Showing 60001 words to 63000 words out of 64938 words
abun na Mumy ya sauya ne.
Itako Mumy yanzu abunda bata so duk bai wuce zowan da Hajiya Kaka keyi lokaci-lokaci ba,dan ko tana son tayi abu to idan Hajiya Kaka na nan baza ta samu damar insa ba.
Yau ma kamar kullum suna gama bearkfast Daddy ya fice yaje wajan aiki,ita ko tana gamawa ta koma part ɗinta ta kwanta dan yau haka takejin jikin ta duk ba daɗi.
Ita ko Mumy na kule da ita, dan haka itama tashi tayi taje ɗakin Fatima taga ni ko da gaske bata da lafiya .
Tana shiga ta same ta kwance tana ta ya tsane fuska.
Ƙarasuwa tayi wajen da take kwance kana tace, "Fatima baki da lafiya ne?".
A hankali ta ɗago kanta murya a dashe bata fita sosai tace "eh Mumy ban da lafiya".
Tambayoye Mumy tayi mata ita ko ta bata amsa,Mumy naji duk alamun haihuwa ne tace "Fatima bari nazo kin ji Allah ya sauke ki lafiya".
Fita tayi taje ɗakin ta ta ɗauko wannan ƙullin maganin da malamin ta ya bata ta haɗe da ruwa ta zo wajan Fatima ta domin ta bata tasha.
Koda ta koma Fatima ta fara fita daga haiya cin ta, da sauri ta ƙarasu wajan da take tana yi mata sannu.
Ruwan magani da ke cikin ƙofin ta ɗauko ta ce "Karɓa kisha Fatima zaki samu sauƙi yanzu......
Kunsan abu ga mai na ƙuda kome ye aka bashi ƙarɓa yake yi, in har ance za'a samu sauƙi..
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*Summy M Na'ige*🌸
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_
Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍?
*Didicated to*
*Family*😘
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*Page 47*
*_________*📖 Kafin suyi mata magana tace, kone ƴan uwan Fatima ?".
Kaka Amo tayi sauri tace ta haihune?".
Sai nurse ɗin tace "eh ta haihu amma bazan faɗe me aka samu ba sai kun ban goron albishir".
Rigan-gan akayi wajan bata Daddy da Hajiya Sa'a,Daddy kuɗe ya bata masu yawan gaske wanda shi kansa bai san yawan su ba.
Hajiya Sa'a ma haka,ita kanta nurse ɗin abun ya bata mamaki sosai godiya ta musu kana tace musu "an haife kyawa-wan twins maza gasu can ana gyaransu bari na ɗauko muko ku gani".
Ai tun bata rufe bakin ta ba Daddy ya fara yiwa Allah kirari yana masa gode akan kyautar da ya bashi.
Itako Hajiya Sa'a har da biye ma Kaka Amo tayi wajan rawa sunayi suna godeya ga Allah da ya sauke ta lafiya.
Hajiya Sa'a kiran ƴan uwa da abukan arziki tayi ta faɗa musu suma sun taya su murna sosai.
Suna cikin haka sai ga nurses sun fito kowace ɗauke da daya ahannun ta.
Da sauri suka ƙarasa garesu suka karɓe yaran suna murna.
Sai da suka gama gani Daddy ya karɓa yayi musu huɗe kana yasama rayuwar su albarka ciki da so da ƙaunan yaran.
Nurse ɗin ya kalla yace "ina ita Mamar su?".
Sai nurse ɗin tace "tana ɗaki tana hutawa amma zaga iya shiga ka ganta".
Tun bata refe baki ba Daddy yace "muje ki kaini".
Suma su Hajiya Sa'a da Kaka Amo bin su sukayi ɗakin da Fatima take.
Kuda suka shiga tana zaune saman gado kamar ba ita ce Daddy ya ɗauko ba rai a hannun Allah.
Ƙarasuwa sukayi wajan ta suka fara yimata yajiki .
Bayan ta amsa suka bata yaran da ta haifa tagani amma saboda kunya cemusu tayi ta gansu.
Da ƙyar suka samu ta karɓa yaran.
Bayan awa biyar aka sallame ta dan ba abunda ke damun ta sai rashi ƙarfin jikin da bata da, koshi sunce zowa wani lokaci zataji ta dai-dai.
Gaba ki ɗaya Daddy ya manta bai kira Mumy ya faɗa mata ba.
Hajiya Shafa ce ta kira ta dan suma har sunji labarin haihuwar Fatima ransu baiyi daɗe ba dan ba haka suka so ba.
Dan kishayar ta Nafisa har rawa sai da tayi ita da sauran amaren saboda murna.
Sai da takira har sau biyu kana Mumy ta ɗauka dan tana ɗaki tana bakin cikin zowan Daddy gida dan son tayi abar ta har ta gama shan woya kafin akai ta hospatal kafi wani lokaci komeye acinkin ya mutu.
Tana cikin haka wayar ta ta fara rura har taso taƙi ɗagawa amma data ga andame ta dakira dan haka ta ɗauka.
Sunan Hajiya Shafa tagani dan haka tayi sauri ta kara akunnen ta.
Bayan sun gaisa sai Hajiya Shafa tace "ko har dake kuna hospatal?".
Sai Mumy tace "warin me?".
Sai Hajiya Shafa tace, "au baki masan ki shiyarki ta haihuba kenan dan naga ko kiran mu bakiyi ba".
Tana cewa haka sai da gaban Mumy ya faɗ baki na karkarwa Mumy tace "yaushe ta haihu kuma me ta haifa, taƙara da cewa nasan kome ta haifa ya mutu".
Sai da tagama jerama Hajiya Shafa tambayoye kana ta buɗe baki tace "ko ɗaya dan niman yanzu naji mutumi yar ta ta fito tana guɗa tana rawa wai anhaifar musu ƴan biyu kuma gaba ɗayan su maza ne".
Ai tun Hajiya Shafa bata kai ƙarshin zancin ba Mumy ta sake waya ta faɗi ƙasa tace tas...
Tan gaɗi ta farayi kamar zata faɗi,kujerar dake kusa da ita tariƙe kana ta fara magana cikin wata muryar kamar ta ƙatti.
Tana faɗin wallahi ƙarya ne ba wata wadda zata haife ɗa namiji a wannan gidan ta zauna lafiya matuƙar ina raye".
Hauka Mumy ta farayi har da cewa ba jinin Daddy ne ba in ma da gaske anhaihu ɗin.
Tana cikin wannan haukar Daddy ya shigo da sauri ta ƙarasa gareshi tace "Daddy Zainab ina Fatima ɗin? tunda har zaka ɗauke ta amma baka sanar dani ba".
Yace "albishirin ki
kin samu yara biyu dukan su maza".
Wannan karun Mumy ta sauya ba kamar da ba dan ƙiri-ƙiri tace "da gaske ko ɗiyan kane? kodai wani wajan tasa musu ta ƙaƙabamaka kai ko ido rufe zaka karɓa".....bai bari ta kai ƙarshin zancin ba ya wanke ta da mari har bayu.
Yana huci yana nunin ta da ɗan ya tsa kana yace "kin san me kika faɗa kowa, yaran nawa zaki fara sheganta su kuma ina raye".
Ba'abun da bai ce mata ba itama haka daga bisani yaga abun nata kamar da taɓin hankali dan haka yafice yabar mata gidan gabaki ɗaya.
Duk abunda akeyina hidamar suna Mumy bataje taga yaran nan ba kuma ta hana yaran ta zowa Zainab ka dai ce taje amma batare da sanin Mumy ba dan tace duk wanda yayi mata maganar Fatima sai ta illatashi.
Mumy takoma kamar sabon kamun hauka dan bataji bata gani ko ina zowa takeyi dan akashe yaran ita dai burin ta su bar numfashi.
```(Allah sarki su yara mesuka sani ko me suka yamata.
Dan Allah ƴan uwana mu daina ƙazamin kishi dan bashida anfani wallahi wani kishi illah ne ga remu.
Kowa na dakishe amma kada kishi yasa muhaɗa Allah dawani,dan haka mukeyaye ƴan uwana.
Allah yasa mufi ƙarfin zukatan mu kuma ya kare mu daga ƙazamin kishi ameen. ```)
Inyi shagalin wajan sunan yaran inda Daddy yace ba zai sauya musu suna ba haka zai a barsu.
Sosai nera tayi kuka dan ba abunda Daddy bai yi mata ba, har sauyama iyayen ta gida yayi kuma yaba mahaifin ta mota har ƙanwar ta sai da yaba mota itama Kaka Amo sai da yayi mata kyau ta mai girma Hajiya Sa'a ma tawa Kaka Amo, aikuwa Kaka Amo kamar tayi hauka dun daɗi.
Duk hidamar da akeyi ta sunan su alhasan bawan da group7 suka je kuma basuyi murna ba.
Watan Fatima ɗaya da haihuwa akayi auren su Zainab da Nabila,anyi shagalin biki sosai anka kashe nera Mumy ma ta narke nara sosai.
Bayan bikin su Zainab da sati uku Daddy yama tsama Hajiya Sa'a amaidam masa da Fatima.
Ba yadda ta iya tashirya taje gidan iyayen ta ta faɗa musu saƙon Daddy kafi kowa yayi magana Kaka Amo tace wani sati da kanta zata maida Fatima ita kam Ummah bata so haka ba, dan taso abar Fatima har tayi arba'in biyu amma ga yadda Kaka Amo tace kuma yadda tace haka za'ayi dan haka bata ce komai ba tayi shuru dan bata iyawa da yayyaƙar da zata mata.
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*Summy M Na'ige*🌸
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_
Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍?
*Didicated to..*
*My lovely Aunty*🥰🥰🥰🥰🥰?
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*Godiya mai tarin yawa ga hasken gaskiya Writers,ina matuƙar jinjina a gareku da godaya agareku sarakan haƙuri da kawaici da yafiya, ina ƙara godiya gareku na yadda kuka fara fitar da tauraruwa ta social media har take haskawa banda kamarku My Aunty nah (Mrs xerks) &Ummu Nabil*?
*Ina sonku*
*irin* *sosai ɗin nan Allah yabar min ku*😘
*Duk inda kuke inanan liƙe daku koda zakuyi min gore bazan barku ba bare nasan ba halinku bane yima mutum gore*😁
*Allah ya baku nasarar abunda kuke nema duniya da lafira Allah ya ƙaramuku basira mai yawa wadda zaku anfanar da dubban mutane da ita sabida Allah👌 Ameen ya Allah.*
*Ina ƙaunarku all gaskya writers😘*
*Masu iya magana sunce, da wasa da yaro gwanda kwana da yunwa*👌
*Page 48*
*_________*📖
Bayan sati ɗaya da dawowar Fatima Kulsum taje ta karɓo Husaini tazo da shi wajan Mumy aikuwa Mumy naganin tazu da shi ta karɓeshi cikin mutumci tace ma Kulsum taje ta karɓo ɗaya.
Da gudun ta taje dumin ta karɓo Alhasan.
Tana fita Mumy tayi sauri taje ta ɗauko wani fauzin tahaɗa shi da madara ta fara bashi.
Suna cikin haka sai ga Kulsum ɗauke da ɗayan,da sauri Mumy ta karɓeshi tace mata ta ɗauke Husaini ta maida ita ko ta karɓi Alhasan.
Haka kowa akayi Kulsum ta ɗauke shi ta maida tana fita Mumy ta ɗauko Alhasan ta bashi wannan madarar mai haɗe da fauzin.
Ko da Kulsum ta dawo Mumy na bashi madara tace "Mumy ashe ya iya shan madara" tana faɗa tana dariya jin daɗi.
Mumy tace, "eh ya iya mana ba gashi yana sha ba".
Mumy sai da taga ya sha madara sosai kana tace ma Kulsum ta maidashi wajan Mamar sa kuka yakeyi.
Kulsum ko ta dauka ta maida shi wajan Fatima.
Tana zuwa tace ma Fatima Mumy tace na maida shi kuka yakeyi dan har madara ta bashi yaki ya daina kuka.
Karɓar sa Fatima tayi tayi masa wanka ta kwantar da su.
Bayan minti ashirin da maida su sai ga yara sun fara fitar da kumfa abaki suna yin wata irin miƙa kamar zasu mutu.
Aikuwa Fatima na gani hak lokaci ɗaya ta riki ce tama rasa me zatayi sai can dabara ta faɗu mata ta ɗau waya ta kira Daddy tana kuka ta faɗa masa abunda ke faru.
Baƙara min ta shin hankali ya shiga ba lokacin da tafaɗa masa haka da sauri ya bar abunda yakeyi ya zo gida.
Koda ya ƙarasu bai tsaya komai ba ya ɗaukesu hankali ta she ya kai su hospatal ɗin dake kusa da su.
Taimakun gwagawa likitoci suka fara basu.
Shiko Daddy sai safa da marwa yakeyi a hospatal.
Ita ko Fatima na zaune kamar ba abunda ke damun ta, amma azuciyar ta tafima Daddy shiga tashin hankali.
*****************
Ita ko Hajiya Kulu tunda Daddy ya dai na kulata taje wajan Malamin ta akace sai ya rabu da Fatima zai dawo dai-dai,to tayi yawo wajan Malamai har tagaji amma bata samu nasara ba acan ne garin yawon ta tahaɗu da wani Alhaji tundaga wannan lokaci suke tare ko ina zaije da ita yake zowa.
Bayan wata uku da haɗuwar ta da shi har tafara tunanin yadda zata dawo wajan Daddy sai ciyo ya kamata ba sauki har sai da akaje hospatal.
Ana mata gwajin farin sai aka gano tana dauke da cuta mai karye gargowar jiki ajikin ta.
Tashiga tashin hankali sosai kuma taneme wannan Alhajin ƙasa ko sama amma bata ganshi ba tayi kuka har ta gaji ba dan son ranta ba ta fara shan magani dan lokaci ɗaya jikin ta ya sauya kowa ya san halin da ta ke ciki har yaran ta sunyi kuka har sun gaji sunyi tir da hali irin na mahaifitar su.
Daga baya da suka ga yadda ta koma lokaci ɗaya dan haka suka sauko daga fushin da sukeyi da ita suka fara bata kulawa.
Amma lokaci-lokaci take zuwa kaɓar magani amma kamar bata sha dan har yanzu jikin nata bashi da kyau gani.
Sunfi awa biyu kafin likitoci su fito.
Ɗaya daga cikin Doctors ɗin da suka fito yace ma Daddy ya sameshi office dan haka ba musu suka biyu bayan shi har ita Fatima.
Bayan sun zauna dactor kewa Daddy bayani kan yaran yace, "ba komai aka basu suka sha ba sai guba mai illah acikin ɗan adam yace amma sunyi ƙoƙari wajan dawo da lafiyar su amma yanzu muna jiran farfaɗowar su lokaci kaɗan amma kuyi addu'a dan koshi abune mai wuyar gaske".
Hankalin Daddy sosai ya tashi lokaci ɗaya ya dawo da kallon sa ga Fatima.
Tambayar ta ya farayi waya ba yaran sa guba.
Irin yadda yake mata magana yasa ta rikice tama rasa me zata ce masa.
Magana yake mata amma takasa koda mutsa baki bare yasa ran zata ce wani abu.
Ai da zuciyar sa ta rufe basan lokacin da ya kai mata mari har biyu ba.
Itako tana can tana tunanin yadda zatace masa tasan komai basa sha inba nonoba sai madarar da Kulsum tace Mumy ta basu ɗazo kuma tana gudun tace Mumy ta basu madara wata rigima ta tashi dan yace ko ruwa kada abasu sai sun kai wata bakwai.
Tana cikin wannan tunanin taji saukar mari har biyu alokaci ɗaya.
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*Summy M Na'ige*🌸
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_
Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍?
*Didicated to..*
*All Gaskiya writers*😘
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*A RAYUWA ILIMI NA DA DAƊI IDAN KASAMU ƘARAN CIN ƊAYA DAGA CIKIN BIYU NAN RAYUWA BAZATAYI DAƊI BA, AllAH KABAMU IKON NEMAN ILIMIN DUNIYA DA LAFIRA*
*AMEEN YA AllAH.🙏*
*Page 49*
*_________*📖 Kanta ta ɗago ta kalleshi shiko inba huci ba ba'abunda ya keyi.
Nunin ta ya keyi da ɗan yatsa kana yace "kigaya min me kika ba yarana wanda ke neman ya ka shesu".
Komai bata ce masa ba dan irin yadda taga yana magana ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba.
Tashi tayi taje nesa kaɗan dashi ta kira Hajiya Sa'a ta faɗa mata abunda ke faru.
Bata jima da kiran taba sai gata tazo .
Yadda taga Daddy ko ita hankalin ta ya tashi amma ta dake ta fara bashi haƙuri da nuna masa cewa yaran zasu ta shi.
Cikin ikon Allah yaran na cika awa uku suka fara mutsawa.
Doctor suka kira ya ƙara duba yaran ya tabbatar musu da lafiyar su sannan Daddy ya samu natsowa.
Daddy ko ya nace sai Fatima ta gaya masa me taba yaran shi.
Badan taso ba tayi masa bayani tace bata basu komai ba inba Kulsum da tace Mumy ta basu madara ba.
.
Ai tun bata ƙarasa faɗa ba ya kama hanyar fita Hajiya Sa'a na kiran sa amma bai san tanayi ba.
Sosai yasa direba gudu basu ɗau wani lokaci ba suka ƙarasu gidan.
Kafin driver yayi packing Daddy ya buɗe murfin mota yafito.
Ba kowa a parlour dan haka da sauri ya ƙarasa part ɗin Mumy .
Koda yaje har zai ƙwalamata kira sai yaji tana waya haɗe da wata irin dariya .
Bai ce komai ba dan abun mamaki ya bashi na wannan dariyar da takeyi.
Wayar ta taci gaba da yi ita da Hajiya Shafa tana bata labarin yadda akayi taba yaran poisen suka sha har yadda taje wajan wani Malami wanda yace a cikin satin nan Daddy sai ya sake Fatima kome suke ta ƙama da shi .
Firar su suka cigaba dayi sai da suka gama kana suka aje wayar Mumy tayi haka ta ɗago kanta suka haɗa ido da Daddy aikuwa ba shiri ta tashi zaune tana burin kunya.
Shiko Daddy gaba ki ɗaya yarasa me zai ce mata abun duniya ya taru yayi masa tsaye azuciya .
Mumy ko gaba ki ɗaya jikin ta yafara karkarwa harda kukan munafurci ta farayi.
Har ta buɗe baki dumin tayi masa magana amma ya daka mata tsawa yace "duk abunda zaki faɗa bana son ji,dan haka kitashi kibarmin gidana na sakeki saki biyu, kuma kisani komai kikayi min na barki da Allah kuma kanki kika cuta bani ba".
Yana kaiwa anan ya ficewar sa zuciyar sa na ƙuna dan ji yake kamar ya faɗi, ikon Allah ne ya kaishi ɗakin sa ya samu ya zauna kana ya ɗauko magani ya sha sannan ya ɗan kwanta.
Ita ko Mumy ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba dan bata taɓa tunanin akwai lokacin da Daddy zai'ayi furta kalmar saki agare ta ba.
Sosai ta shiga tashin hankali waya ta ɗauko dan ta kira Hajiya Shafa ta gaya mata abunda ake ciki.
Kiran ta tayi amma har ta tsinke bata ɗauka ba har sau biyar ta kira batayi picking ba sosai hankalin ta ya ƙara tashi.
Itako Hajiya Shafa koda Mumy ta kira itama tana cikin nata tashin hankali dan Alhajin Aliyu yazu wucewa yaji tana waya tana dariya abunda ta faɗi ne yayi matuƙar bashi tsoro da mamaki hankalin sa ya tashi dan haka bai san lokacin da yaki feta da mariba har sau uku lokaci ɗaya, sai da yaci mata mutunci sosai kana ya bata takardar sakin ta itama biyu