Showing 21001 words to 24000 words out of 64938 words
dauka danace masa ba niba ƴar gidannan bace yara budani, amma a lokacin ma ya nuna yafisona, gashi yanzo yaddana kejinsa idan narashi bansan yazanyi ba".
Tausayin ta yakama Zainab sosai dan tasan yadda takeson Hayatudeen dinnan koma koshi yana mutuwar sonta da har gidasu sunsan yana son Fatima dan ko Mamarshi naso Fatima sosai, danshi ma Fatima tak'ara yadda son gasky Hayatudeen kemata.
Kallon Zainab tayi dataga tayi shuru, tace, "my Zeey gobe zanje gida dan Ummah tace, nazo"sai Zainab tace, "to Allah yakaimu sai muje m muyi kwana biyu ko?" Fatima tace eh".
Aranar haka ta wuni bawani kuzari ajikin tah..
*Muje zuwa*
*Commet*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*KAWAR* *'YATA* *CE*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story & written*
By
*Sumy*✍?
```BISMILLAHI``` ```RAHAMANIR``` ```RAHIM```
```Congrtulations``` ```my``` baby ```intayaki``` ```murnar``` ```kammala``` ``````novel``` *`d'inki`````BABUSHI* *A* *ZUCIYATA* ```Allah``` ```yabaki``` ```ladar``` ```faɗa karwar``` ```dakikayi``` .
*Page*19*
Da sassafe suka shirya bayan sunyi breakfast, d'akin momy sukaje sukayi mata sallama, kana suka wuce part d'in Daddy domin shi ma suyi masa sallama.
Da sallama suka shiga, bayan ya amsa musu suka gaishe shi, sannan suka fad'amasa inda zasuje,dak'ar yabar su,kuma kwana d'aya yabasu.
Aikowa sunje gidan kwanan su biyu basu dawo ba Daddy da yamma yaje dumin ya ɗauko su.
Koda yaje gidan su Fatima ya aika akirasu amma akacemasa basunan suna gidan yayan Baban su Fatima.
Aikawa ya kuma yi yace, "yana so akira mashi su."
sai kanwar Fatima mai suna Salma tafito, bayan ta gaisheshi tace, mishi," Ummah tace, na faɗa maka, ko dama can Baba babba shine ya aika akirata, dan haka yanzu tana can gidan sa".
Sai Daddy yace, "kinsan gidan ne?" tace, "eh nasani".
Sai yace, "zo muje ki kaini gidan."
Salma tace, "to bari nagayama ummah".
Daddy yace, "to jeki".
Batajima dashiga gidanba, ta fito, tace, muje Daddy hanya tamiƙe zatayi tafiya.
Sai yace, "Salma zo kishiga mota muje ko".
Tace, "Daddy ba nisa nan ne bayan gidan."
Daddy yace, "duk, da haka kizo muje dan ni daga can nake son na wuce".
Tace, "to" tana mai dawowa tashiga tana shiga ya tada mota suka tafi tana mai nuna masa hanyar gidan, bakin ƙofar gidan yayi parking.
Sunayi parking Salma tace, "ashe Baba babba ma yana gida."
kallon ta yayi yace, "ina yake ne?".
Tace, "gashi can bisa tabarma zaune."
Daddy yace, "to bari naje mu gaisa."
Salma tace, "to tana mai fitowa acikin motar.
Koda takawo wurin Baba babba, gaisheshi tayi ya amsa.
kallon ta yayi yace, "waye yakawoki a Mota?".
Salma tace, "Daddy su Aunty Zainab ne yace nakawoshi gidannan".
Har yaso yasake yin magana yafasa, saboda Daddy daya tunkaro wajan dayake zaune.sai yace mata,"kina iya tafiya."
Tashi tayi ta shiga gidan,bata k'arasa shigaba Daddy ya k'araso wajan da Baba babba yake zaune.
Sallama Daddy yayi masa yana mai mik'a masa hannu dan su gaisa.
shima hannu yaba Daddy sukayi musabaha, kana yanunama Daddy wurin zama, bayan Daddy yazauna.
Sai Daddy yace, dama nazo na d'auki su Zainab ne akace sunanan".
