Showing 39001 words to 42000 words out of 120090 words
"muje beauty" har mota ya sata sannan yaja motar ya fice da sauri, Jalal na can amma san hankalinsa yaƙi ɗaya haka nan ya samu kansa da tunanin gida,ganin ba'a fara zaɓan ba ya ɗauki ƙaramar wayarsa wacce amsa kira masu muhimmanci yyi dailing number Abbou, Abbou yana tsaka da driving yaji wayarsa na ƙara ɗauka yyi tare faɗin "fatan lfy dai bobo?" Daga can Jalal ya saki ajjiyar zcy yace "Abbou kada a bar yarinyar nan ta fita koda ita da wani ne" murmushi Abbou yayi yace "yanzu dai na kusa gida,in sha Allah hakan bazai faro ba, Allah ya taimaka" Jalal najin hakan ya kashe wayar yaci gaba da sauran abinda wasu ƴa Majalissu suke faɗa masa.
Lamir na fita Abbou na shigowa Mama ce zaune a parlour ta tisa ƙatuwar kaza tana ci, kallonta yayi yace "mutan gidan basu dawo bane" taɓe baki tayi tace "sa dawo tunda sunbar baiwa a gida"kallon ta yayi yace "Jalilerh fa" tace "tana can tayi bacci yanzu tabar nan ai" jinjina kai yyi yace "bari na dubata" da sauri Mama ta miƙe tsaye tare faɗin"ohhhh ƙarya zan maka kenan ko Kabeeru?" Yace "a'a ba haka nake nufi ba kiyi hqr"yana faɗin hakan ya shige part ɗinsa.
6/10/21, 1:11 PM - Buhainat: Yana driving yana murmushi jifa-jifa kafin a hankali ya juya kan motar zuwa wani waje na daban,a gaban wani kango yyi parking tare da kashe motar ya fito,tana zaune cikin motar idanunta a kansa ga hawayen da yyi ƙwance a cikin idanunta,murfin side ɗinta ya buɗe t fuska babu yabo babu fallasa ya kama hannunta zuwa cikin kangon,yana shiga tayi saurin yin bayansa sbd mutanan data gani wajan mutum goma,daga can ɓangaren aka fara tafi kafin Hon Faisal Lawan ya fito daga cikin wani ƙaramin ɗaki hannunsa riƙe da wata Camera yace "aiki da kai huce takaici,kayi ƙoƙari kayi komai cikin sauƙin"
Wata dry Lamir yyi kafin yace "duk wanda yaci tuwo damu ai miya yasha,wannan yarinyar ita zata wargatsa masa dukkan wani shirinsa,ita zata sanya baƙin ciki a zcyarsa,ita zata sanya masa hawan jini,ita zatai siya wargatsa ɗan ƙaramin farin cikin da yake dashi, tabbas wannan yarinyar zata zame masa masifa a cikin rayuwarsa,ita zata sanya yyi baƙin jini a idanun jama'ar ibadan da kewayanta" gaba ɗaya wajan suka ɗauki ihu tare da tafa hannu,kallon wani yyi yace "ɗaureta" riga ta riƙe masa jikinta ya ɗauki rawa a tsorace tace "Kaiji wajan Uncle ɗina,mai dani gida" kallonta yayi yace "haba shalele yanzu zaki koma gida wani aiki zakimin baki son ki taimaki ɗan uwan Uncle ɗinki?" Cikin kuka tace "am scared,ina tsoran mutanan" taɓe baki yyi kafin ya juya yace "ba'a bin da za suyi maki yanzu zan dawo"yana faɗin hakan ya fice daga cikin kangon,cikin motarsa ya shige tare zama ya kyakkyata dry kafin yace "Muhammad Jalal bobo ka gama yawo" yana fita wani yazo yaja hannunta tare ɗura ta a saman wata kujera, hannunta ya kama tare da ɗaurewa da wata igiya sai kuka take tana kiran sunan Uncle,sai da suka ɗaure ta ciff hannu ta ƙafa,kafin ya kalli wani yace "ko kawo jinin" da sauri ya miƙo wani jini a cikin wata ƴar ƙaramar roba,wandon jikinta suka saka reza suka yayyaga har saida cinyoyinta suka fito,duk inda jikinta ya bai yana a jikin wandon suka bi wajan suka shafa jinin,kafin su ɗauki jinin suka shafa a gefen bakinta zuwa hancinta,suna gamawa wani ya ɗauko cocaine a cikin wata leda ya nufi hancinta,cikin kuka tace "kubarni Please banson, Uncle where are you" dry mutumin yyi yace "kina son zuwa wajan Uncle?" da sauri ta ɗaga masa kai murmushi yyi yace "good gril duk