Showing 63001 words to 66000 words out of 98315 words

Chapter 22 - ZAWARCI

06 Oct 2024

8037

a kofi ko alewa babu bare sugar, sannan ta bawa raihana taɓe ɗaya tace tasha kokon zata samu kuzari, niko nace tasha dai wahala koko da taɓe ai baya maganin yunwa,

A ɓangaren faruk kuma yana cikin damuwa sosai, tunaninshi ta ina zai fara ma lamarin?"" lallai zaije ya ɗauki raihana ya sake mata wurin zama, wata zuciyar kuma tana hani ga shawarar shi, yayi haƙuri dai ya sassauto da zuciyar mahaifiyarsa dan tunda bata santa ko ta dawo gidanshi lallai zaman doya da manja zasu ci gaba dayi,

Wayarta ya ɗauko da yaji tana ta kuka, dubawa yayi dan ganin mai kiranta, abinda yaga an sa, babbar ƙawa, taɓe baki yayi sannan ya maida wayar ya ajiye, wani kiran ne ya sake shigowa, amma faruk bai ɗauka ba, haka tayi ta kira har ta gaji ta daina wahalar da kanta,

Gwaggo ce ta shigo cikin gidansu raihana bankam bankam babu ko sallama , ta fara cewa fatima ashe kuma raihana aure ya mutu?"" kam ai dama ina ganin gidan nan nasan ba wurin zamanta bane, gidan "yan gayu haka?"" mutum da kuɗinsa?"" a duniya yayi fice haba nace ina shi ina ɗiyar gidan mai wankin takalmi,..??

Ai kema fatima kinyi wauta, saboda tsabagen san abun duniya kika bayar da "yarki gidan kuɗi to gata nan anci uwarta ansha ruwan kanwa,

daga umma har raihana babu wanda yayi ma gwaggo magana, haka tayi ta wulaƙancinta, da ɓatanci tana dariya kanajin dariyar kasan dancin rai akeyinta,

ran raihana ya gama ɓaci dan haka tace, idan an sakoni miye damuwarki?"" ai kema inace da baba ya aureki aurenki bakwai, kuma duk inda aka sakeki baƙin halinki da mugunta yasa ake sakinki, da kika auri baba shima haka yayi ta haɗiyar gubarki saida kika kashe shi kika zauna lafiya,

Gwaggo tace kam bura"ube?"" keni dan uwarki?"" dan kunga kun samu gidan haya ba"a tasheku ba?"" lallai zaki san na iya sharri yau ɗin nan sai kunbar gidan nan sannan kuma dan ubanki hukuma zata rabank dake, tana faɗin haka tayi waje da gudu tana ihu,

gwaggo na fita Umma ta kalli raihana tace ke waye ya faɗa maki tayi aure aure ?"" raihana tace Umma gani nayi zata man wulaƙaci, ai baba yace zawarace ita ya aureta, umma tace to sai yace maki auren ta bakwai?"" raihana tace dan taji yanda naji a zuciyata,

umma tace tunda shi mutum ɗan sharrine ai saika kiyayeshi, raihana tace to Umma ai maganar ta fito bazata koma ba, saidai a tari gaba,


gwaggo na fita, bata shace ko ina ba, sai gidan wanda ya bawa su raihana hayar , gida, tana zuwa ta fashe da kuka, wai ta tadda suna shawara zasu siyar da gidan su gudu, shima yana ji hankalinshi ya tashi gwaggo tace idan ƙaryane yazo suje, haka gwaggo ta tattagoshi yana biye bayanta ita kuma tana gama zungum zungumm buzum buzum har gidan su raihana,

shi kaɗai yayi sallama amma gwaggo batayi sallama ba, bayan sun shiga suka gaisa da umma, sannan yace miyasa zaku siyawarwa daka tsalle da gida?"" umms tace ranka ya daɗe muda akayi ma halakci ya zamuyi mu zama butulu?"" gwaggo tace wallahi a gaban idon ka take maka daɗin baki ka tashe ta kafin a yaudare ka, yace a,a ku saurara ba haka akeyi ba, ke fatima na barmaki gidan nan bisa amana idan kika cuceni ubangiji yana kallonki zaiman sakayya, Umma tace ni kuma zaka sameni mai amana,

