Showing 36001 words to 39000 words out of 120090 words
nan? Mene za suce idan Ubangiji ya zare ranka a wannan halin? Mene yasa shugabanni basu taɓa cewa matasa su kawo takaddunsu na makaranta domin sama masu aiki ba? Mene yasa basu taɓa bawa matasan da suke sonyi karatu kuma basu da hali damar kai takardunsu domin kaisu wata makarantar domin su samu in gantaccen ilimi.." ƙara ɗago kai yyi kafin ya sauke ajjiyar zcy ya ɗan ja kujerarsa baya kaɗan kafin yace "shima kuna nufin shugabanni basu san hakan ba dai-dai bane?,daku nake matasa da iyayen yara baku taɓa tunani abinda sukewa yaranku ba dai-dai bane rayuwarsu kawai ake ruguza wa..!!!? Ya ƙare maganar cikin tsayawa tare buga mencin dake kusa dashi,calmy yyi kafin ya fara jujjuya kujerar yana ƙarewa mutanan wajan kallo, watch ɗin dake manne a tsintsiyar hannunsa ya kalla wanda ya kasance apple,gani yyi 5:30 saura minti 5, ɗan jaridar ne yace "yallaɓai muna jinka" ware idanunsa yyi waje shi kaɗai yasan suyar da maƙoshinsa yake masa sbd yawan mgnar da yyi,fesar da numfashi yyi ta bakinsa kafin yace.
"FYAƊE zuwa yanzu naga abin ya zama kamar ruwan dare a cikin al'umma,yau kaji an ce anyiwa waccan Fyaɗe gobe kaji an ce ayiwa waccan jibi kuma ba'a san mene za'a ce ba,uhmm an taɓa ɗan kan hukunci akan wanda yyi zina da auransa? An taɓa ɗaukan hukunci akan saurayin daya aikata hakan,daku nake Al'kalai nasan kunsan menene hukuncin wanda ya aikata zina da auransa,haka kuma kunsan hukuncin da akewa saurayin da yyiwa wata fyaɗe ku koma zina, kun taɓa tambayar kanku mene ya saka yawan Fyaɗe yake ƙara yawa a ko wacce rana? To me ina ganin rashin sana'a da matasa basu da ita bare har suyi tunanin yin aure,hakan tasa da zarar namiji hqrinsa ya gaza zaije ya akaita Fyaɗe,nasan da yawan matasa a yanzu suna da burin aure amma rashin...," Shuru yyi kafin ya juya ya kalli Jafar cikin ƙasa da murya Jafar yace ingantacciya, lumshe idanu yyi yace "rashin in...in..ingantacciyar Sa'a da basu da ita yasa kowa ya ajjiye maganar auran a gefe,da ace wata rana gwamnati zata bawa matasa offer ta aiki nasan babu shakka yawaitar Fyaɗe a cikin al'umma zasu ragu" ɗan jaridar ne yace "Yallaɓai kana nufin gwamnatin yanzu bata ƙoƙari akan wannan abubuwan da kake faɗa?" Kallon ɗan jaridar yyi kafin ya gyara zamansa yace "to aini kome na zama sanadin gwamnati ne,why zance ba tayi? Ina faɗin abinda nake ganin suna faruwa da idanuna wanda kuma dalilin hakan ƙasarmu ba'a ci gaba kenan, gwamnati tayi min komai domin ita ta bani damar abinda na zama a yanzu,bazan manta da karamcin gwamnatin baya ba,shekaru kusan 28 kenan" jinjina kai yyi kafin yace "gsky yallaɓai ban taɓa ganin mutum mai karamci da kuma kammala haɗi da hikimar tsara mgn ba, kayi magana ta hankali kuma babu wanda zai ce ka tsoki wannan gwamnatin,samunka matsayin shugaba a yanzu ba ƙaramin cigaba zai haifar a wannan gari namu na ibadan ba, jinjina ga yallaɓai Muhammad Jalal bobo" kamar haɗin baki da mutanan da suke wajan shirar wanda sukai masa rakiya da kuma al'ummar gari sukace "jinjina ga Muhammad Jalal bobo" Hibba take zaune kusa da mahaifiyarta tace "all the best my love" kallonta hajja Ayushert tayi kafin tace "ki iya takunki a cikin gidanan wlh kika sake mahaifinki yaji ko ya gane wa kikeso kinsan sauran basai na gaya maki ba,da wannan shirar Jalal ya kama hanya tare da mutanan da sukai masa rakiya zuwa wajan.