abinda na faɗa maki ki faɗa,kuma ai Uncle ɗinki yace muyi maki hakan" cikin rashin fahimta tace "Uncle bazai ɗaureni ba,ka sakeni ku gyaleni,ohhhh Jesus"dry yyi yace "daman sai dai kice Jesus ɗin,mutumin dake neman taimako ai sunan Allah zai kira bana bawansa ba" yana faɗin hakan ya danna mata gusar cocaine ɗin a cikin hancinta,saurin runtsa idanunta tayi sbd wata azaba da taji a cikin hancinta kafin a hankali idanunta su fara lumshewa cikin ƙasa da murya ta fara faɗin "Uncle.. Uncle ne..!!" dry yayi yace "kice Uncle ya kawo ki nan,kuma kice Uncle ya cire maki kaya,kice Uncle yyi maki Fyaɗe,kice Uncle ya fasa maki baki" cikin maye da gushe war hankali tace "No!! I can't say it" da ƙarfi yace "say it, I said say it" ya faɗa cikin ɗaga murya,a hankali ta buɗe idanunta wanda yake zubar da hawaye kafin ta ƙara jaa ta rufe tace "i can't,my uncle my everything" hudar ya ƙara ɗaukowa ya danna mata cikin hancinta har sai da numfashin ta ya kusa ɗauke wa, kafin ya ƙara shafa wani jinin a jikin hancinta ya hargitsa gashin kanta yace "ohyaaa speak" idanunta ta buɗe wanda ya rini ya koma jaaa tace "Uncle ne..!" tafi mutumin yyi cikin sauri Hon Faisal Lawan ya kunna camerar tare saita ta a jikinta,cikin ƙasa da Murya inda Muryar sa ba zata fito ba yace "what he did to you?" numfashi ta yana fizga tace "Uncle ne ya kawoni zaimin magani...," Shuru tayi kafin ta ɗura da "ya yagamin kaya da reza ya fasa min baki..," nan ma shuru tayi kafin tace "he raped me" ta ƙare mgnar tana fasa wani gigitaccen kuka "ya waye" idanunta ta buɗe tarrr akan camerar kafin tace "Muhammad Jalal bobo, I hate him I don't want to see him in my life ever, he betraying me,he lying to me, seriously I hate him"ta faɗa tana saka wani sabon kukan, cutting camerar Hon Faisal Lawan yyi kafin yyi wani murmushi yace "Jalal bobo ka gama yawo"
Lamir dake cikin mota ganin su Hon Faisal Lawan sun fito suna dry ya fito daga cikin motar tare ƙara sawa inda suke yace "komai yayi?" Dry sukai tare faɗin "harma da abinda bamu sata faɗa ba ta faɗa" jinjina kai yyi yace kuje a nemi wata a tura masa,sannan ya haɗasa a media,a nan kuma gidan t.v da redio zasu ɗauka,ni bari naje nasan yadda zan mata" mota suka shiga tare da barin wajen shi kuma ya shige ciki, ƙwance ya taddata tana shasshekar kuka,da sauri ya ƙarasa inda take ƙwance yana zuwa yasa hannun ta ɗauke ya nufi cikin mota da ita,ruwa mai sanyin gaske ya ɗauka ya shafa mata a fuska tare da saka ruwan a cikin bakinta tasha sosai,kujerar motar yaja bata ta ƙwanta kafin yyiwa motar reverse tare da yi mata key a guje yabar wajan.
Sai kusan 3 aka kammala zaɓen inda Jalal yake da rinjayen mutane kashi 15 a kashi 20 kafin ya faɗi sakamakon ya nufi wajan motarsa wasu manyan securities suka rufa masa gefensa kuma Jafar da Aryan ne,yana zuwa motar aka buɗe masa back side ɗin ya shiga kafin aja motar a rufe, Jafar ɗaya motar ya shiga shida wasu ƴan majalissu Aryan kuma ya shiga motarsa, securities ɗinma motarsu suka shiga,kai tsaye cewa yyi suyi gidan sbd gaba ɗaya baijin da daɗin jikinsa,ga wata faɗuwar dake damunsa,a haka suka isa gida gaba ɗaya sukai parking a parking space na gidan,suna parking motar su Mummy na dawowa,motar aka buɗe masa ya fito suma securities ɗin suka ja gefe a cikin gidan kowa hannunsa riƙe da bindiga,cikin nutsuwa yake tafiya a tare suka jera shida Mameey da Mummy sai tsiya Mummy take masa zai tsofa babu aure Mameey kuma na tare masa Shidai kawai jinsu yake dan sam bai gane abinda suke faɗa masa.
