Showing 75001 words to 78000 words out of 98315 words

Chapter 26 - ZAWARCI

06 Oct 2024

8035

ganin kowa kua bakajin motsin komai sai kuka karnuka , a bakin wani gida ya danne horn ɓit ɓiɓit, boɗe get in akayi sannan faruk ya sulala da motar cikin gida,

zaro idanuwa raihana tayi tana bin gidan da kallo haka sukaci gaba da kutsawa get na biyu , shima wani sojane ya buɗe tare da girmamawa wato sarawa, raihana saidai ta kalli faruk ta kalli gidan kana ganin haka kasan alamar tambayane, bata gama tunanin ba, ya sake horn, get na ukku toufa raihana fa gabanta ya fara faɗuwa, tace mashi wai inane nan?""",,, get na huɗu suka shiga raihana kuka ta farayi wayyo Allah don Allah ina zamuje?""",,,,,, ko kallonta baiyi ba suka get na biyar, kai da gaske raihana kuka take , kallon faruk tayi tace mashi don Allah ina ne nan?""",,,,,


Baiyi magana ba, haka faruk yaci gaba da sulalawa har suka iso wani round, an ƙawata wurin da wasu irin filu masu burgewa wani ruwa yakeyin tsalle yana yin sama sai kuma ya kwararo ƙasa, flawers kuwa gasu nan jere abun burgewa da sha"awa, ga wasu irin karnuka masu birgitarwa ga birai daga gefe,

parking yayi sannan yace ma raihana muje, raihana tace waye zai fita kare ya cinyeshi?""" faruk yace dama kare yanacin mutane?""" raihana tace nidai bazan fita ba, yace ashe kuwa yau a mota zaki kwana?""",,,, raihana tace nidai ina nan kaje ka gama abinda kake ka dawo, faruk yace to ai nan gidanmu , raihana tace nidai don Allah banasan haka , yace wallahi mun dawo gida,

Fita muje ki gani bacci nike ji wallahi, kinga gobe idan Allah ya kaimu zanyi tafiya, kuka raihana ta fara kuma ina zakaje ?""",,,,, yace wurin aiki zan koma, muje idan mun shifa ciki sai kiyi ta kukan tunda kuka bai maki wahala fita yayi, sannan ya zagaya ya fito da raihana, tana fita wani soja ya shiga motar yaje yayi parking ɗinta wurin da aka tana da don ajiye motoci,

hannunta ya kama sukaci gaba da tafiya, duk inda suka wuce girmamawa ake, ga oga ga matar oga, ita dai batasan ko inane ba, faruk ya kawota, sai kallon faruk take amma shi baima san tanayi ba,

duk inda aka wuce raihana saita sake waiwayawa tana kallo, haka tayi tayi har suka isa ciki, har yanxun faruk yana riƙe da hannunta, suna shiga saman gado ya zaunar da ita, sannan ya fita, yana fita raihaɓa tabi ɗakin da kallo, salati kawai takeyi tana mamakin mutane ina suke samun kuɗi har suna tsara gidaje haka kamsr basa tafiya lahira, haka tayi ta juye juye tana kalle kalle, idon ta ya sauka kan wasu jikkuna ne ko kuwa akwatina ne?""",,,, gasu nan dai sunfi 30 tana ta kalle kalle, tace lallai, haka tayi ta jiran dawowar faruk har yanxun shiru baizo ba, ta gaji da kauyancinta tayi kwanciyarta,

Shi kuma fitarshi daga wurin raihana mutane ke jiransa tun ɗaxu don hka a cikin gidan wani ƙaton holl inda aka tanada don ganawa da mutane, saboda haka yana can meeting suke, sai 1:30am sannan faruk ya taho a gajiye,

Yana dawowa ya tashi raihana, wai suje suyi wanka, raihana tace ita gaskiya batayin wani wanka yace ƙarya ne sai kinyi kuma tare dani, agogon hannunshi ya kalla sannan yace taso taso, a lokacin daya ke ɗaga ta, raihana kuka ta fara ita kunya takeji, faruk ya zazzagota daga saman gadon da kanshi ya cire mata daga ita sai bra da pant, towel ya ɗauka yaja ta suka shige ,,,

bayan sun gama wankan suka fito, raihana tace wai miyasa zamu zauna anan ne?""" faruk yace saboda nan nake zaune dama tun kafin zuwanki, raihana tace miyasa aka kaini wancan gidan ne?"",,, yace saboda lokacin bansan da aurenki ba, zuwa man yayi kuma ai kinga bana nan, wancan yafi sauƙi nace a ajiyeki acan,

