Showing 45001 words to 48000 words out of 64938 words

Chapter 16 - KAWAR 'YATA CE

09 Oct 2024

2468

samu yaje ya tasu taba.



Amma yana dawowa gida bai tsaya ko inaba sai part ɗinta.




Ita koma lokacin ta samu ta kwan ta, a hankali yake tafiya har ya kwao part nata,ko knocking ba tsaya yi ba, key ɗinsa yasa ya buɗe ƙofa ya shiga.



Tundan ya kama hanyar part ɗinta wani ƙamshi turare mai daɗi ya fara ziyar tar sa,uwa uba bare yanzu da ya shigo parlour ta .


Wata sanyayar ajiyar zuciya ya saukar,zama yayi sama ɗaya daga cikin kujerun parlour ,sai da yayi ƴan secnds kana ya tashi ya ƙarasa bedroom nata.


Koda ya ƙarasa kwance ya same ta, a hankali ya futa cewa,"kardai ace bata yi sallah ba".



Dan haka da suri ya ƙarasu gare ta,zama yayi ƙusa da ita a hankali ya kai hannusa ga reta,ya fara tashinta.



Da yake bacci nata baiyi nisa sosai ba,dan haka a hakali ta fara buɗe idon ta,ta sauke su akan shi.



Yana ga ta buɗe ido cikin muryar mai kama da rarrashi yace,"tashi kiyi sallah har angama sallah baki tashi ba".


A hankali ta buɗe baki ta fara magana tace, "nayi sallah yanzu ma na kwanta".



Yace, "to shine zaki kwan ta baki san ba kyau ba".




Bata ce da shi komai ba.jin shurun da tayi ne yasa ya ƙarasu gareta,jikin sa ya sanya ta kana yasuma faɗin My teema na, ina kika je na daina ganin ki? kuma kinsan ba zan iya ruwa baki a tari dani ba ko?".


Koma bata ce masa ba inba hawaye da ke zuba a idon taba,tunda ya fara magana.



Aikuwa gaba ki ɗaya ya rikice yafara rarra shin ta,irin yadda taga ya rikice ne yasa ta daina kukan da takeyi.




A hankali ta ɗago ido ta kalle sa kana ta furta cewa,"Daddy da gaske kana sona?".




Saida ya ƙara matseta ajikin sa kana yace.

"Fatima ko ban faɗa ba duk wanda ya kalleni yasan akwai sonki maitarin yawa atari dani".



Tace,"to Daddy amma inson ka nemi tsarin jikin ka,kuma ka ƙara dagewa wajan tsayuwar dare,in har kana son muci gaba da zama cikin kwanciyar hankali,kuma da ka ke faɗin ina naje,niba inda naje ina nan dan kona je ɗakin ka korata kakeyi shiya na dana dan naga yanzu ga daina sona".



Bai bari ta kai ƙarshin zancin ba ya rufe mata baki tare da faɗin,dan Allah kada ki faɗa haka wallahi ina meki son da baki bazai iya faɗa ba,kuma bam masan kin taɓa zowa na ƙureki ba.amma dan Allah kiyi hakuri kuma kada ki faɗama yaya Sa'a,kuma insha Allah zan ƙara neman,anjima ma zanje wajan kawo Gwaggo".




Tace,"kada kada mu Daddy kowa ma bazan gayama ba bare Hajiya".



Idonsa yasa cikin nata yana mata kallon da gaske?kai ta girgizamasa alamar eh".



Yace,"ya akayi naji jikinki da zafi ko baki da lafiya ne?".



Idonta suka suma kawo ruwa a hankali ta buɗe baki tace. "na kwana biyu banda lafiya dan ko aiki da ƙyar na keyin sa".


A razane ya furta aiki! to waya saki aiki ne?,to bari kiji ban yadda ki sake ɗaukar koda wani tsinke ba da sunan aiki, ni bari ma nakira doctor ya dubamin ke, dan inson naje gida Kowa Gwaggo".



Tashi yayi domin yaje part ɗinsa ya d'auko wayar sa.


Har zafita ta kira shi tace, "Daddy ina zuwa" .
tsayowa yayi yana jiran ta,wata kwalbar zuma ce ta ɗauƙo ta ɓuɗe ta zuba a cokali ta fara bashi yana sha sai da ta bashi kosan cokali biyar kana ta aje.



Kallon ta yayi yace,"bata isan ba aƙa ramin".


tace,"a'asai anjima zan ƙarama Daddy".



Yace,to abu biyu zaki bani anjima ko?".


Tace, "meye ɗaya?".


Ido ɗaya ya kanne mata.


Kuka taso mayi tana faɗin Allah ban yadda ba Daddy".



Dariya ya sanya yana mai buɗe ƙofa yafita.





*By Sumy*?





*Comment*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦




*ƘAWAR ƳATA CE* *1441H/2019M.*





®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.?
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}



```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇?*_



Story & Written
By
*SUMY✍?*



```Dedicated``` to..
*Family*🥰🥰🥰






~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.

*Congratulations Mrs Basakkwace, ina tayaki murnar kammala novel ɗikin me suna Samha,faɗa karwa dakikayi akansa Allah yabaki lada,kuskure Allah yaya femiki.kuma ina tayaki murnar fara sabon novel ɗinki mai suna WATA KISHIYA BATAYIBA*
*Allah yasa anfara asa'a*





*Page* 3?5?




*__________📖* Wani kallo Momy ke binta da shi gabiki ɗaya tsoro ya bibiye ta, amma sai ta tuna maganar da matar Malamin su ta faɗa mata, dan haka ta dake zuciyar ta, ta fara ta fiya domin ta koma part nata.




Har zata wuce Momy tayi saurin cin gaban ta,kallon ƙasa da sama tayi mata kana tace, "ni zakima rashin kunya?kice zaki raɓi mijina ko? to bari kiji, ba'ayi wata ɗiya mace wadda zata raɓar mijina ta zauna lafiya ba, dan haka sai naga wanda ya ɗaure miki ƙafa da har zaki ɗau shegiyar ƙafar ki kije part ɗin mijin har da haɗa masa breakfast,kece tsowar munafuka ɗiyar matsiya ta".



sai da tayi mata tas kana ta kyale ta.



Ita ko Fatima ko ɗaga kai batayi ta kalle ta ba bare tasa ran zata tanka mata.



sai da tabari tagama zubar ta kana ta raɓe ta gyafinta ta wuce war ta ba tari data kalle Momy ba.



Haka data yi ba ƙaramin ɓata ma Momy rai yayi ba dan haka da hanzari ta bi bayan ta.



Koda Fatima ta ƙarasa parlour duk sun nan zaune suna fira,amma tayi kamar bata ga wata halitta a wajan ba,dan haka ta kama hanyar da zata sada ta sa shen ta .



Aikuwa Nabila naga nin haka cikin ɗaga war murya ta daga mata tsawa,tari da faɗin, "ke!"


Tafiyar ta taci gaba dayi kamar bata san da ita take ba.


Momy da taga Fatima batada alamun tsayowa, dan haka itama ta daka mata tsawa tari da faɗin,"marar mutuncin yarinya hala bakiji ana miki magana ba".



Sai da Momy tayi magana yasa tayi tsaye cak, batari da ta juyu ta kalle suba,duk da atsora ce take amma tada sosai.



Abunda tayi ya ɓata musu rai sosai,dan haka cikin han zari Nabila ta zo ga banta hannu ta ɗaga dan ta mare ta, ita ko Fatima cikin da dakewar zuciya ta riƙi mata hannu kallon-kallon,suka fara yi tsaka nin su.



Ahankali Fatima ta buɗe baki tace,"Nabila me namiki zaki mareni?".



Iya saƙowa Nabila tasaƙo dan haka hunnu ta ta fizge domin ta kai mata mari,sai Momy ta ɗaga mata hannu tare da cewa, "Nabila bar ni da ita,kishi zatiyi dani,to kijira dan wallahi ko uwarki sai tayi kuka bare ke" Momy na faɗin haka tayi ƙfaci ta kama hanyar part ɗinta da sauri batari da tace musu komai ba.



Itama Fatima ta raɓa ta gyafin Nabila ta koma part ɗinta.



Momy na shiga ɗikin ɗinta wayar ta ta ɗauko,kiran number Hajiya Shafa tasa.


ringing da ba wuce biyi ba akayi picking, sai da suka gaisa Momy ta ƙara da cewa,Hajiya inaga fah kamar aikin nan ya karya".



Hajiya Shafa tace, "a'a gaskya aiki na nan,ta ƙara da cewa me kika gani da zaki ce haka".



