Showing 27001 words to 30000 words out of 98315 words

Chapter 10 - ZAWARCI

06 Oct 2024

8018

dan ta taɓa auren ne ko tana buƙatar namiji a kusa da ita,

Ita kuma a ɓangaren raihana tana so tayi aurene saboda ta rasa mataɓa, dan ita babu wani abu daya taɓa shiga tsakaninta da wani namiji, dan ko aminu daya aureta duk zan da sukai saidai ya ɗanyi wasanni da ita,

Umma ta kalli raihana sannan tace to tunda kina ganin haka ne mafita kiyi ma yusufan magana kiji, tayi ma raihana hakane dan kada taje ta saka rayuwata a wani halin ,,,,

Raihana ta kalli umma tace umma kinyi kalaci ne?"" umma tace ni ɗan kuɗaɗen nawa ma an sace, raihana tace subahanallah""" garin ya?"" umma tace nima wallahi ban sani ba , raihana tace to mi kikaci yanxun?"" umma tace ba komai, raihana tabi mahaifiyarya da kallo cikin tausayi

Umma tace ke ban maki albishir ba, raihana tace nami?"" umma tace na samu aiki wani gida, gaban raihana ya faɗi, tace haba umma, sai ki tafi kina aiki aje ayi ta ɓata maki rai?"" ni wallahi bansan aikin gidajen nan, tace ke wannan basu da wulaƙanci wallahi mutanen kirki ne, raihana tace to Allah ya tsare ,

Umma tace ameen sannan tace to ya kuka ƙare da gwaggon?"" raihana ta ɓoye ma umma dan kada ranta ya ɓaci, tace gwaggo tace wai hadake mu dawo gidanta, dan tasan umma baza ta koma ba, raihana taci gaba da cewa nace mata ah ah, nidai kaɗai zan zauna ke kince baza kixo ba, umma tace kwarai kuwa ko babu sauran gidan zama a duniya,

Dariya raihana tayi sanann tace umma bani kayana kinji inje inyi wanka gidan farida zanje, umma tace wane iri zan ɗauko maki, raihana tace masu kyau zaki bani kala biyar dan saina kwana biyu ban sake dawowa ba, umma tace to,

tashi tayi taje ta ɗauko mata kayanta sannan ta kawo mata, raihana tayi mata bankwana sannan ta tafi,

raihana tafiya take a galabaice yunwa ta isheta har bata ganin gabanta saboda azabar yunwa, daƙel ta iso gidan gwaggo lokacin data iso ta samu gwaggo ta fito zata fita, gwaggo tace har kin dawo ne?"" raihana tace Eh gwaggo tace to ga mabuɗin gidan raihana tace a,a barshi kije ki dawo, gwaggo tace saboda mi?"" raihana tace ai nima gaba zanyi, gwaggo tace to sai kin dawo, raihana ta miƙe da "yan kayanta tayi gaba,


a ranta take magana tace yanxun in anshi makullin gidan nan gwaggo tana iya cewa na sace mata wani abu, a fili tayi magana tace tunda ina san zama zan kiyaye abincinko da makullin gidanki dan in zauna lafiya,


Tafiya take har ta iso wurin wata majalissa suka fara kaɗa mata taken nata, *zawara uwar san banza ke wuta ƙaninki ɓarawo* haka sukai ta faɗi har ta wuce wurin ta isa bakin titi, napep ta tsayar ta faɗa mata inda zata kaita, sukai ciniki sannan ta shiga sai gidan farida,

suna zuwa tace mashi ya jirata ta karɓo mashi kuɗin shi, tana zuwa tayi ta nooking shiru, haka taci gaba da bugawa, wata maƙotarsu ce ta leƙo, suka gaisa tace mata don farida fa?"" tace ai farida sun daɗe basa nan!""" raihana tace ina suka je ne?"" tace sun tafi umara , kuma dama kamar tasan zakizo tace ga saƙo a baki,


shigo , raihana tace to, ciki suka shiga, a farlo ta zauna tana jiran fitowarta, ta ɗan daɗe sannan ta fito, da wata ƙatuwar leda ta ajiye a gaban raihana tace ki duba komai yana ciki, tace taxo gidanku baku nan , gidan a kulle,