A parlour suka tarar da Mama tana bacci gaban cike da tarin ƙashoshowan kazar,zama sukai gabaki ɗayansu,shi kuma Jalal ya nufi part ɗinsa,yana zuwa ya sakarwa kansa shower bayan ya gama ya fito parlour'nsa sanye da wata milk ɗin jallabiya mara nauyi,wajan fridge yaje ya ɗauki bottle water mai sanyi ya ɓalle murfinta ya sanya cikin bakinsa gana gama shanye wa ya ajjiye robar tare miƙewa akan duguwar sofar tare da lumshe idanunsa kamar mai nazarin wani abun.
Suna zaune a main parlour mai aikinsu Laure ta ajjiye masu ruwa da lemo da kuma cake suna shirya sallamar da suka ji anyi yasa suka kalli bakin ƙofar Nihila ce ita da Nusaibat suka shigo,kallonsu Mummy tayi tace "daman ba ƙya gidan" zama tayi kusa da Jafar tace "Mummy kinsan weekend ne,na gaji da zaman gidan shine naje wajan Nusy sai kuma bacci ya ɗauke ni" Mameey tace "ina Jalilerh" parlour'n ta kalla tace "ai a nan parlour'n na barta ita da Mama" Mama da tayi ƙuri jin an tambayar Jalilerh tayi saurin faɗin "Mahammada Rasulullah Ni zakiyiwa sharri da ƙarya,Bihila ki fita ina bacci za kice kin barin da ita,Haram sam ƙarya kike ki tuba kibi Allah da za'a shanshana bakinki tabbas da anjin yana wari" tana faɗin hakan ta miƙe ta nufi part ɗinta tana shiga Abbou ya fito yace "ai Mama tace tana bedroom tana bacci naso leƙa wa amma sai banyi hakan ba" Mummy ce ta miƙe tace "ok bari na duba ta"tana shiga taga babu kowa a cikin bedroom ɗin dubawa parlour bathroom tayi nan ma babu kowa,da sauri ta fito tana daga saman upstairs tace "Abbou Jalal bata nan fa har bathroom na duba" da sauri Aryan ya miƙe yace bari na duba part ɗin Mameey Nihila ma miƙewa tayi tace bari na leƙa ko taje wajan Laure,nan suka fara dubawa amma babu Jalilerh babu labarin ta,a tare suka fito hadda Abbou daya duba gues parlour,kallon juna sukai kowa da alamun tambaya a cikin ransa,kafin Mummy ta juya da sauri ta nufi part ɗin Mama,tana tsaye a cikin parlour sai tafa hannu take tace "Lamiru ni ya haɗawa tuggu,na shiga uku yau ina zankai hakkin marainiya Allah ya sani da niyar taimako na bashi ita,ahhh to data zauna da wannan mugwayen mutanan a jikinta ba gwamma an cire mata su kota ido ne ta huta..," sauri shuru tayi sbd buɗe ƙofar da taji anyi Mummy tace "dawa kike magana" tace "to uwata matseni na faɗa" Mummy tace "Ina Jalilerh Abbou Jalal yace kice masa tana ɗaki tana bacci kuma an duba ko ina bata gidan,bayan tare kuke da ita a gidan" kuka Mama tasa tace "ashe kallon mayya kuke min sbd ko mayyaceni tayaya zan cuci marainiyar Allah wacce babu ruwan ta,shikenan dan ina cin arziƙi a gidanku zaku yimin sharri" ta ƙare maganar tana face majina,fita Mummy tayi a ɗakin tana fita Mama tasa key ta rufe ɗakin, ganin ta fito da tashin hankali yasa Aryan saurin faɗi "bari na duba ɗakin yaya" yana faɗin hakan ya nufi part ɗin bobo,yana ƙwance idanunsa a rufe ya ɗura hannunsa a saitin ƙirjinsa dake buga masa yaji an turo ƙofar ɗakin da sauri, baiko mutsa saima ƙara rufe idanunsa yayi Aryan ne yace "yaya Jalilerh bata gida fa" da sauri ya buɗe idanunsa tare miƙewa tsaye yace "what!! Kamarya bata gida" yace "an duba ko ina bata nan Jalilerh missed" bai ƙarasa jin komai ba ya saka bedroom silefers ɗinsa ya nufi parlour yana zuwa yaga kowa a tsaye hadda Mama data ta kuɓe gefe sai raba idanu take kallonsu yyi ciki ɗaga murya yace "Wanne irin abune wannan? Tayaya zakubarta ita da wannan rikitacciyar matar" kuka Mama ta saka