Sai da Baba babba ya numfasa kana yace,"eh sunanan ko kiramaka Zainab d'in za'ayi?".
Sai Daddy yace, eh akiramin su dan gobe ne zasu koma makaranta".
Sai Baba babba yace, a'a kayi hakuri bada Fatima ba, dan yanzu ko ina bazata koma tafiya ba, saboda data kammala makaranta aure zanyi mata".
Arazane Daddy yad'ago idonsa ya kalle Baba babba, Daddy yace, "aure".
Kai Baba babba ya d'aga masa, alamar eh, sai Daddy yace, "dama ammata miji ne?".
Sai Baba babba yace, "a'a yanzu dai nakeson takawo mijin."
yakara da cewa, inma bata kawo ba ni zan had'ata da wanda yadace da ita".
Sai Daddy yace, "da anbarta takawo wanda take so
zaifi".
Sai Baba babba yace, "intakowa dan kanta inma bata kawo ba ni ina da wanda zanbata".
Sai Daddy yace, "miyasa bazakubarta tayi karatun taba, inyaso, koda tana cikin karatune idan tasamu wanda takeso, sai ayima ta auren".
Baba babba yace, "bamuyi tun farko ba, dan haka bazamu fara akanta ba.saidai indai tayi aure mijin ta yabar ta, to wannan kam bazamu hanaba".
Daddy babu yadda bai nunama Baba babba sai yace, "a'a."
Jikinsa amace yayi mishi sallama yayi tafiyar sa,dan bai ma tsaya aka kira masa Zainab saboda cikin tashin hankali yake.
Daddy nashiga mota yatada bai tsaya ko inaba sai gidan babban abokinsa Alhaji Aminu.
Yana yin picking din motar sa kai tsaye parlour dayasan zai sameshi yaƙarasa.
yana shiga ko ya sameshi, yana kallon news hausa.
Dashigar sa firij yaɓuɗa ya d'auki ruwa masu sanyi yakifa abakinsa sai da yasha sosai sannan ya aje.
Tunda yashigo Alhaji Aminu yake kallon sa, yana mamaki yanayi da yashiga.
saida yabari yagama shan ruwa, ya kalleshi da kyau yace, Alhaji Mansur, lafiya naganka a haka kuwa?".
sai da Daddy yayi ajiyar zuciya kana yace, iyayin Fatima aure zasuyi mata" yana faɗa kamar yayi kuka.
Sai Alhaji Aminu yace, "to miyasa zaka damu, bayan na gaya maka mafita amma kak'i yarda".
Sai Daddy yace," ba nak'i yarda bane, a'a ina dubin yadda zan aure abokiyar ɗiyata kuma ɗiya a gareni".
Daddy yakara da cewa wallahi nayi nayi nafiddata araina amma nakasa, kamar ma ina kara cusata ne a zucuya ta".
Alhaji Aminu yace, "kayi yadda nace ma,dan bari kaji,shi so idan bai shiga zuciya ba ne akecewa abarshi, amma da zaran kabari yashiga to fitar dashi abune mai wahalar gaske, dan haka kaje kanemi magani kafin yayimaka illah".
Daddy yace, "to naji katayani addu'a, dan na sanar da Gwaggo tace Mani na hak'ura.kuma naje na faɗama yaya tah.
Ni ina ma tsoron karta ce bazata samin hannu ba, tunda kasan yadda mukayi abaya".
Alhaji Aminu yace, "Insha Allahu komai zaizo da sauƙi".
Alhaji Aminu yakara da cewa,"ina son ka auri yarinyar nan ko dan ka kuɓuta daga hannun Hajiya Kulu, kada kaman ta, yanzu kashiga harkar siyasa abu kaɗan kayi sai duniya taji ka dan haka kakare mutuncin ka dana iyalinka".
Sai da Daddy yayi ajiyar zuciya, kana yace, wallahi har da ƙarin abunnan yasa nakeson nakara aure dan abun nadamuna, yakara dacewa,"insha Allah da komai yadawo dai-dai zanje na gaya ma yayata Hajiya Sa'a.
kai kuma abunda kaɗai nakesu da kai ka tayani addu'a".
Alhaji Aminu yace, "kada kadamu insha Allah zan tayaka komai, har sai kasamu abinda kakeso".
