Showing 87001 words to 90000 words out of 98315 words
abu yarinyar nan tayi maki ki sanar da ita zata gyara don Allah,,,,
Momy tace zainab keda nake alfahari dake kema zaki kware man ba ko?"",,,, zainab dake kwance ta tashi zaune sannan ta kamo hannun momy ta riƙe,,,, tace momy kina iya faɗin mace nawa yaya ya aura ya saki?"",,, kinsan dalilin da yasa yake rabuwa dasu?""",,,,, kinsan wane irin abu suka shuka mashi?"",,,, to lamarin namiji da mace ba wani ne ya koyama kowa yanda zaiyi rayuwar aure ba,,, kowa tashi take ficceshi,,, don haka kiyi haƙuro tun kafin ki jefa ɗanki cikin wani hali,,,
hafsat dake gefe tsaye ta matso kusa da inda momy take zaune tace momy idan baki manta ba,,,,,,, yaya yace maki baya iya rayuwa da macen da bata san kanta ba, kuma tsanani idan ya daɗe da mace wata biyu ne,,,,ya korata ya kawo wata,,, wata macen ma bata sati ukku a gidanshi,, amma ita wannan gata tayi kusan wata takwai mi kika fahimta game da zamansu?"",,,,,,
Zainab tace aunty hafsa mata wane iri ne yaya bai gani ba?"",,,, kuma tunda yake aure bai taɓa auro sakarar mace ba,,, mata masu aji ya auro wa,,,, wayayyi "yan boko wanda suka san kansu,,,,, amma babu wanda yasan abinda yasa yake rabuwa dasu,,,,,,,,, duk macen daya aura iyakarta wata ɗaya biyu tayi tsananin daɗewa,,,, to an auro mai wata takwas,,,,,,
momy tace idan na fahimceku kuna bayan ɗan uwanku, zainab tace kema kina bayan ɗanki ,, dan duk macen da yake aurowa wannan kika ɗauki ƙaran tsana kika ɗoro mata,, mi tayi maki momy?"",,,, momy tace to dan nace ta zauna nan shikenan sai abun ɓacin rai?"",,,, hafsat tace to miyasa shi ɗan naki baki ce ya kwana anan ba?"",,,, shine ɗanki shi kike iko dashi dasai kice ya kwana,,,,,,,, momy tace aiku yarana baza ku gane abinda nake nufi ba,,,, hafsat tace duk mun fahimceki amma yau kibar miji da mata su kasance tare,,,,,, momy tace aisai yaxo ya ɗauketa,,,,, da hafsat da zainab sukayi dariya,,,,, momy tashi tayi ta fita dan duk "ya"yanta su kware mata baya,,,,,,,
bayan ta fitane,,,, hafsat ta kalli inda raihana take zaune sannan tace matar yaya,,,, wai miyasa kika firgita mana yayanmu ne?"",,,,, zainab tace haba keko ƙanwar miji miyasa kike wannan tambayar?"",,,,dariya sukayi suka kashe amma raihana ko inda suke bata kalla ba,,,,,,,, hafsat tace gaskiya yarinya Allah ya baki sa"ar rayuwa, dan yayanmu jarumin namiji ne ba ko wace gajalar mace zata iya kamashi ba,,,,,, mudai fatanmu Allah yasa ki zama mai adalci,,,,,, zainab tace amin,,,,,
da daddare da faruk yaxo dubasu ya ɗan daɗe sosai , suna fira da momy amma duka babu wanda ya saka baki a cikin maganarsu,,, dan dama idan momy tana magana da faruk bbu mai cewa tuff harsai ya tafi sannan zasu samun bakin magana,,,,
haka suka gama firarsu sannan ya miƙe yayi masu saida safe,,,, inda raihana take zaune ya kalla sannan yace "yan mata zan tafi,,, raihana tace sai da safe,,,,, yace yawwa,,,, harya kusa fita daga ɗakin ya juyo yace raihana babu rakiya?"",,,,, momy tabisu da kallo su duka biyun,,,, ita dai raihana batayi magana ba,,,, faruk yace dake nake,,,, tayi shiru,,,, yace zo kiji,,,,, raihana dai batayi magana ba kuma bata tashi ba,,,,,, momy tace tashi kije,,,,, raihana ta kalli momy ,,,,, kai momy ta ɗaga sanna tace jeki, saida safe,,,, faruk dake tsaye yace momy saida safe kika ce?"",,,,,,,
tace Eh,,,,, kaga yau sai kayi bacci,,, subahanallah inji faruk da sauri ya fice daga ɗakin,,, dariya momy tayi sannan tace raihana jeki,,,,,, kunya ta hana raihana tashi momy tayi juyin duniya amma raihana tace ita anan zata kwana,,,, hafsat tace ke tashi ki tafi kinji ,,,,, raihana tace ita dai A, a, momy da kanta ta tashi ta isa inda raihana ke zaune ta kama hannunta taja ta suka fita daga ɗakin......
tana fita hannun raihana na riƙe hannunta ta fara kiran wayar faruk tace ya tsaya tana zuwa,,,,, momy na fita daga ɗaki da zainab da hafsat suka sheƙe da dariya sannan suka kashe,,,, zainab tace momy taji ance jiya ɗanta baiyi bacci,,,, haka da sukayi ta shaƙiyanci,,,,,,
itako momy har wurin mota takai raihana da kanta ta buɗe motar ta tura ta ciki,, sannan ta rufe,,,, ta juya ta tafi,,,,,, faruk bai tafi ba yabi momy da kallo harta ɓace,,,,, sannan ya maido dubanshi ga raihana yace waye yace ma momy banyi bacci ba?"",,,, raihana tace kana tunanin nice zan faɗane?"",,,, lakatar mata hanci yayi sannan yace nidai ba ruwana a daidai lokacin da yake fara tafiya da mota,,,,,
Momy kuma tana tahowa wuri ta samu tasha kukanta sosai wanda ita kanta bata san dalilin yanshi ba,,, saida ta gama kukanta sannan tace Allahidan yarinyar nan alkairi ce a rayuwar umar Allah kasa man ƙaunarta cikin raina, idan tana da wata manufa ta daban Allah ka ankarar da umar ya gane,,,, ya rabu da ita,,, uhum niko nace ga abinda ya kamata kiyi tun farko,,,,,,
Huhuuuuuu suko masoya sun samu yanda ake so,,,,, suna zuwa masauki raihan da sauri ta cire kayan jikinta ta tafi wanka,,,, faruk shima towel ya ɗauka ya bayanta toilet ɗin yana cewa nima banyi wankan ba,,,,,, bayan sun fito daga wankan ne faruk yake ta dariya ,,, raihana kuma duk ta hayaƙa,,,,,, sai nunawa yake yanda take zama a gaban momy da yanda take magana,,, sai dariya yake mata,,,,, ita kuma tayi banza ta ƙaleshi,,,,,, kwanciya yayi saman gado sanann yace haka kike yin magana,,,,, fa,,,, ya fara kwaikwayon maganar ta,,, yanda yayi abun ne ya bata dariya dan babu banbanci da maganarta,,,, kallonshi sannan itama tace kaima ai haka kake yi itama ta fara nuna yanda yake a gaban momy da sauri ya sauko daga saman gado yana cewa waishi abonki wasanta ne?"",,,, tana dariya tayi farlo da gudu shima binta yayi suna shiga farlo suka fara tsera, faruk ya kasa kamata,, haka tayi ta wanashi yayi ya kamata ya kasa,,,, da yazo zai kamata saida ta zuƙe tayi dariya,,, haka tayi ta wahalar dashi daga baya ya gaji ya koma ɗaki,,,, tabishi tana mashi gwalo yace zan kamaki,,,,, tace an faɗa maka kama raihan abu mai sauƙi ne?"",,,,, dariya yayi yana sauke numfashi, kallonta yayi sannan ya miƙa hannunshi alamar ta taho,,,,,, haka ta matsa ta haye saman gadon a sikwane,,,, dariya yayi yace momy tace wai yau inyi bacci, wai ya akayi tasan nace jiya banyi bacci ba?"",,,, raihana tace yo O,,,,, babu damar tace zainab ta faɗa kada ta haɗashi da "yar uwarshi dan bata san yanda zai ɗauki maganar ba,,,,
kallon raihana yayi sannan yace wallahi kinji yanda naji kunya?"",,,,,, raihana tace nifa?"",,, nima naji wallahi yace yanxun ko bamuyi komai ba, zatayi tunanin muna yi ko?"",,,, harar wasa tayi mashi yanda tayi abun ne ya bashi dariya,,,, yace da gaske ne mana,,,,, ko masu karatu ai haka zasuce,,, jawota yayi a jikinshi sannan yace muyi baccinmu babu ruwanmu ko?"",,, ranar dai faruk ya kwana cikin farin ciki gashi ga raihana.........