Godiya raihana tayi sannan ta miƙe tayo wurin mai napep, ta shiga tace suje, suka dawo, a ƙofar shagon shamsu ya ajiyeta, kayan sawarta data ɗauko daga gidansu umma taba shamsu tace don matsayin manzan Allah S. A. W ka riƙesu ka bani ɗari biyar, dariya shamsu yayi sannan yace kai gaskiya kinajin garin nan, raihana tace kaidai ka sani, karɓar kayan yayi sannan ya bata kuɗin mai napep taje ta bawa ɗaru ukku sannan ta ɗauko ledar da farida ta bada a bata, sannan ta nufi gidan da ake siyar da abinci tana zuwa tasa aka zuba mata na ɗari da hamsin dukanshi ta shafe shi kafff sannan ta anshi amsin ɗin ta fito daga gidan , tana tafiya taga wani yaro yana tallar ruwa ta siya tayo ƙofar gidan gwaggo ta zauna,,,,

tana zama ta duƙar da kanta ƙasa taci gaba da kuka........................
💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦
💦💦💦

*Page* 2⃣4⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

****

*Gaisuwa ta musamman a gareki Hafsat Isa Mamman Katsina, ina maki fatan alkairi, alkairin Allah ya taddaki har binnin katsinar dikko ɗakin ƙara*

*Allah sarki ƙawata Asmeenat Xeeyan ina maraicinkin sosai Allah ya dawo man dake lafiya kema alkairi ya iskoki har sakoton shehu*

*Wannan shafin naku ne ameenci fans Allah ya ƙara mana kaunar juna, muna tare*

******

*K*anta yana ƙasa sai kuka take tare da addu"a Allah ya kawo mata ɗaukin wannan rayuwa da take ciki,

Raihana ta ɗago kanta sannan ta goge hawayen idonta, ledar gaban ta data zo da ita daga maƙotan farida data bada a ajiye mata ta jawo, buɗewa tayi ta fara dubawa, turamen atamfa ne kala ukku da gyale sai mabar riga da hijabi biyu, sai talami kala ɗaya, da kwalin waya ƙirar L9plus , ajiyar zuciya tayi sannan tace Allah sarki idan mutum yana sanka yana kaunar ka, Allah ya ƙara maki kisanci da mijinki ya baki haƙurin zama dashi kiyi haƙuri kiyi zaman ki farida zawarci babu daɗi kixo kiyi ta raɓr raɓe,

ƙarshe ma abinda zakaci yaxo yayi maka tsaye, sannan baka da mutumci da kima a idon kowa, haka tayi ta magana sai kace tana ganin farida,

