Showing 90001 words to 93000 words out of 98315 words

Chapter 31 - ZAWARCI

06 Oct 2024

8029

kin gani ɗan latsa nakiyi,,,,,,

Batayi magana ba ta shige ciki,,, shi kuma ya fita,,,, raihana tana shiga ɗaki zama tayi a gefen gado jawo filow tayi ta ɗan ɗora kanta bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauketa,,,, shi kuma faruk har ya gama abinda yake baiji raihana ta kirashi ba, wayarta ya fara kira saidai ta ƙari ringing ta tsinke ba,a ɗauka ba, haka ya gaji da kira ya tashi ya shigo ciki,,,,

ganin raihana kwance tana bacci yasa ya shiga ciki da sauri,,,, tadata yayi sannan yace miya sameki wai?"",,,, cikin yanayin bacci tana ɗan layi ta ɓata fuska tace bacci nike ji,,,, faruk yace baki da lafiya ne?"",,,, baki ta taɓe sannan tace lafiyana kalau,,, gajiya nakeji, faruk yace to kije kiyi wankan mu tafi mana, raihana tace to, miƙewa tayi taje tayi wanka sannan ta fito,

yana nan kwance saman gado harta shirya,,,,, tace ta gama kallonta yayi sannan yace to muje, gaba tayi ya tashi yabi bayanta,,, har sun fito ne faruk ya fara laluba aljihu yana cewa shi baima ga inda ya saka makullin ba,,, raihana tace naga inda ka ajiye,,, yace to yi sauri ɗauko man,,, tace taho mu tafi tare,,, yace nidai basai naje ba,,, tace to idan baka zo saina daɗe ban dawo ba, yace naji ai zaki dawo dai ko?"",,,, da kai ta bashi ansa sannan tayi ciki,,, tana zuwa makullin yana saman gado hawa sama tayi dan ɗaukar makullin tana hawa kawai taji gadon ya mata daɗi babu abinda take buƙata sai tayi bacci,,,,

tayi kwanciyarta taci gaba da bacci,,, faruk dake zaman jiranta yaji shiru, kallon agogon hannunshi yayi sannan yayi tsaki a zuciye ya nufi ciki, yana zuwa gaya raihana kwance baccinta take hankalinta kwance, da fushi ya fizgota daga saman gadon sannan ya wanka mata mari,,, a gigice raihana tace mi nayi maka?"",,, yace dan kin mayar dani sakarai sai ki barni ina zaman jiranki kamar wani yaronki,,,, kuka raihana ta fara ta riƙe wurin da faruk ya mareta, tana kallonshi,,, yace naje na mara ko zaki rama ne?"",,,, yana maganar ne cikin nuna ɓacin rai da fushi,,,,

Cikin kuka raihana tace basai yace in taso ba,, yace idan nace ki taso inajin tsoronki kenan,, idan baki zuwa sai kice kin fasa amma saboda tsabar kin raina ni saiki barni a waje kixo kina bacci ko drivernki ne ni ai baza kiman wannan sakarcin ba, tsaki yayi ya juya yabar ɗakin da sauri raihana tasa takalminta tabi bayanshi,

Ko a mota babu wanda yayi magana haka suke tafiya kamar masu shirin kai yaƙi,,, har suka iso ƙofar tsohon gidansu faruk yayi horn mai gadi ya buɗe,,, niko nace ummm in sani "yan gayun ba,,, ita ko raihana fushi takeyi,,, tunda faruk ya mareta har yanxun bata dawo hayyacin ta ba,,, niko nace marin soja akwai zafi,

Suna shiga faruk yayi farking ya fita yayi gaba,,,, ganin baiyi mata magana ba,,, yasa itama ta buɗe motar ta fita,,, towai abinda raihana take tambayar kanta, miya dawo da umma nan gidan?"",,, kuma ya akayi gidan ya ƙara girma?"",,,, ummm haka dai taci gaba da bin faruk har suka shiga cikin gida,,,,,

