Showing 21001 words to 24000 words out of 103202 words
ranar ƙwananta ne zakaji ko ina ƙamshi kuma ko ina tsaf,ga ladabo da biyayya ga haƙuri,shiyasa baka taɓa jin kansu matuƙar har idan ba Hajiya kaka ba ce ta haɗosu,mahaifinmu da kanshi ya ce yafi jin daɗin zama da mahaifiyarmu saboda babu ruwanta ita haka rayuwarta take,kuma duk ita mukayo da rashin son magana Salim ne kawai shegiyar zuciya kamar ta kuturu wannan kuma zuciyar babanmu yayo.
ina gama wankan na fito na shafa maina me shegen ƙamshi da kama jiki sannan na wuce zuwa kitchen shima dai ƙazantar ce fal acikinsa ga abinci nan wanda ba a cinye jiya ba duk kyankyasa sun hau kai,kamar zanyi amai a haka na toshe bakina na gyarasa tsaf na saka air freshner ya hau ƙamshi sannan na shiga tsore na ɗebo dankalin turawa da kayan miya nazo na gyara na yi blnending ɗin kayan miyan sannan na ɗakko nama a fridge na wanke shi tsaf na tafasa shi sannan na ɗakko wata tukunyar daban na zuba mai na soya naman da kayanmiyan sannan na ɗan tsar da ruwa kaɗan na zuba curry da mai ɗanɗano yana tafasa na zuba dankaline wanda na feraye sa na wanke na yankasa a slice amman da kauri sosai saboda kada ya narke na zuba tafarnuwa da ƴar citta.haba sai ga girki ya hau ƙamshi sosai,na buɗe fridge na ciro mango ƙato na zo na wankesa tsaf na cire ɓawon sannan na cire tsokar na saka a blender ta markaɗa fruit yana markaɗuwa na zuba ruwa mai sanyi na faro harda ƙanƙara na ƙara blending sannan na juye na ta ce sa sosai,na juye a jug sannan na zuba suger enouph sosai ya fara ƙamshin mangwaro mai warin gawasa.girkina yana yi na sauke na zuba a babbar kula shima lemon mangwaron na saka sa a fridge sannan na wanke ƙwanukan tsaf na goge kitchen ɗin sannan na fito har lokacin bata tashi ba na yi mamakin mugun baccinta ace tun sanda nazo kusan awa uku mutum yana bacci,na zuba abincina na ci cikin ƙwanciyar hankali nasha lemon mangwaro na ina lumshe ido.sai ga ta ta fito daga ita sai rigar bacci iya guiwa duk gashin kanta a warwatse,na kalleta a fakaice na gaisheta ta amsa da ɗan wani guntun murmushi ta ce"au ashe ma kinzo?daman tunda zai tafi ya ce min kema yau zaki xo saboda bani da lafiya ne".sannu na ce mata kawai na cigaba da shan lemona ina kallo.ta ɗan kalleni duk sai taji kunya ta ce"kai rabonda naji ƙamshi mai daɗi har haka har na manta wallahi,gidan ya yi tsaf wallahi ban iya aikinne saboda wannan ciwon da ya sako ni agaba".ta faɗi hakan tana buɗe wamers na abinci ta ce"ta ce wow so delicious bari inci daman tun jiya banci komai ba duk abinda naci dawowa ya ke".duk zubar da take ance mata ƙala ba sai sannu dana ce mata don ni na tsani mace ƙazama duk sai najo ta fice min araina,to da ta ke ce wa ba tada lafiya ta kasa aiki ita me aikin me ye amfanin ta da baza ta iya yi ba sai wani goge farlo saboda wato shi mutane zaso gani.
buɗe cikinta ta yi sosai taci abinci kamat wata sabuwar mahaukaciya tasha lemon sosai tana gamawa ta ce"kai Khairat kin samu ladana wallahi rabon da naci abinci haka har na manta wallahi".ni dai bance komai ba ko da ta tashi daga baccin ko brush bata yi ba ina kallonta amman wai tazo har ta iya cin abinci gaskiya Yaya Aliyu yana ƙoƙari.
