Showing 15001 words to 18000 words out of 98315 words
kawai na tattara abinda zan nema a gida nayi tafiya na,
Tace raihana lokacin dana koma gida, har daɗi naji yanda aka nuna man ƙauna,
Hmmm ina yin sati ɗaya na fara ganin canji, wulaƙancin dai iri iri, wallahi wata rana ma idan ina buƙatar abu saidai inyi haƙuri, na gaji, kuma idan na kirashi a waya baya ɗauka, raihana tayi ajiyar zuciya tace gaskiya daɗi ya maki yawa, ina ruwanki da matar da zai auro?"" kima gode ma Allah bai sakeki ba, farida tace yanxun miye abinyi?"""
Raihana tace murje idanuwanki zaki kawai ki koma ɗakin mijinki, tace haba raihana ai babu aji kuma?"" raihana tace aji tun yaushe kika barshi a baya?"" farida tace kuma kinsan Allah har cewa nayi idan na tafi sai yaxo gidanmu yana haɗani da Allah bazan koma ba,
Raihana tace to kuma kin faɗa mashi wannan maganar miye dalilin da yasa kika kirashi?"" tace wallahi rashin tunani ne, tsaki raihana tayi sannan tace to ita safara"un ta san kin dawo gida?""
Farida tace ta sani mana, tunda data zo na faɗa mata halin da nake ciki sai tace zata haɗani da wani babban alhaji dama ai ba"a zama haka dole sai an ɗan nemi maza dan sune marufar asiri, wai har dubu ɗari zai bani, nace mata toni mijina na sunna ma na hanashi haƙƙinshi sai wani ƙaton banza, dariya tayi sannan tace man ai dama ɗan banzan wayanmu yake hanamu mu more rayuwarmu,
Bayan wani lokaci kuma na kirata nace mata nifa har yanxun mai gida baizo biko ba, tace man wai in shirya ta rakani wurin wani malami , haka na shirya mukaje wallahi raihana na kashe kuɗaɗe da yawa yace man zai kirani, bai kirani ba, saini na gaji na kirashi amma bai ɗauka ba ,
Raihana tace kinji wata matsalar kuma?"" nidai shawarar da zan baki kawai ki koma, idan ma yaxo ya taddaki a gidan kice mashi kawai kin dawo, farida tace gaskiya babu aji,
Raihana tace ai dama abinda yake ƙwararmu kenan matan malam bahaushe, wai ke girman kai kike ji, amma kinje kin kare kuɗinki wajen malamai amma basui maki komai ba,
Farida tayi shiru, raihana tace kixo gobe ni zan raka tunda har kikaga bai sakeki ba yana sanki, sannan kuma abinda yasa baizo biko ba, kila yana ganin kamar zaki mashi wulaƙanci tunda a haka kuka rabu,
Amma idan muka je Office ɗin nasu gobe idan Allah ya kaimu, abinda zakice mashi ,muna zuwa kawai kice ya baki makullin gida, kila zaice mi zakiyi?"" idan ya tambaya kice akwai wasu kayanki da zaki ɗauka ne, daga nan sai mu saurara muji abinda zaice, idan ya bada makullin sai muje gidan daga nan sai mu samu mafita,
Farida tace to Allah ya kaimu, raihana tace ai dole idan kina san zaman lafiya dole ki aje girman kai, idan ba haka ba, zakisha baƙar wahala, ni miye yaja man?"" gani nan ina zaune na rasa mai sona, ameenu kuma yana can ya samu tafi da gidanka, baki ga yanda akace take kula dashi ba, ina nan ina haukan banza, ni yanxun ma banda ubanda yake so na,
Wata rana ma hodar shafawa wahala take man, saboda haka ina baki haƙuri kawai kiyi haƙuri kixo ki koma ɗakinki tunda baizo ba bai aiko wani ba, duk maganar malamai ki barta duk ɓace hanya ce,
Farida tace babu damuwa Allah ya kaimu lafiya, haka sukai ɗan fira daga baya kuma farida ta ce zata tafi sai Allah ya kaimu raihana tayi mata rakiya sannan ta dawo gida,
***
Da daddare gwaggo tace ma raihana tazo takai ma ladi kuɗin adashen ta, raihana ta karɓa ta tafi,
Lokacin da ta isa gidan ta tadda ɗiyar ladi wanda take auren ameenu tsohon mijinta, bayan sun gaisa da ladi ta bata kuɗin, ita kuma ɗiyar ladin lokacin ta fito, ta ɗauki ɗanta ta fita saboda Ameenu yazo ɗaukarta,
Ita kuma lokacin raihana ta miƙe, tayi ma ladi saida safe, tana fitowa waje taga ameenu yana cikin motar zaune, ta matsa kusa dashi tace ranka ya daɗe ana ganin ka?""" kallon sama da ƙasa yayi mata, sannan ya kalli inda matarshi take, ita kuma taɓe baki tayi sannann tace malama ya akayi ne?"" abun yayi ma raihana ciwo saboda haka bata sake magana ba taja saɓa tabar wurin,
