali ya buɗesu ya sauke akan dubban matasan da suke wajan,wani daga cikin matasan yace "ALLAH ya taimaki Jalal bobo,ya ɗaukaka in sha Allah mulki kamar kayi ka gama ne, maƙiyan ka sai dai suji kunya,alfarmar Annabi da Kur'ani saika zama shugaban ƙasar ibadan saika kawo mana sauyin da muke fatan samu,sai ka kawo mana ƙarshen matsaloli mu,sai ka ingatan makarantun gwamnati,sai ka tantance mana ingantattun malamai da kuma likitoci,saika magance mana shigo da gurɓatattun magani cikin wannan ƙasar tamu saika magance mana (women trafficking *_Sabon littafi nan da bayan sallah_*) safarar matan da ake zuwa wata ƙasar da niyar aiki kuma sai anje aga ba haka bane,aita lalata mana yaranmu da iyayanmu in sha Allah kai ne garkuwarmu" gaba ɗaya suka haɗa bakin wajan faɗin "Ameen ina sha Allah"

Murmushin sa na gefe wanda yake ƙara masa ƙyau yyi kafin yaja kujerarsa baya kaɗan ya fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya yace "Ma sha Allah, Allahamdulillah nagode ƙwarai da soyayyarku kuma ina addu'ar Ubangiji ya bani ikon sauke wannan nauyin da zai hau kaina" ya ƙare maganar yana sauke wani wahalallan numfashi sbd tsayin da maganar tayi masa, Jafar dake gefen sa ne yace.

"Munayi maku barka da zuwa,kuma muna fatan zuwanku ya zame mana alkairi,kuma muna fatan zaku mara mana baya har abada zaku jajirce akan abinda kukeso kada ku juya mana baya,ku zama masu ƙarfin guwwa da kuma tsayawa akan ra'ayinsu,sannan muna buƙatar mutum ɗaya a cikinku wanda zai zame maku jagora wanda kuka amince dashi,sannan munasu ku zaɓi mutane wanda zasu dinga yi mana campaign a social media da kuma muta nan da zasu dinga shiga gidan redio,t.v suna yaɗa manufarmu,dukkan wani taimako daza muyi maku zaku samesa ta hannun mutumin da kuka zaɓa matsayin jagorarku"

da wannan maganar suka gama taron,sannan suka zaɓi shugabansu mai suna Prince Hassan,gaba ɗaya matasan wajan sai murna suke suna ihun daɗi,lokaci guda ƙaunar Jalal bobo ta shiga zuƙatansu, Lamir bayan sun gama nasu meeting suka tsaida maganar da suke ganin za suyi amfani da ita wajan ruguje soyayyar da mutane sukewa Jalal bobo, a main parlour Jafar da Jalal suka samu Abbou da Dasu Mameey zaune sai kuma Lamir wanda yake zaune kusa da Mama an cika masa gabansa da kayan motsa baki, Lamir ne yace "wlcm son,kuma president to be" kallonsa Jalal yyi dan ganin inda maganar tasa ta dusa sai dai babu wata alamar da fuskar Lamir zata nuna baya cikin farin ciki, kansa ya ɗauke yace "wlcm uncle" Lamir yace "thanks sai na kejin abin arziƙi,ai nace zama bai kamani ba shine babu shiri na nemi ticket na dawo domin a fara shirin zaɓe dani" Abbou yace "Lamir amma naga kamar ba jam'iyyar kake ba,domin kowa ya sanka da President Mubarak Yahya cibo,shiyasa nake tunanin abun" murmushi Lamir yyi yace "haba Alhaji Kabeer ai gida yafi waje,tayaya zanyi adawa da jini na,dukkan abinda nake samu wajan President bazai kai alaƙar jini muhimmanci ba,dan haka muna nan zamu fafata" jinjina kai Abbou yyi cike da farin ciki kafin yace "kai abu yyi daɗi Allah ya taimake mu, Allah ya ƙara zumunci "gaba ɗaya suka amsa da "Ameen" murmushi kawai Lamir yake tare dacin abincin dake bagabansa,Jalal bai ƙara magana ba ya shige cikin part ɗinsa bayan yyi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska ya ƙarasa parlour'n ya ɗauki apple da maltina ya dawo saman sofa ya zauna, system yaja ya fara searching akan women trafficking ɗin da suka faɗa masa ɗazo da kuma drugs ɗin da ake shigowa dasu ba tare da Nafdac ta sani ba.



A can Birnin nufar Papa ne zaune gaban uwa sundu yana kirari tare da ɗura hannunsa a sama yana jujjuyawa tare dayin sama da ƙahon kansa,sai da ya shafe awa guda kafin wani abu ya fito daga hannun uwa sundu ya sauka a nasa hannun,da sauri ya duba hannunsa abinda ya gani ba ƙaramin tayar masa da hankali yyi ba, cikin tashin hankali ya kalli jinin sannan ya kalli uwa sundu yace "Me nai maki uwa sundu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login