***
"Umma wallahi Alhaji Damas ya tsaya sosai akan wai sai mun sayar masa da gidannan,kin san wannan mutumin yana da hatsari sosai wallahi,shiyasa muke binsa a hankali".
Hajiya kaka ta kalli Abdul malik sannan ta ce"kai ni fa aduniyar nan ina ganin ikon Allah ace mutum ya dinga tsoron mutum?a i'na aka taɓa haka?ashe duk zafin zuciyarka na banza ne?shi dan ubansa ya isa ya karɓi gidan ya siya to wallahi kuce masa inji uwarku ƴar ƙasar uman bai isa yazo ya ce zai wani amshi gida awaje na ba,da a uman ne da banu shakka sai an garƙame shege,ɗan arnan kan dutse kawai".
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[23/09, 16:17] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI🥚*
MALLAKAR
*ummu maher(miss green)*🍀🍏
masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.
*Sirrinmu*
yawan bin ƙwaƙƙwafin miji ma'ana yi masa bincike a ma'ajiyarsa ko a wayarsa yana saka kullum a zauna zargi kuma kunsan aure da zargi haramunne don haka don Allah mata mu kiya ye.
21🟪22
.. . . . .a ƙofar ɗaki na tsaya na bashi jakar na wuce don shiryo masa abinci,ko da ya shiga ɗakin ya hangeta cen nesa da gado tana ta sharɓar baccinta abinta harda yawun bacci,san baiyi mamakin ganin gidan fes ba saboda yadan khairat tana nan,yana shigowa yaji gidan ko ina sai tashin ƙamshi ya ke,tunda sukayi aure da khadija zai iya ce wa bai taɓa ganinta dai-dai da rana ɗaya ta ɗauki tsintsiya ta yi shara ba,kulli yaumin bacci,babu abinda ta iya sai bacci kamar kasa musamman ma da ta samu ciki duk sai abin ya ƙara jagulewa,filon ya fara ɗan bugawa a hankali ta buɗe idanuwanta ta yi miƙa ta buɗe hammatarta gashin nan ya cunkushe sosai ya kauda kansa yana jin rashin daɗi har cikin zuciyarsa ya ce"ke wai me yasa ko da yaushe babu abinda ki ka iya sai baccine?kuma ga ƙazanta ko da khairat tazo ai ba yana nufin ki sakar mata aikin komai bane?musamman yanzu da ki ke da ciki,ai ba'a son yawan ƙwanciya ko ka jibge waje ɗaya kama ta ya yi ace ki dinga ɗan exercise saboda kema zaki fi jin daɗi amman sai ki jibge ki yi ta bacci kamar kasa".
yana gama faɗar hakan ya fita ta kallesa ta baya ta ɗan hararesa ta ce"to ai ya dawo kuma yanxu babu zaman lafiya,wato don ƙanwarsa tana aiki kada ta yi?to wallahi ina ganinta bazanyi aikin komai ba,ƴaƴan ne tsafta duk ta lalatu da wani tsafta-tsafta a damu mutum kawai".tana faɗar hakan ta tashi ta fito waje da kayan jikinta tun na bacci mai makon ta shiga banɗaki ta tsala wanka ta saka kaya masu ƙyau ko babu komai ko don mijinta ya gani yaji daɗi.
ina cikin jera abinci ta fito na kalleta ta gefe na gaisheta,ta amsa tana wani ya mutsa fuska azuciyata na ce"oh Allah ya haɗa yaya da gamonsa mace har mace amman babu tsatfa yadda kasan bola haka ta mayar da kanta,su asalin babarsu ma buzuwa ce,agidanmu ana saka ƴan ɗakinsu a jerin masu ƙyau fari da kyakkyawar halitta amman fa sai dai ƙazanta ce za ta yi maka sallama dasu suna dai ƴammata idan zasu fita idan suka ɗauki ado sai ka rantse ba ƙazai bane amman fa ƙazanta na nan cunkushe jikinsu.
