Showing 57001 words to 60000 words out of 120090 words
rai zai magana za'a iya samun matsala sbd gaba ɗayansa jinsa yake a sama zcyarsa banda tafasa babu abinda take,ba yajin a yanzu zai iya control kansa amma ya zame masa wajibi daya saita kansa, Mama ta taɓe baki tace
"Ayee mama ayeee mama mayeee iyeee,ayeee mama labu labu mama yeee iyeee"
Haɗe rai shima yay kafin yay ƙasa da murya yace
"Ina yini"
Cikin ƙufula Mama tace
"Kaji ance bani da lafiya ne Muhammad? Da ban yini da lafiya ba aida ka samu labari wajan ubanka"
Cije lips yay kana ya zamu daga saman sofa yace
"Haba matar,laifin me mijin yayi ne"
Taɓe baki tayi tare da watsa dakakken goran a baki tace
"Uhmm duniyyanci kenan,Ni za'ai wa sanabe"
Zamuwa yay daga saman sofar gaba ɗaya ya ƙarasa inda take zaunan ya cire hular kansa tare da ɗura kan a saman cinyarta,shuru tayi tana ɗan sauke ajjiyar kafin tasa tafin hannunta a saman sumar kansa ta shafa a hankali tace
"Nayi kewar jikana kuma mijina"
Ɗago kai yay tare da zubawa Mama Idanu wajan 3minutes yace
"Mama mene yasa kikeson dole sai nayi aure ne?"
Washe baki tayi tace
"Kai ɗaya kai ne jikana na miji,sai ƙaramar ƙanwarka Ina son naga ka sama min yara,ina da burin naga ka tara zuri'a masu yawan gaske kuma masu albarka,bana son yadda ban tara iyali ba ace kaima haka tara ba,wannan dalilin ya sanya nake burin naga kayi aure kafin ƙasa ta rufe idona,kullum cikin mafarkai nake wanda bana gane kansu ina jin tsoro dan ban san dalilin wannan mafarkan ba,kaji dalili nason naga ka ajjiye zuri'a"
Ɗago jajayen idanunsa yay yana mai kallon Mama, lokacin guda zuciyarsa ta bada sauti damm Tabbas asiri sa yana gaf da tunuwa, rauninsa yana shirin bai yana abinda ko a mafarki baya fatan ace hakan ya kansace,abinda bashi da ikon faruwarsa haka kuma bashi da ikon hana faruwarsa, ƙaddara juyi juyi ce tana maida mai ƙyau ya zama mara ƙyau ko kuma ta mayar da mara ƙyau ya zama mai ƙyau,yana da yaƙi nin tasa ƙaddarar zata juya daga mara ƙyau ta dawo mai ƙyau,yaushe? Da wanne lokacin? Shine abinda bai sani ba,runtsa idanunsa yayi yana sauraran bugun zcyarsa dake fita da sauri da sauri wayarsa take cikin aljihu ce ta fara ƙara, miƙewa yayi sbd yasan kiran daga wane kai tsaye ya fice daga ɗakin idanunsa rufe, Mama ta bisa da kallo tare da tafa hannayenta tace
"Ohhh ni Abu ina za'a biyewa wannan yaron,dole sai an nema masa taimako ƙilan wata baƙar aljanarce ta aureshi..,"
Sai kuma tasa hannu da sauri ta rufe bakinsa tana juyawa tare da ƙare wa ɗakin kallo tamkar wacce taga aljanar a gabanta.
A main parlour ya samu Abbou tsaye shida samarin gidan,kamar haɗin baki duk shadda iri ɗaya suka saka babu bambanci hadda Abbou.