tace "daman na sani kallon mahaukaciya kukemin,yau ɗin nan zan barmaku gidanku" cikin ɓacin rai yama manta dawa yake magana yace "kin daɗe baki bar gidanma babu da kika iya gashi nan kin salwantar da yarinyar saiki shirya abinda zaki faɗa a court kuma...," Ba ƙarasa maganar ba yaji an ɗauke sa da mari da sauri yyi ƙasa da kansa, Nihila dake gefensa tana kuka tayi saurin ƙanƙamesa sbd tsoran da taji,cikin ɓacin rai Mummy tace "uwata kake gayawa wannan maganar,uwar data haifan nazo na haife ka zaka maka court Muhammad" kafin wani yyi magana Jafar yace "what!!?" gaba ɗaya suka kallesa lokacin daya sauke waya ya nufi inda remote yake ya kunna t.v kai tsaye b.b.c ya kaita yana kaiwa yaga an rubuta breaking news tashin hankali kenan da sauri Jalal ya ɗaga kansa jin Muryar ta cikin kunansa tana faɗin "Muhammad Jalal bobo he raped me..
😂😂 Aunty dan Allah idan kina enjoying labarina ki daure ki biyani haƙƙina babu yawa 300 vip 600 ga number account 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616
6/10/21, 1:11 PM - Buhainat: Gaba ɗaya parlour'n suka zabura tsaye sbd jin abinda Jalilerh ke faɗa,wani gumine ya yankowa Aryan kafin ya juya ya kalli Jalal dake jingine jikin bango idanunsa lumshe, ajjiyar zcya ya sauke kafin ya fice daga cikin gidan, Jalilerh dake jikin t.v ta ɗura da faɗin i hate him I don't want see him in my life ever,he betraying me" ta ƙare mgnar tana sakin kuka, Abbou zubewa yyi akan kujera hannunsa dafe da kansa dake kuya masa, Mummy kuka ta sanya tana faɗin "wlh wannan maƙiyya ne wanda basa ƙaunar ci gaban ka,nasan baza ka taɓa aikata wannan sauƙon Ubangiji ba, dukkan wanda yake neman ka da sharri da izinin Allah sai dai ya gani a kansa,daman abinda nake jiye maka kenan,wlh bana ƙaunar wannan siyasar taka,yanzu duniya da kuma mutanan gari wanne irin kallo za suyi maka? Allah dukkan wanda yace tukunyar wani ba zata ta fasa tasa ko zafi ba zatai ba,duk sharrin mutum sai dai ya gani a kansa amma alfarma Annabi da Kur'ani babu abinda zai sameka" ta faɗa tana zubewa ƙasa tare sakin wani sabon kukan, Mameey dake tsaye kamar butum butumi ta share hawayen dake cikin idanunta tace "yaya akai Jalilerh ta fita shine Abin tunani tabbas aƙwai wani abu a ƙasa,dukkan wani zai ɗauki Jalilerh sai wanda ya san kan gidan kuma...," Kafin ta ƙarasa Lamir ya shigo da sauri tare da kallon bobo yace "yanzu ina cikin driving zani gida nake jin wata magana a redio,ban tabbatar ba sai da aka kirani nace ban yarda ba,daga ƙarshe na kunna data naga abun nata yawo a media hadda photon Jalal a ciki,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wacce irin masifa ce wannan" Mama dake gefe tayi sauri faɗin "kul ka ƙara faɗin masifa a nan,duk wanda yyi haka sai wanda bakin uwa ke binsa,ohhhh wannan duniya za maninmu babu ruwan wani da wani amma yanzu wlh ko kashi kake ka ga mutum zauna akan abinda,yanzu za kaji ana wacce tayi kashi mai tauri,huuuuu ai sai da nace kayi aure kaƙi da duk hakan bai faro ba,ahhh to babu ruwana ba dai ina faɗin abu kuna ganin kamar banda hankali ba" kallonta Mummy tayi tace "haba Mama wannan duk ba abin Suratu bane,neman mafita shine abinyi" tace "sannu uwata ahhh nace sannu Zulai,jika na ne dukkan abinda ya samesa ya saman yooo mai fimini komai a kanki ba" Lamir yace "yanzu mu fara tunanin inda yarinyar dake kafin wani abu ya biyo baya" kallonsa kawai Jalal yayi kafin ya juya yyi shigewarsa part ɗinsa.
