Showing 39001 words to 42000 words out of 64938 words
komai yasa tasa bokanta yayi mata aiki ba sai dan yazama mallakinta ita kadai.
Tunda taga yanayin da yashiga tafara jin wani sanyin daɗi ya rufeta.
Aikuwa tana gani haka ta janye shi daga jikinta cikin murya mai jan hankali da iya bariki tace, "sakeni koda ma nazo ne mu gaisa kawai, kuma gashi natarar aiki kakeyi".
Cikin muryarsa data fara dushewa yace, "kiyi hakura zan ajiye aikin har kitafi, kibarni mu gaisa please ".
Kamar baza tayi magana ba tace, "a'a bazan tsaya ba sai dai kazo muje gidana".
Ba musu yace, "muje to".
Wani farin cikine ya lubeta bata san lokacin da takai masa kiss a lips ba, shiko kamar jira yake yafara mayar mata da martani da ƙyar tasamu ya barta.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan shi kira yace zaifita. adawo lafiya sukayi masa kana suka wuce shida ita.
Tunda suka shiga gidan ta tafara rikitar dashi gabaki ɗaya ya manta da kowa bare wata mai suna Fatima.
Dan koda ta kirashi bai masan a ina wayar take ba.
Bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita, dan ko dama har barci akwai acikinta.
12:pm dai-dai motocin group7,suka fara shigowa gida kowanin su cikin shiga ta alfarma suka fara shigowa, inda aka tanadar musu Momy ta nuna musu suka zauna d'aya bayan d'aya suka fara zuwa har suka kai su bakwai.
Ko wacce daga cikin su idan zata shigo sai ta rangwaɗa guɗa, Hajiya Hafsa ta dubi Momy tace, Hajiya Hadiza naga har ƙiba kinya fah mi yabaki daga jiya zuwa yau"tana mai sanya dariya.
Saida suka tafa kana tace, "komai ma yabani tunda yanzu sai yadda nace".
Aikuwa gabaki d'ayansu suka tafa sukayi wa kansu kirari suna faɗin, sai mu group7 bamu ba kishiya duk wanda yace zai ja damu yayi k'arya. amma idan zaka iya kazo ka gwada.
Haka dai sukayi tayiwa kansu kirari, daga baya sukaci suka sha har da taka rawa sannan sukace akira musu Fatima su ganta.
Momy Kulsum takira tace taje takira Fatima.
Koda Kulsum taje kwance ta sameta tana bacci dagani ba barcin daɗi ne takeyi ba.
Sai data ƙaraso gabanta tafara faɗin, "Aunty, Aunty, kitashi Momy na nemanki".
A firgece ta farka tana faɗin, Kulsum ina Momy take?".
Kulsum tace, "tana parlour tana jiranki".
Fatima tace, "to je yanzu zanzo".
Har Kulsum zata tafi sai kuma tadawo tace, "Aunty hala baki da lafiya ne"?
Har taso tace eh kuma tafasa tace, "lafiya ta ƙalau bacci daine bai ishe niba".
Kulsum tace, "to Aunty idan kika dawo sai kiyi ta barcin ki".
Gajiya tayi da maganar kulsum dan haka tace, Kulsum je kice mata gani nan zuwa kinji".
Aikuwa da gudunta tafice.
Itama Fatima tana ganin tafita tashi tayi da ƙyar ta saka hijab nata kana ta safko, tun bata karasa ba tafara jin hayaniya aikuwa ba shiri gabanta yafara duka uku-uku.
A hankali take tafiya har takawo cikin falon.
Tunda ta tunkaro su suka fara antaya mata harara,nesa dasu ta durƙusa tace, "Momy gani".
saida ta aikamata kallon banza sannan tace, "hala jakar uwarki bata koya miki yadda ake gaida mutane ba? ".
Idon ta tap da hawaye tafara girgiza kai hawaye na zuba a idonta.
Gaishe su ta farayi amma ba wanda ya ƙarɓa mata.