a parking space Jafar yyi parking motar domin Jalal bai cika son securities su dinga binsa ba,ana gama parking Jafar ya fito ya buɗe masa motar yana fitowa ya kaiwa Jafar duka yace "ɗan iska kamar na sashi,kada ka sake buɗen mota ina da hannu" cikin tsokana Jafar ya sunkuyar da kansa ƙasa yace "am so sorry ur excellence ban ƙarawa" banza yyi masa ya shige ciki a main parlour ya samu kusan duk ƴan gida harda Nusaibat,tana ganinsa ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace "ina yini yaya" baiko kalli inda take ba ya huce wajan Mama ganin tana sharar hawaye hadda majina, kallonta yyi da alamar tambaya kafin yyi mgn Nihila tayi saurin faɗin "yaya wai mgnar da kayi ta kema kuka fa" wata majinar ta face a bakin zaninta kafin ta kalli bobo tace "Ashe haka kake da zcyar imani da tausayi buba? Nidai kaya feni dan har zcyta ina maka kallon mara mutunci musamman idan kaƙi siyomin wannan abun na zoƙa,ahhh to bazan munafurceka ba tunda ba ubana bane kai,amma dai angona kayi hqr kada na tafi lahira da zunubinka" dry Jafar yyi yana zama a kujerar dake kallon Nihila yace " Thanks God yau Mama ta yadda zata mutu" waro idanu tayi waje kafin tayi saurin miƙewa tsaye tana karkace ƙwankwaso😂 tace "Tabbas mutuwa sai dai ka gani a kanka,amma wlh ni yanzu na fara zama a duniya"huuu nida nake saka ran yin sabun aure na fice na bar maku gidanku" dry sukai kafin ta ɗura da "ahhh to nidai babu ruwana yuuuu duniyar gaba ɗaya nawa take" tana faɗin hakan ta shige part ɗin ta, Jalal bai tsaya ba yyi hucewarsa part ɗinsa, Jafar zama yyi suka ci gaba da hira dasu mummy da Mameey,yana shiga part ɗin nasa ya fara zare kayan jikinsa bayan ya gama ya saka su a inda yake ajjiye kaya masu datti,kai tsaye bathroom ya nufa ya sakarwa kansa shower sosai yaji daɗin ruwan sbd sanyin dake ratsashi yana sauka akan fresh skin ɗinsa,Lamir ne zaune shida Gwamna Faisal Lawan suna tattaunawa akan yadda zasu lalata zaɓen da za'ai a gobe,gaba ɗaya Jalal ya wargatsa masu plan ɗinsu,tun yana ganin abin wasa har ya gagara fahimtar abinda zai yi, murmushi yyi ya kalli Faisal Lawan yace bani kunanka kaji,da sauri ya miƙa kunna sa wata dryar mugun ta sukai a tare kafin gwamna Faisal Lawan yace "gsky Lamir baka da imani,kuma kasan idan wannan abun yyi yadda muke so kashin Muhammad Jalal ya bushe" tafawa sukai Lamir yace "ahhh niɗin na wasa ne" fitowa yyi cikin shigar sa ta shan iska,daga shi sai wando three gaiter ko singlet babu jikinsa,sai fresh skin ɗinsa wacce take ta sharning,zama yyi kafin ya kunna t.v ya fara kallon labarai har lokacin shirarsa ake watsa,inda akai translation
ɗinta da harshe kala-kala, wayarsa ya ɗauka yyi dailing number Mummy ringing ɗin farko ta ɗaga tace "my love ya akai?" numfashi ya sauke yace "Mom yunwa,bawa beb ko wannan yarinyar su kawo min part ɗina" murmushi tayi tace "ok" kallon Jalilerh tayi tace "my dear jeki haɗawa Uncle ɗinki abinci" kafin ta tashi Abbou yace "dear zauna abinki Nusaibat jeki kai masa..