***
*S*atin su raihana ɗaya amma ita dai tace gida zata tafi,,,, faruk yace ta bari su tafi tare da su momy amma taƙiya,,,, shima baida yanda zaiyi ya haƙura zasu tafi tare,,,,,,
bayan sunje asibiti ne,,,, faruk yace ma momy gobe zasu wuce idan Allah ya kaimu,,, tace baza ka bari sai jibi mu tafi tare ba?"",,,,, faruk ya sosa kanshi sannan ya kalli raihana,,,,, itama momy raihana ta kalla tace ku bari jibi mu tafi baki ɗaya,,, raihana tace ai dama shine yace zamu tafi gobe,,,, kallonta faruk yayi ita kuma murmushi tayi,,,, a ranta kuma tace ni zan faɗa masu saboda ni za, a tafi gobe?"",,, kuma tace ina juya mata ɗa?"",,,,,
Momy tace to kuyi haƙuri duƙanmu mu tafi jibin mana,,,, faruk yace momy da gobe da jibi duk ɗayane a wurin Allah mu tafi goben kawai,,,, zainab tace ni wallahi zaman nan yaya ya isheni,,, mony tace to Allah yasa rayuwarmu takai goben,,, gaba ɗaya sukace amin,
bayan sun fito ne, faruk yace waike saurin mi kike tafiya ne?"",,,,, raihana tace nidai ummana nake so na gani ,,,,, faruk yace ni baki so ki kasance tare dani ne?"",,,, raihana tace aikai kullum ina tare dakai,,,, na daɗe banga ummana ba,,,,, faruk yace to ai dani dake zamuje ko?"",,,,, raihana tace abinda cewa kake baka da lokaci ?"",,,, faruk yayi murmushi sannan yace yanxun ina dashi,,,,, a mota suke tafiya suna fira raihana tace wai yaushe zaka bani labari ne?"........................