Haka sukaci gaba da hira daga baya Daddy yayimasa sallama yayi tafiyar sa.
Bayan sun shirya da Gwaggo Maryam,ya fad'a ma Hajiya Sa'a tace," yabar komai ahannuta."
Bayan kwana biyu shiryawa tayi taji gidan su Fatima.
Koda taje akayi rashin sa'a Ummar Fatima batana be Nan ta tafi Unguwa. Kakar ta kaɗai ce agidan.
Da fara'a Kakar Fatima ta tarb'e Hajiya Sa'a, badai kamar data ga yanayin shigar ta.
Bayan sun gaisa, Kakar Fatima tace, "
naso naganeki amma banganeki ba".
Sai Hajiya Sa'a tayi murmushi tace,"Inna bazaki gane ni ba, dan koni bantaɓa zowa gidan nan ba sai yau".
Sai Kakar Fatima tace,"to lafiya dai ko?"
sai Hajiya Sa'a tace, "lafiya ƙalau, kodama alfarma nazo nema, akan yariyar da ƙanena yagani a gidan nan, yace, yanaso".
Sai Kakar Fatima ta gyara zama tace, "wacece, acikin su, ko ad'auku miki hotonan su dan 'yan matan suna da yawa".
Sai Hajiya Sa'a tace, "basai an dauko hoto ba".
Dan Kaka Amo ta matso taji ko wacece, saboda y'an matan suna da yawa.
Sai Hajiya Sa'a tace, "sunan ta Fatima, dafatan dai ba'ayi mata mijiba".
Sai Kaka Amo tace, "a'a ba'ayi mata mijiba, duk da dai shi Baban ta yace, zai samar mata miji cikin satin nan, amma tunda kinzo ai shikenan sai ayi daku d'in."
Sai Hajiya Sa'a tace, "nagode sosai, sai dai shi ƙanin nawa fah ba saurayi ba ne, yanada mata har ma da yara biyar".
Sai Kaka Amo tace, "ai albarka akeso bawani zancen saurayi ba, dan haka kamar zuwa gobe sai kidawo.don kiga Shi baban nata da yamma."
Godiya Hajiya Sa'a tayima Kaka Amo, jikar ta ta ɓuɗe kuɗi masu yawan gaske Hajiya Sa'a ta ajema Kaka Amo, tace, "gasunan, asai goro".
Aikowa Kaka Amo bakinta kasa rufuwa yayi, ɗaukar kuɗin nan tayi tanata juyawa, tana cewa, "kunga rabo ko. arziki yazo maka har gida.
kana tamaida kallon ta ga Hajiya Sa'a wadda itama ita take kallo, tace, "gobe kidawo in dai aure ne babu fashi. nice nan kakar yarinya sai yadda nace za'ayi".
Hajiya Sa'a godiya tak'arayima Kaka Amo kana tayi mata sallama tawuce tace Sai zuwa goben.
*Muje zuwa*
*Comment*
Nd
*Share*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*KAWAR* *'YATA* *CE*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story & written*
By
*Sumy*✍?
*Bismillahi rahamanir rahim*`
*My baby inatayaki murnar fara sabo book dinki mai suna lZZAR SARAUTA Allah yabaki ikon kammala shi lafiya*
*Page* 2?0?
Da yamma Kaka Amo tashirya taje gidan Baba babba, dan a lokacin ne takesa ran dawowar sa gida.
Aikowa tana zuwa ta same shi a gida. Bayan sun gaisa da matar sa, tashi tayi tabasu wuri dan tasan halin lnna Amo sarai.
Fitar ta keda wuya, Baba babba yace, "Inna lafiya kika zo da kanki ai da aikowa kikayi kira na da yafi."
Inna Amo tace, "a'a magana ce mai muhimmanci, dan shi yasa kaga nazo da kana".
Yace,"wace magana ce lnna?".
Tace," kan maganar minjin Fatima, ko ka tsaida wanda zaka bata ne? ko Kuma ita takawo wanda take so,?".
Baba Babba Yace," a'a lnna ko d'aya ba'ayi ba, dan ita wannda tace tana so ma karatu yakeyi, mu kuma bazamu tsaya jiranshi har ya kammala karatunshi tana gida zaune ba."