Shuru parlour'n ya ɗauka aka rasa mai faɗin wani abu kowa da abinda ke damunsa a zcy, Jalal na shiga parlour'n sa ya fara zirga zirga yaje ya dawo tamkar wani zautacce,a haka Jafar ya turo ƙofa ya samesa,kallonsa yayi cike da tausayin halin da yake ciki,a zahiri idan ka kalli Jalal zaka ɗauka babu damuwa a tare dashi,zaka ɗauka dukkan abinda ake tamkar ba akansa ake ba,dan ko ajikinsa ko fuskarsa taƙi nuna damuwar da yake ciki,amma cikin zcyarsa wani zafi da ƙona ya keji yana jin duniyar na sara masa,gaba ɗaya wani duhu-duhu yake gani a cikin idanunsa ga yadda ƙirjinsa ke bugawa da ƙarfi tamkar zcyarsa zata fasa ƙirjin ta fito,maƙogaransa wani ɗaci yane ya gauraye cikinsa,abinda yake tunani wane yyi masa haka? Wane yyi masa muguwar tsanar da harya zaɓi ya tuzar tashi,tuzarzi mai muni irin haka,mene aka zaɓi ayi amfani da rauninsa wajan cutar da rayuwarsa?,mene yasa magautansa suka zaɓi wannan hanyar akan su ɗauki wata? Ko da wasa ko a mafarki mai taɓa tunanin rayuwar aure ba,bare kuma har yayi tunanin aikata wata aba wai zina,runtsa idanunsa yyi da ƙarfi kafin ya fesar da wata iska mai zafi ta cikin bakinsa, mene yasa zai aikata haka gare ta,yarinyar da take masa kallon uba ko wani jigo nata,tayayama zai aikata hakan bayan yasan tarin ayoyi da hadisan da sukai bayani akan wanda ya akaita zina da auren ko bashi dashi,me yasa suke tunanin wannan abinda sukai zai tauyesa,ko kuma zai sanya tsoro cikin zcyarsa har ya janye abinda yake mafarkinsa tabbas sunyi kuskure, kuskure mai girman gaske domin basu san wanene Muhammad Jalal bobo duk yadda suke tunanin daƙoshe bai taɓa damunsa ba,yana sane da dukkan abinda yake faruwa a harkar siyyasar,amma dole ya sauya damunsa dole yasan wanda ya ɗauke Jalilerh.
Jafar ne ya kallesa kafin yace "Jalal wannan shurun naka a yanzu mazai tasiri ba,nasan kana da hankali tunani ilimi addini kowa yasan kana da wannan,domin ni a karan kaina nasa gane da iliminka na addini dana bature wanne yafi a wajanka,nayi imani da Allah dukkan wanda yasan ka bazai taɓa yarda da wannan ƙazafin da akai maka ba,kada ka damu kanta domin nasan yadda kai shurun nan Allah kaɗai yasan abinda ka keji a cikin zcyarta domin duk yadda wani yakai yaji baƙin ciki ba kamar kai ba, You have to control ur self,wannan selfishness da mai yyi kama" ya faɗa yana dailing wata number a wayarsa.
Tunda ya fara magana Jalal bai ɗago kansa ba,ya hasali ma shi kaɗai yake surutansa,dan "a" na cikin maganar Jafar babu wacce yaji bare ya fahimci abinda yake faɗa, abubuwan da zcyarsa suke faɗa masa daban da wanda yake son aikatawa,me zaibi a yanzu kansa zaibi ko son zcyarsa,ina kuma zai nemu Jalery shine abinda yafi tsaya masa a rai,ina take?wanne hali take ciki? Me suka aikata mata da har ta faɗi wannan maganar lallai sunyi pursing nata ne,duk da yasan ba komai take ganewa ba bare harta fahimta,amma dole zata fahimci wanna kalmar ta rape data ambata,fesar numfashi ya karayi kafin ya sanya hannu cikin tulin sumar kansa ya fara hargitsa ta,a hankali kuma yaja cikinsa zuwa wajan fridge ya ɗauki bottle water ya ɓalle murfinta tare da kafawa a bakinsa sai da ya shanye tass kana ya yar da emty robar a ɗan zafafe