Ita dai batayi magana ba, sai kallonshi take, inda taga akwatinan ya nuna mata da hannunshi yace ga lefenki can, idanuwa raihana ta zaro tare da cewa ina zani da wancan kayan kuma?"",,, yace kiyi taman gayu inajin daɗi, kuka raihana ta farayi, faruk ya jawota jikinshi yace nifa nace maki bana san wannan abun, ni nakine komai nawa naki ne, kedai kawai ki ci gaba da man addu"a kinji?""", raihana tace to , hmmmm ranar dai an gwangwaje sosai, raihana ta kara cin gidansu dan kwata kwata faruk bai sauƙaƙa mata ba,

saida aka fara kiraye kirayen sallahr asuba , sannan faruk ya ƙale raihana, tare suka shiga wanka, suna fitowa faruk ya fara shirin tafiya, saida ya gama shirinsa tsaf sannan ya bawa raihana kuɗin wanda zata riƙe , kuma yace mata akwai masu aiki zasuyi mata komai, raihana tace to, saida ya tashi tafiya, ita dai dukma kunya takeji, da zai tafi raihana ta tashi da niyar rakiya yace no basai kinzo ba, muna da yawa, kwantar da ita yayi saman gado sannan ya lulluɓeta, ya juya ta riƙo hannunshi, juyowa yayi ya kalleta, tace ina maka fatan alkairi Allah ya tsare hanya ubangiji yasa ka dawo lafiya Allah ya tsare ka da sharrin masu sharri, ngd sosai, murmushi faruk yayi sannan ya matsa kusa da ita, saida ya zauna sannan ya sumbaci goshin ta, yace ina sanki, sosai raihan , murmushi tayi batayi magana ba, wayarshi ta fara ringing ɗauka yayi ya miƙe tare da ɗaga mata hannun, yana fita yaja ƙofar ɗakin,

ita kuma raihana kuka tayi tayi tana ƙarawa, Allah ya sani ita dai batasan namiji mai tafiye tafiye, dama faruk ya tafi da ita, haka dai tayi ta kuka, har bacci ya ɗauketa,

Faruk kuwa yana fita, an haɗa motoci dan haka shi kaɗai ake jira, yana fitowa aka buɗe mashi mota ya shiga sai airport, haka ya tafi da maraicin raihan,

****
Watan faruk ɗaya da tafiya amma har yanxun baiyi waya da raihana ba, raihana kuma an wani goge anyi kilinar an wani zama "yan gayu, idan ka ganta baka gajiya da kallonta, ita matsalarta tana so farida taxo amma batama san sunan anguwar ba, kuma ita bata da number faruk haka dai ta haƙura amma tace mata insha Allah idan ya dawo zata xo

Raihana zaune an wani kashe saman kujera , tana ta tunanin duniya iri iri, hafsat ce ta shigo cikin farlon tare da sallma, raihana ta amsa amma bata daga inda take ba, kuma ba baki ta saki tayi dariya ba, tunda ta ansa sallamar ta basae dan tasan ƙarshe wulaanci zata mata,

zama tayi bayan ta zauna tace ma raihana inayini?""",,, raihana tace lafiya qalau, hafsat tace yaya ya aikoni, raihana tace uhum, hafsat tace yace zaiyi magana dake, raihana tace faɗa man number zan kirashi, hafsat ta karanta mata, daga nan bata sake magana ba, hafsat ta gaji da zaman ta, tace ma raihana sai anjima, tace to, daga nan bata sake cewa komai ba, saida hafsat ta tafi sannan ta tashi ta tafi ɗakinta don kiran *Faruku*..................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣2⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*Gaisuwa ta musamman gareki ya sayyada, mujadda, malama, hafiza, kamila, ustaziyya, hajjajju Rabi Musa Alkairin Allah ya isoki har cikin bargon baccinki*

*Ban manta dake ba Ƙawata Asmeenat Xeeyan Alkairin Allah yakaimu ranar 1/1/2018*

*Wannan feji nakune masoya littafin Zawarci ina tare daku dan kune alfahirina, farin cikinku shine maudu"ina, ina kaunarku sosai*😎
***
*SHAWARA GA MAZA* :• Don Allah don annabi ku riƙa riƙe matanku cikin daraja da mutunci ku tuna fa mata marufar asirinku neeeeee😉 domin duk kyan gida da tsaruwarsa idan akace babu mace a cikin gidan ya zama kangoooo☺ don ko "yan uwanka bazasu riƙa zarya a cikin sa ba, saboda gudun zargi, kada ku wulaƙanta matanku ku rinƙa gani dole tayi maku abu kuna ganinta kamar baiwa,,,,,

