Showing 66001 words to 69000 words out of 98315 words
dariya, sannan tace an fara kenan, zawarci nidai badai "ya"yana ba , shi yasa kullum sai an sakoki kamar akuya, ta sake sheƙewa da dariya, raihana dai ta raɓa gwaggo batayi magana ba, ta wuce abunta,
gwaggo sai dariya take ma raihana haka za"a balbaɗe a titi, ita kuma raihana napep ta samu ta hau sai gidan farida, yau acan za"a baje koli.........
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3⃣9⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*Jinjina gareku masoya littafin zawarci, wannan page naku ne, gaba ɗayansa,*
*KISSAR TSAFTA*:• tsafta itace babban jigo a rayuwar aure , "yar uwa da kin tashi kika sallami mai gida ya fita, share gidanki loko da saƙo ko ina, ki fitar da shirgi da karikice, ki gyara wurin sosai,
Ki shiga kicin ki share ki gyara ki goge inda yake da yana, ki kakkaɓe komai ki haɗe wanke wanke kiyi ki gogesu ko wanne ki adanashi a inda ya kamata, toilet ɗinki kisa aizel ki wankeshi ya fita sosai kisa turaren ƙamshi,
A dakin kada ko ina ki cusa kayan wanki kada ki ɗora saman kujera ko matse matsin dorowa kada ko ya kikaga tsakanin wuri kice zaki cusa tsummokara, ko kyan wanki, ba haka akeyi ba,
Idan har haka zakiyi zaki jawo ma kanki sauro ɓeraye da dai sauransu ke wani wurin ma har kudan cixo ya samu wurin da zai lafe, kayanki kala biyu ko ukku haɗasu ki wanke, ko baki goge ba, kiyi masu linki mai kyau, ki saka a wedrop, itama ki goge ta fess ki samu turaren ƙamshi na kaya ki saka dan gudun warin ruma,
Ki gyara gadonki kada ki barshi a hargitse ki ɗameshi da shimfiɗar gado mai kyau, duk ki goge ƙurar jikin gadonki kisa ruwa da ɗan klin ki goge kayan gadonki tasss, da wadrop da madubi, durowowi da dai komai na ɗakinki,
Ki share yana don kada kixo kixo ya samu wurin zama, ki wanke kwatar gidanki ki gyarata dan kada ta riƙa maki wari, idan kin shiga wanka kada kiyi a fujanjan ki warwatsa ruwa ki fito,
Dan zaki tayar ma da kanki datti ƙaiƙayi yaxo yana damunki, ki murji sabulu sosai ki dirje jikinki yana kumfa kina cuɗe shi kina durzawa, ki cuɗa hamatarki sosai da ƙasan nononki da matse matsin cinyarki, da duk inda kika san ɗauɗa zata iya zama da wuyanki ki wanke sosai,
Ki rinƙa askin gabanki da hamatarki akai akai don datti da wari suna ɓuya a wurin,..
Dan Allah hajiyata ki kasance mai gyara jikinki kowane loko da saƙo don duk inda maigida yasa kansa yaji ƙamshi,
****
*A* ƙofar gidan farida napep ta ajiyeta, bayan ta sallami mai napep ta shige, da sallama ta shiga gidan, farida dake kicin da gudu ta fito tana oyoo yooo, amma ni namayi fushi, murmushi raihana tayi sannan tace tuba nake ƙawata,
Farida tace haba sai ayi ta kiranki a waya dan rainin hankali bakya ɗauka?"" raihana tace yaushe kika kira ban ɗauka ba?"" farida tace kullum ma saina kiraki bakya ɗauka, raihana tace Allah sarki wayar ai tana gidanshi,
Farida tace gidan wa?""" raihana hawayen da take ɓoyewa suka zubo daga idonta, sannan ta matsa kusa da farida ta kwantar da kanta saman kafaɗar ta, ta fashe da kuka tana cewa babbar ƙawa an sakeni,
Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, abinda farida ta faɗa sannan tace tun yaushe?"""raihana tace har yau na gama idda, farida tace subahanallah a daidai lokacin da raihana ta ɗago kanta farida taja hannunta suka shiga farlo,
Bayan sun zauna ne, farida duk ta tashi hankali , ta kalli raihana dake ta faman kuka tana shashsheka , itama farida wasu hawayen suka zobo mata dan taya ƙawarta baƙin ciki, saida sukaci kukansu har suka gaji dan kansu sannan sukai shiru,
Bayan sun natsu ne farida ta tambayi raihana abinda ya haɗasu?"" raihana tace ba komai mamanshi tasa ya sakeni, tsaki farida tayi sannan ta miƙe tsaye , cikin faɗa ta fara magana, duk yanda akai baki kyautata mashi ne, da yaji daɗin zama dake babu yanda za"ayi ya sakeki sai dana ce maki ki kyautata amma dan hauka kikaje ke kin samu gado kin haye kin kwance ki faɗa man a haka zakiyi yaƙin da zaki saka kanki a zuciyarsa ne?"""
