Showing 54001 words to 57000 words out of 103202 words
ya cigaba da shafa kan jidda kamar me yi mata shafa.
Da ƙer na buɗe bakina sannan na ce"daman Yaya Bilal ina son ka bani izini gobe zan koma skull ne".
Ko kallon ƙura ta bai yi ba,sai da ƴar gaban goshin nasa ta ce"honey kace ta fitar min a ɓangare na wallahi wari take... .✍🏿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:23] Miss Green🍀: 51. . . .52
. . . .tsananin mamakin wulaƙancin jidda yasa na kasa koda motsawa,sosi maganar jidda ta daki zuciyata,wato ma nice na ke wari?lallai jidda tazo da abinda bazan ɗauko ba.
Kallon ƙasa na yi wa jidda kafin Bilal ya buɗe bakinsa ya yi wata magana,cikin fushi na ce"jidda haƙiƙa ke acikin mutane ta dabance shiyasa kike ganin kanki kamar wata sarauniya,to ki sani dama ɗaya ce arayuwar ɗan adam,idan kuma ka bari ta wuce ka to ta wuce ka har abada,don haka ki taka asannu2 duniya ce tafi bagaruwa jima daɗi".
Ina faɗar hakan na fita da sauri daga ɓangaren,zuciyata tana ƙuna sosai wato yau nice na ke wari awajen jidda?yarinyar da da kuɗina nasha biya mata kuɗin watan makarantar islamiyya,wai yau ita ce ke kira da me wari.na faɗa sashe na ina wani irin kuka mai cin rai,tabbas idan waɗannan abubuwan suka cigaba da faruwa to tabbas barin gidan nan zanyi,don naga alama yaya Bilal so yake ya sakamin ciwon zuciya don gab take da ta buga ƙarshe kuma inyi wa iyayena asara,don ko kusa nasan yaya Bilal ba zaiji ciwon mutuwa ta ba tunda ba damuwa ya yi dani ba.
Ina fita jidda ta kalli Bilal wanda kansa ke wajen system ɗinsa,yana shigar da wasu bayanai akan Damas,sai kuwa jidda ta saka idanuwanta sosai,ta ɗauki wayarta ƙirar iphone,ta ɗauki hoton abinda Bilal ya ke,ganin ya juyo yasa tayi saurin ajiye wayar don kada ya ganta.
Ya ce"jidda bana son kina biyewa wannan yarinyar,don sam ni bana sakata acikin masu hankali shiyasa ma kika ga ban kula ta ba,don ko kallon inda take bana son kalla".sosai jidda taji daɗin hakan ta ƙwanta a faffaɗan ƙirjinsa tana shafa sa ahankali cikin kissa irin tamu ta mata ta ce"hmm shiyasa darling kaga ko kallonta banyi ba.don warin jikinta ma ya ishi mutum".
Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga yana ce wa"Ahmad lafiya dai ko?dan kasan idan ina tare da iyalina bana san kowa ya shiga sabga ta".?
Dariya captain ya yi sannan ya ce"ikon Allah masu mata manya,to idan banda abin ka yaushe ne ma kayi auren?".ya faɗi hakan yana dariya ya ce"to ka fito waje nazo inason yin magana da kai?idan madam ɗin ta bari sai ka fito,Angon Hauwa da khairat".wannan magana ta ƙarshe da captain ya faɗa ita ce tafi tsayawa jidda ta kalli wayar ji take kamar taje ta shaƙe Ahmad ta cikin wayar don Allah ya gani ta tsanesa.
Bilal bai ce komai ba ya fita tare da janyo jidda ya yi mata wani irin hot kiss sannan ya fita,ta tsaya kamar tabi sa taje ta shaƙe wannan captain ɗin,sam ta tsani taji an danganta wata mace da Bilal don son da take wa Bilal,tare da matsanancin kishinsa.
"A'ah kaga angon mata biyu har ka fito?".Banxa Bilal ya yi masa sannan ya ce"kaga mlm faɗi abinda ya kawo ka?kawai ina cikin nishaɗi na da matata ka wani zomin?sai kace gauro,ƙarfe nawa yanzu?".