Abincinta ta Zuba ita kaɗai tana ya mutsa fuska ta fara ci,yaya Aliyu ya kalleta ya ce"yanzu don Allah khadija ke bakiji kunyat kanki da kanki ba?yanzu fa ki ka tashi daga bacci ko alwala bakiyi ba bare brush sannan har kizo ki fara cin abinci a ture ma ta bani haƙƙina don bakisan haƙƙina da ke kanki ba sam".
ture abincin ta yi gefe tana tura baki ta ce"gaskiya honey kana takuramin wallahi?daga dawowarka ai ka bari ka huta ma?amman ka balbaleni da faɗa agaban ƙwanwarka salon ta rainani ko"?.
"raini kuma na nawa khadija?ai wallahi sai dai idan mutum bai san halinki,amman babu komai ki cigaba da wulaƙanta ibada wataran kema sai ta wulaƙanta ki".yana faɗar hakan ya fara cin abincinsa hankalinsa ƙwance,a zuciyata na ce Allah sarki yaya aƙwai haƙuri muddin kaga ya yi magana to abu ya ƙure ne musamman akan ibada,ko sanda kafin ya yi aure ba ƙaramin takura mana ya ke akan ibada ba,sai gashi Allah ya jarabcesa da mace mara ibada wacce sam hakan bai dame ta ba.
ko ajikinta sai ma ƙara lomar abincinta da ta yi tana ta lodawa cikinta abinci wanda ya fito sosai ina tunanin ma ta kusa haihuwa,ana haka ya ce "ƙanwata kun gama waec da Neco ko?".
"Eh yaya mun gama sai jiran sakamako a tayamu da addu'ah".ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"to Allah ya baku sa'a ai nasan sister ɗina aƙwai ƙoƙari da bada himma insha Allah sai kin fito da good result".ya faɗi hakan yana murmushi.
Na lura haushin hirar da muke yi Anty khadija ke yi don haka ni ko inda take ma ban kalla ba,muna gama cin abincin na ƙwashe kayan na kai kitchen na dawo na gyara wajen tsaf,ya janyo wani ɗan kit ƙarami ya ce"ƙanwata ga wannan tsarabarki ce daman Baba ya yi muku alƙawarin idan kun gama makaranta xai yi muku suprise so shine ni na riga sa".da murna ta na amsa ina yimai godiya.
Anty Khadija ta ya mutsa fuska,na buɗe ƙwalin zaro idanuwa na yi ina kallon kan screen ɗin hamshaƙiyar wayar na zaro ta daga cikin ƙwalin aiphone ce mai masifar ƙyau sai sheƙi take.da tsalle na na rungume yaya ina godiya.sai kuwa naji anty khadija na ce wa"ah ah me ye kuma haka xaki wani rungumesa sai ka ce wata yarinya".ta faɗi hakan tana wani muzurai,da sauri na sakesa na cigaba da yimai godiyar ya ce"su Rashida dasu Nadiya anjima zan kai musu tasu".
da sauri na ce"yaya yau zan koma gida nima na yi missing ɗin mutanen gida musamman Hajiya kaka ta".dariya ya yi sannan ya ce"caɓɓi rabani da tsohuwar rigima yanzu ina zuwa sashenta to fa na shiga uku na don sai ta ɗauko laifi ta ɗoramin kinsan kaka ko baka yi laifi ba to fa ita awajenka ka yi laifi".
Sai kuwa Anty Khadija babu ko kunya ta ce"ah ni dai ki bari sai na haihu sai ki koma gida,tunda kinga bana iya komai kuma gashi kina ɗan yimin aiki".kallon ƙasa da sama yaya Aliyu ya yi mata sannan ya ce"ai kuwa tunda ta ce gidan za ta to sai ta tafi,ke ko kunya ma bakiji ba,ke da gidanki sai yarinya ƙarama ta gyara miki?Allah ya wadaran naka ya lala ce".yana faɗar hakan ya yi tsaki ya yi wucewarsa yana jin wani mugun haushin matarsa arayuwarsa ya tsani ƙazanta ko kaɗan sai gashi Allah ya jarabcesa da mace ƙazama.
Nima tashi na yi na tafi abina don idan suna faɗansu tashi na ke in basu waje don ance tsakanin mata da miji sai Allah,don anjima kuma dai kaga sun shirya.