To wallahi ba dole bane, saidai kawai tayi don kyautata da kuma neman aljannarta don cewa akayi , idan kun auri mata komai kuyi masu, ku ciyar da ita, ku shayar da ita ku tufatar da ita😌, abinkin da in kunfita kun nemo mune muke girka maku dan tsaron lafiyar🤓 don kuma kuci mai daɗi hankali kwance, kunsan girki iyalikune duk wani koyi munayin koyi da ma"aki S. A. W

To manzan Allah yana zama yayi wasa da dariya da matansa yana tayasu aiki a cikin gidansa ya lallaɓa matansa baya bari suyi fushi baya girman kai, bayacewa shi annabi ne sai komai anyi masa, manzan Allah yana ɗauko kaya daga kasuwa ya kawo har gdansa , manzan Allah yana huɗɗa da talakawa da masu kuɗi da miskinai baya ware wani yace da wannan zaiyi harka, bazaiyi da wancan ba, fiyyen halitta kenan,

Kai kuma ka gama wasa da dariya a waje sai ka dosa gida ka haɗiye rai kamar wani mala"ikan mutuwa,🙄 waikai kada mata suga fuska su rainaka , to raini na nawa kuma?"" ta gama karewa halittarka kallo da daddare., kayi faramfaram kayi wasa da dariya da iyalinka idan kuna cikin nishaɗi da raha kuyi "yar goyo kuyi wasan "yar ɓurum ɓurum ,ka rufe idonka ko ta rufe nata , idan ta kamaka tayi tsalle tana murna ta kamaka,

Kuyi ƙwallon ƙafa, kuyi wasa kuyi rawa tare kuyi "yar tseral, idan ta tafi kicin ka bita tana aiki kana taimaka mata da wasu abubuwan idan yarane daku ka shiga cikin yaranka su sake dakai ka taimaka mata wurin shirin makarantarsu ita tana haɗa break kai kana sa masu uniform, ka taimaka mata wurin basu break ɗin su shaƙu dakai so soka su rinƙajin kaunarka a ransu duk inda suka shiga su rinƙayi maganar Abbansu, duk abinda kayi wa iyalinka ka wadata "ya"yanka da matarka da sutura, kada kai kana fita fess fesss 😇 su suna fita kamar almajirai, wallahi jama"a rainaka zasuyi😔 za,a daina ganin girmanka,

yaro baya mantuwa duk abinda kayi masa yana ƙarami bazai manta ba, duk yanda ka kula dashi da wahalar daka sha akanshi da yadda ka tsaya masa wurin iliminsa yana sane, wata rana sai yayi maka gata, haba bawan Allah ɗanka ne fa, kuma amana Allah ya baka,

Mata don Allah mu kula kada dan an auro mu munxo mun tarar da ɗan da babu uwarsa a gidan mu shiga mu fita mu raba ɗan nan da ubansa, kece kullu masa wannan sharrin kece ƙulla masa wannan makircin, harsai kin rabasa da ubansa, uban ya wulaƙanta masa rayuwa, ƙarshe yaron ya zama ɗan iska, saboda bai samu gatan da zai gyara masa rayuwa ba, kada mu "yan uwa, akwai ranar da zamu mutu , a gama a haɗa ka za,akaika kabari taku ɗaya na ƙafar ɗan adam za,a zana ayi ta haƙawa duk kibarka duk kaurinka a taku ɗayar nan za"a saka ka, bafa za"a ƙara maka ba, a mayar da ƙasa a rufe jama"a su juya su tafi a barka shikenan ,

Suna juyawa sun fara tafiya za,s dawo maka da ranka, """" tashi ka bisu""" ina zaka iya motsi ƙasa ta gama riƙe ka gam?" kaga mala"iku masu firgitarwa wanda girmasu bazai musultu ba,

suyi maka tambayoyi , waye ubangijinka waye annabinka ?"" idan kayi shiri babu amsa su ɗaga guduma su rotsa maka, saboda tsanin duka sai ka nutse a ƙasa har kaje ƙasa ta bakwai ƙasa tace , """fito fito munafikin Allah bazan ɓoye wanda ya saɓi ubangiji ba, """" ta bultsoka kafin ka gama fitowa ƙashinka ya gama gurgujewa , haƙarƙarinka kana dama ya ɓullo na haggu sun karairaye sun gama gutsin gutsin amma a haka za,a sake mayar da halittarka aci gaba da maka tambayoyi,