Yace ina kyautata maki zato amma kinsan shi mutum canjawa yake, umma tace bana ɗaya daga cikin masu irin halin nan insha Allah, to babu damuwa yace sannan ya fita daga gidan,

raihana ta kalli inda gwaggo take sannan ta ƙalƙale da dariya, tace don Allah ya kikaji?"" kai andai ji kunya, kukan kura gwaggo tayi taje ta haye kan raihana tayi ta dukanta, saida ta gaji dan kanta ta barta, dariya raihana tayi sannan tace kiyi wannan itace damarki dan wallahi wata rana da kuɗi aka haɗaki ki dakeni baki iyawa,

Gwaggo tace shegiya a haka dai za"a balbaɗe an rasa mai aure kullum kayanki na saman kai saboda baki zannuwa, raihana tace tunda dai ke mai baƙin hali kƙa zaunu nima sai an samu wanda zai zaunu dani insha Allah,

wata tukunyar ƙasarsu gwaggo ta ɗauko ƙaton dutse ta rufasa ta ruwan cikin suka fito bull bull gwaggo tayi waje tana cewa sai kin rasa ubanda zai aureki,

raihana ta ɗaga muryata tana cewa haka kike cewa kullum kuma Allah yafi ki, gwaggo na fita Umma tace Allah idan kika sake biye mata raihana saina ɓata maki rai, raihana tace Allah ya baki haƙuri uwa ta gari, ta ƙarasa maganar tana dariya,

*****

*S*atin raihana huɗu a gida, abubuwa sunci gaba da faruwa, rayuwa dai tayi mata haggunce, amma har yanxun faruk baizo ba kuma bai aiko ba, danshi yana can abubuwa sun mashi yawa, amma raihana tayi mashi tsaye a zuciya, dan duk matan da yake aure bai taɓa auren matar data hana ma zuciyarsa saƙatta irin raihana ba, yayi magana da momy amma tace ya saurarareta,

Raihana kwance a saman "yar yaɗin katifarsu tana ta tunani iri iri, kallon umma tayi sannan tace don Allah umma ki barni zanje gidan farida, umma tace gaskiya bazakije ko ina ba sai kin gama idda raihana zatayi magana umma ta dakatar da ita, sannan taci gaba da cewa kin manta ko rabuwarki da aminu haka babanki yace, to tunda bashi raye yanxun dole nima in ɗora yanda yayi maki idan kuma na sake ki satata sai ace kin zama ɗiyar mace babu kyara,

raihana tace to Allah yasa mu dace , Umma tace amin, Umma taci gaba da cewa kiyi haƙuri kada kiga kamar na matsa maki kinji?"" raihana tayi murmushin ƙarfin hali don kada Umma taga kamar wani abu, amma lallai taso taje gida gidan farida kodan ta taje ta faɗa mata damuwarta ta samu sa"ida ,

Umma kuma tashi tayi ta fita ta fara surfen wake, don yi masu alala, itama raihana tashi tayi taje inda Umma take surfe ta ansa ta fara tayata, tana surfen umma tana ɗan bawa raihana labari suna firansu cikin nishaɗi amma raihana hankalinta ba"a wurin yake ba,

Faruk zaune a gaban momy sai haƙuri yake bata maganar raihana amma momy tayi kunnen uwar shigiya dashi, wata ƙanwarshi ta shigo cikin farlon, inda faruk yake zaune taje ta zauna ganin yayanta yana hawaye yasa taji tausayinsa, kallonshi tayi sannan tace Yaya kayi haƙuri nidai ina bayanka, kuma ina tare dakai dan halin momy ni kaina ya fara bani tsoro,

gamu ta tattaramu a gida ta ajiye bansan wannan dalili nata ba, kullum tsohon mijina sai yaxo biko amma momy tace bazan koma ba, to wallahi nidai na gaji dan haka ina neman alfarma ka ɗaura man aure in koma gidan mijina in rufa ma kaina asiri dan ni zamana da momy yasa na fuskanci rayuwa, lallai duk abinda ka wuce ka wuce shi idan har ka wuce zaman gida toya wuce a wurinka idan kuwa ka dawo dole kaga abinda baka so,

Momy dake zaune saman kujera ta hakince kallon faruk tayi sannan tace wato ina nema maku matsayi a rayuwarku bakwa gani ko?"" ke kuma kike maganar wannan sakaran kije dan uban uwarki kice mashi yaxo ya mayar dake, tattaro ma sauran "yan uwan naki inji mai iya zama dani inji mai san zuwa gidan aure ta faɗa man,

Tashi tayi taje ta tattaro su rankatakafff duk suka haɗu a farlo, bayan kowa ya hallara momy ta fara da cewa, ba wani abu yasa na taraku ba, inaso ku faɗa man shin kuma duk ra"ayinku ɗaya da hafsat?"""

"yar hayani ta fara tashi kowa sai gunguni yake, faruk dake zaune gefe ya kallesu kowa yayi shiru sakamakon kallonsu da yayi, sannan yace ba surutu akace kuyi ba, cewa akayi su waye suke so su koma a gidan aurensu?

Hafsat tace yaya ni, kallonta yayi sannan yace to kinsan kina san mijinki miye yasa kika dawo?"" hafsat tace yaya momy ce idan na kawo mata shawara sai tayi ta bayar da shawarar banza idan na faɗa mata halin da nake ciki a gidan aure maimakon ta bani mafita sai ta ɗora shawara marar ɗorewa,

Daga baya ni kuma nayo fushi na taho ita kuma ta murje auren, Faruk yace to ai laifinki ne, ace ku duk abinda mazajenku sukai maku dole dole sai kunxo kun faɗa wa iyayenku, kinga ke yanxun abin ya wuce a wurinki kina so ki koma gdan aurenki amma ita tace baza ta koma ba,

su iyaye ba komai ake faɗa masu ba, kin fahimta?"" sai kixo kijawa mijinki baƙin jini a gidanku dole wani abun sai kinɗan riƙa ragewa idan marinki yayi sai kice faɗa yayi maki, dansu iyaye duk abinda kayi ma ɗansu yana nan ya tsaya masu arai basa mantawa,

Muma mazan haka ya kamata bawak duk abinda mace tayi maka ka kwashe kaje kayi ta yamaɗiɗi dashi, dole ita rayuwa wani abun saika rage, ciki badan abinci kawai kayi shi ba, wani abun ko ƙawa ko "ya"ya ko iyaye dole wani abun kasan maganar da zaka riƙa faɗa,

kuma shima mijin naki ko a gidanku akayi maki wani bai kamata kije kiyi ta faɗa, saboda yau da gobe, kila kuma a wurin mijin naki bake ɗaya bace, ita rayuwa komai yana san sirri,

Hafsat tace to nidai yaya tunda anyi haka gaskiya momy tayi haƙuri in koma godan mijina, ita kuma zainab dama yaji tayo, amina kuma ta samu wani mijin sai mu tattara mu koma,

Dan an fara mana surutai a familynmu wai bama zama aure mu ukku muna *zawarci* ga ɗaya bata samu mijin aure ba, murmushi faruk yayi sannan ya kalli momy yace muna baki haƙuri,

Momy tace to ba komai, zainab Amina hafsat duk kuje gidan aurenku amma ku sani ko zaku mutu koma miye kada wanda ta dawo man na gaya maku, duk suka ce sun yadda, momy tace to Allah ya bada sa"a, faruk yace amin a daidai lokacin dayake miƙewa tsaye,

momy tace kai kuma zauna ina san magana dakai, dawowa yayi ya zauna, su kuma duk suka tashi suka fita daga farlon, gyara zama momy tayi sannan ta fuskanci faruk sosai, shi kuma ya sauke kansa ƙasa,

momy tace kai kuma maganar aurenka fa?"" faruk yace ban samu wanda zan aura ba, momy tace to kai kuma cikin matan daka saki wace ce kake so?"" faruk cikin ladabi yace duk wanda kika zaɓar man, tace to jeƙa zanyi nazari, faruk yace to ngd, miƙewa yayi yabar farlon,

bayan ya fita momy ta tattaro ƙannen faruk , tana neman shawarar su, wace ce matar da tafi dacewa ya dawo da ita?"" hafsat tace momy yaya ya wuce a zaɓar masa atar aure don haka ki barshi da nashi ra"ayin don Allah,

idan mune haka ta kasance kanmu momy baza kiji daɗi ba, kinsa ma yaya ra"ayi auri saki, saboda yana da kuɗi , momy baki tunanin alhaki yasa shi yaci baya?"" kinsan ma ɗaukar alhaki yana sa mutum yaci baya a rayuwa, tunda Allah yasa ya auri wannan kuma hankalinshi ya natsu da ita, ki barshi , idan ma tana da wani hali zai saita ta, tunda kinsan baya san sakarci, ajiyar zuciya momy tayi sannan tace tunda kun haɗe man kai ai sai kuje kuyi duk abinda kuka dama, dariya hafsat tayi sannan itama ta tashi tabar farlon sai momy kaɗai tayi ta nazari iri iri,


****

*B*ayan sati biyu aka ɗaura auren hafsat da tsohon mijinta, zainab kuma ta koma gidan mijinta da tayo yaji, Amina kuma da sabon mijin data samu, sai auta kawai aka bari a gidan, ansha shagali sosai ba zaka ga bikin ba, kace bikin *zawaru* bane, momy tayi farin cikin ganin duk kowa ya tafi ɗakin mijinta,

amma taja masu kunne sosai cewa babu yaji kuma duk wanda ta kuskura aka saketa saidai tasan gidan da zataje, suma sunci ɗamara zama daram a gidan mazajensu,

dan sun gane duk arxikin ka duk mulkinka komai kake dashi idan dai baka da aure to lallai kai hotone, duk girman ka idan baka da darajar aure , sai kiga ko shawara da babu mai saurarenki amma idan ƙanwarki tana da aure ita sai ayi da ita, to lalƙai saidai anyi haƙuri a gidan aure,

***

*R*aihana ce, tsaye a bakin ƙofar ɗakinsu tana ta haɗa umma da Allah ta barta wallahi baza ta daɗe ba idan taje, umma tace babu idan zataje saita gama idda, raihana taci gaba da magiya amma fur umma tace babu inda zataje, raihana tace don Allah umma ki barni naje, umma tace zancen kike so daga nan bata sake magana ba, taci gaba da hidimar gabanta,

momy tasa anxo anguwar su raihana an bincike mata halin raihana kafff, halinta da ɗabi"un ta, sannan kuma bugu da ƙari an faɗa mata cewa ba karuwa bace, sannan kuma ta tambayi abinda ya rabota da gidan mijinta, shima anyi mata bayani, momy taji natsuwa amma wuri ɗaya hankalinta ya tashi saboda ance mata auren dole akai mata, bata san mijin, to lallai irin abun zai faru da ɗanta,

Dan lallai ta lura faruk yana san raihana amma ita tana sanshi?"" lallai tana sanshi saboda tayi kuka a gabanta kada ya saketa, to anya ba kuɗinsa take so ba,?"" kamar yanda akace mata ita alashe morny ce, shin idan ma wace ce ita duk haɗamarsu da zalamarsu lallai sunci su barshi,

wayarta ta ɗauko tana san kiran faruk danshi ɗa ne mai ladabi a wurinta duk yanda yake san abu idan bata so baya so, bara ta kirashi lallai idan raihana zata yadda kawai yaje ya dawo da ita,

kiranshi tayi sannan ta yaje idan wannan yarinyar zata iya zama dashi ya dawo da ita, amma lallai yayi ƙoƙari ya cusa mata sanshi a zuciyarshi., faruk yayi godiya, sannan ya kashe wayarshi,

yana kashe wayar yace Yeeeeee, yana ɗan rawa, a bayyane ya fara magana yace momysco ai da haƙurina ya kusa ƙarewa, nayi haƙuri don dama bana so in dawo da ita ta fuskanci matsaloli, amma tunda kin bayar da goyon baya nasan ta yanda zan juyo ma lamarin, .....................,

Raihana sai wani kuka take wai ita a dole zaman gidan nan ya isheta, umma ta rufa mata asiri ta barta don Allah ta ɗanje ta rage rana gidan farida, Umma tace daga yau idan kika sake man maganar zuwa wani wuri haƙiƙa ranki sai ya ɓaci, waike a kanki aka fara zawarci ne?""" kiyi haƙuri ki zauna a inda Allah ya ajiyeki wata rana sai labari amma sai kije kiyi ta raɓe raɓe akan mi?"" wani irin ihu raihana ta saki da gudu umma ta ɗauko icce zata ƙwaɗa mata, da sauri ta miƙe tayi cikin ɗaki da gudu ta kullo ƙofar, umma tace idan dai wannan halin kike so dani dake a gidan mu zuba, raihana dai tana ɗaki sai ihu take, wai ita an kamata an ƙunƙume ta a gida taya za"asan tana zawarci harma a fara santa?"""