Sosai captain ke dariya harda riƙe ciki,Bilal cikin jin haushinsa ya ce"au daman iskanci ne ya kawo ka?to maza zo ka tafi wallahi".gimtse dariyar ya yi don yasan mutuminsa aƙwai shi da saurin fushi.
Haɗe rai shima captain ɗin ya yi sannan ya ce"to akoma bakin aiki yanzu,kana sane da abubuwanda suke faruwa kuwa?a game da Alhaji Damas?na yi bincike sosai na gane tabbas aƙwai wanda ya ke naɗar duk wani sirrinmu yana kai masa,don a yanzu duk wani plan da muka haɗa masa yasan komai".
"A'ah mlm daga ni sai kai muke wannan binciken,sai dai idan kai ne kake kai masa to sai ka faɗamin"?.
"ah haba mutumina ta yaya za'ayi in haɗa kai da wannan mutumin?kar ka manta fa Damass shine ya yi sanadin mutuwar ƙanwata,shine ya sace ta ya tafi da ita ƙarshe ya kashe ta,duk dalilin taƙi aurensa,saboda munanan aikinsa,kuma ta yaya kake tunanin hakan daga waje na,no matter how hakan ta kasance,ni dai abu ɗaya zan faɗa maka shine aƙwai na kusa damu wanda ya keson ya san komai,sannan ya ruguza mana plan wanda muka daɗe da gama kayanmu".
"hmm zan duba maganarka captain,amman gaskiya ina mamakin wannan waye kuwa"?.
"Hmm Bilal kenan aishi makashinka yana tare da kai,don haka gwara ma kawai musan abinyi yanzu,kada mu tsaya kallon kifi kwaɗo ya yi mana ƙafa."
bayan sun gama wannan maganar ne captain ya ke faɗa masa matarsa zata zo gidansa gobe.
Bilal ya ce"ok Allah ya kawo ta lafiya".amin captain ya ce sannan suka cigaba da hirarsu.
Sosai na ke kallon yaya Bilal wanda ke ta dariya kamar ba shi ba,ina kallonsa ta sama window ɗin ɗaki na,Ina ji araina dama dani yake wannan hirar,yau da har sadaka sai na yi saboda murna,amman kash!ba dani ya ke ba.
Na saki labulen ɗakin na zauna abakin gadona ina tunanin irin wannan zaman dana ke,sai kace wani auren ƙwangila?ah to idan ma auren ƙwangila ne ai da sauƙi tunda dai ana kula da matar?amman ni ina nan dai zaune kamar wata gunki,ko kallon arziƙi ban taɓa samu daga wajen me gidan ba.
****
Ƙarar wayar jidda ne ya karaɗe wajen,tana sama kan bene tana wanka,Bilal na kusa da wayar ya shiga kiranta da honey!honey!!amman jidda bata ma san yana yi ba,ya ɗaga wayar don ya bada uzurin mai wayar shiru yaji anyi don haka ya ajje wayar ya cigaba da aikinsa cikin system ɗinsa.
Tana sakkowa Bilal ke faɗa mata an kira ta,ai da gudu ta ƙaraso wajen tana ce wa"wa. .wa. .waye?".
Kafaɗa Bilal ya ɗaga alamar shima bai san waye ba?.ta duba number gabanta ya bada wani irin rass rass,ta daure ta tashi tana wayan cewa ta ce"au bari in hau sama na manta nan wajen sam babu network,shiyasa idan zanyi waya ta nake hawa sama".ta faɗi hakan tana yin gaba zuciyarta fal tsoro amman ta godewa Allah da Bilal ɗin bai gai ne waye ba.
Tana hawa saman ta shiga ɗakinta ta kulle harda saka key,sannan ta samu bakin gadonta ta zauna,ta kira number hannunta na rawa.
"Barkanki da dare mrs Bilal Admiral B".
Gaban jidda ne ya faɗi sannan ta ce"ranka ya daɗe Oga dafatan kana lafiya?wallahi ɗazu wayar na bari a ƙasa na shiga wanka ashe Bilal ya ɗauki wayar?".ta faɗi hakan tana jin bugawar zuciyarta na ƙara ƙaruwa.