Hajiya Binta cikin tsawa tace, "kitashi kibamu wuri dan ni ko ganinki bana sonyi".
Jikinta na karkarwa ta miƙe zata bar wurin cikin sauri Hajiya Hafsa tace, "ke zonan nagani naga kamar cikine da ita".
A firgice Momy ta mik'e tsaye tana faɗin, "ciki kuma?????"
Sai Hajiya Shafa tace, "ina wadda ko kusantar ta bai ta bayiba ina wani zancen ciki sai dai in wani taje yayi mata amma ba Alhaji ba, dan Malam yace bazai iya kusantar taba har su rabu kunga ko ba wani ciki bakin ciki ne dai zai kasheta".
Sai a lokacin Momy ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi kana tace, wallah yau dana ci ubanta kuma da yanzu zanje a zubar dashi, dubanta ta kai ga Fatima da jikinta ke karkarwa tace bazaki bar wurin nan ba ko sai na ci ubanki".
Aikuwa bata bari ta ƙarasa zancen ba ta tashi da gudunta tabar wajan.
Haka dai sukayi ta k'ullawa da warwarewa har dai suka samu mafita sannan kowa cikinsu ta kama gabanta.
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya, dan Fatima kullum sai abunda yayi gaba ga ciyo ga wahala gashi rabon da taga Daddy har ta manta.
Kuma ko wayar da take kiransa da ita tunda Nabila ta ganta ta ƙarɓeta shiyasa yanzu kowa batada labarinshi.
Dan shima Daddy yanzu yana kwana biyu bai kwana gida ba, yana can ya tare gidan Hajiya Kulu.
Ita ko Momy ko ajikinta dan yanzu taga ko maganar Fatima ba yayi gaba d'aya ya manta da ita......
*By Sumy?*
*Comment*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*_typing✍?._*
*ƘAWAR ƳA TA CE*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.?
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇?*_
*Story & wrtten*
By
*Sumy?*
*Dedicated to*
*Khausar*😍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.
```BISMILLAH``` ```RAHAMANIR``` ```RAHIM```
*Page* 3?1?
*_______📖* Yau ma kamar kullum tana gama sallah asuba ta maga azkar ɗin da takeyi, tashi tayi taje kitchen domin ta fara haɗa musu breakfast.
Tana fitowa falo taga gabaki ɗaya ya yamutsa kamar ba jiya da yamma tayi gyara shiba.
Dan haka sai da ta gama gyaran shi sannan ta wuce kitchen ta haɗa musu breakfast takai dinning ta jera.
Tana cikin jera abinci saman dinnig, sai ga Daddy ya shigo falon, dan sai yanzu ya dawo daga masallace.
Tunda ya fara shigowa parlour ya kejin wani ƙamshi mai daɗi ya fara ziyar hancinsa.
Ta kunsa ya ƙara domin ya ƙarasa parlour ya zauna ko new ɗin safe ya kalla.
A hankali yake tafiya har ya kawo cikin falon, har zai zama bisa ɗayan kujerun da ke falon, sai idon shi ya kai gareta tana tsaye tana jera abinci saman darning.
Ido ya zuba mata yana kallonta, tunani ya shiga yi ina yasan wannan?har yaso ya tuni nan take zuciyar sa ta fara yi masa zafi sosai, bashiri ya kauda wannan tunanin.
Parlour ma ga baki ɗaya yaji bazai iya zama ba, dan haka ya tashi domin ya koma part ɗinsa ya kwanta koda zai ji damar zuciyar sa dake masa zafi.
Mutsen da taji ne yasa ta ɗago kai ta kalle taga ko Momy ce dan tunda ya shigo bata ma sani ba dan gabaki ɗaya ta maida hankalinta ga aikin data keyi.
Aikuwa tana ɗago kanta suka haɗa ido dashi gabanta ne ya faɗi, dan rabun da ta sanya shi a ido tun lokacin da yace zai kaita gidan su.
Gaba d'ayan su kowane kallon ɗan wun sa yake, ita tana mishi kallon, Daddy mena maka,shiko yana yi mata kallon ina ya santa.