Allah ka kiyashemu ka nufemu da aikata alkairi Ameeeeeeen,,,,😭🙏🏻

***
*ZAWARCI*

*T*ana shiga ɗaki saman gado ta haye, saida ta kwanta sannan ta fara lalubar number faruk, haka ta shiga ta ƙari ringing bai ɗauka ba, sake kira tayi, shima bai ɗauka ba, saida ta tsinke sannan ya biyo kiran a karo na biyu,,,,,,,

Raihana ta ɗauka da sallama ta fara magana, bayan ya ansa ne, tace Raihana, murmushi yayi sannan yace ai na gane, ya kike?"",,,,, tace lafiya qalau, yace bakiyi maraicin mijinki ba?""",,,,, raihana tace nayi mana, yace gaskiya bakiyi ba, tace miyasa banyi ba?""",,,,, yace da kinyi aida kin kirani mana, tace ai banda number ka, yace ni na damu ke na kiraki inji lafiyarki,

raihana tace lafiya qalau komai , amma inajin babu daɗi saboda baka tare dani, dariya yayi sannan yace nima nayi missing naki sosai, nayi missing ɗin bargonki , kullum sanyi baya barina ina bacci , raihana tace kai nima duk haka nakeji, yace da gaske?"",,,, raihana tace sosai ma, yace to kina so na?"",,,, bata bashi ansa ba taji an banko ƙofa da ƙarfin tsiya,

da sauri ta miƙe gabanta ya fara faɗuwa don ganin wanda ta shigo ɗakin, tabar wayar a saman gado shi kuma sai fama hello yake, lallai wato har kin samu matsayin da Faruk zai ajiyeki a gidan nan ne?""",,,, gaban faruk ya faɗi jin muryar momy, raihana yaji tana cewa Momy sannu da zuwa, momy tace sannu da zuwan uwaki,

Kinxo kin wani bi gado kin lafe kin samu gidan gayu uwarki na gidan haya, hada wani kwanciya saman gado da uwar wa kike wayane?""",,,,, cikin ladabi raihana tace da faruk, momy tace umm lallai, to miyake cewa?""",,,, raihana tace yace ina lafiya?"",,,,, nace lafiya qalau nake, sai yace mi?"",,, raihana tace sai kikax xo ,momy tace to kira man banzan inji,

saboda ke harsai an taso man ɗiya daga gidan aure?"",,, wato ke kina ɗakikin ki kin zauna ki samu lada, ni kuma ɗiyata taxo ta samu zunibi ki shiga aljanna tawa taje gidan wuta, raihana tace momy kiyi haƙuri don Allah,

tsaki tayi sannan tace to bani wayar dan ubanki, ni nama barki ki aihu gidan nan?"",,,,,, bani wayar, da sauri , faruk ya kashe kiran, ita kuma ta ɗauki wayar ta miƙawa momy,

ansa tayi sannan ta duba number faruk ɗin, tace ummm lallai lifepartner ko?"",,,,, to idan na raba ku kuma ya zai koma?"",,,,raihana tayi shiru, momy ta fara zagaya ɗakin tana ɗan ɗage ɗage, wato da nace kada yayi maki lefen nan saidai yayi?""",,,,, kam kenan ba a bakin komai nake ba?"",,,,,, to wuce mu tafi dan ubanki a gidana zaki koma da zama,,,,,,,

kallo raihana tabi ta dashi sannan tace momy yace kada in fita, tsawa ta daka mata sannan tace munje dan uwarki"""",,,,,, raihana ta ɗauki hijabinta tabi bayan momy zugui zugiii, drivern momy yajasu har gidanta.........,,,,,,,,