Raihana tace farida ba haka bane, farida tace da Allah rufe man baki, wannan ai sakarci ne da sakaci irin naki, bakisan mazan yanxun ba su basu san sakarar mace bakauya ba?"" maza sunfi san mace wayayya amma dama kinxo kin dunkume ɗaki miji na farlo kina ɗaki ki faɗa man taya zaki jiga ranshi?"", babu magana mai daɗi babu sannu da zuwa babu addu"ar Allah ya tsare hanya, raihana tace duk fa inayi farida,
Tsaki farida tayi sannan tace da Allah rufe ma mutane baki, miyasa udan wasu matan suna kyautata ma mazansu sai ake ganin kamar asiri sukai masu ne?"" dole idan kina ajiye wannan kyaucin naki ki ajiyeshi nama gaya maki, yanxun haka zakiyi ta aure aure don Allah, farida ta sake fashewa da kuka ta faɗa saman jikin raihana sukaci gaba da kuka tare,
saida sukaci kukansu suka gaji sannan farida tace to raihana miyasa ma don Allah tun farko kafin ki gama iddar baki faɗa man ba?""raihana tace babu waya a hannu kuma umma ta hanai fita ne,
miƙewa farida tayi sannan tace bara inje in duba girki na, raihana itama tashi tayi tabi ta suka je kicin ɗin tare, tana kama mata aiki suna ɗan fira jefi jefi amma farida taji baƙin cikin dawowar raihana gida, kuma ta tayata addu"ar samun miji na gari, farida tace to saki nawa yai maki ne?"" raihana tace banma duba ba, farida tace gaji hauka an taɓa sakin ki bazaki duba ba?"" ki duba kiga idan saki ɗaya ne sai asan yanda za"ayi,
Ɗan rainin hankalinma ko an kira baya ɗaukar wayar, ta ƙarasa maganar da ɗan guntun tsaki, haka dai suka yini suna fira da raihana tace zata tafi farida ta shiga ta ɗan haɗa mata sha tara ta arxiki sannan ta bata waya, amma ba sabuwa bace ta tace data canja infinix hotnot, raihana tayi godiya, farida tace mata bata so, tana mata haka, farida da kanta ta mayar da raihana gida,
bayan sunje saida ta shiga ta gaishe da umma sannan raihana tayo mata rakiya taja motar ta tayi gida.........,
Itama raihana gida ta dawo, tana shigowa ɗaki ta shiga, ta cire kayanta, ta sake wasu, sannan ta zauna tana ta lallatsa wayar da farida ta bata,
Umma dake tsakar gida ta kira raihana, ansawa tayi daidai lokacin da take miƙewa, ta fita tsakar gidan, umma gani ta faɗa, umma tace ga faten dankali nan nama ga yayi ruwa, kixo ki zuba, raihana tace umma banjin yunwa , umma tace to ɗauki tukunyar kikai ɗaki mayi kalaci dashi da safe, raihana tace to ta ɗauki tukunyar tayi ɗaki da ita,
***
*A* ɓangaren faruk kuwa ya rasa ta ina zai hudo ma lamarin raihana, shin wai takardar daya bata anya kuwa ta gani?"", kai gaskiya bata gani ba, to momy ta bata kuwa?"" tambayar dai duk babu amsa, wata zuciyar tace mashi ya tura Alhaji, wata zuciyar tace ba wurinshi bane kaine zakaje da kanka, murmushi yayi sannan ya miƙe ya shige ɗakinsa dan fara shirin zuwa biko, murmushi yayi dan bai taɓa ba, shi baima san yazaice mata ba idan yaje, hmm yace sannan yace kai gaskiya bazan iya zuwa ba, kada yarinya ta raina ni,
Wani tunani yayi sannan ta jinjina kansa dan lallai ya samo ma kanshi mafita, wanka ya shige, yana fitowa daga wanka bayan yayi shirin sa, shiga mai kyau yayi sosai, kallonka kansa yayi a mirrow murmushi yayi sannan ya sake kallon kansa gaskiya bazan iya ba,