Atamfofin ta fiddo ta fara dubawa ɗaya bayan ɗaya tana dorawa saman cinyarta, saida ta gama fitowa da kayan duka sannan daga ƙasa taga takarda , da sauri ta jawota, ta buɗe, kuɗi ne ciki 5k, a jikin takardar kuma anyi rubutu kamar haka,


```Assalam ƙawata da farko dai ina godiya sosai dan banma san da bakin da zan gode maki ba, naxo gdanku a rufe , naxo maki bankwana ne, munyi tafiya saudiyya, wannan saƙon kuma mai gda yace a baki, kuma shima yana godiya sosai, insha Allah zan maki addu"a sosai kema Allah ya baki miji na gari, daga mai ƙaunar aminiyarki farida ahmad```

Hawaye ya gangaro daga idon raihana tace Allah sarki rayuwa, wallahi naji maki daɗi Allah ya ƙara ma duk macen duniya haƙuri da juriya a gidan mijinta, dan idan kayi haƙuri a gidan aurenka shidai aure ibada ne, idan kuma mutum ya zalinci wani Allah dai shine mai sakayya,

Goge hawayenta tayi sannan ta maida kayan a leda tace bara inje inkai ma umma baiwar Allah kila ma har yanxun bata ci komai ba,

Bayan ta gama maidai kayan kaff ta ɗauki ledar ta nufi shagon shamsu ta bashi kuɗinshi data ranta, ta amso kayanta , bakin titi ta nufa dan hawan abin hawa wai tunda ta samu kuɗi bara ta more su tunda idan suka tafi tana shan wahala kafin ta samu,

Abin hawa ta hau tayi ma gidansu ummarta tsinke, lokacin data isa ta samu umma ita kuma tana fitowa daga cikin gida a ƙofar gida suka haɗu,

Umma tace lafiya kika dawo?"" dariya raihana tayi sannan tace lafiya fess umma, kusa da ita umma ta matsa, wuri raihana ta samu ta zauna itama umma zaman tayi, kallon raihana tayi sannan tace gwaggon ƙoroki tayi ne?""

raihana tace a,aa abun arxiki na samu, tana magana tana fiddo kayan tana miƙa ma umma, umma sai yashe baki take tana cewa waye kuma ya baki?"" jikin raihana yana ƙarma ta fiddo wayar ta miƙa mata , tace umma kalli harda waya, umma tace ni sai nuna man kaya kike faɗa man wanda ya baki, dariya raihana tayi sannan tace kamar lefe ko umma?"" dariya umma tayi sannan tace gaskiya ke yanxun yanda kike zawarcin nan kika samu kamar wannan ai kinyi goshi, dariya sukai gaba ɗayansu sannan raihana tace wallahi farida ta bani,

umma tace farida taki?"" raihana tace farida tawa kau, kinga kuɗi nan, saboda haka muje mu kama haya umma kema kibar wannan gidan don Allah, hannu umma ta miƙa ta karɓi kuɗin sannan tace itama tana da 1k saboda haka akwai wani gda nan kusa da gidan gwaggo sai muje mu kama ko?"" raihana tace wannan gaskiya ne,

haka dai sukayi ta firarsu cikin tausayi da kuma hali na damuwa, bayan wani lokaci raihana tayi ma umma sai anjima, umma tace zata shigo idan Allah ya kaimu zata shigo dan suje su biya kuɗin hayar, raihana tace to sukai ban kwana umma ta shige gida raihana ta nufo gdan gwaggo,

a ƙofar gida raihana tayi zaune har yanxun gwaggo bata dawo ba, tana nan zamanta tana jiran zuwanta, tun daga nesa ta hango zulaiha ta tun karo wurinta sai yage baki take kamar ƙefen sakara, tana tafiya kamar ana ingixo ta,

da ɗan gudu ta iso tana zuwa takai ma raihana duka , tace banza albishirin ki?"" kallonta raihana tayi sannan tace miye, zulaiha tace naje gidansu umma tace man yanxun nan kika taho, kinsan abinda ya faru?"" raihana tace ah ah sai kin faɗa,

Zulaiha tace an saki kishiyata, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un raihana tayi tare da zaro idanuwa cikin tashin hankali taci gaba da salati, tana cewa kam amma na tausaya mata wallahi,

zulaiha tace ke bar "yar iska, raihana tace haba kiji tsoron Allah kinyi *zawarcin* nan kinji yanda yake kinsan wahalar da take cikin shi da yamutsi sai kiyi murna dan an saki wata?""

Zulaiha tace wallahi nayi, raihana tace duk miye yayi zafi haka?"" zama tayi kusa da raihana sannan ta fara cewa,

ke tunda kika bani shawarar in mayar mashi da yaran shi na maida su, tace ita Allah ya kasheta bata zama da su, yace tayi haƙuri tace wallahi bata zama da wa"an nan tsinanin "ya"ya dan ita ba ɓautarsu taxo ba, idan ya zama dole sai sun zauna saidai ya dawo da uwarsu,