Tana tafiya sukazo suka wuce ta fuuuuuiiiii a mota, raihana ta matsa da sauri saboda ji tayi kamar aminu zai bigeta, lokacin da suka wuce raihana tace ikon Allah ashe aminu ba sona yake ba?"" har in ganshi in zuwabar da ajina inyi mashi magana amma ya basar dani,
Uhum Allah ka zaɓa mana alkairi haka kawai raihana ta faɗa a bayyane,
Lokacin da raihana ta iso gida, ta tadda an dawo da baba babu lafiya, duk su umma suna kusa dashi suna mashi sannu, itama raihana wurin taje tana mashi sannu,
Gwaggo tace raihana anshi maza kije ki sawo mashi maganin ciwon kai da masassara, tace to, gwaggo tace kada ki daɗe, raihana tace to, haka ta tafi taje ta siyo maganin ta dawo, baba yasha ya kwanta bacci,
****
Da safe baba yaji jiki da sauƙi abinka da ciwon talaka yace bara ya lallaɓa yaje kasuwa, haka ya lallaɓa ya tafi...............,,,,
Da rana misalin 1:34pm farida taxo, raihana itama taci shirin ta , tayi kyau sosai, saboda haka suna shirin tafiya *Office* ɗin mijin farida, niko nace lallai *zawarci* yayi zawarci tunda har mata zasu biko!!!
*A* madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ni ```meelat``` nake cewa ku kasance tare dani,
📚✍🏻
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 1⃣7⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELART* 🌹
*T*are suka fito daga ɗaki farida da raihana Umma tana zaune a tsakar gida, raihana tace Umma sai mun dawo, umma tace to Allah yasa ku dawo lafiya ita dai umma bata san inda zasuje ba
Amma raihana tace mata ganin marar lafiya zasuje,
Suna fita daga gida suna tafiya kafin su isa wurin titi su samu abun hawa, duk inda suka wuce sai an nuna raihana , ga *zawara* uwar san banza ke wuta ƙaninki ɓarawo, dan a unguwar cewa suke ita a dole mai kuɗi take so bata aure sai mai kuɗi,,,,,
Ita kuma raihana kwata kwata ba haka bane a wurin ta, amma mutane sai fassarata suke, wai ita ba kowan kowa ba galadiman kashi, ita ɗiyar talakawa amma baki aure sai gidan masu kuɗi,
Lokacin da suka isa bakin hanya sun ɗan dade sannan suka samu mai napep farida ta kwatanta inda za"a kaisu, saboda haka suka hau sai office in mai gida,
Lokacin da suka isa wurin aikinsu tun a bakin get in shiga, ƙawayen mijin farida aka fara ah ah ah, madam yau da kanki?"" farida saidai tayi murmushi, kafin su isa cikin office in mijinta har an mashi waya cewa ga madam nan zuwa,
Allah sarki sha"anin miji da mata sai Allah, lokacin da suka shiga cikin office in cikin mutumci ya karɓe su, sannan ya basu wurin zama, bayan sun zauna raihana ta gaishe shi ya amsa cikin mutumci, ita kuma farida sai wani basarwa take,
Shine yace madam barka da rana, ko inda yake bata kalla ba, murmushi yayi lokacin daya miƙe, ya nufi wurin da frig yake, ruwa da lemo ya ɗauko ya ajiye a gabansu,
Sai kallon farida yake, bayan ya zauna raihana tace ranka ya daɗe key muka zo a bamu aro don Alƙah zamu ɗan ɗauki wasu kaya a gidanka,
Murshi yayi sannan yace wane irin kaya zaku ɗauka?"" farida tace nawa, kallonta yayi sannan yace da kanki?"" farida tace Eh, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace to ki bari idan na tashi office sai muje tare mana, farida tace a,a, ka bani idan mun gama zan dawo maka dashi,
Raihana tace Eh ka bamu dan sauri muke akwai inda zamuje kuma abinda zamuyi amfani dashi yana gidan naka, yace to, gashi, raihana tace ma farida karɓo mu tafi, ita kuma tace kedai ki ƙarɓo,
Dariya yayi sannan ya miƙe tsaye ya nufo inda suke zaune, miƙa ma farida makullin yayi, yace karɓi, ta miƙa hannunta da niyyar amsa, ya haɗa da makullin da hannunshi da nata ya rige, raihana tana ganin haka ta miƙe ta fita daga office ɗin,
Tana fita inda ta tashi a wurin ya zauna, ya jawota jikinshi, yace bakijin magana, wato yaji ko?""" farida tayi shiru, yaci gaba da cewa wato dan ranshin ta ido harda wani zuwa karɓar makulli zaki je ɗaukar kaya ko?""
