Showing 69001 words to 72000 words out of 98315 words
ka nuna man a jikina miye bani dashi?""" mai wata "ya mace tafi da har zaka tafi wurinta,?"" sai ki girza ƙirjinki meye baiji maka ba a halitta daka raina, zaka barni kaje ka ƙarewa wata kallo?"""""
Sai ki saka kuka ki faɗa saman gado haba hajiyata kinsa sheɗaniyar rigar baccinki kin girgiza jikinki yaga komai yana motsi kin faɗa gado yaga komai naki yana rawa kinfa ɗaga masa hankali , babu idan zai fita dole ya nufo inda kike "yar uwa donme bazamu rinƙa jawo hankalin mazajenmu garemu ba?""" zamu bari wasu suna yaudarar mana su a waje ?"" ko zuwan da zaiyi ya ɓata ƙokaci a wurinta suna fira, an ƙwareki bare kuma ya ɗauki wani ya bata kinga ai an rage ki, dan udan yayi niyyar sabowa maki kaza a daren idan yaje ya bawa wata kuɗin ke sai kiga ko ƙifi bazai kawo maki ba,
Kinga sakacinki yaja maki, da rashin kulawa, da girman kai, waike a dole kada miji ya raina ki, wallahi muna sakaci fa ko wani abu ya haɗamu da mazajenmu sai kiga mace wai bata girki bata shara babu wanke wanke, ba wanka ba wanki, sannan kuma bazaki bashi haƙƙinsa ba waike an ɓata maki rai sai ki rama ta haka?"" to wannan bashine gyara ba, wannan ɓatawa kikayi idan miji bamai tsoron Allah bane miye zai hana bazaije neman matan banza ba?"" dama su haka sukeso kinga an barki da hauka, sai ya kawo ido ya zuba maki, kafin ki ankara kuma an tadaki aiki, don Allah mu kula mu gyara saboda samun kwanciyar hankalimu Allah yasa mu dace,............
***
*Zawarci*
*A* ƙofar gida raihana tana fitowa daidai ƙofar gidansu nan tayi tsaye, shi kuma ɗan girman kan yana kallonta baiyi mata magana ba ita kuma bata matsa ba, nan tayi tsaye, tunda yaga bata matso ba kuma bata da niyyar tahowa yasa yayi alƙawari da zuciyarsa ko zasu kwana a haka shi bazai mata magana ba, wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa ya tsani yaje wurin mace, wai idan anzo a wurinsu lokacin suke jin wani rashin mutumci waisu anzo biko, tsaki yayi sannan ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗora saman ɗaya, wayarsa ya fiddo yaci gaba da latsawa,
Raihana kuma tana ganin haka, wata zuciyar tace mata kam lallai yama raina maki hankali wata tace ba haka ake rayuwa ba, mutumin daya taso daga wani wuri yaxo saboda ke, ya kamata kiyi mashi uziri kiji abinda yaxo dashi sannan kinsan miye mafita,
kallon inda yake zaune saman dakalin ƙofar gidansu , shiko hankalinsa yana kan wayarshi, ganin baida lokacinta yanda ya nuna ma baisan Allah ya ajeta ba, yasa ta sauƙi girman kai ta matsa kusa dashi,
Kugu ta riƙe taɗan jijjiga kamar mai shirin kai masa duka, sannan tace malam ya akayi ne?"" bai ɗago ba kuma baiyi magana ba, ƙara matsawa tayi kusa dashi tace gani........., har yanxun idonshi yana saman wayarshi, baiyi magana ba, raihana tace wallahi idan baza kayi magana ba, zan koma,
murmushi yayi amma bai kalli raihana ba, yace to ai kina iya komawa, sai kixo kaina haka gatsal babu sallama babu gaisuwa kixo ki riƙe kugu kamar zaki zaneni?""" tsaki raihana tayi , kallonta yayi sannan yace ki daina wulaƙanci babu kyau, raihana tace a ina nayi wulaƙancin, murmushi yayi sannan ya ajiye wayarsa a gefe,
hannunta ya jawo ya zaunar da ita kusa dashi, sannan yace barka da yini, yana kallon fuskarta, shiru raihana tayi, Faruk yace miye?"" raihana tayi shiru, sai buɗa hanci take kamar wanda ta kada ƙato,
Faruk yacd ina magana baza kiman magana ba dan nazo gidanku?"" ya faɗi maganar cikin sigar wasa, amma raihana an wani murtuke fuska wai ita anzo biko, murmushi faruk yayi sannan yace muje zanga mom ɗinki, raihana tace ita ba mom ake cewa ba, sunan ta umma, yace to muje in gaishe da umma, raihana tace saboda mi?""" baiyi magana ba, ya miƙe tsaye, ganin yana neman shiga cikin gidansu tace du Allah malam dakata, ina zuwa bara inje in faɗa mata zaka shigo ko?"", dariya yayi har dinfull ɗinsa ya fito, komawa yayi ya zauna,
Ita kuma jiki yana rawa tayi cikin gida, tana shiga ko sallama babu ta faɗa ɗaki, tana ɗa zaro ido, tacd Umma gafa Faruk nan da gaske zai shigo duk kece kikai mana baki , haka zai shigo yaga ɗakin nan umma,?"""