Miƙewa Nusaibat tayi zcyarta fal farin ciki, kitchen ta shiga ta ɗauki tray ta haɗa masa dukkan abinda ya dace dashi, bayan ta gama ta nufi part ɗinsa,da idanu kawai Jalilerh da Nihila suka bita, Abbou murmushi kawai yyi kafin ya miƙe ya nufi part ɗinsa,yana zaune yana operating system ɗinsa yaji anyi sallama,jin baƙuwar murya yasa ko ɗaguwa baiyi ba,yace "Wasallam" yana faɗin hakan yaja bakinsa yyi shuru,ƙarasa shiga tayi tare tajan table ta ajjiye masa tray ɗin abincin akai,durƙusawa tayi kafin tace "ina yini yaya?" banza yyi mata kamar baiji me tace ba,kanta a ƙasa ta ƙara cewa "yaya" da sauri ya juya ya kalleta kafin cikin ɗaga murya yace "out!!...
6/10/21, 1:10 PM - Buhainat: _Duk yadda kaso kayi rubutu perfect ba tare da wani matsala ba hakan ba faruwa,nayi mamakin yadda na kasa gane kuskuren, sannan nai mmkin yadda marubutan da suke karantawa suma suka kasa ganewa,sai wata daban ta gane, a Nigeria muna da state 36 muna da OYO wacce ta kasance state,sannan muna da IBADAN wacce ta kasance Capital a garin OYO, nace *Muhammad Jalal Kabeer bobo* na neman takarar shugaban ƙasa president kenan,bayan idan president ke nema sai dai nace na Nigeria baki ɗaya😂,a nan kuskuren yake *Muhammad Jalal bobo* ta karar governor yake nema a IBADAN ba president ba,so Please gusy babu baya kuskure aimin afuwa, shi RUBUTU kamar rayuwa ce,kamar yadda babu wanda yasan mene zai faru da mutum gobe ko jibi,haka babu wanda yasan mene zai faru next a cikin littafi abinda muka sani labarin daga farko zuwa ƙarshe an riga da an gama tsara shi,rubutune kawai ya rage✍🏻kuma shima in sha Allah babu tsayawa sai lokacin da Al'ƙalamina yaje ƙarshen labarin_
Uncle ne is not free is 300 0116886423 sulaiman Naima s union bank, evidence of payment 08119226716
_36-37_
Da sauri taja baya sbd tsawar da taji yyi mata, kafin ta kallesa tace "Abbou ne yace na gaisheka fa,me nai maka ne da baka son kulani yaya"ci gaba yyi da latsa system ɗinsa,ganin bashi da niyar kulara yasa taja jikinta zuwa parlour,tana fita ta samu Jalilerh zaune ita kaɗai ta rufe idanunta,zama tayi tace "Jalilerh ke ɗaya ce?" buɗe idanunta tai kafin ta ɗauke kai tace "eh" murmushi tayi tace "kinga na daɗe ko,yaya ya tsaidani wai muyi Shira"kallonta kawai Jalilerh tayi dan a halin bobo yanzu babu abinda bata sani ba tace "yana da kyau ai" Nihila ce ta sakko tana faɗin "har kin fito?,naje ɗaki ɗauko laptop ɗina zan nunawa Jalilerh wani abune"miƙewa tayi tace "Nima zan huce ne,ashe haka bobo yake da kirki yau kam munsha Shira"waro idanu waje Nihila tayi kafin tace "Allah sarki" sallama tayi masu tabar gidan