yace mata shi bazai maidoni ba, tace to wallahi bata zama dasu , saidai ta tafi gidan ubanta itama, haka dai sukayi ta tashin hankali idan ta dafa abinci bata basu da sunyi abu sai zagi sai duka, idan yace mata yaro saida lallashi sai tace ba yara bane iskanci ne sunsan abinda suke,

wannan saɓanin ne dai yasa har aka rabu, raihana ta sake salati tace lallai amma tayi hauka , matsalarmu mu mata wani lokaci bamu da lissafi, in banda hauka ka nuna ma namiji baka san yaranshi?""

kama so su wace Allah cika?""" kuma idan ta girka abinci ta basu ina zata ragu?"" ai duk macen da bata san yaranka kaine bata kauna, yanxun kinga ita wanna haukan yaja mata sanadin mutuwar aure?""

keda kika raɓa kici arxiki?"" kuma da nata ne yaran idan taso tazo dasu *agolanci* idan yace baya rigewa sai kiga kuma ta nuna damuwa, don Allah mata mu riƙa haƙuri da "ya"yan miji duk abinda zakai kayi tsakaninka da Allah komai kayi Allah yana kallonka baka da tabbas kai zaka rayu da naka idannka ci zalin na wani, idan babu rabuwa akwai mutuwa , duk abinda kayi a rubuce yake baya canjawa dole wani abun sai mu riƙa danne zuciyarmu dan sama ma kanmu salama, Allah yasa mu dace ameen,

raihana ta kalli zulaiha da take ta faman rawa, girgiza kanta tayi sanann tace ai dama haka duniya take sai wani ya rasa wani yake samu, amma ita dai wannan rashin haƙuri yaja mata,

zulaiha tace ke banza ranar juma"a za"a ɗaura mana aure ,idan na shirya sai in tare haka yace, raihana ta kalleta tace in baki shawara?"" zulaiha tace bani aike baki bada shawarar banza, murmushi raihana tayi sannan tace kada ki yanda sai wani lokack ki tare ana ɗaura aure a ranar ki rufa ma kanki asiri kiyi gidan mijin ki,

sannan kin ɗanɗana kinji abinda yake cikin *zawarci* yanzun saidai kiyi ma wasu nasiha, idan kin koma kuma kici gaba da haukan da kikai a baya, zulaiha dariya tayi sannan tace haba ai ɗan ba ƙari godiya da kwanan garke, idan na koma kinsan abinda zanci da safe?"" raihana tace a,aa zulaiha tace wallahi shayi zansha da wainar kwai, wata irin munafikar dariya raihana tayi sannan tace shegiya shi kike yunwa ne?"" zulaiha ta ɗaure fuska tace kema matsalarki iskanci wallahi raihana tace Allah ya baki haƙuri,

zulaiha taci gaba da cewa wallahi rabon da insha shayi kinsan Allah ba wasa ba har mantuwa ta manta, kai ai idan naje akwai abubuwan da zanma yaushe rabo, tsaki tayi sannan taci gaba da cewa bira"uba babu a gida babu a maƙota,

Gaskiya raihana *zawarci* baiyi ba, kema Allah ya baki naki kije kindan raɓa, murmushi raihana tayi cikin sigar tausayi sannan tace aini kila ma ban sake aure, zulaiha tace saboda mi?"" raihana tace to ai har yanxun ma na rasa wanda zaice yana so na, bare azo maganar aure , ni wallahi gani nake kamar hada alhakin Aminu, na samu yana kauna na, da nayi haƙuri nayi zamana duk da abun baikai haka ba,

zulaiha tace ba komai Allah yana tare da mai haƙuri duk abinda yayi tsanani sauƙi yana nan tafe, kiyi haƙuri wata rana sai labari,

raihana tace Allah ya nuna man ranar nan in ganni a gidan mijina ɗakina ni ɗaya inci abinda nake so inyi wanka da sabulu, danni tuni na koma wanka da omo dan yafi auki idan na siyo na 20 sai yayi man sati ina ɗan lallaɓawa, mai ma man gyaɗa nake amfani dashi idan na siyi na 100 yaman wata ukku,

zulaiha tace Allah dai yasa mu dace, idan kana zaman tun kana burge iyayenka har ka fita a ransu, miƙewa tayi tace bari in tafi dare ya gabato don Allah ki shigo gobe sai muga abinda ya kamata muyi, dan yau idan yaxo zan faɗa mashi ranar da aka ɗaura aure a ranar zan tare, raihana tace haka yayi , tare suka miƙe da raihana da zulaiha , zulaiha ta dafa kafaɗar raihana tace kinsan fa yaga canji dan yanxun idan yaman abu godiya nake sosai kamar wata "yar maula, kinsan namiji yana san yayi maki abu kina godewa tare da mashi addu"ar Allah ya ƙaro mashi buɗi daɗi suke ji har a ransu wallahi, raihana tace to ai duk abinda kasan zai fishshe ka sai kayi dan zaman lafiya, haka suka ci gaba da "yar tafiya saida tayi mata rakiya sosai sannan ta dawo ta zauna ƙofar gida tana jiran dawowar gwaggo,