Momy tace,"komai nagani Hajiya".


Nan Momy ta shiga faɗama Hajiya Shafa duk abunda ta gani har ma da wanda bata gani ba.



Sai da Hajiya Shafa ta numfasa kana tace,"kada kisa damuwa aranki,kinga jebi sai mukoma mugaya masa abunda ake ciki,dan kinga yau bara nar zuwane wajan saba sai jibi muyi samma ko sai muje wajan sa".



Momy tace,"to Hajiya zanyi iya hakuri har jibi? dan wallahi ni ka dai nasan me nakeji a zuciya ta".



Hakuri Hajiya Shafa ta shiga bata, da nuna mata wannan karun ɓatar da ita za'ayi babu mai saki ganin ta kuma babu mai saki maganar ta har abada.




Aikuwa Momy ba ƙaramin daɗi tajiba dan haka tasaki jiki suka cigaba da fira har daga baya sukayi sallama.



Parlour tadawo ta sa mesu zaune.



sai da ta zauna Maram ta kalle ta kana tace,"Momy haka kuke fama da yarinya ƙarama tana muku rashin mutun ci kuma baku ɗau mataki ba?".




sai da Momy ta numfasa kana tace,"Maram yarinyar nan shegiya ce, duk abuda kayi mata sai ta kwance shi,amma nasan wannan karun tayi ƙaɗan ta kunce shi".



Maram tace,"haka yafi dan na tsane na ganta agidan nan. Momy ni gani nake kamar ciki ne da ita".


Momy tayi saurin faɗin, "a'a Maram bata da komai".



Tace, "Allah Momy haka nake gani,amma zan sa ido akanta kafin na bar gidan nan".



Sai Momy tace,"to kisa dan wallahi in shine sai naci ubanta kafin na zubar da shi".






Haka dai suka cigaba da firar su,Zainab kam ko mai bata ce musuba duk abundan da suke iya kar ta kallon su.

Dan yanzu ta rage jin tsanar Fatima a ranta.





Ita ko tunda ta shiga ɗaki ta faɗa saman gado ta fara kuka mai tada hankalin mai sauraru kamar wadda aka niƙama duka.


Sai da tayi mai isar ta,kana ta tashi taje toilet tayo alwala ta zo ta fara sallar walha.



Bayan ta kammala tajima tana addu'a kafin ta shafa,ta ɗauko husunl musulima ta fara karan tawa,har sai da akayi sallah azahar tayi sallah kana ta kwanta bacci.



**********

Daddy ko tunda ya fita daga gida gida Kawo Gwaggo ya fara zuwa,bayan sun gaisa,Daddy ya faɗa masa abunda ya kawo shi.



Sai da yayi ma Daddy faɗa mai haɗi da nasiha kana ya haɗa masa magana ya bashi,man habba ya ɗauko ya bashi yace ya tabbatar duk zai kwanta barci ya shefe ƙirjin sa da shi,dan yana kariya sosai koda an jefeka acikin barci da ikon Allah ba abunda zaiyi ta siri akan kai.



Ya ƙara dace masa kuma ya dage da azkar safe da yamma insha'Allahu ba abunda zai same shi.

Godiya mai yawa yai masa,kana yayi mishi alhairi sannan ya wuce gidan Gwaggo ya gaisheta kana ya wace office ɗinsa.



Bai jima da zama office ba doctor ya kirasa yace, "gashi nan zuwa ya kawo saka makon abunda ke damun Fatima".



Daddy yace, "sai dai kasameni office dan yanzu nafita daga gida".




Doctor yace, "oky ganinan zuwa".



Daddy yace, "tom yana mai aje wayar.



Bai sujima da yin wayar ba.doctor ya ƙarasu.


Damar shiga ya bashi sannan ya shigo.



Sai da suka ƙara gaisawa sannan doctor ya fara yiwa Daddy bayani.



Yace, "da farko dai congratulations,ina tayaka murnar matar ka na dauke da cikin wata biyu da sati uku".


Daddy ba abunda yake faɗa sai "Almhdullah"lokaci ɗaya farin ciki ya mamaye fuskar sa.




Doctor ya ƙara da cewa, kuma abar barin ta tana shiga damuwa saboda haka kan iya haifar da illa sosai ga abunda ke cikin ta".




Ta kardar magani ya ba Daddy yace, "sai ta rinƙa sha insha'Allahu zata samu ƙarfin jiki,kuma zata daina zazzafin da takeyi akai-akai.




Godiya Daddy yayi masa sosai kana yayi masa alhairi mai tarin yawa.




Shima doctar godiya yawa Daddy kana yayi masa sallama ya wuce.




Tunda doctor yatafi Daddy yasu ya koma gida amma aiki ya riƙi shi,dan ko kiran da Hajiya Kulu kema sa baibi ta kan saba,daga ƙarshe ma da yaga ta dameshi da kira kashe wayar yayi yaci gaba da aikin sa.







Itace bata farka ba sai da akayi sallah la'asar, tashi tayi tayi sallah kana ta sauka ƙasa domin ta shiga kitchen.





Har ta ɗura sanwa tana cikin yin blending ɗin kayam miya,sai ga Nabila ta shigo ita da yayar su Maram.




Ko kallon inda suke batayi ba taci gaba da aikin ta.



Tunda Maram ta shigo takefe Fatima da ido tana su ta gane gaskiyar lamarin.



Itako bata ma kula dasu ba dan aikin ta takeyi.



Tana cikin haka Nabila ta zo har wajan da take tana leƙin me take girka wa.



Kallon ta tamaida ga Fatima kana tace,ke idan kin gama ki haɗa mana kun aya dan yau shi muke son shi".


Kamar bata san da halitta awajan ba haka tayi musu.


Maram ce ta daga mata tsawa tana faɗin, "ke bakiji ana miki magana kinyi banza da mutane".





Sai alokaci ta ɗago ta kalle su,kana tace,"kuyi hakuri ban ɗauka dani kuke ba".



Har Maram zatayi magana Momy ta shigo tace,"wai me kukeyi ne naji kamar hayani ya".



Nabila ce tagaya mata ƙarya da gaskiyar abunda ya faru.


Momy tace, "ku kyale ta, bana son kuna haɗa baki da ɗiyar ta lakawar nan,dan haka kuje idan tagama girki dole ta ta kawo kuci".



Duk abunda suka ce ko kallon su bata yiba, bare har su sa ran zata tanka musu.



Suna fita taci gaba da aikin ta,ƙarfi biyar,ta kammala,sai da ta haɗa komai ta koma part ɗinta,wanka tayi kana tazo gaban mirrow ta fara ɗan-ɗasa kwaliya tayi kyau sosai bayan ta shirya ta kashe ɗauri ba shakka tayi kyau sosai,turaruka masu kamshi ta ɗauko ta feshe jikin ta dasu,kana ta ije ta zauna jiran dawo warsa.


Oyoyo, dataji Kulsum nayi yasa tasan Daddy ne ya dawo dan haka,takalma masu tudu ta sanya kana tafara saukowa ƙasa.



Ahankali take tafya har ta kawo setop ɗin ƙar she,lokacin ita ma Momy tafito cikin shirin ta dan ko ita ba laifi tayi kyau.




Yana ƙara suwa parlour da Momy yafara cin karo,sannu da zuwa ta masa kana ta ƙarɓe jikar dake hannusa,yana mai ƙarasuwa cikin parlour.



Su Zainab gaisheshe suka farayi,ya amsa ciki da sakin fuska.


Momy ta dube shi tace,"mu ƙarasa daga ciki sai ka ɗan huta".



Ba musu yace, to muje".



part ɗin Fatima ya kalla,aikuwa tsaye ya ganta tana sakar masa murmushi mai ƙara mata kyau.





Alama yayi mata da hannu tazo.



Bamu ta fara tako ahankali har ta ƙarasu wajan da yake.



Durkusawa tayi, tayi masa sannu da zowa.



Amsawa yayi ciki da fara'a afuskar sa, tari da faɗin, "ya jikin naki".



Sai da tayi ƙasa da kanta kana tace, "Ahmdllh".




Tashi tayi domin ta koma part ɗinta.


Kallon ta yayi yace,"Fatima ki kawomin ruwa na sha".


Ahankali tace, "to Daddy".



Wani kallo ne Momy ke aika mata wanda bana ko mai bane sai na tsana.wanda ita ko Fatima bata masan tanayi ba.




Fatima tafiya tayi, ta dauko masa ruwa masu sanyi da lemun kwa-kwa,ta kawo masa,yana zaune a parlour shi shi da Momy.


Ajewa tayi domin ta tayi fiyar ta, amma yace ta zuba masa ya sha.


Ba musu ta zuba masa ta bashi ya karɓa.


Lura da kallon da Momy keje far ta dashi ne yasa ta tashi domin ta koma.


Har ta kai ƙofa fita daga parlour Daddy yace,Fatima ina zakije ki tsaye muyi fira mana".


Tace,"a'a Daddy idan kayi wanka zan dawo".



Yace,"to yanzu ko zanyi".



Tana fita Daddy ya kalle Momy yace,"ki haɗamin ruwan wanka".





tashi tayi ta haɗa masa ta dawo tace masa ta haɗa tashi yayi yaje yayi wanka ya fito.





Sai da ya kammala shirin sa sannan ya fito parlour inda ya bar Momy anan yazo ya sameta.



Zama yayi ta haɗa masa abinci ya ɗan ci bada yawa ba, tashi yayi yana faɗin,"Alhmdullah".


Momy tace, "ba dai har ka kushi ba yace,na kushi Hajiya,fita ma nakeson nayi dan jira na akeyi".



Momy tace,"haba Alhaji yaushe ka dawo da har zaka fita".



Yace,kiyi hakuri ba jimawa zanyi ba".




Adawo lafiya tayi masa kana yasa kai ya fice.


Da fitar sa part ɗin Fatima ya ƙarasa zaune ya sameta,riƙi da lattafi tana karan tawa.



Sallama yayi yana mai ƙarasuwa gab da ita.


Amsawa tayi ta mai ƙara gaida shi.

Kallon ta yayi yace,"kin ci abinci kowa?".



Kasa tayi da kanta kana tace,"a'a yanzu zanci".



Yace,"to zo muje kici sai kasha magani, dan doctor ya kawa maganin ki".




Rau-rau tayi da ido kana tace,ni fah nawarke Daddy".



Jikinsa ya jawo ta sai da ya kai bakinsa dai-dai kunne ta kana yace,baki son kije ki gada Ummah da Gwaggo,ko?".



Kallon sa tayi cikin muryar shagoɓa kana tace,"Daddy kai fa kace zaka kaini"tana matsar hawan shagoɓa.



Yace,"eh zan kai ki amma saikin ci abinci kin sha magani da".



Da hanzari ta yunkura zata tashi saman jikin sa sai ya riƙita kana yace,"so kike kiman ɓarna ko". Yana mai lalubar cikin ta.


Bata bi ta kan magar da yayi ba dan burita yanzu taje gida.



Kamar zatayi kuka tace, "Daddy sakeni naje naci sai mutafi".



Yace, "naji amma kitafi ahankali".


Tace, "to" dan ta ƙagar yasake ta.




Tashi tayi taje ta ɗauko abinci taci, kana ya bata magani ta sha, sannan yace taje ta canja kaya jikin ta waɗan da kejikin ta turare ne dasu,kuma tasan ba kyau saka turare ga macci idan zata fita.





Dan haka taje ta canza ta ɗauku faya finta ta fito tasa meshi parlour zaune yana jiranran ta.




Sai da ya kalle shigar yaga tayi mai kana yace,"su tafi".




Ahankali suke taka setop ɗin har suka sauka.


Alokacin Momy na zaune ita da yaran ta Zainab ce kawai bata wajan.




Momy kallan Daddy tayi tace,"aw bakaje ba?na ɗauka katafi".




Yace,"aa yanzu zanje"yana mai takawo dan ya fita.


Momy kallon ta ta maida ga Fatima wada kebin sa a baya kana tace,"ke ina zaki ne?".




Daddy ya juyu ya kalle Momy yace,"tare zamu fita"....bai tsaya jin me zata ceba suka ƙara gaba.



Suna kaiwa wajan da mota take driver ya buɗe musu suka shiga kana yaje suka wuce.




Momy ko har suka fita bata sani ba,dan sun barta da baki buɗe tana mamaki tare zasu fita.....







*#Comment*
*#Vote*
*#Share*






*Sumy ce*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦




*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*






®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_



```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_


Story & Written
By
*Sumy✍?*



*Dedicated to..*
_Gaskiya_ _writers_


~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~





*Page* *26*







*_________*📖 Maram ce tadube Momy tace, " wallah tun wuri ki ta kama yariyar nan birki dan inba haka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login