Sosai Alhaji Damas ke dariya sannan ya ce"Banyi magana ba mrs Bilal,idan da na yi magana yau nasan gidanku Boom wuta zata tashi kinga mutum ya yi asarar dukkanin wannan aikin dana sakaki,to kinga yaya kuma zan ɓata aiki na,i zuwa yanzu kin samu wani rahoto ne?".
ya jeho mata wannan tambayar?jikinta na rawa ta ce"eh ranka shi daɗe yanzu haka na samu ka jiraye zuwa na gobe insha Allah,zan masa ƙaryar zuwa gida daga nan dai inzo".
Dariya sosai ya yi irin dariyar basawa,sosai jidda take jin tsoron dariyar Alhaji Damas,tana cikin wannan halin ne taji yana ce wa"yauwa kinji ina dariya ko?ba komai na kewa dariya ba sai yadda kika mayar da ƙwaƙwalwar kamar wata babyn roba,duk da basirarsa da kuma fikirarsa,shiyasa akace mace tafi shaiɗan iya annamimanci."
shiru jidda ta yi don ita lamarin Alhaji Damas yabar bata mamaki,don mutumin yasan kan rashin tausayi da kuma rashin sanin darajar ɗan adam.
Suna gama wayar ta kashe wayar baki ɗaya,don haryanzu bata dawo nutsuwarta ba,anya kuwa ta yiwa Bilal adalci arayuwa?mutumin da ya taimaketa ya tsamota daga ƙangin rayuwar da take ciki?amman shine duk ta manta wannan kyakkyawan halarcin,yana sonta so na haƙiƙa,ta haɗa masa ƙarya amman kuma bai nuna mata komai ba,koda afuska ne kuwa. saboda Tsananin sonta da ya ke.
Wata zuciyar ta ce mata,haba jidda Yanzu akan ɗan wannan abinda ya yi miki ne har ki ke wani tunanin har wani halacci ya yi,Alhaji Damas daga haɗuwarku ta farko ya baki gida mau shegen kyau da kuma tsada.ya bata shi halak malak,sannan duk zuwan da zata yi da kuɗaɗe take zuwa dami guda,tuni account ɗinta ya zama popular saboda muguwar cikar da ya yi da kuɗaɗe,ko shi Bilal ɗin da yake wani ƙafafar ya taimaka mata tasan sarai Account ɗinsa babu rabin kuɗinta,koda aƙwai ma waɗannan ƴan gidan nasu ba bar masa shi zasuyi ba,saboda yadda ya ke taimakonsu sosai.
****
"mero!mero!!mero!!! Salim ne ya taƙar ƙare yana ta ƙwala mata kira,da sauri ta fito daga cikin ɗakinta da radionta akunne wacce Hajiya kaka ta saka ta siyo mata,wai ita baza ta iya zama ita kaɗai ba,ita kuma Hajiya kaka da taya ɓera ɓarna ta siyo ɗin,don ita da mero yadda kasan remote da tv haka suke.ita Hajiya kaka tv ita kuma Mero remote,don sai yadda mero ta yi da kaka ha suke zamansu,don ita hajiya kaka aƙwaita da ɗaurewa jikokinta gaba.
Tana zuwa ta tsaya tana kallonsa shima yana kallonta,ta wani ture baki gaba tare da turo ɗaurin ɗan ƙwalinta ma gaba na rashin kunya.
Sai kuwa ta ce"haba Yaya Salim nifa shiri na keji kazo ka tsaida ni,yanzu gashi nan har sun wuce ni".ta faɗi hakan kamar xa tayi kuka.
Kallon banza ya yi mata sannan ya ce"ah lallai mero rashin kunyarki ta ƙara bunƙasa sosai,yau satinki uku agidan nan amman kullum idan na dawo sai dai inje in siyo abinci?a matsayi na na mijinki? Me ki ke nufi da hakan?,ko kina nufin kullum sai na dawo da uwar gajiya ta sannan inje inyo miki take away ki buɗe wannan ƙaton tunbinki,ki cinye ke gaki uwarcin tsiya,take away ɗaya baya isarki saboda haɗamarki,amman idan wajen girkine sai ki maƙale hannu ki ƙwanta ke gaki uwar san jiki ko?to ki buɗe kunnuwanki sosai kiji,wallahi daga yau na daina siyo abinci,ga kayan abinci nan a store komai aƙwai ki duba abinda ki ke da buƙatar dafawa ki dafa amman wallahi ni na daina siyo wani abinci kinji ko?".