A bakin ƙofar wani kayataccen farlon yayi sallama,,, daga ciki raihana taji maganar umma tana ansa sallamar tare da cewa ku shigo mana,,,,, faruk ne ya fara shiga raihana tabi bayanshi,,,

suna shiga faruk ya zauna saman kujera ita kuma raihana tabi shi da kallo,,,, umma dake fitowa daga cikin ɗaki raihana ta nufi wurinta da gudu ta rungumeta tana kuka,,, gaban faruk ya faɗi yace Allah yasa dai yarinyarcan ba cewa zatayi na daketa ba,,,, niko nace kai kukan farin ciki ne,,,

Umma tace miye haka kuma?"",,,, faruk yace kyaleta umma,,,, kallon inda raihana take tsaye yayi ya faki idon umma sannan ya nuna mata da hannu alamar nidai ko?"" yi tayi kamar bata ganshi ba,,, umma tazo ta zauna suka gaisa da faruk, bayan sun gaisa ta ƙara godiya,,, faruk yace ba komai ,,,, yaɗan daɗe sannan ya tashi zai tafi,,, daga inda raihana take zaune tace Allah ya kiyaye,,, baiyi mata magana ba, yayi tafiyarshi,,,,

kamar jira take ya fita da sauri ta matsa kusa da umma tace umma miya dawo daku gidan nan ne?"",,,, kuma waye ya gyara shi?"",,, godiyar mi kike ma faruk?"",,,, umma tace to wace ansa zan baki ne?"",,, raihana tace dukansu zaki ansa man,,

umma tace to ranar da kika tafi, da mijinki yazo ya ɗaukeki,,,, gwaggo bansan tudun data dafa ba, taje ta cinnoni da mai gida yazo ya tasheni,, bayan na tashi na sake kama haya a cikin unguwar nan,,,, ina zaune gidan sai mai gidan yace idan ina da hali in sayi gidan nan zai siyar dashi,,,,

kuɗin da faruk ya bani miliyan biyu ne, ciff akayi ma gida kuɗi miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar,,,, ina zaune cikin gidan bayan na siya,,, sai Allah ya ɗorawa fiddausi rashin lafiya akayi ta kashe kuɗi amma an kasa gano ciwo, kinga gidan gadon nan muna da haƙƙi a ciki amma suka hanamu, haka akayi ta kashe kuɗi dan neman lafiyarta amma abu furrr,,,, naga wahalar da take sha na ɗauki sauran kuɗin hannuna, na cire dubu ɗari biyu nakai masu dubu ɗari ukku,,,,

Raihana kullum ciwo rikecewa yake,,, saboda haka suka rasa madoga sukace in sayi gida su nemawa fiddausi magani nace masu banda kuɗin siye,,, to nidai bansan waye yakai wa faruk labari ba, don haka wani abokinsa sadiq, bayan yaxo muka gaisa dashi yace nawa akayiwa gidan nan kuɗine?"",,,, nace mashi ban sani ba,,,

danni a lokacin bansan ko waye shi ba, haka yaje yayi cikin gida ya biya kuɗi,,,, bayan wani lokaci ya dawo yace man faruk yace zaiyi magana dani,,, aka bani waya faruk yace man umma kiyi haƙuri don Allah kiɗan samu wuri ki koma zuwa wani lokaci,,, nace mashi mi akayi ne?"",,, yace inyi haƙuri dai ni bai faɗa man za,aman gyara ba,,,