zcyarta cike da takaicin da kuma haushin abinda bobo yyi mata,tana fita ya ajjiye system ɗin tare da miƙewa tsaye ya nufi bedroom kai tsaye bathroom ya shiga ya ƙarasa gaban sink ya wanke hannunsa,yana fitowa ya zauna gaban table ɗin tare da buɗe wermers ɗin,dambun shinkafa ya gani wanda yaji albasa da zugala da gyaɗa,sai tashin ƙamshi yake yaji kifi,yana gama zubawa a plat Jalilerh na turo ƙofar parlour'nsa tana shigowa,zama tayi kusa dashi tare da yin shuru ta sunkuyar da kanta ƙasa,spoon ya ɗauka ya ɗibi dambun tare da kaiwa bakinsa, daɗi da kuma garɗin gyaɗar daya ratsa kunansa yasa yyi saurin lumshe idanunsa,tunda ta shigo bai kalleta ba a hankali yaci gaba tacin dambun har yaci rabi, ɗaya wermer ɗin ya buɗe yaga zallar kayan cikin rago wanda akai farfesun yaji daddawa da kayan ƙamshi, spoon yasa sau uku yaci ya rufe wermer ɗin, miƙewa yyi ya nufi ƙaramin fridge ɗinsa ya ɗauki bottle water mai sanyi ya ɓalle murfinta sai da ya shanye tass sannan ya ajjiye emty bottle ɗin a side ɗin fridge,sai a lokacin idanunsa suka sauka akan ta yanzu tana durƙoshe ta cure waje guda jikinta duk rawa yake gargasar dake jikin ta duk sun mimmike,idanunsa ya ɗauke tare ɗaukan remote ya sauya channel zuwa sunna t.v yaci Sa'a ana karatun Kur'ani,yana kaiwa yaje kujerar da yake ya zauna.
Miƙewa tayi da sauri zata fice daga ɗaki shima da sauri ya miƙe ya nufi inda tayi tako ɗaya yyi zuwa biyu ya zafkota,dukkan ƙarfin ta tasa ta hankaɗesa baya yyi yana mai dafe kujerar dake kusa dashi,hakan ya tabbatar masa ba ƙarfin ta bane, ƙara suwa yayi wajan ta da sauri ya samu harta isa parlour,tsaye yyi sbd kokawar da yaga sunayi ita da Aryan gaba ɗaya ta wajigasa,jingine jikinsa yyi da jikin bangon tare na daɗe hannunsa a ƙirjinsa ya zoba masu idanu.
Mama dake rakuɓe a gefen kujerar jikinta duk rawa yake ta kalli Nihila itama da take a tsorace cikin ƙasa da murya tace "wlh kada ki yadda ta ganki,gaba ɗaya aljanun zasu dawo kanki,Nima ina budurwa haka wata tayimin wannan muguntar,sai gani da yada zani,kee abindai babu kyau,ba kiga yanzu na ɓuya ba"
Kallon Nihila tayi kafin tai magana taji an ƙwala ihu tare da zubewa ƙasa,ihu Mama tayi itama tare faɗin "wa'innahu sulaimanu wa'innahu bisimillahir rahim" shuru itama Nihila tayi tare toshe bakinta hawaye na zuba ta cikin idanunta, Abbou dake tsaye shima ya kalli Jalal yace "Bobo kana ganin abinda take,tana shan wahala fa,kuma Aryan ya kasa da ita" tagumi Mummy tayi abin na mata mmki Ita dai tunda take ba'a taɓa aljanu a gabanta sai yanzu dan duk ta tsorata tausayin Jalilerh ya cika mata zcy, Aryan ne ya kalli Abbou yace.