Yana faɗar hakan har ya yi nisa sai yaji mero na ce wa"oho dai ai naga ni ban iya girkin ba?idan kace inje wani hito in ɗakko kayan girki ni ta ina na sansu ma?ni koko kawai na iya damawa,don shi kaɗai hansai ta koyamin,kuma ni wannan ƙaton abin girkin na madafa wallahi ni dai ban iya kunnasa ba,kawai wataran inje ya babbake ni".
abin dariya abin takaici,wai bata iya girki ba?to a gaba zai sakata yana kallo idan bata iya girkin ba?wata shawara ce ta faɗo masa aransa don haka kawai ya fita daga gidan ba tare daya ƙara magana ba.
***
"Lafiyarki khairat bakya zuwa skull,ɗazu wannan malamin naku ya kirani wai bakya zuwa,me yake faruwa ne agidan naku?"
Kasa ce wa yaya Aliyu komai na yi,don bana son tona asirin halin da na ke ciki.... .✍🏿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:23] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*
📃LITTAFI NA 2
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
Matso kiji👂🏻
Kada ki kasance mai yawan yiwa mijinki musu wallahi yin hakan yana dakushe ki a wajen mijinki don haka a kiyaye,ba da faƊa ko fushi miji ya ke saka ya soki ba,A'ah da rarrashi da kissa ake mallake miji.
-------------------------
53. . .54
. . ."haba khairat da ke fa nake magana kinyi shiru?".Yaya Aliyu ya faɗi hakan cikin fushi don shima baya son rainin hankali.
"Yaya Aliyu ka yiwa Yaya Bilal ɗin magana,wallahi ni nayi masa magana amman bai ce komai ba,idan ka yi masa magaba kai zai yadda".na faɗi hakan cikin shaƙewar murya,ya fuskanci tsoron Yaya Bilal ɗin na ke don haka ya ce"ok ba komai insha Allah zan yi masa magana,kada ki damu".yana faɗar hakan ya kashe wayar ya kira yaya Bilal awaya ya faɗa masa.taɓe baki ya yi ya ce"go a head kawai ni ban hana ta zuwa skull ɗinta ba,amman ka shaida mata kada ta kuskura idan taje ta kai dare ko kuma yamma,idan kuma ta taka doka ta to tabbas zan soke makarantar".ya faɗi hakan cikin gadara.
Yaya Aliyu yasan halin Bilal sosai ɗan zafin kai ne,bai da tsoron faɗar magana idan ta fito masa,suna gamawa shima yaya Aliyu ya kirani ya faɗamin yadda sukayi tsaf,a zuciyata na ce kaji ɗan rainin hankali wato ma kada inje indaɗe kamar ma ya damu dani.
Tun dare na kira su zuhra da kuma zainab na shaida musu gobe monday,ina skull insha Allah,sosai suka yi murna suka ce a to ai gwara ki dawo ana ta karatu babu ke,harma anyi wasu c/A ɗin baki nan wata ma mune mukeyi miki ita,naji daɗi sosai don sun cika ƙawaye na ƙwarai.
Washe gari da wuri na shirya na fice makaranta,sanye na ke cikin wata doguwar rigar material mai kyau,ta rufe min ruf jikina na samu nayafina babba na yafa da takalmina mai ɗan tsayi,kasan cewa ba doguwa cen ba.banyi wata ƙwalliya cen ba daman ni ba ma'abociyar yin hakan ba na dai gyara ƙwantacciyar gira ta wacce take acike ɓam da ita gata kuma baƙa ƙirin,na kalli madubi,ni dirarriyar macece sosai,baƙina bai hana aga kyau na ba.na ɗakko jakar skull ɗina na saka na fito na ɗan kurɓi ruwan tea kaɗan,na zuba dankalin dana soya acikin ɗan launch box ɗina mai kyau,na kulle sashe na fito,naji duk babu daɗi saboda na saba saka turare yau kuma har zan shafa sai kuma na ajje tunowa ta a matsayin matar aure.
Ganin rashin dacewar tafiyata ba tare dana sanar dashi ba .har na yi hanyar ɓangaren jidda sai kuma na tuno da irin wulaƙancin da ta yimin rannan,kawai sai na yi hanyar waje duk raina babu daɗi.
Nafi kusan minti talatin a bakin titi ban samu abin hawa,na fara tafiya a ƙafa zuwa cen babban titi kafin in samu abin hawa,saboda unguwar mu G.R.A ce babu adaidaita sahu.
Sosai naji ana ta yimin hon amman ban wani juyo ba,saboda nasan idan na juyo wata ƙila irin ƴan iskan nanne,cen dai dana gaji na juyo ina juyowa sau naga Captain,ya washe min baki ya ce"a'ah kaga mata agidan Admiral B.ya akayi kuma kike tafiya aƙafa?".
Fara gaishesa na yi yace"ikon Allah yanzu duk motocin A/D sai arasa wacce zata kai ki unguwa?".sunkuyar da kaina na yi ina wasa da ƴan yatsuna.fuskantar kamar aƙwai matsala ne yasa ya ce"ok shigo in rage miki hanya".
Na shiga amman baya na zauna,wannan ɗin ma don nasan aminin yaya Bilal ne shiyasa na shiga,ya waiwayo da kansa ya ce"khairat ina zakije ne?".
"Makaranta zanje Bayero university".murmushi ya yi sannan ya ce"ayya ashe kin koma skull Allah ya bada sa'ah,anjima Halisa zata zo to na kira Bilal sai ya ce wai ita jidda zata je gidansu,to shine na ce ai gaki agidan tazo wajenki.ashe ma kema makaranta zaki".
"ayya ba komai idan naje bazan daɗe ba,daman yanzu test muke yi idan naje zan dawo da wuri,ka faɗa mata tazo".murmushi ya yi azuciyarsa yana ce wa oh wannan yarinyar baiwar Allah,gashi yaga alamar wannan ita ce ya kamata ta zamowa Bilal garkuwa agidansa.don ya fara zargin jidda,don duk abinda sukayi da Bilal tamkar a gabanta ne,don matuƙar yaje inda ya ke laɓewa don ɗaukar wasu abubuwa a gidan Damas sai yaga khairat,abin ya tsaya masa sosai kuma ya rasa yadda zaiyi ya faɗawa Bilal hakan,tabbas jidda ta cika butula me mantawa da alkhairi.
*****
Na yi sa'a ina zuwa makaranta na haɗu da mutanen nawa musamman ma Zuhra,tana ganina ta rungumeni tana ihu,ga amarya ga amarya ai kuwa ƴan ajinmu suka zagaye ni suna tsokana ta,nan dai aka shiga hira da bani labarin abubuwanda suka faru da bana nan,kun san ƴan makaranta da gulma.
Sai dariya na ke kamar ba niba,Zainab na zuwa ta dinga kallona up and down,na kalleta na ce"ke dalla banza me kuma ki ke wani ƙare min kallo?".na faɗi hakan ina dariya dimpils ɗina sai lotsawa suke gwanin sha'awa.
Ta magantu sannan ta ce"haba khairat ba dole in kalleki ba,kinyi aure madadin muga kinyi ƙiba .sai wannan uwar ramar da ki kayi,jibe kifa da ma har kinfi ƙibar?".
Shiru kawai na yi na sunkuyar da kaina don bansan ma me zance musu ba,lamarin aure wuyar sha'ani gare sa,balle kuma na karanta na sani Allah ya tsinewa mai tonawa mijinsa asiri,na wayance na ce"hmm rashin lafiya na yi ne maleria ke damu na,amman yanzu naji sauƙi sosai."
Haɗa baki sukayi wajen yimin sannu,nan dai aka cigaba da hira na ke tambayarsu abinda za'ayi yau.Zainab ta ce"hmm mutuminki ne kuma kinsan ya yi tafiya".
"Na ce to ni ina ruwa na da tafiyarsa Allah