Ina kitchen ina girki sai na ɗanji hayani na fito da sauri,Anty khadija naji tana ce wa"wallahi yau sai na fasa wannan wayar idan wannan shegiyar yarinyar ta ƙara kiranka."
"to idan kin isa don Allah ki fasa min waya kigani wallahi sai kinyo nadamar yin hakan,ke babu abinda kika iya na farantawa miji sai kullum faɗa da zargi da tashin hankali,to wallahi ko mema zakiyi ki yi idan naso yin aure na baki isa ki hana ba,wawiyar mace kawai".yana faɗar hakan ya kalleni ya ce"khairat ki shirya zanzo anjima na ɗaukeki".a ɗan ɗarare na ce"to yaya".na laɓe ajikin bangon kitchen ɗin.
Anty khadija ta zube guiwowinta awajen ta saki kuka kamar ƙaramar yarinya,a hankali na ƙarasa kusa da ita ban iya ce wa komai ba,don ta bani tausayi masu iya magana kuma sukace baƙin cikin ƴa mace na ƴa mace ne.
A hankali ta kalleni da idanuwanta waɗanda suka rine sukayi jawur kamar gauta, alamar ma ta daɗe tana kukanta ,ta tashi da ƙer saboda cikinta daya tsufa haihuwa ko yau ko gobe ta tafi ɗakinta,kallonta na yi sosai na fuskanci itama tana bala'in son yaya Aliyu saboda yadda take nuna mugun kishi ko da akai na ne idan muna hira sai inga har wani haɗa rai take,sai dai kawai in kalleta inyi murmushi.
Inw gama girkin na zuba akula na ajje a kitchen ɗin ba tare dana jera a dining ba,don na ga mutunen gidan acikin fushi suke.nima ban iya na ci abincin ba saboda ni arayuwata na tsani tashin hankali ko kaɗan.
Bai wani daɗe ba sai gashi ya dawo,nima lokacin na shirya,shima wankan ya sake ya saka manyan kaya shadda ruwan army colour ta yi masa masifar ƙyau ya saka hularsa i'tama kalar army colour da ɗan ratsin fari da baƙi yana fitowa ya kalleni yana ɗaura agogon hannunsa ya ce"to ABIN CIKIN ƘWAI tashi mu tafi,yau sai ganin hajiya kaka ko?"ƴar dariya kaɗan na yi don tun ɗazu da sukayi faɗa da anty khadija sai duk naji babu daɗi.
Na tashi kenan zan shiga ɗakin antt khadija inyi mata sallama sai gata ta fito fuskar nan tamau kamar zata yi kuka ta ce"sai ina kuma"?.ta kalli yaya Aliyu tana gwalalo mai idanuwa.
Ɗan murmushi ya yi alamar rainin wayo samnan ya ce"inda kika aikeni uwata".?yana faɗar hakan ya fita abunsa amman dai da tasha gabansa tana kuka ta ce"wallahi Aliyu babu inda zaka je wato kasha ƙwalliya kana sauri ka tafi wajen zance shine zaka wani fake da kai ƙanwarka gida ko?to wallahi duk inda kaje nima sai na bika".
da alama tashin hankalin ya fara isarsa don haka ya ce"Khadija!je ki shirya mu tafi sai kiga inda zani ɗin ko?".
Ai kuwa da sauri ta sako mayafinta ta saka har tana neman faɗuwa saboda sauri sai na jiyo sa yana ce wa"yi a hankali kada ki jiwa ɗana ciwo".hararsa ta yi ta shiga gaban motar ni kuma na zauna abaya sai wani cin magani take.ni dariya ma abin na su ya ke bani wallahi kamar wasu yara ƴan ƙananu.
Sai da muka tsaya a super market ya lodomin kaya sosai ya ajje a bayan boot,ina kallon anty khadija tana wani hararar kayan sanda ya fito daga super market ɗin.ni kuwa a zuciyata mamakinta kawai na ke yadda take nuna baƙin cikinta afili babu ko kunya.