Haka na tattara nabar gidan, da tashina da gyaran gidan raihana duka cikin wata biyu akayi aka gama,,,, saida aka gama sannan sadiq yaje yace man in dawo, komai na gidan nan shine ya saka man,,, raihana tace kin gode,,, umma tace kuma duk ƙarshen wata yana aiko man kuɗaɗe sosai da komai da komai babu abinda na nema na rasa,,,, amma yanxun na fara kasuwanci tunda na samu jari,,,,

raihana tace mi kike siyarwa ne?"" tace shinkafa nake rabawa sai wata a biyani, raihana tace to Allah ya tsare, umma tace amin,,,, raihana tace to ina gwaggon yanxun?"",, umma tace ta samu wani ƙaramin gida suna ciki yanxun, to jikin fiddausin fa?"" da sauƙi harta koma gdan mijinta,, raihana tace to Allah dai ya kyauta, umma tace amin,, tashi kije ki gaida gwaggo raihana tace ai baice inje ko ina ba,,,,, amma bara in kirashi inji,,,,

wayarta ta ɗauka ta fara kiran faruk,,,, bin wayar yayi da kallo sannan ya ɗauka, raihana tace ya kke, yace qalau tace zanje gidan gwaggo, yace A, a, cikin shagwaɓa tace don Allah yace Allah kada kije, gani nan ma zanzo yanxun in ɗaukeki, raihana tace to kayi haƙuri sai anjima,,,, kashe wayar tayi,,,

Faruk dake zaune yace yarinya kinma ja ma kanki bari inje in ɗauko ki, ita kuma raihana tace ma umma yace kada taje, umma tace to,,,, raihana tashi tayi tabi gdan tayi ta dubawa lallai gidan yayi kyau sosai,,, dawowa tayi ɗaki ta kwanta taci gaba da bacci,,,,,,

Shi kuma faruk tunda yayi waya da raihana sallah magrib yayi ya taho ɗaukarta,,,, ita kuma umma ta tasheta tayi sallah sannan ta kawo mata abinci amma raihana tace ta ƙoshi,, dan rabonta da abinci tun na gidan nasir, haka umma ta tattara abinci ta mayar,,,,

suna nan zaune suna fira faruk ya shigo, dan shima yanxu an wani zama ɗan gida, bayan sun gaisa da umma ta kawo mashi abinci, yaci bayan ya gama ne, yace suje,,, shine ya fara fita, ita kuma ta ɗan daɗe sannan ta fito,,,,,,,,,

a mota sai kakarin amai take,,,, faruk ya harareta yace kinsan Allah kada kiman amai,, batayi magana ba,,,,, yace mi kikaci ne?"",,,,,tace banci komai ba, faruk yace mi kike jine?"",,,, tace batajin komai yace kinajin yunwa ne?"" raihana tace A, a, yace to miye?"",,,, tace ba komai,,, yace tou na lura shegantaka kike ji zanyi maganinki,,,,

Kai tsaye gidan momy suka nufa,,,, a bakin get ya ajiye raihana yace in anjima zai dawo akwai inda zaije,,, ɓata fuska tayi taƙi tafiya,,,,, haryaja motar kuma komi ya tuna ya dawo Oho, fitowa yayi daga motar sannan yace muje,,, yayi gaba tabi bayanshi har ciki,, a farlo suka samu momy zaune tana cin abinci faruk ya gaisheta, itama raihana gaisheta tayi cikin girmamawa, momy ta ansa cikin kulawa,,,,

faruk ya miƙe yace ma momy zaije ya dawo, tayi mashi fatan alkairi,, bayan ya fitane momy tayi ma raihana ya jiki, tace da sauƙi,,,, abinci ta zuba ta miƙa mata amma raihana cewa tayi batajin yunwa,,, taƙi cin abinci,,,, tana nan ta jingina da kujera sai bacci....

momy ta tasheta tace idan bacci zatayi ta shiga ciki zainab tana ɗaki,, batasan tayi mata gardama ta miƙe tayi cikin ɗaki,,, tana shiga warin turaren zainab yasa tayi toilet da gudu tayi ta gwarara amai,,,,, zainab dake kwance saman gado tayi dariya, tace in sani yaya harka bindigeta,,, dariya ta ƙarayi sannan ta miƙe tayi toilet ɗin tana cewa sannu,,,,,

