Showing 54001 words to 57000 words out of 64938 words

Chapter 19 - KAWAR 'YATA CE

09 Oct 2024

2509

taga Daddy rungume da Fatima lokaci ɗaya fuskar ta ta sauya amma sai ta wayin ce tayi kamar abun bai dame ta ba.




Bayan Daddy ya amsa sallama ta ƙarasa gabansu tana faɗin,




"Ashe kun dawo gashi har na shirya nasa drivir ya kaini sai Zainab ke cemin kun dawo"..tana magana tana ya mutsar fuska kamar da gaske.




Daddy yace, "koda ma aman ne ya wahal da ita amma yanzu da sauki".



Tace, "masha'Allah,Allah ya ƙara sauƙi,taƙara da cewa to Daddy su zainab meke damun ta?".




Yace, "ba komai bane sai matsalar ciki ce".





Ganban momy ne yayi mum-munar faɗuwa amma ta dage tace,



Tace, "kamar ya?ko ciki ne da ita?" ta faɗi haka muryar ta na rawa amma sai ka natsu za ka gane haka.




Cikin rashin damuwa Daddy yace, "ciki ne da ita har na tsawon wata uku".




Gaban mumy ne yayi dummmmm amma da yake ƴar duniya ce tace, "amma shine baka gaya mun nasamu ƙaruwa ba sai yanzu " tafaɗa aɗan shagwaɓan ce.



Hakuri Daddy ya bata da ƙyar ta hakura kana tace, bari taje ta haɗa ma Fatima koda tea ne ta sha.




Godiya Daddy yayi mata kana ta fice.




Da ƙyar ta ƙarasa part ɗin ta dan gabaki ɗaya tafiya gagarar ta tayi.



Tana isa ciki da ta shin hankali ta ɗau waya takira ɗiyar ta Maram ta faɗa mata abunda ke faruwa.




Sai da tagama faɗa mata kana tace, "amma yanzu zan haɗa mata tea sai na zuba wani magani wanda ko cikin ya zube baza a gane meyesa cikin zubewa ba.




Maram tace, "haka yayi Momy kiyi sauri kiyi".




Suna yin sallama bata tsaya ko ina ba sai kitchen,ruwan tea ta haɗa da madara kana ta ɗauko wani magani ta zuba a ciki sai da ta juya shi sosai ya haɗe da madara kana ta ɗauko ta kawo musu.




Sallama tayi kana ta shigo ko yanzu yadda ta barsu haka ta same su.




Ƙarasuwa tayi gaban su tace, "gashi ta tashi tasha sai ta sha magani zata ji daɗin jikin ta.



Karɓa Daddy yayi tare da yima Mumy godiya yace, "Fatima tashi ki sha".



Ba musu ta tashi dan koda ma yunwa take ji kofin yami ƙa mata ta ƙarɓa yace, "ta sha".




Kofin ta ɗauka zata kai bakin ta tare da faɗin bismillah....