Imran yace
"Abbou lokaci na tafiya" gaba Abbou yayi Irfan da Imran suka take masa baya sai kuma Aryan na ukunsu,har suka fice daga cikin gidan Jalal na tsaye yana kallon su, Irfan ya kula Jalal bai taho ba ya juya baya a hankali ya hangesa yana tafiya lokacin daya iso wajan har sun shiga mota, Aryan a motar sa da Imran a gaba sai Irfan a bayan motar, Jalal shi kuma ya nufi motar da Abbou ya shiga ya zauna a back seat kusa Abbou,sai kuma motar securities ɗinsa ta rufa masu baya,misalin 1:30 suka isa harabar babban masallacin juma'ar jama'a sai ɗagawa motar Jalal hannu suke, yana daga cikin motar yake kallon kowa ɗai-ɗai har suka ƙarasa wajan parking,sahun farko Jalal ne tsaye bayansa kuma ƴan uwansa gefensa kuma Mahaifinsa a haka sukai sallar har aka idar,ana idarwa kowa ya fara tashi, Abbou hannun Jalal yaja suka nufi ƙofar baya sabida dubban jama'ar da suka tare ƙofa suna jiran fitowar sa,a haka suka ƙarasa wajan motocin su ba tare da angansu ba,kai tsaye suka nufi gida,tun a hanya aka fara sakin breaking news a gidan t.v da gida redio akan
_Governor Muhammad Jalal Kabeer bobo mai neman takarar kujerar Gwamna a jam'iyyar D.R.P ya hallarci sallar juma'a shida danginsa_
A ka rubuta hakan tare da photonan sa dana ƴan uku, da yawanci photonan wasu ne sukai masa a wajan,duk halin da yake na ƙunci da rashin sukuni bai hana shi yin wani lafiyayyan murmushi ba,hannu yasa yaja sajen fuskarsa kana yayi baya tare da lafewa jikin kujerar yana sauke ajjiyar zcy.
Da yamma wajan biyar da rabi governor Mubarak Yahya cibo ne zaune gaban wani mutumi dake sanye da wasu jajayen kaya jikinsa duk anyi rubutu da jan fenti, idanunsa manyan manya wanda ƙwayar cike ta kasance jajir tamkar zata zubar da jini,gabansa ƙasa ce da kuma wasu manyan ƙoƙuna,dariya bokan yay yace
"Kana cikin halaka wacce idan kayi sake ta faɗa maka ka shiga uku babu mai iya cireka daga cikin ta, abubuwa da yawa suna shirin faruwa amma ba zaiyu na faɗa maka yanzu ba,sai dai abu guda zakai wanda zaka iya tseratar da kujerarka da kuma mutuncinka,idan kai hakan babu shakka zaka daumawa ne tare da kujerarka babu wani wanda ya isa ya karɓa daga wajanka"
Mubarak Yahya cibo jikinsa na rawa yace
"Na maka al'ƙawarin ko mene zan aikata dukkan abinda kake so zan baka muddin ba rayuwata ka nema ba,burina ni bai huce a dauwamar dani a matsayin zaɓaɓɓe kuma shugaban dake wakilan wannan yankin na IBADAN ba,na mulki kowa na juya kowa yadda nakeso,na zama shararre tako wanne ɓangare"
Boka Saƙib yace
"Abubuwa uku muke nema wajanka,biyun farko buƙatun aljanu ne wanda suka saba maka aiki,na ukun kuma buƙata tace,domin aikin da zan maka ba ƙarami bane zan sanya kaina cikin hatsari,Amma muddun ka biyamu abin da muka ɓukata kai da mulki sai mutuwa"
Jikin Mubarak Yahya cibo yana rawa yace
"Faɗi abinda kake so zan baka,ko mene shi kuma komai girmansa"
Boka Saƙib yayi wata mahaukaciyar dry nan take wani hayaƙi ya fara fita ta cikin bakinsa,wajan mintuna biyar sannan yayi shuru tare da tsuke fuskarsa yace
"Muna buƙatar jarirai guda biyar sabbin haihuwa,sai kuma idanun yara masu wayo guda biyu...,"
Shuru yay na wani lokaci kafin ya ɗora da faɗin
"Buƙata ta ƙarshe kai da matarka muke buƙata,zanyi amfani dakai kuma zanyi amfani da matarka ne bayan kaci zaɓen"
Cikin hanzari Mubarak Yahya cibo ya ɗaga kai ya kalli boka Saƙib kana ya maida kan zuwa ƙasa yace
"Ban gane mene kake son faɗa ba"
Wangalelen bakinsa bokan ya buɗe yace
"Ina nufin zanyi amfani dakai ma'ana zamuyi luwaɗi (Astagafirullah) sannan idan kaci zaɓen zaka kawo min matarka na ƙwanta da ita,wannan bawai shawararka nake nema ba kusan dole ne sabida ka riga ka aminci da abinda nace tun kafin na gaya maka abubuwan da muke buƙata,idan kaƙi kuma zaka kaga abinda zai faru da kai"
Tunani Mubarak Yahya cibo ya fariyi,shin boka Saƙib nada cuta ko bai da ita? Kullum zasu dinga aikata hakan ko kuma na wani lokaci ne,sannan idan yaci zaɓen zai iya ƙin kawo masa matar tasa sbd burinsa ya riga daya gama cika bashi da ikon da zai sanya a ƙwace masa mulkinsa, numfashi ya sauke kana yace
"Buƙatar ka a gareni na yini guda ne? Ko kuma na wasu ranaku ne?"