Abun yaso ya ba Umma dariya amma ta basar, raihana taci gaba da cewa ai sai a bari inyi gayu na in tafi ko wani ya ganni yaxo ya aure ni, Umma tace duk inda bawa yake haƙiƙa rabonsa yana binsa, koki fita ko kada ki fita lallai idan Allah ya ƙadda aurenki bayan gama idda sai kinyi shi, daga ɗaki raihana tace wancan zama bana shekar kusan huɗu ina gida babu wasu mazan kirki kowa kame kamene , umma tace ke kin isa ki kawo ma kanki na kirki?"" kiyi haƙuri ki samu natsuwa sai kiyi ta addu"a, don zaɓin Allah yafi na kowa, kuma shi aure lokaci ne dashi, raihana idan kikaji jarabawa da wasu suke ciki sai kinji ke a aljanna kike, duk abinda yayi tsanani sauƙi yana zuwa, kiyi haƙuri kuma ki zama mai haƙuri da jarabta, wata ma tunda take bata taɓa aure ba, kuma tana so kamar ta jawo namijin tace ya aureta don Allah, wata kuma har taxo duniyar ta koma batayi auren ba,

wasu ma sai ansa ranar aurensu su mutu, wasu su mutu ranar aure wasu ranar walima, raihana kar ki bari zuciya ta tunxuraki kiyi abinda zakixo kina dana sani wata rana,

tsaki raihana tayi sannan tace banma kara auren bare a sakeni , umma tace ai wanda ya halicceki yana jinki, maza ma ki tuba tun kafin mala"iku su amsa da amin, wayyo Allahana raihana tace, tana istigifari,

Cikin kuka take cewa Allah ka yafe man idan wani laifi nayi maka ya ubangiji ka yaye man, ka bani haƙuri akan wannan jarabta ya Allah ka haɗani da mijin dazai riƙeni bisa gaskiya da amana, Allah ka tsallakeni daga sharrin uwar miji, yiiiiii yinnnnn yiiiii wayyyoooo hummmmmm haka take ta ihu kamar taɓaɓɓiya, Umma dake zaune a tsakar gida tausayi raihana ta bata, itama addu"a take tayata, lallai idan ka wuce abu ka wuce shi, haƙiƙa zaman gida bashi da daɗi ,

yinin ranar nan raihana kuka ta yini yi har muryarta ta daina fita saboda hitina,

***
Da safe haka raihana ta tashi fuskarta tayi suntum, umma ta kalleta sannan tace raihana jiya fa k"b yaxo yaji labarin aurenki ya mutu yaxo zawarci kuma,

raihana tace ɗan iska aini na gama dashi, shege macuci mai cutar sida, umma dai batayi magana ba, raihana ta kalli umma sannan tace umma yaufa saura kwana ukku in gama idda, umma tace a fita lafiya, raihana tace ina gamawa gidan farida zanje umma tace wai uwarmi ake gidan faridar ne, dariha raihana tayi sannan tace umma bazaki gane bane, umma tace yazan gane ki gane ?"" ai ganewa saiku "yan makarantar boko,

Dariya raihana tayi sannan ta miƙe tabar ɗakin, umma dai tabi raihana da kallo tana fassalo abubuwa daban daban.....................,


****

*Y*au raihana tana cikin farin ciki don yau ji take kamar sallah anci uban gaye ansha kyau sosai, tana ta shiri zuwa gidan farida, wai ta gama idda, niko nace kodai ta gama hauka,

Ban kwana tayi wa umma sai ta dawo, umma tayi mata fatan alkairi, raihana aka fito waje, a ƙofar gidansu tayi tsaye tana kallon santocin cikin unguwarsu murmushi tayi sannan tayi magana ƙasa ƙasa, tace to mun dawo kuma, a daidai lokacin data ziro ƙafarta ɗaya waje, ta fara tafiya kanta yana hayaƙin *zawarci*

tayi tafiya sosai suka haɗu da gwaggo, tana ganin raihana ta bushe da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login