Nan ma shiru tayi, yace hmmm yau kwananki nawa baki nan?""" nan ma batai magana ba, yace kin tafi ke zafi kishi kin bar mana gida duk yayi datti, kin barni yunwa ta kamani bana iya cin abinci bana iya shara sannan kumanidan dare yayi bana iya bacci, ya ƙarasa maganar cikin sigar shagwaɓa tare da jan hankali,
Kallon farida yayi sosai yaga duk ta rame tayi baƙiƙƙirin duk dai ta koma wata iri, sai yaji tausayinta, yace kinsan wani abu?"" kanta ta girgiza alamar a,a, yace zan baki makullin gida a bisa sharɗi guda biyu!!!""" kin yadda?"" ɗaga kanta tayi alamar Eh,
Yace yawwa na farko zaki gyara gidan kuma kiyi man girki, sharaɗi na biyu kuma zan faɗa maki shi ina nan zuwa bayanki bada daɗewa ba, sannan ya saki hannun ta, ta miƙe jiki a sanyaye babu kunya simi simi ta fice daga office ɗin,
Tana fita yayi dariya, yace "yar rainin hankali, kafin kibar gidan zan rutsa ki, yau jikinki saiya baki labari,
Lokacin data fito ta samu raihana, harta tseda masu napep, saboda haka suka shiga suka tafi sai gidan farida.....................,
Bayan sunje gidan, a farlo suka zauna, farida ta sauke ajiyar zuciya, hawaye suka biyo mata fuska tace haƙika na gode ma Allah da kika bani shawara kinsan Allah babu gidan ubanda zan tafi ina nan gidan idan ya dawo yace ban tafi ba?""" zance mashi ai nayi aiki na gaji anan zan kwana da safe na wuce,
Raihana tace ai mu mata wani lokaci muna da matsala, lokacin da muke da ƙima da daraja a idon namiji sai muyi ta iskanci muna wulaƙanci shi kuma namiji duk lokacin da kike wulaƙanta shi kike mashi rashin mutumci kullum sanki raguwa yake a ranshi,
Ke kuma harda wani horashi da hana shi haƙƙin sa, wannan duk haukace kikayi, yanxun da ɗan wulaƙancine wallahi dasai ya ƙare mana rashin mutumci a office ɗinshi, tashi farida tayi ta shiga ɗakin ta, tana ta leƙe leƙe a gidan kamar wata baƙuwa, tace Allah sarki wallahi raihana wani lokaci ko ruwan da zanyi wanka sai mama tace wai naci ka ɓata ruwa, kuma anan gidan ya saba man da shan ruwa faro, kai wallahi naci ubana a gida,
Raihana tayi dariya sannan tace ai yanxun saiki rufa ma kanki asiri, farida tace ina ai yanxun na tuba, suna cikin maganar wayar farida ta fara ringing, tana dubawa tace ke mamana ce take kirana, raihana tace ɗauki kiji abinda zata ce!!!!
Sallama tayi bayan ta ɗaga wayar, mama tace ina kika shige ne?""" kashe wayar tayi, sannan ta faɗa ma raihana, dariya raihana tayi sannan tace kawai kice mata kin dawo ɗakin mijinki, a daidai lokacin da wayar mama ta sake shigowa, farida ta ɗauka, mama tace dan ubaki bakiji ina magana ne?""" shine kika kashe man waya?""" nace kina gidan uwar wa?""" farida tace ina gidana""""" mama tace gidanki ubanwa?"" farida tace na dawo ɗakin mijina,
Mama tayi salatai sannan tace dan ubanki baki bari sai yaxo biko?""" farida tace ai na jira har yanxun baizo ba, mama tace dan ubanki maza maza ki dawo gida shegiya kafin yaxo ya taddaki ya rainaki, farida tace tou , kawai ta kashe wayarta,
Tana kashe wayar tace ma raihana kinji wai inyi maza maza in dawo gida, raihana tace to yanxun komawa zaki?"" farida tace keda Allah rabu da ita, dariya raihana tayi, a daisai lokacin da sukaji ƙarar buɗe get, wato dai mai gida ya dawo,
Raihana tace tashi muyi kamar muna haɗa kaya, farida tace to, da sauri suka tashi suka nufi bedroom, suna shiga suka fara sauko kaya, shi kuma lokacin ya shigo cikin bedroom ɗin ,
Sallama yayi ya shiga ciki, raihana tayi mashi sannu da zuwa, tace ranka ya daɗe har ka dawo bamu tafi ba""" a gidan ƙin buɗewa yayi, daƙel muka samu ya buɗe, dariya yayi sannan yace ai babu damuwa, ita kuma farida tace saka man wannan kayan a cikin can, yace ina zakije kuma da kaya?""
Farida tace bikin ƙawarmu muke shine nazo ɗaukar kaya, murmushi yayi sannan yace da izinin wa zaki fita?"" dan shima tafiyar farida gaskiya ya jigata kawai haƙuri yake amma kullum dare cikin taƙura yake kwana,
Farida tace ban gane da izinin wa zan fita ba?"" yace Ey inda raihana take tsaye ya kalla yace hajiya muje in sauke ki a gida, raihana tace to ita kuna ƙawar tawa fa?"" yace ta dawo gida,
Farida tace wane na dawo gida?"" so kake ace banda kunya na dawo ɗakin mijina babu ɗan rakiya?"" yace ai dan baki da kunyar kika dawo kuma abinda kika zo amsa zan baki, da sauri raihana ta fita daga ɗakin, ita kuma farida irin kamar bata san zaman nan ta fara cewa bani hanya,
Yace babu fa inda zakije, cikin shagwaɓa ta faɗa kan gado yanda tayi abunne yasa yaji wani iri, shima wurin gadon yaxo yace yarinya yanda kika haye wannan gadon nima in rama mashi bara dai inyi ma raihanar rakiya in dawo , mu fara sabon lissafi daga inda aka tsaya,
Lokacin daya fito ita raihana tuni ta ɓace, danma kada inyi ƙarya da nace yanxun takai gida............,,,
Dawowa yayi yace farida ƙawarki fa tayi tafiyarta Allah dai yasa ba fushi tayi ba?"" dariya tayi tace barta zanje gobe, yace ke babu fa inda zaki ƙara fita na faɗa maki,
A daidai lokacin daya zauna kusa da ita, daga nan karatun nasi ya fara nisa, nidai babu ruwana bara inbi raihana baiwar Allah,............,
Raihana lokacin da taji mijin farida ya fara naganganu tayi dariya, tana fitowa, tace a ranta wannan bari in basu wuri, fita tayi ta samu abin hawa tayo gidansu,
Cikin farin ciki ta dawo gida, Umma tace mata ina kikaje kika daɗe haka?"" tace Umma gamu dai, tana faɗin haka ta shige cikin ɗaki,
Tana shiga ɗaki kayanta ta cire ta saka wanda take zama dasu a gida, kwanciya tayi tana tunanin farida tace shi mijin naki ma mai sauƙin kaine, ita fa dama so ɗaya take zuwa a rayuwa ya kamata mu riƙa haƙuri , dan wallahi idan har mace ta fita a ran namiji ta gama tasiri a rayuwarshi, gyara kwanciyarta tayi ita kuma tana addu"ar Allah ya zaɓa mata miji na gari,............,