Raihana tace bari inje ince kawai kinyi bacci don Allah, Umma tace haba ba haka za"ayi ba, barshi ya shigo raihana tace haba umma don Allah ji ɗakin nan?""", kalli katifar nan mai kama da tabarma, haba don Allah,
Umma ko a ajiyeshi a zaure ne?"",,,, ko a tsakar gida?"" Umma dai bata sake magana ba, raihana tayi ta magana umma bata bata amsa ba, ganin haka yasa ta tattara katifar da cusa bayan ƙaure ta ɗauke lodin kayansu da aka ɗaɗɗaure kamar ɗakin "yan bodin ta fita dasu takai wani ɗaki, da sauri ta dawo ta sharw ɗakin sannan ta shinfiɗa tabarma, garwashen wuta ta ibo tasa turaren wuta, sannan ta fita............
tana fita umma tace hegiyar mata da zakixo kiyi ta man ƙa"ida, tashi tayi ta fita ɗakin da raihana takai kayan ta samu kaya masu kyau ta saka, amma bata fito daga ɗakin ba, ta zauna,
Raihana kuma a zaure taci karo da faruk, yajowata jikinshi yayi ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya, raihana cikin masifa tace haba don Allah miye haka kasan Allah ya tsine ma masu irin wannan halin babu kyau fa, tana ƙoƙarin kwace jikinta,
Sakinta Faruk yayi sannan yace miye haka?"" miye abun zunubi idan na taɓa ki ne?""" raihana tace du Allah idan kana shigowa ka shigo dare yana yi tayi gaba, saida ta shiga tsakar gida ta juyo dan cewa faruk ya shiga, amma sai taga wayam, gabanta ya faɗi, da sauri ta dawo zaure, baya nan, subahanallah abinda ta faɗa, da gudu ta fito ƙofar gida,
Zaune ta ganshi saman dakali, ajiyar zuciya tayi sannan ta matsa kusa dashi tace miye haka ?"" taɓe baki yayi sannan yaɗan ɗaga girarenshi yace, to ai naji sai faɗa kike kada in shiga gidan naku ki zane ni, hmmm raihana tace sannan tace to muje, kayi haƙuri, yace to miyasa kike cewa nayi xunubi idan na riƙe ki?"",,, raihana tace ai kasan dalili kaima, Faruk yace wane irin dalili ne?"" ki kikasan hakan amma ni bansan komai ba ,
Raihana tace baka sakeni ba?""" idanuwa Faruk ya zaro tare da miƙewa tsaye cikin sauri, yace waye yace na sakeki?""" raihana tace kaine ka rubutu?""" Faruk yace ni?""" yana dafa ƙirjinsa, raihana wallahi ko, sassauta magana faruk yayi sannan yace ina takardar da nayi sakin ne?""" raihana tace tana nan umma ta ɓoyeta, Faruk yace to ni Allah ya sani ban sakeki ba, amma waye ya baki?""" raihana tace nima bansan wanda ya bani ba, amma umma ta ajiye, Faruk ya kalli raihana sannan yace ba kince kada kn sakeki ba?"" raihana tace idan nace ai maganar nawa batayi amfani ba,
Faruk yace waye ya faɗa maki maganar ki bata da amfani a wurina?"" muje gidan, raihana tayi gaba faruk ya bi bayanta , har cikin gida, sallama tayi ta shige ɗaki, bayan ta shiga ta bawa faruk damar shiga, sallama yayi shima ya shiga ɗakin,
Raihana ta nuna masa wurin zama ya zauna, sannan tace bara ta kirawo umma, yace tam, fita tayi shi kuma yabi ɗakin da kallo, yana ɓata fuska kamae yaga kashi, Allah ya sawaƙe, Allah mun gode maka, a daidai lokacin da raihana tayi sallama ta shigo, umma na biye da ita, suka shiga baki ɗaya,
Bayan sun shiga ne, faruk ya cire tabarau ɗin idonsa, ya gaishe da umma cikin girmamawa da ladabi, bayan gaisuwa , raihana ta fita ta kawo ma faruk ruwa, shiru ya biyo na wasu lokutta, sannan faruk ya fara magana, cikin sinnar da kai,