Muna zuwa gidan da sauri na fito har ina haɗa hanya,yaya Aliyu ya ce"ke zo nan"?.ina zuwa ya ce"kina sauri kije kiga tsohuwar kakarki ko?to tsaya ki tafi da tsarabarki".ƴar dariya na yi na tsunna na ɗauka na shiga cikin gidan,daga nan itama uwar rigimar ta fito da ƙaton cikinta tana tafiya daƙer,tana ganin ya koma motarsa zai tafi da sauri ta dawo har tana tuntuɓe ta ce"ikon Allah ka shigo cikin gidan mana ku gaisa ina kuma zakaje".bai ko kulata ba ya haye motarsa ya tafi.
Don shi yaya Aliyu yana da wasa ba kamar yaya salim ba amman kuma baya son raini ko kaɗan,don yaga idan ya biyewa khadija sai su ƙwana atsaye shiyasa ya yi wucewarsa don ayau zai nunawa Khadija sam ba tada wayo.
ina shiga cikin gidan ban zarce ko ina ba sai sashen hajiya kaka,tana ganin na shigo ta yi saurin ɓoye wani abu,na kalleta irin kallon tuhumar nan na ce"Hajiya kakz duniya,me kuma ake ɓoyewa?"da sauri ta ce"kai ke kuwa khairat me zan ɓoye,ashe kina tafe?da yau na ke cewa Ammar zai kaini gidan Aliyu ɗin tunda dai tunda ki ka tafi ko awaya ma ba'a samunki"?.
ɗan murmushi na yi sannan na ce"wallahi nima kaka na kasa nutsuwa sai dai na takura masa ya kawoni".
iv ɗin ɗaurin aure na gani abayanta na ce"au Hajiya kaka i.v ɗin ki ke ɓoyemin?na bikinsu Rashida ne ko?".
"kai khairat ƙureni kuma zaki yi?to wallahi ko inyamura ce tazo nan yasin baza ta gani ba".dariya kawai na yo muka cigaba da hira na buɗe tsaraba ta ina ba ta,sai ga Nadiya ta shigo ko sallama babu ta faɗo.Kaka ta yi salati ta ce"ke jahilar banza baki iya sallama bane?".turo baki Nadiya ta yi sannan ta ce"na iya mana?ni dai gaskiya kaka na gaji da wannan uban aikin da ki ke lodo mana kayan wankin kutanen gidannan duk mu muke wankewa?ba'a barmu anan bama harda sharar harabar gidannan duk yawansa?gaskiya kaka ki duba mana?".
riƙe baki Hajiya kaka ta yi sannan ta ce"eh lallai yarinyar baki da ko kunyar yin magana?au don ban saka soja ya ƙar lakaɗa muku na jaki bane shiyasa ki ke faɗar haka ko?to yasin ko fulanin daji ce tazo nan wallahi sai kinyi aikin nan,ƴar banza mara mutunci kawai,halin fulanin daji na hauka tsaf ikilima ta kwasa muku,ni dai Allah yabi wa ɗana haƙƙinsa,irin wannan ɗibar albarkar da me ya yi kama haka?"sai ta ɗakko wani madoki za ta ƙwaɗawa Nadiya da gudu ta fita.ta sauke labulen ɗakinta wanda ta ɗagashi saboda duka ta ce"da mana ki taho ki cigaba da haukan da kinsan kinyi da ƴar halak".
ta dawo tana haki na ce"ke kuwa hajiya kaka me ya kaiki dukan nadiya ai jikinki sai ya yi ciwo,kinga yadda take fa kamar wata ingausa".kaka ta ce"yo ƴar nema ai ta saba da shaƙe ƴaƴan mutane ai dole ta munmurɗe haka,ni dai Allah ya karemin jikana kada wataran ra murɗeshi shima".dariya kawai na saka awajen don hajiya kaka ba dai abin dariya ba,muna cikin haka wayata ta fara ƙara na ɗaga da sallama ta.
"Maryam ykk y ƙwana biyu"?.ina jiyo dariyarta ta ce"ke khairat bar wannab zancen wai yau sai ga yaya Aliyu a gidanmu?".
*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar