Showing 45001 words to 48000 words out of 103202 words

Chapter 16 - ABIN CIKIN ƘWAI

22 Jan 2025

4495

Kai tsaye babban gidansa na shaƙatawa suka isa,suna zuwa yaransa suka fito suka buɗe masa ƙofa,duk jikin jidda ya yi mugun sanyi ga wani mummunan tsoro da take ji.

Suna shiga ya kalleta sannan ya ce"ki saki jikinki jidda kada ki sake ki nunamin tsoro,don wannan harkar mun fara ta kenan,har sai naga bayan abinda na keson gani".

A takure take dashi wani abu taji an shaƙa mata a hancinta tun daga nan bata ƙara sanin inda kanta ya ke ba,sai tashi tayi ta jita acikin mummunan yanayi,ta yi yunƙurin tashi taji ta kasa tashi ta fasa wani irin mugun kuka mai cin rai,wato daman wannan mutumin ya kawo ta nan ne don ya wulaƙanta mata rayuwa?a satin ɗaurin aurenta?yanzu me zata ce wa Bilal idan hwt ya gane ce wa ita ba budurwa bace?hankalinta ya yi mugun tashi ta saki wani kuka me mugun ƙarfi.

Da kansa ya shigo ya kalleta sosai sannan ya ce"jidda wannan abinda na yi miki nima ba ui sane amtsayin ramuwar gayya akan Bilal,saboda yadda ya keson wulaƙanta ni a idon duniya,shiyasa na nemi wannan hanyar don baƙanta masa,idan ki ka yi gangancin faɗa masa wallahi duk ida kika shiga sai na nemoki,bazan taɓa barinki ba".

ya turo mata wata jakar kuɗi sannan ya ce"wannsn kuɗin duk na kine,idan kinso ki sakasu a account,idan kinso ki barsu?idan kika haɗa kai dani babu abinda bazan miki ba".

yana faɗar hakan ya cillo mata mukullin gida ya ce"wannan mukullin ɗaya ne daga cikin gidajs na waɗanda na keji dasu,shine na baki shi halak malak,gidane ns haya mai part 50 dai yadda ki ka yi dashi yanzu ya zama naki".

habawa kunsan mutum da kuɗi tuni Jidda ta saki jikinta da Alhaji Damas,tun daga ranar ta zama kamar wata yarinyarsa,kafin ƙwana tara na aurenta,sai ta yi wa iyayenta ƙarya tace sun fita da Bilal alhalin tana wajensa,aƙwai ƙawarta Wata Rabi'atu babu abinda bata sani ba na dangantarka Damas da kuma Jidda.

Saboda kuɗi yasa ta yi shiru da bakinta tunda ana ɗan gutsira mata,sosai jidda ta kashe kuɗi saboda gyaran kanta don tasan ayadda take,naira na gugab naira dubu ɗari biyar haka ta bayar wai duk don ta dawo budurwa.

Sosai iyayenta suke tuhumarta akan kashe kuɗinta,amman da ya ke tana musu ƙarya da Bilal sai suka daina tuhumarta ta cigaba da wandaƘarta da kuƊaƊa,sosai ta ware kuƊi don siyan wasu kayan kitchen da sauran abubuwa.

Alhaji damas ys samu yadda ya keso,don haka yanzu wani kallon tara saura Ƙwata ya kewa Bilal,gani ya ke tamkar fankonsa ya ke ganinsa,tunda wadda ya bawa amanarsa,ya Ɗauketa matsayin mai tarbiyya to fa ta watsar da komai ga Alhaji damas,ta bashi komai ta yadda shi Bilal Ɗin ko alfarmar riƘe hannunta bai samu ba.

sosai wannan abu yake masa daƊi saboda ko ayanzu ya gama da Bilal, gamawar har ya mutu bazai taƁa mantata ba.
****

koda aka tashi yin dinner babu yadda Rashida bata yi dani ba,akan inje dinner Ɗin naƘi zuwa tunda dai ni ba sona ake ba,to kuma me zanje inyi?Don yaya Bilak bazai ji kunyar wulaƘanta ni awajen mutane ba.

Da Rashida tarasa yadda za tayi dani sai taje ta sanu yaya Aliyu ta gaya masa komai,yazo ya yi min faƊa akan inje,kuma su yaya salim ma duk zasuyi idan har banje ba baza suji daƊi ba,haka dai na haƘura amman can cikin zuciyata tsoro fal.

Ana cikin maganar hajiya kaka ta fito daga kinta baya sun gama faɗa da mero.sai kuwa ta ce"kai Aliyu rabu da ƴar banza,ina cewa nan naji kina gayyatar ƙawayenki fatin?sai yanzu za'a wani zo ana wani rarrashinki akan kije?to yasin kada kije ni daman haka zanso sai in hakimce akan kujerarki ince ni ce uwargida.

Duk wanda ke wajen sai da ya yi dariya sosai,ni kuwa kallonsu kawai na ke,ɗaurin aurena da za'ayi da Yaya Bilal shine kawai ya tsayamin aƙoƙon zuciyata,ko wani irin zama zanyi dashi oho?.

Ƙwalliya aka yimin sosai wacce ni da kaina sai da na yaba kaina,wani farin les ne wanda ya gaji da haɗuwa gashi yaji ruwan stones sai walƙiya ya ke,kamar ka ɗaukeni,ƴar pos ɗina da kuma takalmi na duk ash ne suma sunji ruwan stone,diri na sosai ya fito da ya ke ni dirarriyar macece,sai na haska na yi wani irin bajajjan ƙyau wanda ya amsa sunansa aƙyau,head ɗina ma arsh ne sai net golden shima sai walƙiya ya ke,aka yafamin shi akaina.

"Wow gaskiya amaryarmu kinyi ƙyau sosai,gaskiya yaya na zaiyi santin kyaun nan".cewar Rashida wacce ke ta faman ɗauka ta a hoto kamar babu gobe.

Bansan lokacin da naji wani hawaye yana zubomin ba,da gudu na tafi naje na rungume mahaifiyata tsam kamar wani zai ƙwacemin ita,i'tama ɗin rungume ni ta yi tana ɗan buga bayana tana rarrashina,har cikin zuciyarta take jin babu daɗi arabuwa da tilon ƴarta mace da zata yi.

Su mero ana gefe ansha ƙwalliya sai ka rantse ba meron hajiya kaka bace,ganin khairat na kuka dai yasa duk jikinta itama ya yi sanyi sosai,ta koma gefe ta rakuɓe tana kallon uwarta hansai wacce ke ta shirinta cikin haɗaɗɗiyar atamfarta super wacce Hajiya kaka ta bata.

Itama da gudu taje ta rungume hansai tana ta kuka,Hajiya kaka ta ce"kai ku ganemin wani shashanci,don kunga iyayenku na wajen suna ƙefta muka idanuwa ku taso kuyi kuka shine zaku faramin kuka kamar gidan mutuwa?to wallahi ba dani ba,duk shegiyar da ta ƙaramin kuka yasin sai na saka jikana fasa aurenta".

dukkanmu juyowa mukayi muna kallon hajiya kaka,wacce ta yi mirsisi kamar ba ita ce ta yi maganar ba,ta ɓantari guntun goronta ta saka abakinta tana tauna,ganin duk muna kallonta sai kuwa ta ce"meye ne kuma kuke kallona?To wallahi kuruwa ta kurr akanku,ina ƙwanannan aka samu wata shegiyar ta yi min asiri cikin matan ƴaƴana?duk da ban yarda da hakanba,don ni dai naci dubu sai ceto,mai dambu kafin ta mutu ta barmin tsari ajikina.kunga kuwa kuma sai dai kuci kanku".ta faɗi hakan tana zare fici-ficin idanuwanta.

Dariya mero ta tintsire da ita sosai sannan ta ce"ah to mudai ma idan mayun ne ai sai dai kece kika shafamin?Tunda nidai Babana ƙaninki ne,ita kuma khairat kece ki ka haifi Babanta,kinga kuwa sai dai daga kene wannan matsalar".

Hawaye kaka ta farayi sannan ta ce"Allah ya isa na mero da wannan zagin da ki kayimin,kuma wallahi ki yi asannu,don ba ƙaramin aikina bane in saka jikana ya fasa aurenki".

Dariya sosai mero ta yi sannan ta tashi taɗan riƙe doguwar rigarta mai kalar blue da fari da ƙaton takalminta me tsini kalar blue,ta tashi a hankali don takalmin shirin faɗar da ita ya ke,a kunnen hajiya kaka taje ta raɗa mata wani abu,ai da gudu ta fita Hajiya kaka tana ce wa"wallahi uwarki hansai ki ka faɗawa magana bani ba,ƴar banzar yarinya mara kunya".ta faɗi hakan tana fashewa da kuka.