Yace Umma dama naxo ne zan tafi da matata, Umma tace matarka kuma?""" Faruk yace Eh, murmushi umma tayi sannan tace ai ta gama idda, idan akana ra"ayin sake zama da ita, aisai kaje ka sanar da dangin babanta, amma idan ita ta yadda zata sake zama dakai, Faruk yace wata irin idda kuma Umma?""" Umma tace wadda kasan anayi dai kamar yadda addini ya tana da, Faruk yace to waye ya saketa da zatayi idda kuma?"" Umma tace kaine, girgiza kai faruk yayi sannan yace ko ɗaya, ni ban saki *RAIHAN* ba, waye ya baki takardar ne?"""
Umma tace wata mata ce, Faruk yace mu gani?""" Umma tace to ai babu buƙatar gani tunda kasan abinda ka rubuta a ciki, Faruk yace ai da kunga abinda na tubuta da bakice ta gama idda ba Umma, Umma ta kalli raihana sannan tace saki nawa ne yayi maki,?""""
Turo baki raihana tayi sannan tace ai gaya a gabanki ya faɗa maki mana, kai nawa ne ka bayar ma?""" ɗaure fuska faruk yayi sannan yace ban bayar da ko ɗaya ba, ɗauko man takardar nace miki, ya ƙarasa maganar cikin hargowa, tashi raihana tayi a bayan ƙaure inda ta rataye jakarta, ta sauko ta fiddo takardun saki na aminu dana faruk, tazo ta kawo mashi,
ansa yayi sannan ya fara buɗe ta aminu, saki ukku ne ya gani, murmushi yayi ya ajiyeta a gefe, tashi ya buɗe yaga ganda ya bada rubutun haka yake dai, ya miƙama raihana yace ta karanta da ƙarfi kiwa yaji,
Ansa tayi ta karanta, bayan ta gama faruk yace kuma kamar yanda nace idan komai ya daidai zanzo in dawo da ita, don haka yanxun zan tafi da ita, Umma tace a,a ba"a haka, kaga dangin babanta da mutane duk haka na faɗa masu an saki raihana amma ka bari idan Allah ya kaimu gobe zanje in masu bayani, sai kaima kaje , Faruk yace A,a matata ce ni bana buƙatar zuwa wurin kowa tunda nasan banyi saki ba, amma miye ya hana ku duba Umma?"" tace aini kawai raihana tace ka saketa, ni kuma ban iya karatu ba, na duba amma sai kawai na ajiyeta, kuma na tambayeta saki nawa ne tace bata sani ba,
Faruk yace to babu damuwa Allah yasa rayuwarmu takai goben, Umma tace amin, tashi tayi ta fita daga ɗakin, kamar jira yake ta fita, inda raihana take zaune ya miƙe yaje, yana zuwa hannunta ya riƙe itama ya miƙar da ita,
Yace yarinya yau da kin bini munje gida tare, hmmm, raihana tace hmm miye?"" yace ki bari sai Allah ya kaimu goben, raihana tace hmmm , murmushi yayi sannan yace kema kin rama ko?""",
Murmushi tayi, batayi magana ba, agogon hannunsa ya duba yaga 11:02pm yace kinga baɗa inxo in wuce, raihana tace to sai Allah ya kaimu, hannunta yaja suka fita tsakar gida, ƙofar ɗakin da umma take yaje kusa da wurin yayi mata saida safe, amma bai shiga ciki ba muma bai ɗaga labulen ba,
Kuma har yanxun hannunta yana cikin hannunshi, a zaure yace to ta koma, sai Allah ya kaimu, raihana tace tom, saida ya tafi sannan ta kulle gida ta dawo,
lokacin data dawo har umma ta shinfiɗa masu katifarsu, raihana tana dawowa kwanciya tayi, tana kwanciya, umma tace to miyasa kikace man ya sakeki ne?""", Raihana tace Umma mamanshi tace saiya sakeni ne, tsaki Umma tayi sannan tace amma ai da kin duba sai a baka abu bazaka duba kaga miye ba?"", yanxun da baizo ba sai kiyi aure da auren wani akanki?"", ki daina haka na faɗa maki, idan ance an sakeki kawai ki duba ki gani abinda Allah ya rubuta baya gogewa, raihana tace to Allah ya bamu dacewa umma tace Amin,