ta ɗaɗe sosai dan har an gama sallar magrib sannan ga gwaggo ta ɓullo, raihana tayi mata sannu da zuwa sannan gwaggo ta amsa, makullin ta bata tace ta buɗe masu ƙofa yau akwai labari, raihana tace labarin mi?"" gwaggo tace kedai buɗe gida mu shiga kiji ikon Allah, raihana tace to, da sauri tayi ta buɗe gida suka shiga,

suna shiga rainaha tayi alwallah dan gabatar da sallah magrib , bayan ta gama sallah gwaggo tace , ashe ɗiyar ladi sata take ma mijinta?"" idanjwa raihana ta zaro tace wace ladin kuma?"" gwaggo tace wace kika sani?"" raihana tace ai ladi da yawa, gwaggo tace ladi aminiyata, tana nan gida mijin ya maidota, amma auren bai mutu,

tsaki raihana tayi sannan tace su suka sani, in banda hauka da taɓewa mi yakaika yima miji sata?"" ai yima namiji sata ba ƙaramar lalacewa yake sa mace tayi ba, kuma ko ba komai idan ka fita da tambarin sata wane namiji zai aure ka?"" tsaki tayi sannan tace Allah dai ya rufa asiri, gwaggo tace ameen,

miƙewa raihana tayi taje ta sako alwallah , tana tunanin irin halin gwaggo wato ɗiyar aminiyarta wanda take auren mijin daya saki raihana, tace umm kada ince wani abu kuma taje ta ƙarani, miƙewa tayi sanann ta nufi ɗakin gwaggo tana zuwa tayi sallahr isha"i, tana gamawa a wurin da tayi sallahr anan ta kwanta, bata daɗe da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita,


Allah yasa mu dace ubangiji ya ƙara mana haƙuri a gidan aurenmu idan bakayi haƙuri don Allah ba sai kayi dan banza, hausawa sunce wanda bai share masallaci ba ya share kasuwa, Allah ka zaunar da kowa a gidan mijinta lafiya, ameeeeeeeeeeen,


da haka nake cewa ku kasance tare dani, 💋💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 2⃣5⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*Wannan shafin naku ne ameenci writer's association, ƙungiya mai haɗin kai da kaunar juna, kullum ƙoƙarinsu ganin sun kyautata wa juna Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, ubangiji ya ƙara basira da hazaƙa , Allah kuma ya ƙara lafiyar idanuwa, abinda muke rubutawa wanda mukai daidai Allah ya bada ikon amfani dashi inda mukai kuskure Allah ya yafe mana , ku kuma masoyanmu muna maku fatan alkairi ubangiji ya barmi tare*

*Asmeenat xeeyan har yanxun ba zan daina maraicinki ba, saboda kina cikin babban birni zuciyata* 😜

*Hafsat isa maman katsina ta dikko ɗaƙin kara muna godiya sosai bisa ƙaunar da kike ma aminci writer's mun gode sosai da kulawarki alkairin Allah yakai aki har cikin bargon baccinki dan nasan yanxun dai baki tashi ba,*

*****

*G*ari na wayewa raihana bayan tayi sallah bata koma bacci ba, suna nan zaune da ita da gwaggo suna ɗan taɓa fira, har hantsi ya fito, gwaggo ce ta tashi ta fita daga ɗakin dan sarrafa abinda zata bawa cikinta,

Daga tsakar gida ta kwaɗawa raihana kira , tana cewa fito ki siyo man alewa, raihana ta fito daga ɗaki tana miƙa, da hijibin ta rataye a kafaɗa, naira 10 gwaggo ta bada ta siyo mata alewa, raihana tace wai mi zakiyi da itane?""

Gwaggo tace kunun tsamiya zanyi, idanuwa raihana ta zaro sannan tace banda abinki waye zaisha kunun tsamiya da alewa?"" gwaggo tace ni, raihana tace haba kiyi haƙuri a siyo maki sugar kona ishirin sai ki ɓalɓaɗa, gwaggo tace ƙarshen canjinta kenan, dariya raihana tayi sannan ta anshi kuɗin ta fita daga gidan,

Ita kuɗin ta suna hannun umma data siyar ma gwaggo sugar nan , tsaki tayi sannan tace Allah yayi mana tsari da talauci, niko nace ameen ,

Tafiya take sosai har ta isa shagon shamsu, akwai layi dan haka ta samu wuri ta raɓe, saida aka rage sannan ta miƙa mashi kuɗin , bayan ya riƙe kuɗin a hannunshi ne kafin ya ɗauko mata alewar ya fara cewa raihana jiya anxo binciken halinki amma nidak Allah ya sani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login