Showing 60001 words to 63000 words out of 120090 words
kamar na wuta ya bai yana a É—akin.
Tafiya take a hankali daga ita sai wando da kuma ƴar ma dai-dai ciyar riga iya guiwa kanta sanye da hula,sosai take tafiya lokaci zuwa lokaci tana duba bayanta sabida babu wanda yasan fitowar ta,bata wani buri daya huce taje inda ake kiranta,domin tayi amana kiran alkairi ne,tunda ance mata UNCLE NE ke kiranta,dukkan abinda aka haɗa da Uncle ɗinta tasan alkairi ne,tsayawa tayi bakin wani layi inda akai mata ƙwatance dashi,tana tsaye tana rarraba idanunta,wata dalliyar mota ce ta tsaya a gefenta,baya taja kaɗan,zuge glass ɗin motar akai wani matashin mutum ne age mate ɗin Uncle ɗin ta,ya leƙo da kai waje yace
"JALILERH KO?"
Kai ta ɗaga masa alamar "eh" murmushi yayi yace "ok shigo to, Yallaɓai Jalal yace akai ki wajansa yana gidan gunarsa" cikin murna ta buɗe murfin gaban motar ta shiga reverse yayi yaja motar da gudu,sosai yake tafiya tun tana ganin abin wasa harya tsallake tunaninta sbd ganin sun fara shiga cikin daji,kallon mutumin tayi tace "a ina Uncle ɗin yake?"
Murmushi yay mata yana kara giyar motar ba tare da yace komai,sosai tsoro ya kama JALILERH,cikin tsakiyar wani daji yay parking tare da fitowa daga cikin motar, buɗe mata yay ta fito lokacin idanunta harya fara zubar da hawaye,hannunta yaja tana tirjewa tare dayin ihu amma ko kaɗan bai raga mata ba,juyawa tayi taga dajin babu alamun mutane ko guda ɗaya ga yadda dajin yake da duhun gaske,ahaka harya shigar da ita wata bukka, wani matashin saurayi ne zaune daga shi sai three gaiter ko riga babu jikinsa,sai facemask daya sanya ya rufe fuskar gaba ɗaya,kallonsa ta shiga yi tare da ƙarewa fatar jikinsa kallo,ganin hakan yasa wancan mutumin yay saurin fita tare da rufe ƙofar bukkar,tana tsaye sai ihu take har muryarta bata fita sbd kuka, mutumin ya miƙe tare da ɗaukan wata igiya ya nufi inda take tsaye,yana zuwa ya fincikota ta faɗa saman tabarmar kabar bukkar bai tsaya jiran komai ba ya ɗaureta da igiyar hannu da ƙafa yadda ko mutsi ba zata iya ba, idanunta ta rufe sabida sam ba zata iya kallon abinda yake ba tana a ƙwancen taji ya faɗa kanta tare da tura kansa..,wata razananniyar ƙara ta fasa tare da kiran sunan UNCLE....!!
is not free is for sale 300 kawai 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 081192376
By
NIMCYLUV
6/27/21, 5:45 PM - Buhainat: *UCL NE*
*BOOK 2*
64-65
Kai tsaye kujera dake can gefe da ita ya zauna tare da juya mata baya,a hankali yaja idanunsa ya rufe tare da fesar da iska mai zafi daga cikin bakinsa,sai lokacin kallon da Nusaibat dake masa ya faɗo masa, ɗan ƙaramin tsaki yaja haka nan yaji yarinyar bata ƙwanta masa ba,bata iya ɓoye abinda ke ranta tana abu tamkar wata zautacciya,yasan cewa rayuwa mai sauƙi ce kowa yana da ƴan cin yin abinda yaga dama,amma shi mene yasa bashi da wannan ƴan cin,mene yasa komai yake zuwar masa a baibai ba kamar yadda yake tunani ba,ji yake inama bai nemi wannan kujerar ba,inama bai tsaya takarar governor na ba,da duk hakan bai faro ba,da yanzu jama'a basu saka masa ido ba,yanzu haka dukkan abinda yay idanun jama'a na kansa wani abin kafin yay an samu wani ya fitar dashi,tayaya hakan ke faruwa? suwaye suka sanya rayuwarsa ido har haka? ƙara gyara zamansa yay yana mai jin yadda kansa ke juya masa,tafin hannunsa ya sanya a saman forehead ɗinsa ya fara murzawa a hankali, Jalilerh