***
*W*ashe gari wurin 2:58pm, umma tana ta shirin tafiya wurin dangin baban raihana dan faɗa masu komai, taji sallama yayan baban raihana, yana cewa a kawo tabarma suna tare da baƙi, Umma tace to baƙin bama su shigowa bane?""", yace a zaure zamu zauna, umma tace to, ɗaki taje ta ɗauko tabarma ta bashi, yana ansa ya fita da ita,
A zaure bayan baba yaje ya shinfiɗa masu tabarma , aka zazzauna, baba ya kalli Alhaji ya kalli faruk sannan yace to ina saurarenku Alhaji,
wato shi Faruk da safe gidan Alhaji yaje yayi masa bayanin duk yadda sukai da umman su raihana, sannan yace mashi suje wurin dangin baban raihana, saboda abun yaxo haka, to shine lokacin da sukaje suka sameshi da baƙi, su kuma wasu sunje neman auren raihana, saiga su Faruk suma sunxo da nasu zanje don haka aka rantafo akayo gidan su raihana don jin ya abun yake.........,,,
Baba yace to Alhaji kace Faruk bai saki raihana ba, Faruk da yake zaune gefe guda ya duƙar da kansa ƙasa, Alhaji yace lallai bai saketa ba, matsala ce daga gida, kuma haka ya rubuta, baba yace to a kira raihana,
bayan an kira raihana, gaisuwa tayi wa kowa dake wurin , sannan baba yace tsakaninki da Allah saki nawa faruk yayi maki?""" raihana ta ɗago fuskarta ta kalli kowa na cikin zauren sannan ta mayar da dubanta ga baba, tace a takardar daya bani babu saki,
Baba yace miyasa kkace ya sakeki?""",,,,, tace saboda naji mamanshi tace sai ya sakeni, kuma naga yayi rubutu ya bani, dan lokacin da ya rubuta bana cikin yanayin iya magana ne, dana zo gida nace an sakeni, baba yace a lokacin baki duba ba?""" Raihana tayi rantsuwa bata duba ba ,
Alhaji yace taje ta kawo su gani, miƙewa rainaha tayi taje ta kawo, suna dubawa kowa ya gani kuma aka tabbatar da rubutun Faruk ne, dan haka dai akayi dai "yan cecekuce daga baya, Alhaji yace to ayi haƙuri,
Duk abunda ya faru sai ayi haƙuri tare da addu"ar Allah ya kyauta gaba, bayan an gama duka an natsu Faruk yace to zaizo ya ɗauki matarsa anjima, baba yace kayi haƙuri a saka lokaci, Faruk yace shifa lallai yau zai ɗauketa, Alhaji yace kayi haƙuri su saka lokacin?""" Faruk yace tam, baba yace kayi haƙuri, inda raihana take ya kalla sannan yace ke raihana yaushe zaki koma ne?"", jin an kira sunan raihana yasa Faruk ya ɗago kansa da sauri yana kallonta, itama shi take kallo, ƙanƙace idunuwansa yayi sannan ya buɗe su duka, yana jiran yaji abinda zatace,
Raihana tace sai bayan sati biyu, baba yace to Allah yasa rayuwarmu takai, Faruk ɗaure fuska yayi har aka tashi bai sake magana ba, daya tashi tafiya haka yayi wa su baba bulalar kuɗi ya tafi yabarsu da jinya,
bayan su Faruk sun tafine , su baba suka shigo, suka nunawa Umma, Umma tace sun gode wallahi, haka suka ba Umma wani abu daga cikin kuɗin amma furr umma bata karɓa ba, sunyi juyin duniya amma taƙi ta ansa, haka suka haƙura suka tafi,