Kunsan me mero ta raɗawa hajiya kaka?Hmm ku matso kunnuwanku kuma kuji,cewa ta yi to idan ya fasa aurena ke zai aura ki haifa masa yara.

kun san kuwa dole maganar ta yiwa hajiya kaka zafi,har aka fara tayi party ɗin bani da niyyar tashi,mama sai rarrashina take amman kukan ƙara bulbulowa ya ke tamkar dai an buɗe famfo.

Itama hajiya kaka na bata tausayi sosai,ta rungumeni tana bubbuga bayana sosai da ƙer dai hawayen ya tsaya.Rashida tana tsaye itama kukan take tana sharewa.

Tabbas dole ne khairat ta yi kuka,saboda ko ba don komai ba sai abinda ya faru da ita,tasan halin yayanta tsaf yana da zargi sosai,bazai taɓa amsarta amatsayin matarsa ba,musamman yadda taga mahaifiyarsu na nunawa akan auren yaya Bilal da khairat,ta kasa gane cewa komai muƙaddari ne daga Allah,Daman Allah ya ƙaddara khairat matar Yaya Bilal ce babu yadda kuma za'ayi don Allah ya ƙaddara faruwar hakan.

Da gudu Rashida ta taho ta rungume khairat,ta bayanta tana ta kuka itama,tuni suka fara bawa Hajiya kaka haushi ta ce"Innalillahi gaskiya nidai ku fitarmin daga ɗakina tunda babu wanda ya mutu balle ku sakani agaba kuna kuka,kamar za'a kaita inda za'a dinga figar namanta ana miya dashi?Haba abinnan ya yi yawa wallahi,duk kowa ya tafi wajen partyn har wannan uwar rawar kan mero ta tafi amman ke kina zaune kina aikin kuka."
Mama ce ta rarrashemu mu duka har bakin motar da zata ɗaukemu sai da ta kaimu sannan muka shiga ita kuma ta dawo,ƴan uwanta da sukazo tare muka tafi,don ita ta ce baza ta jeba,don haryanzu zuciyarta bata mata daɗi idan ta kalli gidan mijinta da ta bari abisa sharrin da aka laƙabawa ƴarta,shi kuma Malik ba tare da binciken komai ba ya ɗora mata laifi,bayan wannan ma har da tukuicin saki,ta goge hawayen da suka zubo mata.

Hajiya kaka na kallonta tausayin ta duk ya cika mata zuciyarta,ita fa har yanzu bata yadda da abinda aka faɗa akan khairat ba,tabbas aƙwai saran ɓoye acikin lamarin.


****
wani irin mummunan bugawa naji gabana ya yi,hango Jidda wacce ta gaji da haɗuwa wajen yin ado da ƙwalliya,ga gogan A.D a kusa da ita,ta saƙalo hannunta ta bayansa ana musu hotuna,na kalli kujera ta babu kowa akai,na rasa tudun dafawa na tsaya kawai,ganin abinda ke faruwa yasa Rashida zuwa wajena,ta riƙemin hannuna ta kalleni sosai cikin dakiya ta ce"khairat ki nutsu fa,kada ki diririce yadda ki ke aduk sanda kiga yaya Bilal,muje ki zauna".ta riƙe hannuna har kan kujera ta.

Na zauna duk jikina a sanyaye,ina kallonsu ta gefe,ko ƙura ta basu kalla ba hotunansu kawai suke cikin farin ciki,kana kallon fuskokinsu kasan cike suke da son junansu.

Juyar da kaina gefe na yi ina ɗan kallon mutanen wajen,hall ɗin ya cika ɓam,kamar ba gobe kowa sai harkokinsa ya ke,sai dai fa ƴan gulma sun kasa sun tsare don suga abinda zai faru.

Ƙawaye na da suka zo sai rungumeni suke muna hotuna,suna dariyarsu sai dai suma sun fuskanci ce wa nifa ko tani mijin ma ba ya yi,wata ƙawarmu Safiya ta ce"hmm ni dai idan baka mutu ba ka yi kallo?ki duba kiga namiji har namiji amman khairat ki ka damu sai kin auresa,yanzu ai gashinan ya samu kyakkyawa irinsa,sun barki sai ka ce wata bolarsu".

wani malulu ne ya tsayamin aƙoƙon zuciyata ƙwalla ta sauka akan fuskata,wata me suna Hajara ɗaya daga cikin ƙawayen namu ta ce"Haba Safiya ai bai kamata kice haka ba,shifa ubangiji babu ruwansa da mai kyau da kuma mara ƙyau,idan Allah yasa ka auri miji mai kyau dole ne ya kula da kai,matuƙar yana so ya gama lafiya".. . . . .✍🏿

07068606171



*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨


_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:21] Miss Green🍀: 43. . . . .44


. . .taɓe baki Safiya ta yi sannan ta ce"hmm ni dai duk da haka wallahi ina jiye mata zama da miji irin wannan,yawancinsu kansu kawai suka sani,babu ruwansu da mutum za kiga har wani ɗagawa matar kai suke wai su gasu masu kyau,ko kuma kiga ana miki layi agida na neman mijinki".

"To Safiya ko ma dai menene ta auresa,don haka daga baya kenan,Allah dai ya basu zaman lafiya".cewar Hajara.

Ni dai sunkuyar da kaina kawai na yi,sai hotuna ake a hakan ni kuwa hankalina sam baya kansu,na tafi duniyar tunanin halin da zan sinci kaina aciki,don yaya Bilal sam bai son haɗa inuwa ɗaya dani.

Tunda akazo wajen ko kallon ƙurata Yaya Bilak baiyi ba,hankalinsa duka yana ga jidda wacce take wani yimin kallon tara saura ƙwata,ni dai Allah2 nake atashi daga wajen don duk jikina amatuƙar sanyaye ya ke.

Cen sai ga Hajiya kaka ta zo ansha gwaggwaro itama leshinta fari ne tas,ta yi sosai farinta na salin fulani da kuma kyaunta ya fito sosai,kai tsaye ɓangarena ta taho,ta kalleni sheƙeƙe sannan ta ce"yau naga ikon Allah ke saboda ba'a sonki sai suka matsa cen ke shine suka barmin ke anan?To yanzu zanji dalilin yin hakan?yadda waccen mara kunyar ta matsa sosai jikinsa kema haka zaki yi,yo in banda kalan dangi ai kece ma ƴar uwarsa amman shine zai wani matsa cen gefe,zanji abinda ya kawo wannan wariyar."

tana faɗar hakan ta yi gaba abinta,ina janyo mayafinta don in hanata amman sai da taje,ta kusa dasu maryam ta wuce wacce ke zaune kusa da Yaya Aliyu sai zuba soyayya ake,ta wuce kusa dasu Yaya Salim da mero,su dai ba lallai ka gane basa son juna ba,don dukkansu sai hotuna ake gwanin sha'awa.

"Inye au daman kai Bilal sakarai ne?tun daga yanzu mace ta fara juya ka?yadda uwarka ke juya ubanka?ah lallai su Ruƙayya za'a ɗauki darasi anan,kana wulaƙanta ƴar uwarka saboda wannan yaloluwar yarinyar wacce ko ƙugun arziƙi ba tada shi,aba kamar muciya an ɗaura mata zani,shine ka ke wani rawar ƙafa da rawar kai,kai ga me mata ko?to wallahi ka sake ka cuci jika ta Allah ya isa".

Tana faɗar hakan ta dawo inda na ke ta janyo hannuwana fuuuuu,sai gani gaban Yaya Bilal,na tsaya da ƙer ƙafufuwa suna ta rawa saboda tsoro da fargaba.

"Yauwa tsaya nan!".
Hajiya kaka ke faɗar hakan ta ce"yauwa kema tsaya adinga yaƙe bakin dake tunda tallan makilin suke,ana wani hoto ana yaƙe haƙora kamar wasu masu tallan makilin".ta faɗi hakan tana harararsu.

Abinda kaka bata sani ba,ashe duk ana jinta acikin lasifiƙa don kusa da lasifiƙar take,haushi sosai Bilal yaji akan wannan cin fuskar da kakarsa ta yi masa,don kakar tashi ta ƙara jin haushi sai ya riƙe hannuwan Jidda ƙam kamar wani zai ƙwace masa ita.

Sai kuwa kaka ta ce"Hmm ai kin ɓur inji tusa,ai idan baka mayar da ita ciki ba,kai baɗan Ruƙayya da Abdullahi bane,shasha mara sanin ya kamata,ke kuma kina nan kamar wata ƴar tsana da wani jememmen jikinki".

sosai aka saki dariya awajen,Hajiya Ruƙayya abinda surukar tayi ya tsaya mata sosai,kaɗan ya rage ta yi kuka tsabar takaici,wata ƴar uwar Hajiya Ruƙayya ta ce.