na gefe tunanin mafarkin da tayi ya hanata sakat,a mafarki ma mutum ɗan uwanka na neman cutar da kai bare a zahiri? Abinda ke ɗaure mata kai yadda akai amfani da Uncle wajan ganin an tarwatsa rayuwarta,mene yasa komai idan zai faru da ita ake haɗawa da Uncle ɗinta?a wancan karan ansa ta muzan tashi,taci zarafinsa ba,a wannan karan kuma an nemi aci zarafin ta ta hanyar amfani da sunan Uncle ɗinta,me yasa a iya kanta kawai hakan ke faruwa?meyasa ba'a amfani da sister ɗin sa? Mene yasa ba'a amfani da wata matar?ko dan ta kasance mara addini hakan take faruwa da ita? Bata da wata addu'a da zata zame mata makami akan maƙiya ko abokan gaba,shuru tayi tana tunanin maganar Nihila inda take cewa *_kiyi tunani da zuciyarki,abinda ta amince maki shine dai-dai_* ajjiyar zcya ta sauke domin zuwa yanzu ta gama yarda da abinda zuciyarta ta amince mata,ta amince da aminda take kwaɗai ta mata tana ganin shine abinda yafi dacewa da ita a yanzu,wanda zai zama garkuwanta,mutsin da taji a bayanta yasa ta juya da sauri,mamaki fal fuskarta take kallonsa, yaushe ya shigo? Tana wanne tunanin? Shin ya ganta daya shigo ko a'a? Meyasa bai kulata ba? Jiki a sanyaye ta miƙe tare da nufar inda yake zaune,tana zuwa ta zauna gefen ƙafafunsa daga ƙasa,sosai bobo yaji idanunta a kansa amma yay kamar bai ganta ba domin a yanzu yana so ya kasance shi ɗaya babu takura,yana buƙatar yay tunani,tunani mai zurfi a kan rayuwar sa yanzu da kuma wacce zai fuskanta nan gaba,suna zaune babu wanda ya iya cewa komai kowa da abinda yake tunani,ita tana buƙatar sanar masa abinda ta yanke, shi kuma yana tunani akan zaɓen dazai gaba a sati mai zuwa, ƙafarsa data zauna akai ya ɗan mutsa kaɗan da sauri itama ta janye jikinta,ganin bashi da niyar tambayarta abinda ya kawo ta wajansa yasa tayi ƙasa da kai tare da kiran sunansa a hankali "Uncle" lumshe idanunsa yay kafin ya fesar da numfashi,bai amsata ba kuma bai mutsa ba,wajan 5minutes ta ƙara kiran sunansa "Uncle" murya can ƙasa yace "uhm"kanta ta ɗaga tana ɗan turo baki gaba,ido biyu sukai dashi kasancewar kansa a ƙasa yake dai-dai lokacin data ɗago kai a dai-dai lokacin shima ya ware manyan gajiyayyun idanunsa,da sauri ta janye nata,shuru yayi mata still yana ƙara ware manyan idanunta a kanta,a zahiri kuma bawai ita ɗin yake kalla ba, fararen ƴan yatsunsa na ƙafa ta zubawa idanu,ko wanne yatsa gargasa tayi ƙwance a samansa,cikin muryar ta mai rauni tace "Uncle nayi tunani kamar yadda baby tace nayi,kuma na amince da abinda Zuciyar tawa take faɗa min,amma bazan samu cikar muradin zuciyata ba sai ta dalilinka"tunaninsa gaba ɗaya ya tattaro zuwa gareta kafin yace "uhm inaji" cikin muryar kuka tare kuma miƙa wuya da kuma yadda da amincin zuciyar ta tace "Uncle ina son kalmar shahada,ina son yadda da annabi Muhammad Rasulullah (S.a.w), Uncle ina son rabauta da addinin musulunci" ta ƙare maganar hawaye na bin fuskarta,kamar saukar ruwan sama haka yaji saukar Muryar ta,da saurin da bai san yana dashi ba,yayi sauri sanya hannunsa ya ɗaga ta zuwa saman kujera, haɓarta ya tallafo idanunsa na yawo saman fuskarta yace "Are you sure? Kin tabbatar da abinda kike faɗa gasky ne?" Cikin kuka tace "na yarda Uncle ba tare da faɗar wani ba,ko kuma tursasawar wani ba,na yarda da hakanne sabida yarda da Annabi Muhammad Rasulullah,kuma da yarda da addinin musulunci shine addini guda kuma mafi suyowa, musulunci shine addinin gsky,kuma shine garkuwan ko wanne ɗan adam" sabida murna da farin cikin kasa cewa komai yayi sai kallonta yake da ido, miƙewa yayi tare da kallonta yace "muje ciki" a ƙofar shiga parlour suka haɗu da Nihila da ido take kallonsu, musamman bobo wanda fuskarsa take ɗauke da matsanancin farin ciki,wanda ta daɗe bata gansa a ciki ba,ganin yadda ta tsaya take kallonsa ya saka yasa hannu ya matsar da ita gefe kana ya shige cikin parlour'n, kusan gaba ɗaya jama'ar gidan na nan hadda Jafar wanda zuwansa ke nan, Mama ce tace "kai kuma lafiya kake farin ciki kamar wanda akaiwa ƙyauta da kujerar Makkah?" Lumshe idanunsa yay few seconds ya buɗe su a kan Mama yace "ko aikin hajji bai kai darajar wannan abunba"jin haka yasa Mummy ta gyara zama tace "bobo bamu musha mana" hannu yasa yaja gefenmu fuskarsa kafin ya sauke tagwayen ajjiyar zcya yace "gaya masu" ya faɗa yana sauke ganinsa akan Aryan kafin ya janye idanunsa,jiki a sanyaye ta faɗa masu the same abinda ta faɗawa Jalal,farin ciki ya sanya kusan gaba ɗaya wajan suka miƙe tsaye,cike da jin daɗi Abbou yace "me ake jira, Muhammad maza bata kalmar shahada, wannan ai abin farin ciki ne"gyara tsaiwa yay dan baya jin zai iya zama, Mameey miƙewa tayi ta rufe wa Jalilerh gashinta da wata red ɗin hula, cikin taushi murya yace "kin yarda kin amince zaki shiga addinin Musulunci ba tare da takurawar wani ko wata ba?" Jiki a sanyaye ta ɗaga masa kai, girgiza kansa yay kana yace "da baki zaki amsa" cikin rayuwar murya tace "eh" jinjina kai shima yayi alamar "good" kana ya ɗura da faɗin "kinyi hakanne bisa rafin kanki,tare da amincewar zuciyarki?" Nan ma tace "eh" cike da farin ciki ya ƙara sakin murmushi,wajan fridge ɗin dake parlour'n ya ƙara gorar ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle murfin gorar ya sanya cikin bakinsa,sai da yasha fiye da rabi kafin ya sauke gorar ruwan yace "kafin nan zanyi tsokaci akan ADDININ MUSULUNCI" gaba ɗaya wajan suka miƙa masa hankalinsu,banda Aryan da yake latsa wayarsa cikin tsaftacciyar muryarsa ya fara da faɗin.
MUSULUNCI
addinin Musulincci yazo ne daga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi, shine manzon da Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki daya kuma na karshe annabawa a duniya domin yasake jaddada addinin Allah ayi imani da Allah daya wanda Ya halicci kowa da komai. Addinin musulunci na da mabiya a duk fadin Duniya kuma mafiya yawan su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin Afirka ta arewa wadanda mafiyansu Larabawa ne masu bin adiinin musulunci, sai dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci ako'ina a fadin Duniyar mu, Ma'anar Addinin Musulunci shine " Yarda da Mika wuya ga kadaituwan Allah Madaukakin Sarki, wato Shaidawa babu abun bautawa da Gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzonsa ne (Ma'aikinsa ne), bayan haka ka yarda da dukkan abubuwan da ya kebanta dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai"Allah Madaukakin Sarki shi ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma domin yazamo shiriya da Rahma ga Halittu baki daya, an bayyana musulunci a matsayin addinin dake da saurin karin yawa a duniya a kullum wanda ke da Adadin musulmai na Duniya sun kai kusan kashi 24.1% na dukka mutanen Duniya wato fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari takwas (1,800,000,000) a fadin duniya.