raihana kuwa waya ta bugawa Farida ta kora mata duk bayani, Farida tace yayi daidai , ya kamata ki kimtsa hajiyata a gyareki ki koma sabuwa, a dilke mana ke, gobe insha Allah zanzo raihana tace Allah ya kaimu lafiya sai kinxo,
Faruk yaji baƙin ciki da raihana bata yadda ta biyoshi ba, duk ki gama zaki zo ki sameni da hukuma kike magana, wato ƙarshn sunan sa, Faruk Ahmad Hukuma, shine yake cewa zata san da hukuma take magana,
****
*D*a hantsi Farida tazo gidansu raihana, bayan sun gaisa da Umma suka shige ɗaki da raihana saidai su ƙulla wancan aka kwance, don haka farida tace mai dilka zatazo yau ta fara mata, kuma ta sallameta , wasu kayan matan da ta siyo mata ta fiddo ta bata, tace aci gaba da gashi hajiyata komin kyau ɗinka sai ka ƙara da wanka,
haka dai taci gaba da bata shawarwari, suna ɗaki har mai gyara jikin taxo ta fara, saida farida taga an fara sannan tayi masu sallama ta tafi gida, ita kuma mai gyaran jiki zata zauna nan taci gaba da aikinta,
Tunda faruk ya tafi har yanxun bai sake dawowa ba, gidansu raihana, yana can shima yana uzirin sa,
***
Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah raihana dai ansha gyara an gyaru sosai , kuma yaune ranar da Faruk zaizo ya tafi da ita, dan yace baya buƙatar kowa ya rakata, kuma shine zaizo da kansa ya ɗauki matarsa,
da farida da zulaihat ne kaɗai a gidansu raihana tunda ba wata gayyar arxiki tayi ba, kunsan dai halinmu mu mata, sai ɗora raihana akeyi ana bata shawara mai ɓillewa ba wadda zata halakar da ita ba,
Suna nan har aka kira sallah isha"i saida raihana taci gayunta cikin shiga ta alfarma da burgewa, saida suka tabbatar ta gama ƙimtsuwa sannan sukace ma raihana zasu tafi, farida tace ma zulaihat suje ta ajiyeta a gida, haka suka tattara suka tafi gida ya rage daga umma sai raihan
*F*aruk baizo ba, sai wurin 9:30pm, kamar yanda yayi alƙawari, don haka bayan yayi parking ne, ya samu yaro ya turashi cewa zai shigo tunda baya da number raihana,
ba ɓata lokaci yaron ya dawo yace ance tana zuwa, bayan yaron ya tafi Faruk ya shiga cikin zauren gidan su raihana, bayan ta fito ne, suka gaisa yace suje ciki, juyawa tayi suka shiga tana gama zuiiizuiiii yana bin bayanta,
bayan sun shiga ne, suka gaisa da umma , sun ɗanyi fira sosai, sannan faruk yace ma raihana ta tashi su tafi, yana magana kamar jira take ta fashe da kuka, wiwiii, Umma tace miye haka?"", Faruk dai baiyi magana ba , umma tace bakiji abinda yace ba?""" raihana tace ita bafa yau tace yaxo sai gobe, ko inda take bai kalla ba, umma ma bata sake magana ba, tashi tayi tabar ɗakin,
Tana fita faruk ya miƙe inda raihana take tsaye tana dirdira ƙafafuwanta kamar yarinya ƙarama, duk da ya matsa kusa da ita bai hanata wannan tsallaenba tana kuka, binta yayi da kallo yanda take tsalle tsalle, da idanuwa kawai yake binta da kallo, saida ya gaji da haukan nata sannan yasa hannunshi ya daɗe mata baki,
sannan yace miye?""" tace bazanje ba yau, Faruk yace ƙarya kike sai kinje, cikin shashshekar kuka tace du Allah ka barni sai gobe, yace A, a, zata sake magana ne, yace bana san kina man gaddama, kixo muje, raihana bata sake magana ba,
Faruk ya fito ya tsaya a tsakar gida yana jiran fitowarta, ta daɗe sosai shi kuma yace a ranshi duk ki gama kixo ki sameni, ta daɗe