A hankali ta buɗe baki dan tayi masa magana, har zatayi taji mutsi kamar za ashigo dan haka da sauri ta koma kitchen.
Momy ce ta fito daga part ɗinta, Daddy ta gani tsaye da haka da hanzarinta ta ƙarasu gaban sa tana faɗin.
Alhaji ka dawo ne? Kallon ta yayi fuskar sa ɗauke da murmushi yace, "eh yanzu na dawo kuma yanzu nake son nafita dan akwai wani meeting ɗin da zamuyi yanzu, dan haka ki haɗa min breakfast ki kamin ɗakina dan yanzu wanka zan shiga".
Tace, "to Alhaji".
Wanjan dinning ta ƙarasa domin ta had'a masa abinda yace har ta fara haɗawa sai ga Fatima ta fito daga kitchen zata koma part ɗinta.
Momy ce ta kalleta a ya tsane tace, "kizo ki had'a ma mijina breakfast dan waya nake so nayi dan haka kiyi sauri ki haɗa ki kai masa part ɗinshi dan haka kiyi sauri bana son shiriri ta".
Tana gama faɗin haka ta wuce zuwa parta ɗinta.
T ajima tsaye kafin ta ƙaraso wajan dinnig, ta fara haɗa masa duk abinda tasan yana da buƙata, kana ta ɗauka zuwa part ɗinsa.
A hankali take ta fiya har takai falon sa, kuma shigar ta tayi dai-dai da fitowar sa bedroom ɗinsa.
ido ya kife ta dasu ya fara tunani ina yasanta? Kayan dake hannu ta ta aje kana tafara taku a hankali har ta kawo gabansa.
Durkusawa tayi hawaye na zuba a idon ta, kana tafar faɗin.
"Daddy dan Allah idan wani laifi nama maka dan Allah kaya feni please". tana mai sanya masa kuka mai cin zuciya.
Shi dai sai kallon ta yake kamar ya santa amma ya kasa ganu ina ya santa, dan haka yace, "ke waya baki damar shigowa part ɗina a matsayiki na yar akin?".
Kuka data takeyi tada kata kanta ɗago ta kalle shi tace.
"Daddy nice fah Fatima? Duba kagani ba tar aiki ceba".
Ai bata kai da ƙarasawa ba ya daka mata tsawa mai ban firigi ta wanda tasa jikinta ya fara karkarwa lokaci daya.
Bashiri ta mike tsaya, Hanyar fita ya fara nuna mata dan ko magana baya son yayi mata dan haka da hannu yayi mata nuni da tafita.
Da gudu ta tabar ɗakin tana mai zubda hawaye, part ɗinta ta wuce ta faɗa kan gado tafara sabon kuka mai ciki da kunar zuciya.
Ta jima tana kuka, kukan da take taga ba shine mafita ba dan haka bashiri ta tashi, hijab ɗinta ta tasaka tafito.
A hankali take tafiya har ta kawo parlour.
Tayi sa'a kowa babu dan haka cikin sauri tafit harbar gidan.
Tana kawo wa geta mai gida ya gaidata kana ya ɓuɗe mata tafice.
Tana fita ta fara tafiya har ta kawo bakin titi kuma kawo war ta yayi dai-dai da zowan mai adedeta, taran sa tayi sai da ta shiga take faɗa masa uguwar da zai kaita.
Kana yaja suka tafi......
*Sumy*?
*Comment*
Nd
*Shere*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*_typing✍?._*
*ƘAWAR ƳA TA CE*
®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*.?
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira_.}
```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN K'ARFE•🏇?*_
*Story & written*
By
*Summy*?
```Dedicated``` ```to```
*My daughter*🥰
*(Zainab)*
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.
*BISMILLAH RAHAMANR RAHAM*
*Page* 3?2?
*_______📖* Tafiya sukeyi basu tsaye ko ina ba sai wata ungowa mai ƙarancin jama'a.
Bakin wani k'ofar gida tace ya sauke ta,fita tayi ta bashi ɗari biyar, ko canji bata tsaya karɓa ba ta ƙarasa cikin gidan.
Da sallama tashiga gadan, matar gidan ta amsa mata, kana tace ta wuce ta zauna.
Sai da ta zauna kana ta gaishe ta tana cewa, "Fatima yau kece a gidan mu dafan dai lafiya kuke?".
Fatima sai da tayi k'asa da kanta tace, "Lafiya ƙalau muke mama, inasu Nafisa?".
Tace, "duk sunje makaranta".
Shuru ya biyo baya, sai da Fatima ta nunfasa kana tace, "Mama malam baya nan ne?".
Sai da ta kalle Fatima tace, "wallahi bai jima da fita ba, amma bari na kira shi in bai yi nisa ba nace mishi gaki kinzo".
Fatima tace "tau Mama nagode".
Waya ta ɗauko takira shi ta faɗa masa ga ɗalibar shi Fatima tazo neman sa.
Yace ta jira shi gashi nan zuwa. Mama kallon Fatima tayi ta faɗamata yadda yace.
Tace, "tau mama nagode".
Ba tajima da kiran sa ba sai gashi yazo cikin hanzarin sa.
Da sallama yashiga gidan. Sai da suka amsa kana ya shigo.
A hankali Fatima ta kai duban ta gare shi ido suka haɗa, yace, "Subuhanallah, Fatima hala baki da lafiya ne?".
Aikuwa ba kai da rufe baki ba ta sanya mishi kuka mai tsoma zuciya.
Ido ya kifeta da su, dan ko magana ya kasa.
Mamace tayi ƙarfin halin ta fara rarrashi Fatima da ƙyar tasamu tayi shuru.
Sai da yaga tayi shuru kana yace."Fatima meke damun ki?".
A hankali ta fara buɗe baki ta faɗa masa duk abunda ke damun ta.
Aikuwa tana kai ƙarshe Mama ta fara salati tana faɗin, "duniya ina zaki damu kalli ji har gani".
Sai da malam ya numfasa kana yace. "Fatima kiyi hak'uri ko wane bawa da inda Allah ke jarbtarsa, dan haka ki kara hak'uri kinji, kuma sai kin tashi tsaye sosai wajan namen tsarin jikinki ki nutso sosai ki dage da addu'a, kuma insha Allahu muma zamu ta yaki kuma duk wanda ya shiga tsakanin ki da mijinki Allah ya fishi, dan Allah baya kwana dan hakk'in wani akan wani kici gaba da rok'on Allah sauki kuma ki nace da rok'on Allah, duk abinda yayi tsanank yana tare da sauki kinji".
"Badan koma muka baki shawara kiyi wannan auren ba sai dan ki samu ki gama da iyayenki lafiya dan haka kiyi hak'uri, yanzu zan haɗa maki magani da zaki affani dasu insha'Allahu lokaci kaɗan ko meye zai sake shi amma fah, sakin dage da addu'a".
Tashi yayi yaje ɗakinsa.ya jima kafin yafito, sai da ya zauna, ya kalleta kana yace.
"ga wannan maganin keje ki fara aikin da shi muga abunda Allah zaiyi".
Man zaitu da habbatus sauda ya fara bata kana yace, "kisan yadda zakiyi ki haɗe masa su cikin man da yake shafawa a jikin sa , ki ƙoƙar ta kada kisa wasa".
Wani ɗaurin magani ya bata yace. wannan ko ki samu lemu ki haɗa masa yasha kuma ki tabbatar da yasha kinji".
Sannan ya koma bata wani yace, ga wannan turare ne sai ki haɗa shi da turare mai kamshi sai kirinƙa yima gidan hayaƙi da shi".
Kuma kema idan zaki kwanta ki shafe kirjinki da man zantun dan yana kariya sosai".
Yace," insha'Allahu idan kin kiyaye abunda nace to komai zai dawo kamar ba'ayi ba".