"Wai ni Anty har yanzu wannan masifaffiyar tsohuwar bata daina rashin mutuncin nan ba?kawai ki saka yara agaba,don ba'ason jikarki,to uban waye yasa ta nace sai ta aureshi?ai yanzu gashinan agaban mutane ya wulaƙanta ta ai ni ya yi min dai dai daya wulaƙanta ƴar banza".

Ita dai Hajiya Ruƙayya kasa magana ta yi saboda tsabar ɓacin rai,ji take kamar ta kama Hajiya kaka ta yi ta dukanta,saboda yau Hajiya kaka ta kai ta ƙarshe.
Jidda taji zuciyarta kamar zata fito saboda haushin tsohuwar take ji,amman ta yi alƙawarin sai ta koya mata hankali sosai.

Ko da akazo wajen yanka cake,sosai akayi drama don da Bilal ya bawa Jidda ta basa,sai ya kasa juyowa ya bawa Khairat sai dai abinda ya bawa kowa mamaki da sha'awa bai wuce yadda Khairat ta yanko cake ɗin ta saka a bakinta ba,sai da ta bawa kowa tausayi awajen,abinda kuma ya ƙara bawa kowa mamaki bai wuce yadda khairat ta juyo da Bilal ba,ta saka masa cake ɗin abakinsa.

Ya samu kansa amai haɗiyesa,yana kallonta da mamaki da kuma ƙarfin hali irin na ta,Jidda kuwa ta cika ta yi ɓam,saboda haushi tana ta hararar Khairat.

Ran Hajiya kaka ya yi fes da abinda ya faru,hajiya kaka ta kira mai hoto ta ce ya yi mata ita kaɗai da jikarta,haka kuwa akayi mai hoto yazo ya ɗandasa musu hotuna masu matuƙar ƙyau,ta janyo hannun Bilal ta saka ana khairat suka kalli junansu unexpected mai hoto kuwa ya ɗauka ƙes.ƙes.
Sannan aka yi musu da hajiya kaka ma.

Anci ansha amaren sai hidimarsu suke,gwanin sha'awa,nima yanzu na saki jikina gani ga su Rashida ga Maryam ma,ƙannen Anty khadija ko mutum ɗaya bai zo ba,saboda suna taya ƴar uwarsu kishi.
Sai ƙarfe tara aka tashi goma sha ɗaya aka tashi daga dinner ɗin,muka koma gida duk a matuƙar gajiye,mun fito daga cikin wajen kawai idanuwa na suka kaimin kan Jidda da Yaya Bilal,tana rungume a ƙirjinsa har suka shiga cikin motar mai ƙyau.

Na kafesu da idanuwa na,zuciyata sam babu daɗi sai yanzu na gane ce wa ka auri wanda ya ke sonka ma wani abune arayuwa,rai na duk babu daɗi muka tafi gida.


Kowa ya yi bacci sai munshari suke,na wurwucesu duk sun baje akan kafet ɗin,suna ta bacci wasu akan gado wasu kuma a ƙasa,na wuce banɗakin na ɗauro alwala sannan nazo na tada Sallah na yi raka'a huɗu,sannan na ɗaga hannaye na sama ina roƙar ubangiji ya kawo min sauƙi acikin lamarin aure na,ya cusawa yaya Bilal sona wanda har yafi ƙarfin son da na ke masa.

Na shafa addu'ar ina kuka,Rashida da ke kusa dani ta kalleni ita ma hawayen take muka shafa addu'ar tare.
****


Washe gari da wuri su Rashida suka fara shirinsu,ni kuwa sai bacci na ke mai cike da son Yaya Bilal,wai gamu da wasu fararen yara aƙasan wata bishiya mai kyau muna lilo gwanin sha'awa.

Rashida ta ce"ikon Allah sai kallo mu duk mun tashi mun shirya amman ke da ki ke matsayin amarya sai baccin asara ki ke?ta faɗi hakan tana tashi na,miƙa na yi sannan na tashi ina salati.

Kai tsaye banɗaki na shiga na shiga na yi wanka tare da brush,don na yi sallah tun asuba tare da yin azkhar ɗina na safiya,wanda kuma wannan tarbiyyar gidanmu ce,duk wani yaro ko babba da asuba ya ke salla tare da karatin qur'ani da kuma azkhar.

Ɗaya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login