tsit wajan yayi banda ƙarar a.c babu abinda kake jin mutsinsa a wajan,hatta Mama zaune take ta tafka tagumi tana jin abinda Jikan nata yake faɗa tamkar balaraban Makkah wanda yake jan sallar ashan yayin azumi, Jalal kam shuru yayi yana jin yadda maƙoshinsa ke suya sabida yawan maganar da yayi,gefe guda kuma yana jin yadda yake samun nutsuwa a cikin zcyarsa,a hankali kuma ya juya ya kalli Jalilerh wacce kanta ke sunkuye sai zubar da hawaye yake, ɗan haɗe rai yay sabida kallon da yaga ana masa,kafin ya sauke idanunsa zuwa ƙasa haɗi da kama hannunta ya sanya cikin nasa ya ɗura da.
Dukkan addini na gaskiya ko na karya, dukkan jam'iya mai anfani ko mai cutarwa, dukkan kungiya mai alkhairi ko mai sharri�
Dukkan wadan nan suna da akidodin su da kuma ginshikai da manufofin manufofin su, manufofi da ke zama kamar kundi ga mabiyan su.
Idan mutun yana son shiga cikin ko wane daya daga ababen da suka gabata, abu na farko da yake dibawa shine wadanan akidodi da gimshikai, idan ya yarda da su, kuma ya kudurcesu ba tare da shakku ba, bayan ya fahimci abinda suka kumsa, sai ya mika wuya, ya kuma zama daya daga ma biya wanan kungiya ko addinni. Bayan haka sai ya kasance wajibi akan shi ayukkan da ke wajibi akansu, ya kuma nisanci ababen da shi wanan kundi ya kumsa tare da ikhlasi a cikin dukkan ayukanshi a kowane lokaci, ya na mai kira zuwa gare shi.
Kasancewar mutun a cikin wanan kungiyar yana nufin ya san dokokin wanan kungiyar, ya kuma kudurci manufofinta, bayan haka ya yarda da hukunce hukuncen ta, tare da bayyana wadannan dokoki da hukunce hukumce a aikace. haka ne Muslunci ma.
Wanda yake son shiga cikin muslunci ya zama wajibi a kansa yayi imani da kudurce kudurce na muslunci dan ya kasance ya na akida ta muslunci.
Wanan akida ta kunshi imani da kasancewar wannan duniyar da muke gani ba ita ce kway ba, akoy abubuwa wa 'ynda ba ma ganinsu, akoy kuma wata rayuwa bayan wannan rayuwar ta duniya.
Dan adam bai samar da kanshi ba, bayan haka wani abun halitta bai samarda shi ba, ba wanda ya samarda shi banda ubangijin da ya samarda halittu gaba dai bayan babu su, wandake bada rayuwa ko mutuwa, shine Allah wanda ya halicci kowa da kome, idan kuma yaso sai ya kasha su gaba daya, wanda babu mai kama da shi, babu wani abu da yake buya gareshi, shine na farko babu wani abu gabaninsa, shine kuma na karshe babu wani abu bayansa, shine mai ikon da ba shi da iyaka, shine mai adalcin da bay a kama da adalcin ababen halitta.
Shine ya saka ka idodi na dabi ia da rayuwa ke tafiya a kai , ya kuma sanya kome a matsayin sa da ya cancanta tun fil azal, ya kaddara motsi ko aiki da rashin su, yakuma baiwa da adam hankali da yake gane abubuwa da yawa da shi, wanda kuma da shine Allah ya bashi damar zabin abin da yake so a cikin rayuwa.
Bayan wannan rayuwar takaitatta ya sanya wata rayuwa wadda take mai dorewa ita ce lahira domin ya sakauta wa masu biyayya gare Shi a kan ayukkan su nagari da aljanna, wadanda suka ki biyayya kwa da jahannama.
Allannan shi daya yake ba shi da abokin tarayya, bai sanya tsani tsakanin shi da bayin Sa ba, babu mai ceto agurin Sa ba tare da izinin Sa ba, Shi kadai ake wa bawta, ko wan irin bawta ne.