Kaka Amo tace, "a'a baza mu jira sa ba kam.
sai kuwa Inna Amo ta gyara zamanta, ta kwashe duk yanda suka yi da Hajiya Sa'a tagaya masa.
Takara da cewa, "kuma daganin ta matar y'ar babban gida ne,dan har kud'i tabani akalla zasu kai dubu dari.
Da karfi Baba Babba yace, "dubu dari fah kika ce lnna? ".
Tace, "sosai kuwa,don shiyasa ma nazo dasu dan kagan su".
Jikkar dake sanye ajikin ta taɓuɗe ta ɗauko masa kuɗin tace," gasu ka ƙirga kagani".
Karɓa yayi hannusa na karkarwa yace, "lnna duka tabaki?".
Tace, "sosai kuwa, kaga abin "arziki har gida ko?"
Inna Amo ta numfasa sannan ta k'ara da cewa,"ni tsoron da nike yarinyar nan kada tayi mana tsiya".
Da sauri Baba Babba ya ɗago kai ya kalli lnna Amo yace, "lnna bari ma wannan zancen, dan indai naga shi wannan daki kace yayimin to ita Fatimar ko bayyi mata ba baruwana, kuma yadda nace haka za'ayi da ita,ko uwar ta tayi kaɗan ta canja abinda nace".
Numfasawa Yayi sannan yaci gaba da cewa, "badai kince gobe ita Hajiyar zata dawo ba?".
Inna Amo tace, "tabbas gobe zata dawo.
Sai Baba Babba yace, "zan tsaya na jira ta ma"lnna Amo tace, hakama zaifi kyau,don gaskiya ayi komai a gama".
Haka sukaci gaba da fira sai da akayi kiran sallah, Baba babba yatashi yaje masallaci, itama Kaka Amo takoma gida.
Koda ta koma Umma dasu Fatima duk sun dawo, amma komai bata ce wa mahaifiyyar fatimar ba.
Koda gari yawaye Kaka Amo tashirya tanajiran zowan Hajjiya Sa'a, kusan sha biyu na rana, sai ga Hajiya Sa'a tashigo da sallamar ta.
Da fara'a Ummar Fatima ta amsa ma ta, aikuwa Kaka Amo da sauri tafito daga d'akin ta, dan har Hajiya Sa'a zata shiga ɗakin mamar Fatimar,sai Kaka Amo tafito tana cema, "mamar Fatima bafa wajenki tazo ba,ehe wajena tazo kisani".
Sai Ummar Fatima tace, "lnna kiyi hakuri naga kar a bar ta a tsaye ne shiyasa nace, ta shigo, kuma bansan wajenki ta zoba dana kai ta wajenki".
Hajiya Sa'a ita dai kallon ikon Allah take yi.
Inna Amo tace, "Hajiya mutafi can gidan yayan Babanta".
Hajiya Sa'a tace "to lnna muje".
Inna Amo tana gaba itako Hajiya Sa'a nabiye da ita har suka kawo gidan Baba babba.
Da shigarsu kai tsaye d'akin Baba Babba lnna Amo takai Hajiya Sa'a.
Da sallama ta shiga, ya amsa mata da fara'a afuskar sa.
wajen zama ya nuna musu suka zauna. Bayan sun zauna ne lnna Amo tace ma Baba Babba,"ga fa Hajiya nan tazo".
Baki ya washe ya gaishe ta ta amsa.
Baba Babba yace,"ai lnna ta faɗa min abunda ke tafe dake."
Sannan yaci gaba da cewa," toshi k'anin naki yafaɗama ita Fatimar ne?"
Hajiya Sa'a tace, "nidai yace ya faɗa mata amma bansani ba ko da gaske ne? amma zaku iya tambayar ita Fatimar kuji".
Sai Baba Babba yace, "a'a ai tunda ya gaya mata bakomai, kawai ko aiko da magaba tan ku".
Abun yaba Hajiya Sa'a mamaki taga babu wani bincike sai kawai aturu.
Numfasawa tayi sannan tace, "to ai bakusan waye mijin ba kuma naji har kunce muturo, kodai yazo ne bansani ba?".