Wayarshi ya ɗauka ya fara kiran hafsat ƙanwarsa, bayan ta ɗauka ta gaishe shi ya amsa cikin isa da gadara, yace ina zuwa gidanki yanxun,,, tace to yaya Allah ya kawo ka lafiya, yace amin,
Daya gama da hafsat ya kira wayar wani abokinsa bayan sun gaisa, yace sadiq kana ta ina ne?"", ya faɗa mashi inda yake, faruk yace mu haɗu dakai a gidan hafsat yanxun nan, yace to ba damuwa sai nazo, yana kashe wayar yace tam ya za"ayi?"" wayarsa ya ɗauka ya fito, yana fitowa da sauri duk wanda yake wurin suka miƙe dan jinjinawa,
motar aka buɗe mashi ya shiga, babu ɓata lokaci yace sulaiman gidan hafsat, wanda aka kira da sulaiman yaba mota wuta, aka buɗe masu get suka ɓace daga wurin,
A gidan hafsat dukansu a farlo suke zaune, ga sadiq ga faruk sai kuma ita hafsat ɗin, bayan ta gaisheshi ta kawo mashi ruwa da lemo, sannan ta samu wuri a ƙasa ta zauna, sadiq yace ranka ya daɗe gani, kallo yabisu dashi sannan yace sadiq dama maganar wannan yarinyar ne, sadiq yace wace yarinya?"" yace ke hafsatu miye ma sunan ta?"" dariya hafsat tayi sannan tace sunan tace yaya raihana , uhumm inji faruk ya faɗa , yafa san sunan ta iskanci ne,
yace to dake da sadiq kuje ku dawo da ita, sadiq yace ah ah ranka ya daɗe ba haka akeyi ba, faruk yace ni haka za"aman sadiq yace ai ba munce ah ah ba, kaga yanxun ta daɗe a gida dole sai iyaye maza zasu je, faruk cikin ƙulewa yace anƙi aƙa saka iyaye mazan, hafsat tace yaya tunda saki ne, kai kaje biki da kanka mana?"" harararta yayi tare da ɗaure fuska sosai sannan yace banda kike mahaukaci ke da girmana anje biko?"" so kike yarinya ta raina man hankali ne?"", dansu na lura matan nan da sunga ana bin kansu sai suyi ta raina ma mutane hankali,
sadiq yace "yar laɓai tunda dai kaine kake so dole kaji da kanka kaga idan ta ganka zataji daɗi a ranta, faruk yace duk ku barshi na gode, miƙewa yayi tsaye, da sauri hafsat ta miƙe tana cewa yaya kayi haƙuri , bakin shi ya taɓe ta tare da yayi magana ba, ya fice daga farlon , yana fitowa sule ya buɗe mashi motar suka bar gidan ,
hafsat tace aishi yaya saurin fushi wallahi kuma don Allah tunda kana san abu ba dole sai ka sauke girman kai ba?"", hmm lallai yarinyar nan dan ta samu yana santa ma take rainawa mutane hankali, niko nace taje ta raina , 😏
Tsaki yayi sannan yace ma sulaiman kasan gidan su wannan yarinyar?"" sule yace wace yarinya ce ranka ya daɗe?"" daka mashi tsawa yayi sannan ya faɗa mashi sunan unguwarsu raihana yace jeka ta can, da sauri sule ya juya sitiyarin motarsa suka doshi unguwarsu raihana,
Banda tsaki babu abinda faruk yake yi, shi kullum ɗan zaiyi aure sai kace tattabara, dangin babanshi har sun gaji da halinsa, tsaki ya sakeyi sannan yace su basu ma san ban saketa ba, mahaukatan banza, idan na faɗa ai sunje su faɗa ma momy tace na raina ta, amma basarwa kawai zanyi , yauwa nan yayi,
Ƙofar tsohon gidansu raihana suka tsaya, Faruk yace fita ka samu yaro ya kirawo ta, da sauri ya fita, wani yaro ya samu sannan yace kai shiga nan kace raihana taxo, yaron yace ba nan bane gidansu, sule yace ina ne?"" yaron ya nuna mashi da hannu, godiya yayi sannan ya koma motar,
bayan ya shiga ya zauna yace Oga ga gidan can, Faruk yace nan ne, sule yace ai cewa akayi sun koma can, tsaki yayi sannan yace muje, jan motar yayi suka silala ƙofar gidansu raihana, bayan yayi parking ne, Faruk yace nashi nan, wata waya ya bashi sannan yace idan an kirata kanajina?"" yace Eh ranka ya daɗe, to ku gaisa kaga bata sanka ba, ku gaisa sosai sannan idan zaka tafi ka bata wayar nan kace akwai layi a ciki zakuyi magana, sule yace to, ya nashi wayar sannan ya fita,
Raihana tana zaune a ɗaki tana ta faman ɗura kalanzir a fitilar kwai, yaro ya shiga yace ance ana sallama da raihana, da sauri raihana ta kalli inda umma take sannan tace kila ma k"b ɗin banzar nan ne, umma tayi dariya sannan tace ma yaron je kace waye yake kiranta,?"" bayan ya fita ya dawo yace wai ance kalifa ne, raihana tace kai ban zuwa, Umma tace a, a, jeki kiga waye, raihana tace wani kalifa umma?"" kodai kalifan munafunci, mutum ya faɗi sunan sa sai yace wai kalifa, tsaki raihana tayi sannan tace jeka ana zuwa,
bayan yaron ya fita, raihana ta ɗauki hijabinta tayo waje, tana fitowa ta kalli sule sosai, sannan tayi tsaki, malam ya akayi ne?"" sule yace babu gaisuwa, tsaki ta sakeyi sannan tace kai nifa na tsani masu kayan soja idan baka sani ba, ta ƙarashe maganar tana yamutsa baki,
Shi kuma sule baisan dalilin daya sa faruk ya bashi waya ya bawa raihana ba, kuma shine yasa sukaxo amma bai fito ba, sule kallon raihana yayi sanna yace ai bani ne na aiko kaina ba, Oga ne, raihana tace waye Ogan?"" da sauri sule ya dawo hayyacinsa yace sowry gashi wayar ya miƙa mata, tsaki raihana tayi sannan tace an faɗa maka ina buƙatar waya ne?""""" tsaki tayi kawai ta juya ta shige gida,......,..
Sule ya koma motar ya faɗa ma faruk yanda sukayi da raihana, tsaki yayi sannan yace jeka zan taho , sule yace ranka ya daɗ........., tsawa ya daka mashi sannan yace nace ka tafi, buɗe motar yayi ya ajiye wayar sannan ya tafi ,
Fitowa faruk yayi ya ƙare ma gidansu raihana kallo , taɓe baki yayi sannan ya girgiza kansa a wannan kangon matarshi tae rayuwa?""" lallai ya tausaya mata, niko nace dan baka san ma gidan na haya bane,
Umma tace ma raihana har kin dawo ne?"" Raihana tace bar ɗan rainin hankali wai wani Oga ya aiko shi, kinji zancen banza, raihana bataci gaba da magana ba, taji yaro yana cewa ance raihana taxo inji mijinta,
Daga Umma har raihana tare sukayi magana waye mijin nata?"" dukansu haka suka faɗa, yaron yace wani ne, raihana tace je kace nan gidan babu matar aure,
yaron ya fito ya faɗawa faruk, murmushi faruk yayi sannan yace kaje kace Faruk ne, yaron ya dawo yace wai ance Faruk ne, Raihana tace kaje kace mashi anyi mata aure,
Umma da bata san kowaye ba, tace ma yaron kai yakanan, yaron yace to, ƙofar ɗakin umma ya matso sannan yace gani, umms ta kalli raihana sannan tace waye shi?"", tsaki raihana tayi tace shine ya sakeni, Umma tace ma yaron je kace tana zuwa, bayan yaron ya fita, Umma tace kije kiji kiran da yake maki, raihana tace da Allah umma ki barshi uwarshi bata so na, tasa ya sakeni to mi kuma yake nema a wurina?""",,,,,,
Umma tace kedai jeki, raihana tace Umma don Allah ki barshi, Umms tace wallahi idan baki fita ba, zanje in shigo dashi yaga wannan ɗakin da aka jera layin jikkuna kamar ɗakin "yan bodin, dariya raihana tayi sannan tace yi haƙuri,
Umma tace kije kiji uzirinsa, duk yanda kake da mutum idan ya tako yaxo gidanku ya wuce wulaƙanci, kije kiji abinda zaice maki,
Raihana tace to, turare ta feshe jikinta dashi sosai ta ɗan gyara fuskarta , ta ɗauki kaya masu kyau ta saka, Umma tace to kin gani, ke ba yarinya bace , ki fitar da tsoro ko shakku tunda shi kai tsaye cewa yayi ace matarshi taxo, tsaki raihana tayi sannan ta yafa gyalenta tayi ƙofar gida,..................,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 4⃣0⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
***
*KISSAR SHAGWAƁA* :• "yar uwa kinsan rayuwa ba ta tafiya daidai yadda kake so, dole saika ƙanƙantar da kanka a wajen wanda kake ƙarƙashinsa, dole ke mace ke aka sani da aji da yauƙi da yanga , don Allah kada ki rinƙa buɗe murya kamar wata gardi idan kina magana da mijinki, kada ki rinƙa sakin baki kina kwakwata dariya,
Dariya da mai gida dariyar aji akeyi mai cike da salo na kiss , duk sadda kike tare da mijinki ki narke masa ki zamar masa "yar beby, duk sanda yake zaune baki da wurin zama sai jikinsa, ki rinƙa masa fira mai ɗan shirme a ciki wadda zata riƙa saka shi dariya,
Kada ki saki ciki a gaban mijinki ki ta faman haƙar abinci yana kallonki , Allah raina miki wayau zaiyi idan kince baza ki iya abu ba, yace duk cin da kike yi?""", Ai kin iya cinye abinci,
Idan miji yana nan kaɗan akecin abinci ana yauƙi da yanga kamar dole kike ci, zakiga gar ririta ki yake yi, idan ya gaji da yangarki ya karɓi cokalin yace shi bara ya baki a baki, ya fuskanci bakya san cin abinci, idan miji yana nan abinci kaɗan zaki zuba a filet, wanda zaki ci, idan kuwa baya nan ki loda abincinki kici ki ƙoshi,
Idan shi zaki bawa abinci ki zubo masa da yawa idan ya fara ci yace miki ya ƙoshi kada ki yadda sa masa rigima kice baki yadda ba idan dai bai cinye ba, yaje wani wuri yaci a can , ke kuma ya barki da wahalar girki yaƙi ci, yita tura masa sai kinga ya cinye,
Saboda abinfi san namiji ya rinƙa ci yana ƙoshi , idan ba haka ba sai ya zama raggon namiji bazai iya biyawa matarsa cikakkayar buƙatar ta ba, kada ki yadda idan mijinki ya shigo daga masallaci sallahn isha"i da daddare yace miki zai kuma fita, sa masa kukan kissa marar hawaye,
Ni bazan yadda ba ka fita ka barni a gidan nan ni kaɗai ba, saidai mu tafi tare idan yace kiyi haƙuri yanxun zanje na dawo sai kice ah ah nidai ban yadda ba, saidai idan zance zakaje, nidai gaskiya banzan yadda ba, sai ka gaya man wurin wacce zakaje, sai kiyi fushi ki juya kiyi cikin ɗaki,
Kina mai kuka amma fa ba kuka mai hawaye ba, zai fasa fitar ya biyoki ɗaki dan ya lallaɓaki ya fice zaman majalissa ko raka wani abokin zance ko kuma shi yaje wurin wata buduwar wai dan ya rag dare, jifa rashin aikinyi, ya bar matarsa ta aure a gida ya tafi neman magana wurin wata budurwa da yasa ba aurenta zaiyi ba,
Idan ya biyoki ɗaki zai baki haƙuri dan ya samu ya fice sai ki miƙe tsaye ki cire hijabin da kika ɗora akan rigar baccin ki ko kuma after dress da kika ɗora kan rigar baccin kice