***
Jikin baba yayi tsanani sosai dan yanxun ma baya gane wanda yake kanshi ciwo sosai, saboda haka duk "ya"yanshi sunxo maza da mata duka "ya"yan gwaggo sun haɗu,
Lokacin da suka zo suka ɗauki baba suka kaishi asibiti, ciwo baya buƙatar komai sai kuɗi, dan haka sunyi tsaye gam suna nemar wa baba lafiya,
Tom satin baba biyu a asibiti yace ga garinku nan,
Kai bazan iya tsayawa faɗa maku irin halin dasu raihana suka shiga ba, ita dai mutuwa kowa yasan tana da ciwo, amma haƙuri ake Allah ya bamu kyakkyawan karshe ubangiji kuma yasa mu cika da imani idan ajalinmu yaxo...........ameen,
Bayan rasuwar baba da wata ukku, "ya"yan gwaggo suka fara maganar rabon gado, baba baya da komai sai wannan gida dasu raihana suke ciki, saboda haka kuma sunce gidan nan bazasu raba shi ba, amma zasu sa ayi ma gidan kuɗi sai su fitar da umma,
Umma tace ita dai ko ɗaki ɗaya ne a bata , yayan su raihana shine babban ɗan gwaggo yace wannan gida babu abinda za"a bata a ciki saboda ɗiyarta ɗaya, sa"a ma taci za"a bata kuɗi,
Umma da raihana sunaji suna gani duka abinda aka basu dubu ishirin , kuma ranar da aka basu kufin ranar gwaggo tace su tashi su bar mata gida,
Allah sarki haka raihana sunaji suna gani suka tattara yanasu yanasu suka bar gidan.....................,,,,,,,
Cikin unguwa suka samu wani gidan haya wanda ɗakuna ne sunkai 20 a gidan nan suka kama haya, ɗaki ɗaya kuma a gidan kewaye biyu ne,
Ranar dai raihana tayi kuka kamar ranta zai fita, ga kukan maraici da wulaƙanci da aka masu ga kuma kukan *zawarci* toi wannan zama nasu ya zai kaya ne?"""
Ku kasance tare dani , a madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻 ni *meelat* nake maku fatan alkairi,
💋
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
*Page* 1⃣8⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
****
*T*o a gidan dasu raihana suka kama haya, kowa dai yasan yadda rayuwar gidan haya take bare kuma ance ɗakuna ne sunfi 20, kuma toilet guda biyu ne, ga matan aure ga mazan aure ga yara ga tsofaffi ga kuma zawarawa ga "yan mata,
****
*T*unda safe gidan ya yamutse ba babba ba yaro layine kowa ya jera bakin toilet masu san wanka su tafi kasuwa sunayi masu san fitsari ko bayan gida duk dai gasu nan sun haɗu, raihana kashine ya dameta amma hankalinta ya tashi dan ta hango kawai saura kusan mutum 11 a gabanta,
Kuma abun nasu da gayya sukeyi dan idan kana jin haushin wanda yake binka layi idan ka shiga baka fitowa da wuri,
Wani matashi ne wanda yayi auren farko bada daɗewa ba, bayan wata mata ta fito daga toilet, ya ɗauki bokitin ruwanshi ya shiga, da alama wanka zaiyi saida ya daɗe sosai bayan ya gama wanka ya samu wurinshi yayi zauniyarshi,
Su raihana suna nan tsaye suna bin layi saiga "yar matarshi da bokitin ruwa tazo ta karkatasu ta shige, mutane marasa haƙuri suka fara magana, wannan ai zalinci ne ɗaukar alhakine in banda iskanci sai ka gama abinda kake ita bata bin layi saidai kawai taxo ta shiga wanka?""" a daidai lokacin da mijin ya fito daga toilet in yace, ai layi nabi?"" saboda haka du wanda ya isa ya leƙa mashi mata tana wanka,
Wani yace kaidai ɗan iskane wallahi , kai danma bakajin kunya kana wanka har waccan yarinyar taxo ta ganka bakajin kunya?"" dariya yayi sannan yace gani kuma har nawa?"" taga wanda yafi wanda ta gani yanxun, da gani dai ɗan duniya ne saboda haka ya shiga rattafo magana marar amfani,
Raihana dai dukar da kanta tayi ƙasa , haka yaci gaba da batsarshi, a ran raihana kuwa cewa tayi tou pha dama shi gidan haya yake?""" Allah ka rufa mana asiri da haya, ina ma amfani?""