"Abbou zan iya kula da ita kabar yaya ya huta"kallon sa Mameey tayi tace "rufen baki kalli yadda kake haɗa zufa tun ɗazo sai kokawa kuke kace Zaka iya" Mummy tace "no kibarsa mana,ai kinsan ƙarfin aljanu dana mutum ba ɗaya bane" Shidai Jalal na tsaye yana kallon kowa da ido,ana haka Lamir yyi sallama ya shigo, kallon su yyi tare faɗin "lfyanku kowa?" Abbou ne yace "inafa mutanan ɓoye suka fara damun dear a ƙwana biyun nan" kayan hannunsa ya ajjiye saman sofa kafin ya ƙarasa inda take ƙwance yace "ai ba'a barta haka ba, aƙwai wani malami dana sani sai a kaita can" sai a lokacin Jalal ya ɗaga kai ya kalli Lamir kallonsa yyi shima kafin yace "sannu bobo" jinjina kai kawai yyi kafin yasa hannu ya shafi sumar sajensa a hankali kuma ya fara takawa zuwa inda take ƙwancen yana zuwa yasa duk hannayensa ya ɗauke ta cak,kai tsaye part ɗinsa ya nufa,wani numfashi Aryan ya fesar tare dabin Jalal da kallo shi kaɗai yasan abinda ya keji a ransa,yana zuwa parlour'nsa ya shimfiɗeta a saman duguwar sofa kafin ya zauna gefen ta tare ɗagota zuwa jikinsa.
Tafin hannunsa a saman forehead ɗinta ya fara murzawa tare da ɗan bubbugawa,a hankali kuma yakai bakinsa saitin kunanta ya fara hura mata iska,cikin natsuwa kuma ya fara yi mata karatun yana jin yadda take fizga yaƙi sakinta saima ƙara matseta da yyi a jikinsa, sama da 30minutes yana abu ɗaya amma ko tari taƙiyi balle ya saka ran zatai magana,hannunsa dake saman goshinta ya ƙara murzawa tare da dukan goshinta wata ƴar ƙara sukai kana tayi atishawa,lufff tayi a saman ƙirjinsa tana sauke numfashi, shuru yyi shima yana jin yadda jikinta ya ɗauki zafi,tambayar da yake wa kansa dama tana dasu ne,ko kuma yanzu ta samu,idan yanzu ta samu a ina?wanan shi ne tarin tambayoyin da suke zcyarsa amma babu wanda zai tambaya.
Ajjiyar zcy Aryan ya sauke yace "Abbou tunda kaji nace ina sonta ai aurenta nake da niya,wlh ban taɓa ganin macen da tayimin irinta ba, tun lokacin da yaya yazo da ita na fara sonta, Abbou idan kaƙi bani ita wazan nema ya ban ita,kace naje wajan bobo kana ganin ko kulani bai yi ba bare na saka ran zan samu abinda nake so a wajansa" Abbou ne yace "shikenan kaje ka samu soyyarta tukunna" sai lokacin Mummy tace "kada ka damu son zanwa bobo mgn,nasan bazai ƙi ba" miƙewa yyi tare da yin waje yabar gidan gaba ɗaya.
"Amma ya dace a sama mata magani domin naga da ƙarfi suka kamata" Mameey ta faɗa cikin tausaya wa, Lamir ne ya ƙarasa cin abincin dake bakinsa yace "ahhh to ai nayi mgnar hakan babu wanda ya tanka" Mummy tace "ba haka bane yaya, lokacin hankalinmu ne gaba ɗaya baya jikinmu" da sauri Lamir yyi baya tare faɗin suwaye a bayan sofa kuma?" Kafin ai magana Mama fito tana rarraba idanu, kallonta Mameey tayi tace "Mama mene a jikinki kamar ruwa?" Daga bakin ƙofa akace "mene kowa banda fitsari" Abbou ne yace "gidanku Irfan Mama kake gayawa haka" ita dai Mama babu wanda ta kula tayi part ɗinta ruwan fitsari na bin jikinta,daman Nihila tunda aka ɗauke Jalilerh daka wajan tayi nata part ɗin da gudu.