Raihana dai ta kasa magana, zainab ta jawota ta fitar da ita farlo, momy tace miye?"",,,, dariya zainab tayi sannan tace ɗiyarki babu lafiya, momy tace mi ya sameta ne?"",,,, murmushi zainab tayi sannan tace ki tambayeta gata nan,,,, momy tace raihana miya sameki?"" raihana tace ba komai,,,, dariya zainab tayi dan lallai ta fahimci raihana bata san tana da ciki ba,,

Zama sukayi a farlo suna fira, amma raihana ba sosai takeyin magana ba, idan anyi abun dariya to ba baki take saki sakaka take dariya ba, dariya takeyi ta aji da tsare gida,, tun tana magana har bacci ya ɗauketa,,,,

Faruk bai dawo ba, sai 10:39pm ya shigo, lokacin itama momy tayi bacci sai zainab dake zaune tana chat sannu da zuwa tayi mashi sannan taje ta kawo mashi lopton, saida ya gama sha sannan ya tashi raihana dan tafiya gida,,,,,,, saida safe tayi ma zainab suka tafi,,,,,

Suna fitowa raihana tace ina zaka?"",,,, yace gida zamu , tace ƙasa zamu?"",,,, yace Eh ba kince kinfini gudu ba?"",,,, yau ina so dani dake aga wanda zai riga zuwa gida,,,, ɓata fuska raihana tayi sannan ta matsa kusa dashi ta shige cikin jikin ta fara sakata,,, dariya sannan ya ɗagota daga jikinshi yace kinsan wani abu?"",,,, tace A, a, yace idan har kika rigani zuwa gida ni kaɗai nasan abinda zan baki,,,, raihana tace abinda kai kullum kanayin training ni banayi dan kasan bazanje ba kawai kace haka,,,,,

yace to yi haƙuri muje,,,, tace itafa batayi, yace to bari inje in ɗauko motar,, harya juya zai shiga gida raihana tace saika tahoooo,,,, ta ruga da gudu,,, faruk yace banyi,,, motar ya ɗauko yabi bayanta, lokacin harta kusa isa, yana zuwa daidai inda take ya tsaya sannan ya sauke glass yace shigo muje tunda kin kasa,,, raihana ta zagaya ta shiga, sai sauke numfashi take kamar ta kada giwa,,, faruk sai dariya yake mata,,,, ita kuma wannan dariya haushi take bata,,,

tace bari man dariya yace anje anyi, ya haɗa mata da gwalo,,,,, raihana tace kai idan anyi maka abu sai kace baka so amma kai sai kayita ma mutane,,, yace to ke na raina,,,, kece ƙawata,,,, yaci gaba da dariya,,, daga nan bata sake magana ba, har suka isa gida,,,,

suna zuwa,,, ita tayi ɗaki shi kuma ya nufi ɗakinshi, yana zuwa alwallah yayi ya fara sallah ita kuma raihana wanka tayi sannan tabi lafiyar gado..... Niko nace ko sallar daren baki taya mijinki?""",,,,,,,,,
[1/8, 9:46 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 5⃣0⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔚🔚

****

*R*aihana kuwa jin fitar motoci, da gudu ta fito kafin ta ida isowa tuni sunbar gidan,, wayarta dake hannunta ta fara kiran wayar faruk,,,,,,,,,,

Wayar tana shiga ya ɗauka tare da cewa aciciya abincinki?""" raihana tace da Allah malam wane abinci?"" dariya yayi sannan yace Allah ya baki haƙuri, miye?""" raihana tace wallahi banda lafiya sosai,,,,, murmushi yayi sannan yace ina maki addu"a sannu,, daga haka bai sake magana ba ya kashe wayarshi,,,,,

Ita kuma jin ya kashe wayar yasa ta fara kiran wayar ummanta,,, bayan umma ta ɗauka suka gaisa, raihana tace mata umma banda lafiya , umma tace miya sameki?""",,,,, raihana tace kawai dai wani iri nake ji,,,, dariya umma tayi sannan tace to sannu,,,,, ko asibiti zaki?"" raihana tace Eh,,, umma tace to ki faɗawa maman faruk ɗin mana,,, raihana tace ita dai A,a, umma tace kedai faɗa masu ki fita haƙƙinsu idan basu da hali ki kirani, raihana tace to sannan ta kashe wayarta,,,

Da sauri ta sauko daga saman gado ta durƙushe ƙasa,,,, tana innalillahi wa"inna ilaihir raji"un,,,,, tana ci gaba da maimatawa, zufa kusa sai keto mata take saboda azaba,,,,,,, kwanciya tayi daƙel ta iya ɗaga wayarta ta fara kiran zainab, dan kiran momy ya mata nauhi,,,,

Zainab tana ɗauka babu gaisuwa cikin murya jigata da wahaltuwa raihana tace ban lafi.......,,,,,, ai bata ƙarasa maganar ba, wayar ta faɗi ƙasa,, zainab taci gaba da cewa hello hello da sauri ta fito tana kiran momy,,,, momy dake farlo zaune tace miye?""" zainab tace gdan yaya babu lafiya fa,,,,,,

Momy tace wani abu ya faru ne?""",,,,, zainab tace naji tana cewa bata lafiya,,,, amma ta kashe wayar kuma na sake kiran wayar bata ɗauka ba,,,,,, momy cikin damuwa tace muje mu gani,,,,,,,,,, zainab ta koa ɗaki ta ɗauko gyalenta,,,, momy kuma akwai hijabi a jikinta, don haka da sauri zainab ta ɗauki makullin motar tayi gaba momy tabi bayanta .....

Ita kuma raihana,,,,, tana kwance har yanxun a wurin,,, ga wayarta a gefe sai kira yake shigowa tanaji amma bata iya ɗauka,,,,,, da momy da zainab tare suka shigo,,, da sauri momy ta ƙarasa inda raihana take kwance tana tambayar lafiya?""",,,

Raihana dai ta kasa magana,,,, zainab tace sannu matar yaya,,,,, momy tace wane sannu matar yaya, kamata asibiti zamu,,,,, zainab tace to,,, haka suka kama raihana, sukaje suka sakata mota, sai asibiti.....

Kafin suje tuni raihana tayi lugufff saboda jagalgalar mota,,,,, suna zuwa aka anshi raihana sai ɗakin ido ya raina fata,,, raihana sai salati take tana ƙarawa, momy kuwa sai addu,a take,,,,, zainab kuma sai kuka taketana kiran number hafsat, ta sheda mata , itama tace gata nan zuwa yanxun insha Allah,

Umma kuma ta kira wayar raihana harta gaji don haka ta haƙura, shi kuma faruk kiran wayar raihana bata ɗauka ba yasa shi dawowa,,,, a asibiti kuma momy tace zainab tunda an kawo raihana ta koma gda ta ɗauko mata kayan da zata canja, idan ta aihu ,

Suna nan jigumjigum, suna sauraren ikon Allah har zainab taje ta ɗauko kaya ta dawo, dan tunda cikin raihana ya shiga wata haihuwa ta haɗa komai a akwati da kayan babies ɗinta,, komai da komai da za,a buƙata,,,

zainab bata daɗe da dawowa ba, 6ter ta fito tare da cewa an sauka lafiya,,,,,, momy tace mi aka samu?"" dariya tayi, bata faɗa ba , tace sai ta shiga ta gani,,,,, momy tace wannan wane irin abune?"" ai tun ana aihuwa ake sanin abinda aka samu,,,, tace yi haƙuri momy, haka aka samu ta nuna da hannunta,,,,,, momy sai dariya take tana Allah raya,,,,,,

Ɗaukar kayan tayi ta koma ciki, kulawa mai kyau raihana ta samu dan asibitin kuɗi tasha banban , saida ta gyara jikinta ta shirya sosai,,,,, abinda aka samu suma aka shirya su,,,,,, sannan aka fito da raihana dan kaita ɗakin hutu,,,,,

da hafsat da zainab da momy da amina, sai murna suke wai yaya yayi twince yara masu kyau dukansu maza ne, sai farin ciki suke,,,,,,,

Momy ce tace hafsat taje ta faɗawa umma an aihu,, tanata kiran wayarta bata zuwa,,,, Amina tace Aunty hafsat ki tafi dani in riƙe ɗauka maki jariran ta gansu,,,,, momy tace aike mahaukaciya ce, a ina kika taɓa gani?"",, tace momy wai dan ta gani da idon, tsaki momy tayi ita kuma hafsat ta fita,,,,,

faruk kuma tun farlo yake kiran aciciya shiru,, ɗakinta ya shiga bata nan, ya duba toilet bai ganta ba,,, har zai fita yaji wayarta na ringing,,,, juyawa yayi ya kalli inda wayarta take,,,,,, sannan ya juya yabar ɗakin bai ɗauki wayar ba,,,,,

ɗakinshi yaje bai sameta ba, duk inda yasan zai ganta bai gani ba,,,,, yacw to ina aciciya ta tafi ne?""",,,,, wayrshi dake ringing ya zaro daga aljihu,,,, ganin zainab ne yayi tsaki, bai ɗauka ba,,,

kiran wayar ya sake shigowa,,, tsaki yayi sannan ya ɗauka da cewa miye?"",, zainab tace yaya albishirinka?""" tsaki yayi sannan yace idan zakiyi magana kiyi bana san albishir,,,,, murmushi zainab tayi sannan tace nidai albishirinka,,,,,,

yace naji,,,, tace sai ka fara bani goron albishir sannan,,, yace faɗa man abinda kike,,,,, zainab cikin zalama da haɗama tace miliyan ɗaya, murmushi faruk yayi sannan yace na baki, zainab cikin ihu da hauka tace matar ta haihu yara biyu maza,,,,, dariya faruk yayi sannan yace Allah ya raya, na ƙara maki miliyan huɗu,,, ihu zainab tayi sannan tace muna asibitiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii

ta kashe wayar,,,, faruk kuwa ɗakinshi ya shiga yayo alwalla yayi sallah don nuna godiya a wurin Allah, daya sauki matarshi lafiya ya kuma azurtashi da zuria, sannan yayi addu,a Allah ya shirya su ya albarkaci rayuwarsu,, ameen,

yana gamawa ya miƙe cikin farin ciki yayi ma asibiti tsinke,, ita kuma lokaci da hafsat taje gdan umma ta sanar mata aihuwa umma taji daɗi, sannan tace su bari aje a faɗawa gwaggo sai su tafi tare,,, hafsa tace to, lokacin da umma taje ta faɗawa gwaggo da farin cikin, amma a gwalshe gwaggo ta taɓe baki tare da cewa Allah raya,,, daga nan bata sake magana ba, umma tace to kuje asibitin gwaggo tace ban zuwa sai gobe, umma tace Allah ya kaimu,,,, daga nan bata sake magana ba, tayi tafiyarta,,,,

bayan ta dawo tace ma hafsa taje ashe ma gwaggon taje kauye,,,, hafsat tace ba damuwa,tayi tafiyarta,

Faruk kuwa yana zuwa asibiti,,,, cikin murna "yan uwanshi duk suka rungumeshi suna mashi murna,,,, bakin nan nashi yaƙi rufuwa, niko nace wayaga angon jego?""",,,,,,

bayan sun gaisa da momy ne,,, zainab sai rawar jiki take ta ɗauko jariran ta miƙa mashi,,,, ya ansa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login