Zane boka Saƙib yayi a jikin ƙasa kafin ya ɗago kai yace
"Na Sa'a biyu ne kacal,da zarar mungama shikenan ka gama aikinka sai bayan zaɓe"
Murmushi Mubarak Yahya cibo yayi yana mai jin wani farin ciki tare da anushuwa a cikin zcyarsa, gani yake tamkar ya yaci wannan zaɓen ne hakan tasa cikin sauri yace "na amince..
By
NIMCYLUV
6/26/21, 2:43 PM - Buhainat: *UCL NE*
BOOK 2
60-61
Dariya boka Saƙib yayi kafin ya daki wani ƙoƙo daga cikin ƙoƙonan dake gabansa,nan take photon Jalilerh ya bai yana tana zaune a gaban dressing mirror tana shafa lotion daga ita sai ɗan kuntun towel,
Tsora mata ido boka Saƙib da Mubarak Yahya cibo sukai ko wanne da abinda yake saƙawa a ransa,can boka Saƙib ya ƙara dukan ƙoƙon nan take photon ya ɗauke,kana ya ɗago kai ya kalli Mubarak Yahya cibo yace
"Wannan tana da muhimmanci a gareka,idan ka sameta ba governor har shugaban ƙasa sai ka zama"
Baki ya washe domin nan take ya fahimci wacce yarinya ce domin har abada bazai manta da ita ba,numfasawa yayi cikin hanzari kuma yace
"Mene muhimmanci ta a gareni?"
Miƙewa boka Saƙib yayi yace
"Ba yanzu ba sai nan gama kaɗan zan sanar dakai muhimmanci ta,da kuma abinda za'ai mata,zaka iya tafiya duk sanda na kiraka ranar zan gabatar da ƙudiri na a kanka,kada ka manta da jaririran da kuma idanuwan"
Yana faɗin haka ga shige cikin wani ɗan ma dai-dai cin ɗaki, farin ciki fal fuskarsa ya fita tunda a hanya ya sanarwar da Lamir ya kira masa p.a ɗin sa..
Da daddare Jalal ya na zaune a parlour'n sa shida Jafar yana masa bayanin abubuwan da Prince Hassan ke yaɗawa a media ya wanci duk yaɗa manufa ne da kuma tunasar da al'umma muhimmanci al'ƙawari,da kuma gaya masu irin nagartarka, ajjiye glass cup ɗin hannunsa yayi,a hankali kuma ya kalli Jafar yace
"Me kake harshashe akan wannan zaɓen?"
Wayar hannunsa Jafar yayi kafin yace
"Eh to,da alama bamu da magauta, sannan kuma ya maɗiɗi da ake dakai akan abinda ya faru yay sanyi domin yanzu ba'a maganar,abu guda mutane suke yawan surutu akai wanda nima shi yake ban mamaki da kai boddy,kuma koni ina son na san mene yasa hakan?"