Dan haka ki tashi ki koma gidanki Allah yayi miki abarka ya k'ara baki hak'uri, Allah kasa adace kuma idan kena neman ƙarin bayani sai ki gaya man".
Godiya tayi masa sosai kana tasoma tashi, sai mama tace Fatima zonan kiji".
Kallon ta malam yayi yace. "Dan Allah ki barta ta tafi kinga kilama bada izinin shi tazo ba".
Mama tace, "malam kayi hak'uri ba jimawa zamuyi ba".
Yace, "to kuyi sauri gani ina jiran ku".
Tashi Fatima tayi ta same mama a ɗaki, wajan zama ta nuna mata ta zauna, kana ta kalleta da kyau tace.
"Fatima ki buɗe kunneki da kyau kijini, dan naga ba ainkin sihiri kaɗai ke cin kiba har da tsoro".
Dan haka, bari kiji koda malam ya baki magani karya wannan sihiri bashi zai sa ya karye ba sai kin cire tsoron su a zuciyar ki. Dan haka kiyiwa mijinki biyayya, in har kina son kema ki zama mace kamar kowa ce a gidan mijin ta. Dan haka Tashi kije malam najiran ki a waje".
Wani kullin abu ta ɗauko ta bata tace, gashi duk lokacin da kika ga abun yayi sauki ga mijinki to kisa madara kisha, duk da naga alamun ba ke kaɗai kike ba, amma zaki iya sha".
Karɓa tayi tana godiya, dan ita bata san me take nufi da ba ita kaɗai take ba.
tashi kije ga malam can ya fara magana.
Tashi tayi tana mata godiya.
Koda ta fito gaba yasa kata sai data shiga adedeta sahu kana ya hucewar sa wajan aiki.
Tunda ta fita daga cikin ɗakinsa yake tuna ne wai a ina yasanta dan shi gani yake ya santa amma ya manta inane?.
Yana cikin wannan tunanin Momy ta shiga ta same shi tace,
"Alhaji yana ganka a tsaye ko har ka fito?".
Kallon ta yayi yace, "nafito yanzu nake son nayi wuce jira na akeyi".
Har zai sake magana wayar sa ta fara ƙara, sunan da yaga yana yawu saman sereen ɗin wayar shi ne yasa da sauri yayi pinkig, yana faɗin "ganin zuwa".
Momy data ke tsaye ya kalla yace, "Hajiya ni zan wuce office dan jirana akeyi".
Yana faɗin haka ya kama hanyar fita.
Tace, "Alhaji ko breakfast baka tsaya yi ba".
Yace, "ba komai idan naje can zanyi".
Sai da ta mishi rakiya har wan motar sa, driver yaje mota tadowa ta wuce part ɗinta.
Dai dai kofar gida mai adai-daita ya tsaya tafita. knocking tayi mai gida ya zo ya buɗe mata ta shiga ciki.
A hankali take tafiya har ta kawo parlour, ko yanzu tayi sa'a ba kowa dan haka da sauri tayi hanyar part ɗinta, saida ta shiga ta dafe kirji tana fitar da numfashin ɗaya bayan ɗaya.
Bedroom ɗinta ta ƙarasa ta kai kayan ta aja waje daya kana ta kwan ta ta fara tunanin yadda za'ayi taje ɗakin daɗi.
Can tayi wani tunani dan haka da hanzari ta tashi ta sauko ƙasa.
Kitchen taje ta ɗura sanwar rana, sai da ta kammala ta kai dinning ta jera kana ta fara tsaftace gidan gabaki ɗaya.
Turukan ka aka bata taje ta dauko ta haɗasu da masu kamshi ta fara turare gidan dasu har parta ɗin Daddy sai da taje ta turare shi da turare kana ta ko ina na gidan dan har wajan part ɗin Momy sai da tayi karfin halin kaiwa can, cikin lokaci kaɗan gida ya ɗauke da kamshi ma haɗe da turarin isaka na kaya sihiri.
Har ta gama bawan da ya fito, Aikuwa da taga haka da sauri