[1/8, 9:46 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 4⃣6⃣
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
**
*D*aure fuska yayi sannan yace wai miyasa kin matsa man ne?"""",,,, raihana tace kawai faɗa man zakayi fa,,,, yace to miye amfanin in faɗa maki ?"",,,,, raihana tace saboda inaso inji kawai,,,, kallonta yayi sannan yace kina shiga rayuwata da yawa,,,, aure auren da nayi raihan sirri ne tsakanin nida zuciyata,, rayuwatace don Allah ki janye kudirin sai kinji ,,
Raihana tace niko babu abinda zan iya ɓoye maka,,, dan inajinka sosai a rayuwata,,, amma tunda baka so daga yau bazan sake maka maganar ba,,, kayi haƙuri,,,, yace kema Allah ya baki haƙuri dan naga kin ɗau zafi,,, bawai naƙi faɗa maki ba,,, ina tsoron idan na faɗi maki abun kamar zai zama matsala ne,,,, raihana tace kada kaji komai ka faɗi man kai tsaye ina tare dake,,,,
Faruk yace kinyi alƙawari?"",,,, raihana tace nayi alƙawari,,,, dariya yayi sannan yaɗanyi wata "yar rawa kana ganin rawar kasan ta sheganta ka ce,,, yace soyayya ke nabai dukkan kaina haƙiƙa babu laulayi kin zauna, yan mata karda ma ku raɓo guna ba sauran gurin da zani baku ku zauna, a raina ke kaɗai nasa kinkai kwance ki huta babu wanda zaizo sashenki,,, dariya raihana tayi sosai sannan tace ashe ka iya waƙa?"",,, shima dariya yayi sannan yace kinsan hausawa sunce daɗin aure kesa mata tace miji baba,,, to duk mulkin namiji duk sarautarshi duk isarshi duk wani tunƙahonshi idan yana gaban mace sororo ne,,, dariya raihana tayi tace lallai kam, haka dai sukaci gaba da fira har suka iso masauki,,,,,
***
*S*u raihana da momy da zainab da hafsat da faruk gaba ɗayansu a gidan nasir danyi masu bankwana,,, momy tayi godiya nasir yace haba ai duk abinda nayi maku momy ban biya ba,,,,, momy tace suna dai godiya duk da hakanan,,, sa,adatu tace don Allah kada su tafi basu ci abinci ba,,,, faruk ne yayi magana cikin sigar wasa,,,, dan idan raihana tana gaban momy dariya take bashi,,,, yace sa,a,, a bawa aciciya taci,,,, hararshi tayi tare da murguɗa mashi baki,,, amma batayi magana ba,,,, yace na gane,,, karatun hajiyata,,,,, yana magana yana wani tsadajjen murmushi,,, momy ta kalleshi sannan ta harareshi,,,, murmushi yayi sannan ya miƙe ya fita ,,,,, momy tace ku maida hankali muci mu tafi,,,,, suka fara cin abinci amma raihana ko inda abinci yake bata kalla,,,, momy tace ke bazaki ci ba?"",,,,
Hafsat tace ya zatayi taci kin kora mata miji waje,,,,, gaba ɗaya wurin aka ɗauki dariya,,,, sa,adatu tace gaskiya ne momy,,,, miƙewa tayi tace ma raihana taso muje kinji ,,,, miƙewa raihana tayi tabi bayan sa,adatu, wani farlo suka shiga,,,,, suna shiga ta hango faruk kwance saman kujera yana waya,,,,, sa,adatu tace bara in kawo maki abincin anan,,, dan tun ranar da sukaje asibi ta kula da irin tsangwamar da suka nunawa raihana,,,
shiga raihana tayi,,,, yana ganin ta shigo ya tashi zaune,,,, da sauri ta isa wurinshi ta zauna kusa dashi,,,, saida ya gama wayar sannan ya kai hannunshi wurin cikin ta ya fara shafawa,,,, yace har kinci abincin ne?"",,,, raihana tace A,a yace baki ci ne?"",,,, tace na ƙoshi,,, yace mi kikaci ne?"",,,,, batayi magana ba, sa,adatu ta shigo da abinci,,,,, faruk yace mun gode pha,,,, tace to ranka ya daɗe,,,, sannan ta fita daga ɗakin,,,,