Da sauri Jalilerh ta ƙwace jikinta daga na Jalal wanda bacci ya fara ɗauke sa, miƙewa shima tare dasa hannu ya kamota ganin kamar bata cikin nutsuwarta cikin wata murya tace "Uncle ka fita dani,banson gidan nan, Uncle zasu kamani ga sunan wlh,wayyo Uncle zasu kasheni"saurin rungome ta yyi a jikinta yana bubbuga bayanta tare shafa sumar kanta,
Ƙanƙamesa tayi tare da ƙara faɗin "Uncle ka gudu dani zasu kamani ina tsoransu Please Uncle" bakinsa ya sanya cikin nata sbd bai ƙaunar jin abinda take faɗa,gaba ɗaya idanunsa ya sauya kala zuwa jaaa,jijiyar kansa ta mimmiƙe,a hankali shima jikinsa ya ɗauki rawa sbd sarawar da kansa yyi masa, ƙara rungome ta yyi sbd jin yadda jikinta ya ɗauki rawa gaba ɗaya,bakinsa ya cire daga nata tare dasa hannunsa ya ɗauke ta cak yyi cikin bedroom da ita,yana zuwa ya ƙwantar da ita,shima ya ƙwanta remote ya ɗauka ya ƙaro gudun a.c,gaba ɗaya a tsorace take hakan yasa ta shige cikin jikinsa tana sauke numfashi, lumshe idanu yyi a dai-dai kunanta yace "sleep, nothing happen am with you, Uncle ɗinki na tare dake" ya faɗa yana bata peak a goshinta,kanta ta ɗura saman ƙirjinsa ta ƙanƙamesa,shima rungome ta yayi babu jimawa bacci yayi gaba dasu a tare.
Washegari tun da safe ya fita sbd a ranar za'a gabatar da zaɓen primary election wato zaɓan cikin gida,wanda yake neman ƴan majalissu su mara masa baya kuma yaji Sa'a a kaso 10 7 zuwa 8 suna bayansa, parking Lamir yyi a compound na gidan yana gama parking ya fito daga cikin motar ya nufi parlour, Mama ya samu sai Jalilerh kallonsu yayi yace "Mama ya naji gidan shuru?" Taɓe baki tayi tace "Salamutu da Jamal sunje kasuwa,Nibala ko niwad ohuuu mata,ta leƙa nan maƙota daga Ni sai wannan mai aljanun" ta faɗa tana nuna masa Jalilerh, murmushi yyi yace "daman nazo ɗauka ta ne zuwa wajan malam"washe baki Mama tayi tace "yawwa irin albarka maza kuje a cire su,nake gaya maka ƙwana nake babu bacci sbd far gaba" ledar hannunsa ya miƙa wa Mama yace "banson mutum gidan susan nine nai mata magani,dan haka kada ki gayawa kowa nazo na tafi da ita,idan zan dawo zan ƙaro maki wani naman" cikin farin ciki Mama ta yagi cinyar kazar takai bakinta tace "jeka abinka daman wake faɗar aikin lada, nina san me zance" murmushi yyi yace "my dear zo muje ita dai Jalilerh kallonsu kawai take dan bata da ikon cewa ba zata bane,kwaɓe fuska tayi tace "Mama ban sanshi ba ai" tsaki Mama taja tace "kamar yadda buba bazai cutar dake ba shima haka,to na taƙaice maki zance ni nayi naƙudarsa na shayar dashi da wannan nonon dake jikina,maza tashi kuje keda za'a taimaka ina ke ina iya yi" jiki na rawa Jalilerh ta miƙe hannunta ya kama yace