Lumshe idanunsa yay kafin ya buɗe su akan Jafar,cikin ƙasa da murya kuma yace
"Mene?"
Jafar ya maida hankalinsa akan Jalal sosai kafin ya numfasa yace.
"Tayaya wanda bashi da iyali wanda bai son yadda ake mulkar iyali ba har yake tunanin mulkar dubban jama'ar gari?" Wasu ana gane adalci ne a lokacin da suke adalci a cikin iyalansu,uwa uba idan mutum ya kasance yana da zuri'a masu yawa, Jalal nima yanzu ina son nasan mene yasa aduk lokacin da akai maka maganar aure saika bauɗe? Afuwa bawai ina saka maku ido a cikin gidanku bane,amma ina kula da komai kuma ina fahimtar ka,ka girman sosai amma a yanzu ace da ba Nihila nake jira ba dana manta dayin aure,kana da dukiya,kana da ilimi,kana da kyakkyawan tsohe asali kuma nagarta,babu wata ƴar mace da zata kalleka tace bata sonka,kai ko a matan ka rasa wa zaka ɗauka, aƙwai matan da dayawa zasu kawo maka tayin soyayyar su,bama ni ba maganar da ake yanzu Aryan ma shirin yin aure yake"
hannunsa ya tura cikin sumarsa ya ɗan birkita ka ɗan kafin ya saki wani guntun murmushi yace
"ALLAH ya sanya alkairi"
Jafar ya kalli Jalal cikin serious magana yace
"Meye damuwarka?mene yasa baka son yin aure ina son sani indan har da gaske kallo aboki nagari kake min kuma wanda yake da kusanci dakai"
Miƙewa Jalal tare da nufar cikin bedroom yana tafe yace
"Ina sharing damuwata ne da iya zuciyata"
Yana faɗin hakan ya shige cikin bedroom ɗinsa.
Da ido Jafar ya bisa yana son fahimtar abinda yake zuciyar Jalal ta hanyar ƙurawa fuskarsa ido amma bai fahimci komai ba,domin fuskar bobo wasai take. Abu alamar damuwa ko guda.
Agogon hannunsa ya duba yaga 9 saura, miƙewa yayi shima ya fice daga cikin part ɗin Jalal
A main parlour ya tarar da Mama hannunta riƙe da mahaifi gefenta kuma Nihila ce tsaye itama sanye da Orange ɗin abaya tayi rollig kanta da vail ɗin abayar, Mama ta kallesa tace
"Kai Allah dai yay wadarar rashin ƙiba,ji yadda kake tafiya babu masali,ohhh ƙilan durune ko?"
Ɗan haɗe rai yayi sabida ganin Nihila tsaye yace
"Ke kuma sa'ido Mama,banda haka mene naki da rashin ƙibata dan Allah?"
Taɓe baki tayi tana gyara zaman kalbin kanta tace
"Kaga bana da lokacin surutu yanzu, ni ba asa rariya bace maza jeka kira min Jalalu ya kaini shufin"
Waje ya nema ya zauna yace
"Tab ai sai dai kiji da kanki,nidai aka gama yiwa ba'a"
Da sauri ta juya tace
"Waye yay maka ba'a kuma? a'a wlh babu ƙyau ai haramun ne,kamar wani yay maka jikin ba Ubangiji ba"
Kusan a tare Jalilerh da Aryan suka fito daga parts ɗinsu,da sauri Mama ta washe baki tace
"Yawwa takwarar Jalalu ki kiramin malamin naki"
Aryan dake tsaye yay saurin faɗin
"Malami kuma Mama?"
Ta gefen ido ta kallesa tace
"Ehmn,ba ankul naji tana faɗa ba?duk da dai ba makaranta nayi ba amma nasan ai malami ake faɗawa"
Jafar ya miƙe tsaye yana kallon Nihila kafin ya maida direction ɗinsa zuwa ga Mama yace
"Kin faɗi gsky da kikace maki makaranta ba,wanda yay yasan ma'anar ta"
Bata kulasu ta kalli Jalilerh wacce har yanzu take tsaye da riga da wando sai vail da tasa ta yane sumar kanta tace
"Maza jeki kinji yarinyar kirki,na maki alƙawarin wannan lemon na zuƙa"
Kanta a ƙasa jikinta kuma sanyaye ta nufi hanyar da zata kaita part ɗin,da hanzari kuma Aryan yace
"Mama bari na kira maki shi,ita aƙwai abinda zata"
Haɓa Mama ta riƙe tace
"Kaji kinibibi,to ba sallamammiya bace ni,maza ban waje"
Bisa dole ya matsawa Jalilerh hanya ta shige ya bita da ido yana mai jin wani raɗaɗi a ransa,musamman da yay duba da kayan data saka.
Zama Mama tayi a saman kujera ta tattauna dakakken goran data zuba a bakinta, Nihila tayi dariya tace
"Me yasa kike daka goro ne bayan ya haƙora nan a bakinki?"
Harara Mama ta watsa mata kafin tace
"Sabida ban samu haƙori ba ina uwarki, yooo inama ruwanki danine ba dai ni kikaiwa ruwan dubulan ba,kawai dai nafi jin daɗin cinsa a haka,ba kiga har ƙashi nake taunawa ba"
Nihila ba tace komai ba saboda alama da Jafar yay mata da hannu da tayi shuru
Ƙwance ta samesa ya ɗaga kansa sama yana kallon silin dake cikin bedroom ɗinsa,tunani ne fal cikin ransa akan abubuwa da suke faruwa dashi,wato bayan ahhalinsa dake ƙwalla fa ran yay aure yadda al'ummar gari,to duk mene yasa hakan ke faruwa ne? Shi kaɗai ne namiji wanda bai da aure?ko kuma mulki da yake nema yasa duk hankali mutane ya dawo kansa? Yasan da ba'ai masa wannan surutu,to inama za'ai masa tunda gaba ɗaya ba'a ƙasar yay rayuwa ba,rabin rayuwarsa a yanzu haka a Paris yayi ta sai dai kuma nan gaba,kuma yasan cewa abune mai wahala yakai adadin shekarun da yay a Paris da ransa,yasan bashi yake tsara rayuwa ba amma yana roƙan Allah ya ɗauki ransa akan ya ƙara adadin shekarun da yayi a Paris,mene a duniyar da har za kaji daɗin zama a cikinta? Aure! Aure! Aure bayan da yawan mutane ba kowa yasan darajar aure ba...,"
Daga ƙofa yaji ance
"Kayiwa aure mummunar fahimta,duk ba sanin al'adun ku na sani ba da kuma yanayin zaman aurenku,amma da yadda su Mummy ke rayuwa a nan gidan zaka fahimci ba duk aka taro aka zama ɗaya ba,ko anamu Yaren ya nuna mana yadda ake zaman aure da kuma yadda ake daraja auren kuma na tabbatar da hakan wajan Ammi na"
Lumshe idanunsa yay kafin ya sauke numfashi a hankali yace
"Me kika sani akan auren ke?"
Duk yadda zcyarta ke bugawa akan abinda yake addabar ta a ƴan lokutan nan bai yana tace
"Ban san yaya aure yake ba,sabida bana da tabbacin zanyi sa,amma yadda Ammina keyi duk da ba komai take ganewa ba nasan aure a wajan hausawa yana da daraja"
Miƙewa zaune yayi kafin ya ɗan kalleta da hannu yay mata nuni data ƙarasu ciki,hannu tasa ta danne saitin zcyarta,kafin tayi ƙarfin halin shiga ta ƙarasa inda yake zaune,a gefen ƙafarsa ta zauna saman carpet tace
"Uncle Mama tace kaje"
Zamuwa yayi daga saman bed ɗin ya ɗura kansa bisa shoulder ɗinta yace
"Meyasa ke baza kiyi auren ba tunda kin isa?"
Runtsa idanunta tayi da ƙarfi ka ta ɗan ware bakinta tace
"Tayaya wani zai ganni a halin da nake a yanzu har yayi sha'awar aure na, muna da saɓanin addini kuma babu wani na mijin da zai sha'awar aure na,koda yayi danginsa ba lalle su aminta ba,kuna Sallah,azumi,kuna sadaka kuna bada zakka kuna ziyartar ɗakin ALLAH,uwa uba wanda babu yadda dashi ba ku kun yarda dashi,kaga muna da banbanci mai yawan gaske,wazai yarda ya ajjiye guba cikin abu mai ƙyau,na sani koda na amshi musulunci wata rana zan haɗu da fushin uwa sundu,zan fuskanci zalunci wajan jama'ar birninmu, mutum biyu zasu samin garkuwa a birnin"
Ta ƙare maganar muryarta na rawa,wajan 10seconds yace
"Su waye?"
Cikin rawar murya tace
"Uncle Jabir da Ammi"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka,a hankali yaja idanunsa ya lumshe kukan nata da yaji ya tsananta yasa ya jawo ta jikinsa tare da rungome ta ya shiga bubbuga bayan ta,shuru sukai gaba ɗaya kafin ta miƙe da sauri daga jikinsa tace.
"Uncle ina son komawa gida, Please ka mai dani kaji"
Hannunsa yasa ta tallafo haɓarta tare da cewa
"Look at me"
Kasa kallonsa tayi sai idanunta dake zubar da ƙwalla, murmushi yay dan yasan daban ba zata kallesa ba,komai nata ya sauya saɓanin da,tana da kunya hankali nutsuwa,komai nata daban yake kallonsa a yanzu, ƙasa yay da murya yace
"Why kike son haka? Ko kin mata da saurayin naki na can me jiran ki?"
Turo baki tayi tana ƙara sautin kukanta, baya yayi ya jingina da jikin bed jin tare da zuba mata shanyayyun idanunsa,
Ajjiyar zuciya Aryan ya sauke da sauri lokacin daya gama kallonsu,tunda ɗazo ya shigo da Mama tace taji shuru yaje ya duba,fita yayi daga part ɗin yana tafe yana dailing wata number kana yay kira, ɗauka akai daga can ɓangaren Lamir yace
"Lafiya kira a wannan daren?"
Aryan kamar zai sanya kuka yace
"Aƙwai matsala Daddy Lamir"
Lamir ya kalli p.a dake kusa dashi tana driving yace
"Yanzu ina hanya,amma meke faruwa ne haka?"
Aryan ya kwashe komai ya faɗawa Lamir,shuru yayi yana sauraran abinda Lamir ke faɗa masa,cike da murna yace
"Ngd sosai Daddy Lamir"
Camerar wayar ya kunna tare da komawa ɗakin
Jalal yace
"Iya jeki ƙwanta"
Kanta a ƙasa tace "me zan cewa Mama to?kasan masifa zatai min"
Ɗan haɗe rai yayi yace "kakar tawa take masifa Jaalilerhhhh"
Da sauri ta ɗaga kanta dan rabon da taji ya kira sunanta ta manta,da mamaki tace
"Uncle kasan sunana daman?" Juyawa idanunsa yayi yace "a'a"
Ta kwaɓe fuska tace "gashi ka faɗa yanzu" hankalinsa akan agogon ɗakin yace "a'a" turo baki tayi tace "Amma Mama tace sunanmu iri guda ne" ɗan waro idanunsa yay cike da mamaki yace "laaa haba!? Ni meye nawa sunan" sunkuyar da kanta tayi a cinyarsa tana dry ƙasa-ƙasa,hannu yasa ya ɗago ta yace "ohhyaaa out" turo baki tayi tare da marairai ce fuska girgiza kai kawai yayi kafin yasa hannu yaja lips ɗinta,baki ta buɗe zatai kuka yayi sauri bata light kiss a gefen lips ɗinta a dai-dai nan kuma yaga haske