Tana fita faruk yace miƙo muci kada momy tace mun ɓata lokaci,,,, ɗaukar abincin tayi ta miƙa mashi,,,, bayan ya ansa ne,,,, ya fara bata,,,,, saida ta ƙoshi sannan yaɗan ci kaɗan,,, bayan ya gama ne ya miƙe yana gyara belt ɗin ƙugunshi, saida ya gama yace muje,,, miƙewa tayi yace zo kiji wata magana,,, kusa dashi ta matsa yayi mata raɗa a kunnen ta,, baki ta saki tana kallonshi yace wallahi,,, raihana tace nidai ba ruwana,,, yace nidai da ruwana zatayi magana yace keko sai kowa ya gane karatun ?"",,,, muje muje,, duƙawa yayi ya ɗauki ruwa yayi waje da sauri itama bayanshi tabi da sauri,,,
Lokacin da suka fita harsu momy sun shige mota,,, bankwana sukai da sa,adatu ,,, sa,adatu tace sai nazo insha Allah,,,, dan tana so ta bawa raihana wani abu amma baya yuwuwa haka ta haƙura,,, raihana tace to Allah ya kawoki lafiya tace amin,,,,,
Tayi ma raihana rakiya har wurin mota,,, faruk ya shiga gaba , su kuma su hafsat fitowa sukayi aka sake shirin zaman motar,,,,, bayan raihana ta shiga suma duk suka shige, har suka tafi sa,adatu tana ɗaga masu hannu,,,,
Basu daɗe da fara tafiya ba,,, faruk ya fara kallon raihana ta cikin madubin gaban mota,,,, ta duƙar da kanta,,, shi kuma ya tsira ma wurin ido, tana ɗago kanta suka sake haɗa ido idanuwan shi ya buɗe duka, sannan ya fara lunshe su a hankali murmushi raihana tayi ta sauke kanta tana kallon ƙasa,,,,, murmushi yayi a daidai lokacin data sake kallon wurin,,,, da kanshi yayi mata alama da kada ta sake ɗauke fuskarta,,, duk abinda suke momy tana kallonsu haka su hafsat,,,,, murmushi yayi sannan ya ɗaga mata gira ɗaya,,, sai a lokacin idon shi yakai inda momy ke kallonshi,,,, da sauri ya ɗauke kanshi,,,, yace ma nasir wai yaushe zaka dawo ne?"" yana maganar cikin kame kame ne,,,,, nasir yace insha Allah bada daɗewa ba,,, faruk yace Allah ya nuna mana,,,,,
haka sukayi ta tafiyarsu har suka iso filin jirgi,,,,,, suna fita daga mota,,, momy ta raɓa tace ma hafsa kinga abinda faruk yake yi?"",,,, dariya hafsa tayi sannan tace wallahi na ganshi momy,,,, momy tace ni abinma tsoro yake bani, zainab tayi dariya sannan tace ki kwantar da hankali komai ya daina baki tsoro,,,, momy tace wallahi faruk duk ya wani susuce ko baku gani ne?"",,, shegiyar yarinya kamar aljanna duk ta firgita man ɗanɗa,,,, hafsa tace don Allah momy ki zuba masu ido,,, momy tace to aini abinma harna rasa abin cewa,,,,,
zainab ce tace momy muje,,, tafiya sukayi dukansu raihana dama ba wurinsu take ba,,,, tana can gefe ɗaya,, tunda taga uwa da "ya"yanta suna magana,, nasir yayi masu bankwana tare da addu"ar sauka lafiya sannan ya tafi, suma suka shige jirgi suka ɗaga dan dawowa gida,
Suna isowa duk da darene amma faruk cewa yayi basu kwana abuja wucewa zasuyi,,,, don haka driver yayi ma waya sun iso, babu ɓata lokaci motoci sukaxo,,,, haka suka tattara sukayo gida,,,
suna isa saida aka ajiye su momy sannan faruk ya wuce gida dashi da "yar matarshi,,, suna zuwa raihana kamar jira take su iso ta faɗa saman gado ko takalmin ƙafarta bata tsaya cirewa ba ta fara bacci,,,, shi kuma "yar laɓai wanka yayi yasha ruwan lipton , bayan ya dawo ɗakine ya cire ma raihana gyalen jikinta da takalmin ƙafarta sannan ya gyara mata kwanciyarta,, buɗe idonta tayi a gajiya ta kalli faruk murmushi sannan yace swry,, itama ɗan murmushi tayi cikin yanayin bacci sannan ta rufe idonta taci gaba da bacci,,,,, shi kuma alwallah yayi yaci gaba da sallah,,,,,
****
*T*un cikin dare raihana ke kwarara amai har da safe bata ƙaƙƙauta ba,,, duk tabi tayi luguf,,, shidai faruk baiyi mata magana ba, saidai ta wuceshi da gudu ta dawo, binta yayi da kallo amma baice mata sannu ba,,, ita ta gaji tace mashi ko sannu ma baka iya cema mutane,,, dariya yayi sannan yace to raihan cikine kin hanashi zaman lafiya daga kici wancan sai ci cusa wancan ba dole kiyi amai ba,,,
raihana tace to tun jiya mi naci don Allah?"",,,, banci komai ba,,,, yace kila kin laɓe ban sani ba kinci don kifini girma,,, raihana tayi shiru faruk yaci gaba da hayaƙa ta,,, bata sake magana ba,,, tashi tayi zata fita yace ina zaki?"",,, tace bar maka ɗakin zanyi,,,, miƙewa yayi yana cewa to mun gaji da zaman ɗaki bara mu koma farlo,,,,
Biyota yayi yaci gaba da cewa wai don Allah mi kikaci ne,,, raihana tace ban sani ba,,,, dariya yyi sannan ya fice daga farlon,,, ita kuma wuri ta samu ta zauna, bata daɗe da zama ba bacci yayi gaba da ita,,,,,
shi kuma yana fita,, gidansu ya nufa,,, dan gidanshi na yanxun daya dawo kusa da gidansu ne,,,,, bayan yaje suka gaisa da momy yayi mata ya gajiya?"",,,,, tace alhamdulillahi,,, itace tace mashi ya raihana?"",,,, yace tana can bata da lafiya,,, momy tace miya sameta ne?"",,,, faruk yace wallahi ban sani ba,,, momy tace to Allah ya sawaƙe,,, faruk yace amin har a ranshi yaji daɗi addu,ar da momy tayi ma raihana,,
Miƙewa yayi yace sai anjima, tace to insha Allah anjima zanzo in dubata,, faruk yace A, a, tace zatazo tayi maki sannu da gajiya, momy tace to sai kunxo, yace to ya fita,,,,,
yana dawowa gida,,, yaga raihana kwance tana bacci,,,, dariya sannan yace nima zan rama abinda kike man yarinya,,,, fita yayi ya samo gashin ɗawusu sannan ya dawo,,, kusa da ita ya duƙa daidai hancin ta yasa yana murzashi,,,, da sauri ta miƙe tana salati,, kallonshi tayi sannan tace kai ni ko?"",,,,
dariya yayi sannan yace kema haka kike man nima ramawa nayi, raihana tace dakyau 1/0,, yace Oho dai koma miye na rama dai,,, wucewa tayi ta nufi hanyar ɗaki,,, yace bacci zamuyi ne?"",,,, batayi magana ba,,, yace kin fasa zuwa gidan ne?"",,, juyowa tayi sannan tace yanxu?"",,,, yace E shirya zan ɗanyi wani abu kafin in gama,,,,
tace mi zakayi ne?"",,,, yace budurwata ke kirana zanje gidansu zance,, dariya raihana tayi sannan tace lallai wannan budurwa da sa,a take,, faruk yace kuma bakiga yanda take kauna na ba,,, raihana tace amma bata kaini ba ko?"",,,,, yace tafiki da inci ɗaya,,, tace to dani da ita kuma fa kai waye kafi kauna?"",,,,, yace ita..... Idanuwa raihana ta zaro sannan tace mi kace?",,,,, yace abinda kikaji haka nace,,, raihana tace to ai naga wanda zai dafa maka tea anjima, dariya yayi sannan yace ke wasa nake maki wallahi kinga kalli yana nuna mata wayar sadiq ne zanyi magana dashi,