Ajiyar zuciya faruk yayi sannan yace kai momy ta shiga rayuwar yarinyar nan mi raihana tayi mata ne?"",,,,,, lallai koma miye hafsa ce tayi munafincin amma lallai zatci ubanta wallahi,

suna isa gidan momy, bayan sun fito daga motar wata yayar momy suka gani, tace haba ni na gaji da jiranki har zan tafi nazo bakya nan, momy tace E naje inci uwar yarinyar nan, tace wace yarinya,?"""""""",,,,,,,, juyawa tayi ta nuna mata raihana, tace ina kika sako ta ita kuma?""",,,,,,,

momy tace matar Faruk ce, tunda ya auri tsinanniyar yarinyar nan baida zama lafiya, gaba ɗaya ta burkuta man hakalin ɗa, dan ubanshi har sawa nayi ya saki ɗiyar nan ashe ɗan iskan yaron nan bai saketa ba,

waisai ya rubutu kiyi haƙuri raihana ki zauna a gida idan komai ya daidata zan dawo dake, tana maganar tana taɓe baki ne, yayar tace haka ne?"",,,,,, momy tace E, tace ki rufa ma kanki asiri kada ki kuskura ki shiga rayuwar ma"aurata idan har kikace wannan halin zakiyi haƙiƙa rabo dai aikaki lahira,,,,,,

Cikin bala"i momy tace ai nice rabo kuma saina raba wannan ɗan iskan aure, yarinya tabi man ɗa ta kanannaɗe kamar masifa, duka auren wata biyu da satittika amma har idan baiyi waya da ita ba, zai taso ma ɗiya daga gidan aure takai mata waya, saboda ya raina nasu auren,

da nayi mashi magana nace duk ina masu gadi bazaice sukai wayar ba?"",,,, sai yace wai kada suje su gane mashi mata, sai ita hafsat da mijinta baya kishinta?"",,,,,, to wata biyu kenan, ina ga tayi shekara ko ta aihu?""",,,,,

Yayar momy tace keda ba ruwanki faruk kuma ba ƙalle bane, mata nawa ya aura?"",,,,, ke zaki nuna mashi matar data dace dashi?""",,,,,,,,tunda ya auri wannan ki barshi kiyi mashi uziri, da kanshi zai saketa dan wannan yarinyar ni na bata wata huɗu badai faruku ba?"",,,,,, hmmm dan Allah ki barta, momy tace to wallahi saidai in kaita gidan uwarta can idan ya dawo zai saketa,

Tace kedai barta ta koma gidanta, momy cikin bala"i tace gidanta?"",,,,, harma gidan ya zama nata kenan?"",,,,,,, yayarta tace towai ke wannan masifar duk ta miye?"",,,,,, momy tace koma ta miye wallahi yau gidansu zata kwana, aje can ayi wanka a bayin tsakar gida,

da safe abinda za,aci ma sai yayi wahala, aje kwana biyi baza,asha AC ba, ɗakin uwarki ko fanka babu, bare ledar tsakar ɗaki wallahi bansan ki, bako wani dalili yasa bana kaunarki ba, saboda kawai ina ganin zaki rabani da ɗana, dan na tsani auren zawara, saboda idan ta kama namuji batai mashi sauƙi,

da yana da mata nasan kila yanxun da kinyi waje da ita, wuce mu tafi dan ubanki, yaya momy tana mata magana amma ina, tace wallahi sai raihana ta kwana gidansu, haka ta tasa ƙeyarta suka shiga mota gar ƙofar gidansi takaita, tace a fita yau akwana cikin sauro, haka raihana ta fita jiki a sanyaye, sannan momy ta wurga mata wayarta,

Su momy najan motarsu raihana taga gwaggo tsaye gabanta, wata irin dariya gwaggo tayi tare da tafa hannu, tace an ƙara dawowa?"",,,,,,, ai na gaya maki babu ke babu zaman aure, "ya"ya masu gata ma basu tafi gidan kuɗi ba sai ke?"",,,, ke a suwa?"",,,,,,, dariya ta ƙarayi sosai sannan tace gidan kuɗi sai masu matsayi , ta ɗaga hannunta tayi ma raihana dakkuwa, ta wuce tana dariya,

duƙawa raihana tayi ta ɗauki wayarta ta shige cikin gida, tana shiga wayarta ta fara ringing, Faruk ne, tsaki tayi bata ɗauki wayar ba, wani kiran ya sake shigowa, bata ɗauka ba, Umma dake ɗaki tace waye?""",,,,, raihana kamar jira take ayi magana ta fashe da kuka, umma da sauri ta fito daga ɗaki tana tambayar lafiya?""",,,,,,,,, ashe gwaggo biyowa tayi ta laɓe, raihana tace umma na gaji nidai wannan auren na haƙura dashi kamar kaina farau uwar miji?""",,,,, kullum da abinda zatace nayi mata?"",,,,,,,, uma tace kiyi haƙuri, ɗauki wayarki ana kiranki,

raihana tace bazan ɗauka ba umma faruk ne, umma tace to miye yayi maki?"" wannan laifin ai ba nashi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login