Ya nada ababen halitta wadanda muke ganin su kamar yanda yake da halittu, masu motsi da wadanda ba sa motsi, da ba ma ganin su.
Halittun Sa sun kasu kishi uku:
Masu alkhairi kadai ( su ne mala' iku ).
Masu sharri kadai ( su ne shaidannu ).
Wadanda suka hada alkhairi da sharri ( aljani da mutun ).
Allah ya na zaben wasu mutane wadanda mala' ikun Sa ke sabkar da shari' a gare su domin su isar da ita ga al � ummomin su; wadannan mutane su ne manzonni.
Shari' a ta karshe daga cikin Shari' o' in nan ( shari' ar musulunci ) ta shafe dukkan Shari' o' in da suka gabace ta, dan haka littafi na karshe da Allah ya sabkar shine Alkur' ani , wanda ya kore dukkan litattafen da suka zo gabanin shi, domin litattafen nan an cancanza su, wadan su kuma sun bace, wasu kuma an manta su; Alkur' ani kadai ne ya kubuta daga ababen da su ka gabata.
Kuma hake ne muhamad ( tsira da rahama ta musamman su tabbata a gare shi, shi da dukkan annabawa ) shine manzo na karshe da ALLAH ya aiko, shi kwa dan kabilar kuraishawa ne a cikin larabawa, dan haka da shi aka cika annabci; babu wani annabi bayan shi.
Alkur' ani shine kundi na Muslunci , dukkan wanda ya gaskata cewa daga Allah yake shi wannan al kur' ani, ya kuma yi imani da shi gaba daya, to wannan ana kiran shi mumuni.
Imani ko da wannan ababe da suka gabata babu wanda ke ganin shi a cikin zuciyar mutane banda ALLAH; domin shi kadai ne ya san abin da zuciya ta kumsa, mutane sun san abinda ke zahiri ne kadai.
Domin haka ana dauka mutun musulmi idan ya yi firici da shahadar cewa babu wani abin bauta wanin ALLAH, kuma muhamad ( tsira da rahama ta musamman su tabbata a gare shi, shi da dukkan annabawa ) manzon ALLAH ne.
Idan ya firta wannan shahada lalle ya zama daya daga cikin musulmi, ya nada hakki kamar dukkan musulmi, haka kuma dukkan abin da ke hawan musulmi ya na hawan shi.
Wadannan abubuwa da ke rataya a kan shi abubuwa ne masu sauki, kuma ba masu yawa ba, daga cikin su:
1- sallah; zai yi ruku' u ga ALLAH so biyu da safe, wannan ruku' un kwa ganawa ce da ubangijin shi domin ya nemi rahama da tsarinshi daga dukkan sharri.
Gabanin wannan ganawar zai yi alwala ( tsabtace gabban shi ), ko yayi wanka idan akoy janaba a tare da shi.
Sa' annan idan rana ta kau da tsakiya sai yayi raka' a hudu.
Idan kuma inuwar shi ta lunka tsayin shi so biyu sai ya yi raka' a hudu.
Ya kuma yi raka' a uku yayinda rana ta fadi.
Da dare zai cika sallolin shi da raka' a hudu.
Wannan sune salloli da ke wajibi a kan shi, ko wace daya daga cikin su bata wuce minti goma ba, ba' a kuma kayyade su da wani guri na musamman, ko wani mutun wanda dole za' a yi ta da shi, ba kuma wani tsani a cikin ta tsakanin mutun da ubangijin shi.
2- a cikin shekara akoy wani wata wanda musulmi yake azumta; a cikin wannan wata yana nisantar abinci da abin sha, ko saduwa tsakanin namiji da matar shi, daga safe har faduwar rana, wanan ko dan ya tsarkake zuciyar shi, ya kuma futar da tubin shi, ya kuma gyara halayan shi.
Sa' an nan wannan watan wata ne dake karantar da musulmi game da haduwa akan aikin al kheiri.
3- idan dukiyar musulmi ta haura bukatar shi da ta iyalin shi, ta kai wani haddi da shari' a ta kayyade, ta kuma shekara ba tare da ya bukace ta ba, ya na zama wajibi a kan shi ya fitarda wani kaso kankane ( biyu da rabi cikin dari ), ya bayarda shi ga mabukata da talakkawa � abin da zai kawo hadin