*#Vote*
*Cmment*
*Shere*









*Sumy M Na'ige*🌸
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦



*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*





®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_



```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_




Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍?






*Didicated to..*
*My Shemah*🥰



~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~





*Page 42*





*_________*📖 Har ta kai bakin ta sai taji ƙarnin madarar ya dake hancin ta aikuwa lokaci ɗaya ta fara kakarin amai.




Amayar da wanda ta kurɓa tayi tare da aje kofin dan jin take zuciyar ta na tashi sosai.




Shi ko Daddy duk rikicewa yayi yana ta faɗin,



"Sannu ,meke damunki Fatima?".




Ita ko Mumy ranta ne ya ɓaci sosai gani tabbas Fatima bata sha tea ɗin da ta kawo mata ba.




Sai da aman ya lafa Daddy ya jawo ta jikin tari da faɗi,




"Mekike ji yanzu?".



Ahankali tace, "komai banji Daddy".



Momy ko cikin ranta faɗa takeyi yariyar nan munafukace fah ji yadda ta wani shige masa ajiki wai ita bata da lafiya wai me ciki.





Ƙaraso wa tayi gaban su kana tace ma Daddy, "tunda aman ya lafa kabata ta sha sai tasha magani kaga zata ji daɗin jikin ta".



Ba musu Daddy ya ɗauko kofin tea ɗin ya miƙata yace, " "sha Fatima".




Kai ta girgiza masa kana tafara magana a hankali tace, "Daddy bana son madara amai zanyi".




Sai da Momy ta fake idon Daddy ta wanka mata hara-ra kana tace, "to me kike su sai akawa miki?".




Sai da Daddy ya mai-mai ta mata kana tace,"fura nake su".




Faɗima Momy yayi abunda tace dan ƙasa-ƙasa tayi maganar dan Mumy bata fahin ta ba sai da Daddy ya faɗa mata.




Momy tace, "to bari na kawo mata" tana faɗa tana aikama teema hara-ra.




Tana fita Daddy da kansa ya kai Fatima toilet ya taima ka mata ta gyara jikin ta kana ya fito.





Kuka ta sanya masa tace sai ya kai ta gida.



Da ƙyara ya samu ta haƙura zuwa ajima zai kaita kamar yadda yace.




Mumy ko kitchen ta koma ta ɗauko fura ta sake zuba wannan maganin kana tafito domin ta kai mata.




Salamar da akayi ce ya da katar da ita daga saurin da take.




Kallon-kallon suka fara yi ma juna kana Mumy ta ƙaƙalo murmushin karfin hali tace, "yau wa muke agani agida".




Ita ma Hajiya Sa'a martanin murmushin da tayi mata ta mai da mata.




Gaisawa suka fara yi kana Hajiya Sa'a ta tambaye Mumy yara da kuma Fatima.




Sai da Mumy tayi ajiyar zuciya kana tace, "yara duk suna ɗakin su,Fatima ko batada lafiya dan yanzu itace ma zan kai ma fura tashi".




Hajiya Sa'a tace,"ash-sha meke damun ta?".



Mumy tace, "lamarin ciki ne".




Sai da Hajiya Sa'a ta dube Mumy da kyau kana tace, "tana ina yanzu?".



Sai Mumy tace, "tana ɗakin ta".




Hajiya Sa'a bata sake yiwa Mumy magana ba ta haura sama,Mumy ita ma tana bin bayan ta har suka karasa ciki.




Ko yanzu kwance take shiko Daddy na gefe ta yana jera mata sannu.



Sallama sukayi kana suka shigo .


Aikuwa yana ganin Hajiya Sa'a ya faɗa-ɗa murmushin sa kana yace,"Babbar Yaya kece agidan?".



Tace, "nice tunda ku baku neman ba aigwara na zo na-nemeku naji ko lafiya".





Sai da ya sosa kai kana yace, "Hajiya Babba hak'uri zaki ƙara yi damu yanzu ayuka sun muna yawa sasai".





Tace,hmm "ko bada aiki ba haka kuke Allah dai ya kyau ta.




Fatima ko tana jin muryar Hajiya Sa'a taji wani daɗi sosai dan haka tayun ƙura ta tashi zaune dumin su gaisa.




Fatima gaida Hajiya Sa'a tayi itama ta amsa ciki da sakin fuska haɗe dayi tamata yajikin?".




"Da sauƙi tace mata".


Mumy ta miƙo mata fura tace, "gashi ta sha sai ta sha magani dan yau kome babu acikin ta".



Hajiya Sa'a ta karɓe furar ta buɗe sai da tayi mata kallon tsaf kana ta rufe ta aje aƙasa batare da tace komai ba kuma bata ba Fatima ba.


.
Bata cema kowa komai ba suka cigaba da firar su game da yadda bikin zai kasan ce na sauran ƙannen ta.




Mumy na tsaye komai bata ce ba da taga alamun ba furar zata bata ba dan haka ta fice zuciyar ta na zafi dan a duniya bata ga abunda ta fi tsana ba irin Hajiya Sa'a,saboda tana mata shi-shige ga lamarin ta.




Sai da sukayi fira sosai kana Hajiya Sa'a tayi musu sallama dan tafiya zatayi.



Aikuwa Fatima nagani tafiya zatayi lokaci ɗaya tayi rau-rau da ido ba shiri sai ga hawaye sun fara zuba sai tafara sha-shekar kuka .




Hajiya Sa'a ta juyu ta kalle ta tace, "Fatima lafiya meke damun ki?".



Ai kamar kada tace haka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.




Kallon-kallon aka fara yi tsaka nin Hajiya Sa'a da Daddy.






Jikin shi amace yace, "wallahi ba abunda na mata Yaya".



Komai bata ce mishi ba ta ƙarasa wajan Fatima,kan ta taɗago tare da kura mata ido.



Jikin ta aɗan sanyaye tace, "Fatima me akayi miki lafiya ki gaya min kinji?".




Sautin kukan da takeyi ne ta rage kana tace,"ni zanbiki bani da lafiya".





Sai da Hajiya Sa'a ta sauke ajiyar zuciya kana tace,"to dai na kuka da ke zanje kinji".





Tace "to na daina tana mai ciki da farin ciki".





Tashi Hajiya Sa'a tayi ta fara haɗa mata kayan ta.



Da sauri Daddy ya ƙarasu gaban ta yana faɗin, "dan Allah Hajiya kada kitafi da ita wallahi komai ban mata ba kiyi haƙuri Hajiya.




Kallon sa tayi da kyau kana tace, "ai bance kayi mata wani abuba zan dai je da ita sai taji ɗan sauƙi".





Ruk'un ta ya ciga ba dayi ta bar masa matar sa amma tayi kamar bata ji shi ba.




Sai da tagama haɗa mata kayan ta kana ta bata hijab tasaka tari ƙi hannu ta suka tafi.





Haƙuri Daddy yaci gaba da bata amma taki saurarin sa har suka kawo babban paulour.




Mumy suka tarar zaune ita da yaran ta,gashe da Hajiya Sa'a sukayi kana tayi wa Mumy sallama taje hannu Fatima suka wuce.



Aikuwa Mumy naganin da Fatima za'aje wani tashin hankali ya ƙara ma-maye zuciyar ta kuma bata da halin maganar kada aje da Fatima dan tasan Hajiya Sa'a wuta ce idan aka taka ta akwai bila'i, kuma idan tayi niyar abu ba mai hanata sai Allah.





Aikuwa Daddy nagani da gaske Hajiya Sa'a keyi ya kama bakin sa yayi shiru dan yasan halin ta sarai,amma zuciyar shi ba daɗi.



Akuwa tunda ga wannan lokacin Daddy kulum yana hanyar gidan Hajiya Sa'a kuma ta hanashi ya ga Faty shi yayi magiya har ya gaji har ƙara ya kai ta ga Gwaggo amma suna magana da Gwaggo tace abar ta har taƙara jin sauki.



Shi wallahi ya gaji matar sa yake buƙata dan yanzu ƴar nacin can ta dawo masa kuma baya sun yana biye mata kuma gashi sun riƙi masa matar shi.




Koda Mumy nanan amma ya fisun ya haɗa biyu bare ma teemar sa ta daban ce agun sa.



Dan haka yaje ya sanar da Hauwa ƙawar Fatima a yanzu.




Bayan kuwa biyu Hauwa Ta shirya taje gidan Hajiya Sa'a bayan sun gaisa take tambayar ta Fatima.




Ɗakin da Fatima take Hajiya Sa'a ta kai ta.



Sai da Hajiya Sa'a ta fita kana Hauwa ta matso kusa da Fatima bayan sun gaisa Hauwa ta dube Fatima da kyau kana tace,



"Ke yanzu teema kina jin daɗin zama haka ba mijinki tari dake?".



"Wai ma me kika gaya ma Yaya Babba da har zata hana masa ganinki?"



Fatima tace, "ba abunda nace mata kuma dakika ce bana jin daɗi zama haka to bari kiji wallah ni nafi jin daɗin zama haka dan ba mai ta kuramin shi kuma Daddy ya fiye ta kurama mutum dan shi ban wani da muba".




Wani kallo Hauwa ta watsa mata kana tace,



"Sai kiyi ta zama wata rana sai akawo miki labarin zai aure Hajiya kulu".



Gaban tane ya bada dumm! kana tace,



Waye Hajiya kulu kuma?".




Komai bata ce mata mayafin ta ta yafa zata fice.




Riƙe mata maya fi Fatima tayi tace, "haba Aunty Hauwa kin san bama haka dake dan Allah ki gaya min" tana magana kamar zatayi kuka.



Kallon ta Hauwa tayi tace, "ni dai nafaɗa miki kiyi yadda nace dan inba haka ba hmmmmmm taƙara da cewa yanzu mijin ki ko gida baya zama ya can...bari nayi shuru amma inkin tashi komawa gidan mijikin to ki kirani a waya" tana faɗin haka ta fice war ta batari da ji abunda Fatima zata ce ba.






Jikin Fatima ne yayi sanyi sosai kuma lokaci ɗaya taji tana son ganin Daddy ko jinsa dan tunda tazo ko wayar sa bata ɗauka ba bare ma taji wani hali yake.....








*#Vote*
*Comment*
*Shere*







*Sumy M Na'ige*🌸
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦









*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*




®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_



```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_





Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍?




*Didicated to..*
*My Hafsa*😍




~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~





*Page 43*




*_________*📖 Jikin ta a sanyaye ta jawo wayar da ke gaban ta ta dan na masa kira tana ringing ba'a ďauka ba, har sai data yi masa kusan miss call biyar amma ba'a ɗauka ba.


Gabanta ne ya fara dukan uku-uku saki kira tayi ko nan ba'a ɗauka ba.



Ai bata san lokacin da hawaye suka fara tsiyaya a idon ta ba.




Lokaci ɗaya ta shiga rera kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.




Shi ko Daddy lokacin da ta kira bai ma san takira ba dan yanzu ba ita ba ko Mumy ta daina ganin shi kuma da Mumy ta tambaye shi sai yace mata aiki ne ke re ƙishi.




Dan yanzu ga baki ɗaya ya tare gidan Hajiya Kulu sai yadda tayi dashi.



Ita ko Mumy ta ɗauka da gaske aikin ne ke riƙeshi dan haka bata sake maganar ba,bata san Hajiya Kulu ce ta sashi agaba ba.




*Wace ce Hajiya Kulu?*


Hajiya Kulu gogagayar ƴar duniya ce ta bugawa a jari da,tunda mijin ta yarasu bata sake aure ba sai taci gaba da harkokin ta na bariki, tana da yara biyu Salim, Naja'atu,naja tayi aure har da yara biyu shi ko Salim na Dubai yana karatu.



Ita ko Hajiya Kulu bata da wani aikin da ya wuce shiga cikin ƴan siyasa da ƴan kasuwa da manya mutane data ji za'ayi wani taro ko metting to babu abunda ke hana mata zuwa ko dan ta samu wanda ya kwan ta mata arai idan taga namiji ya kwan ta mata to fah duk yadda zatayi sai tasa ya kula ta ko baya so.




Haka tafaru haɗuwa su da Daddy wata rana sun yi metting suna fitowa shi kuma yana sauri ya tafi gida dan Mumy ta kirashi tace mishi Kulsum ba lafiya har sun kaita asibiti.




Karu yaji yayi da mutum dan bai masan da mutum ba.




Kansa ya ɗago ya kalle ta, hak'uri ya bata ba tare da ya tsaya ba ya wuce war sa.




Ita ko tunda ta ganshi taji ya kwanta mata arai aikuwa tunda ga lokaci tabi duk wata hanya da zata bi har ta samu ya fara kula ta.




Taso ya aure ta amma yaki amma wannan lokaci kuma tace dole sai ya aure ta kuma da alamu zai amince.





Hankalin Fatima ya tashi sosai,bata tsaya wani abu ba tafito falo zaune ta same Hajiya Sa'a tana kallo dan haka ta ƙarasu wajan da take, zama tayi tare da gaishe ta.




Bayan sun gama gasaiwa Fatima tana son tayi mata magana kuma tana jin nauyi abunda zata faɗa ɗin.




kula da haka ɗin da Hajiya Sa'a tayi dan haka ta kalle Fatima da kyau kana tace,




"Fatima ko kina buƙatar wani abune?".




Tana son tace eh kuma da kunya ta faɗa mata abunda take su.




Mai-mai tama ta Hajiya Sa'a ta koma yi,amma sai tayi ƙarfin halin cewa "a'a ba komai Hajiya".



Bata yadda da abunda tace ba dan haka tace,



"Fatima ni aganina ni dake ba wani abin boye-boye in har kin ɗauke ni amatsayin Yaya kuma uwa ina son ki gayamin meke da munki?".




Shuru Fatima tayi sai can ta numfasa kana tace,



"Dama ba komai ba ne Daddy ne naga ya bar zowa gidan nan kwana biyu"...tana faɗa tanayin ƙasa da kanta muryar tana rawa.




Sai da Hajiya Sa'a tana numfasa kana tace, "kada ki damu anjima zan neme shi naji ko lafiya" daga haka bata sake magana ba dan ta kula Fatima tana son ta kuma gidan mijin ta kuma ita bata son ta koma yanzu sai taji sauƙi laulayin da take yi.




Ita ko Fatima duk kunya ta bi-biye ta saboda abunda ta faɗa gani take bata yi dai-dai ba da ƙyar ta tashi ta kuma ɗakin ta.




Bayan magarb Hajiya Sa'a takira Daddy tace gobe yazo ya d'au Fatima.




Sosai Daddy yaji daɗin abunda ta cemasa kuma wani gefe fargaba yake yadda zai tun kare Fatima da Hajiya Sa'a da maganar auren Hajiya Kulu,duk da shi har yanzu baya jinta aran sa amma gani yake gwara ya aure ta zaifi.





Washi gari da kusan ƙarfe goma sai ga mai gyaran jiki da Hajiya Sa'a takira ta zo.



Bayan sun gaisa da ita Hajiya Sa'a ta kai ta ɗakin Fatima tace mata ga mai gyaran jiki za'ayi mata har kitso da lalle.




Shuru Fatima tayi tana tunanin gyaran jikin me za'ayi mata.



Kamar Hajiya Sa'a ta san me take tunani sai tace, "Fatima da taga ma miki sai ki shirya dan mijinki zai zo ya ɗauke ki kinji" bata bari taji me Fatima zata ce ba ta fice warta aɗakin.




Binti da kallo Fatima tayi aikuwa ba bashiri sai ga hawaye sun fara zuba sai kuka.



Wayar ta ta ɗauko ta kira Hauwa ta ta faɗa mata yadda sukayi da Hajiya Sa'a.



Haƙuri Hauwa ta bata kana tace ta daina kuka yanzu ga tannan zowa gidan.






Koda Hauwa ta ƙarasu har in fara mata gyaran jiki tana zowa tafara kiran "amaryar Daddy yau kam ba zai gane ki ba haka" tsaya kala-kala ta dan ga yi mata bayan ta gama zama tayi suka fara fira.




Sunan ta ta kira har sau uku tace, "Fatima ina son ki bani arun hankalinki idan kin koma ki ƙara saka mijinki ajinki sosai,dan gaskya bazan ɓoye miki ba aikawai aiki ga banki amma idan kika ƙara saka shi jikin ki ko meye zai zo miki da sauki insha Allah".




Haka dai suka cigaba da fira har aka gama mata gyaran jikin,Hajiya Sa'a tazo tace tayi sauri ta shirya dan ga Daddy nan ahanya.



Hauwa kayan da tazo mata dasu na ƙamshi da gyaran jiki ta bata kanan tayi mata sallam ta wuce war ta.






Hauwa na fita Fatima ta shiga toilet tayi wanka bayan ta fito daga wanka sosai ta ɓata lokaci wajan kwalliya tayi kyau sosai bare gashi ta sha gyara kuma abu ga mai ƙaramin ciki.






Ƙofar da aka turuce yasa ta ɗago da kan ta.




Hajiya Sa'a ce ta shigo tace, "Fatima inkin gama ki fito yana jiran ki kuma dan Allah ina son ki ƙara da gewa da addu'a sosai kuma idan kinga abunda bai miki ba to ki kirani ki faɗamin dan haka tashi muje kada yaga kin daɗe".






Komai Fatima bata ce ba dan ita bata ta so ta koma yanzu ba tadai mata magana ne dan ta ganshi.




Mayafin ta ta yafa ta fito ahankali take tafiya har ta ƙarasu parlour .



Zaune yake yana fira da Hajiya Sa'a har ta ƙarasu wajan da suke .



Tashi yayi yana cewa, "Hajiya mudai zamu wuce dan yamma tayi".




Tace, "to Allah ya ƙiyaye ya kaiku lafiya kuma dan Allah arinƙa kula da ita kasan yanzu ba ita kaɗai take ba".




Sai da ya dobe Fatim kana yace, "kada kidamu Hajiya tah insha'Allahu zan ƙara kula ta sosai".


Rakiya ta musu har wajan da sukayi parking ďin motor su.



Sai da suka shiga driver yaje

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login