Baba Babba ya shiga mazurai Saboda Shi kanshi yasan abinda sukayi ba Haka ya Dace ba,don haka Sai cewa yayi,"a'a bai zoba, Amma dai mun san zai zo kafin auren".
Hajiya sa'a tace, "insha Allah". Sannan ta kallesu gaba d'aya tace, "amma fa kusani, kar kuce kun bamu kuma daga baya ku ce kun fasa.K'ara ku fad'a mana gaskiya."
Sai su lnna Amo sukace, ba komai indai tasan ƙaninta mutumin kirki ne, to babu matsala".
Hajiya sa'a ta girgiza Kai tace "a'a wannan ba hujja ba ce gaskiya".
Takara da cewa," amma, gaskya zan faɗa muku,kuma amatsayina na uwa mace gaskya zan iya bashi aure amma fa gamai irin ra'ayina, dan kaga shi ba yaro ne ba, saboda yace min ita Fatima abokiyar diyarsa ce, Zainab".
Kaka Amo tace," ai mutunci yafi komai tunda yanada mutunci ai babu matsala".
Godiya Hajiya Sa'a tayi musu, sannan tayi musu alhairi mai tarin yawa wanda yasa Baba Babba rikice wa, har yanace wa yaushe magabatan sa zasuzo?"
Sai Hajiya sa'a tace, "dana koma gida munyi magana da Baba duk, yadda yace, zan faɗa muku".
Sai Kaka Amo tace, "ba komai ai mun gode, haka suka rakota su nayi mata godiya, har tashiga mota ta wuce, tabar su nan baki yaki rufuwa.
Aikuwa cikin sati d'aya akayi komai amma, babu wanda suka gayama wa.
ko mahaifin ta kayan da aka kawo nasa ka rana suka gwada masa.
Sukace masa ga kaya nan, dan nan da sati uku masu zuwa za'ayi auren Fatima.
komai bai ce musu ba, addu'a yayi mata kana yawuce gida, badan yasan waye ne mijin taba.
Haka akayi ta shirye shiryen bikin Fatima, amma ko ita Fatima har yanzu bata san waye mijin taba.
Dan lokacin da Daddy, yake gaya mata yana son ya aureta bata fahimci mi yake nufi ba, ita dai abinda ta fahimta shine yana son yak'ara aure.
Haka abubuwa sakayi ta tafiya biki yarage saura sati d'aya Daddy yazo ya gaida Baba Babba shi da abokin sa Alhaji Aminu.
Bayan sun gama gaisawa, Alhaji Aminu yaga batar masu da kansu.
Kana yayi musu kyautar, kujerar Hajji da Umura.
Hmm zokaga murna wajen lnna Amo da Baba Babba, dan har makota sai da sukaji Mijin Fatima yabiya musu kujerar hajji.
Koda Ummar Fatima da Baban ta sukaji suka taya su murna.
Amma duk da haka Kaka Amo sai da taje har d'akin mamar Fatima taci mata mutunci, wai tayi bakin ciki, dan bada ita akace za'a ba.
Ita dai Ummar Fatima batace, mata komai ba, har ta gama tayi tafiyar ta.
Ai babu babban tashin hakali daya wuce Zainab, data kira Fatima take Mata,"Fatima Wai da gaske ne Daddy ke zai aura?".
Fatima tana kwance ta mik'e zumbur ta tashi zaune tace,
"Zainab, wannan wace irin magana ce haka?"
"Daddy fa ki kace? to ko hauka nayi na warke bazan aure Daddy ba, danni uba yake gareni kamar yadda yake uba a wajen ki".
Zainab tace," naji to yanzu wanene mijin naki?".
Sai Fatima tace duk jikinta Yayi sanyi"koni Zainab, bansan waye ba, dan bana bukatar na sani tunda ba shine zab'i na ba".
Zainaba tace, duk da haka kije kiyi bin ciken waye mijinki".
Bata bari tayi magana ba, Zainab ta yanke wayar.
Sai da ta gama nazarin maganar Zainab kana ta tashi tayi wajen Ummar ta.
Koda taje a d'aki ta same ta zaune tayi tagumi kamar mai tunani..
*Muje zuwa*
*Comment*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*KAWAR* *'YATA* *CE*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya