Showing 48001 words to 51000 words out of 103202 words

Chapter 17 - ABIN CIKIN ƘWAI

22 Jan 2025

4468

daga cikin kayan da Hajiya kaka ta bayar aɗinkamin na ɗakko shadda ce fara sol,wacce ta gaji da aiki ga shi tasha tsone work,ɗinkin doguwar riga,ni da mero ta bayar aka yimana,amman ita mero nata kalar ash ce shaddar.

Munyi kyau sosaj sai ɗaukar ido muke,na fito daga ɓangarenmu sai sheƙi na ke,lalle na ya yi kyau sosai a hanya muka haɗu dasu Salimat da Iman,duk suna da cikinsu har ya fito ma,Salimat ce ta yi dauriyar ce wa"oh su khairat amarya?babu magana ne?".

Banyi niyyar yi musu magana ba,na gaishesu iman tana wani cin magani ta wuce gaba tana ce wa"hmm Allah dai yasa cikin ya fita kada akaiwa wani gidansa".ta faɗi hakan tana hararata.

Sosai naji zuciyata ta yi wani irin zafi,na wuce ina goge ƙwalla acikin idanuwa na,kai tsaye na wuce sashen Hajiya kaka.

Ɓangarenta acike sosai na wuce cen cikin ƙuryar ɗakinta ina gaida mutanen da ke wajen,ɗakinta babu kowa aciki ashare a goge sai tashin ƙamshin turaren wuta ya ke,daman Hajiya kaka aƙwaita da tsaftace waje.

Na baje akan gadonta tare da cire golden ɗin mayafina,na cire awarwarona da ɗan kumne na cire kayans nabar iya under ɗin dake jikina,na hango kayan lefena akan sif ɗin hajiya kaka saiti tara cif,wanda daƙer yaya Bilal ya yi lefan wai shi bashi da kuɗi,alhali ko ƙwanan nan an ƙara masa matsayi kawai dai bai so na ne shiyasa zai ce hakan,jidda kuwa abakin mutane naji ana cewa dozin biyu ya yi mata.

Na rintse idaniya ta ina kiran sunan Allah,a haka wani bacci mai nauyi ya ɗaukeni,sai da naji Hajiya kaka na tashi na tana ce wa"ikon Allah wannan amarya da lalaci ki ke,ga mero cen ta shige cikin gida ana ta hotuna da ita,ita da ma yaushe tazo gidan?amman ke da kika rayu agidan kina nan kina wani baccin asara.

Banɗaki na shiga na yi wanka na fito Hajiya kaka ta ce"buɗe cikin sif zakiga wata atamfa super ɗakko ta ki saka, jiya na amso miki ita,amman banda mero saboda ita na barta ta saka kayan lefanta saboda ita babu rashin mutunci aciki,amman Ruƙayya ji bi lefan da ta haɗo miki duk aƙwatin bai cika ba,ai wallahi baza ko saka ko ɗaya ba,ana gama bukin zan mayar mata tsiyarta,don itace matsiyaciya don ni dai ban gada ba,ɗinki kala goma na yi miki ki yi ta sakawa kina fita,kuɗi na ware sosai na bawa Rashida ta yi komai,sai da aka ɗinka sannan ta kawo min,yarinyar arziƙi wacce bata yo mugun hali irin na uwar taba.
Ni dai ina jin hajiya kaka bance komai ba,na shirya cikin atamfata blue da kuma ratsin brown ɗinkin riga da zanine amman ɗinkin ya yi ƙyau sosai,musanman ma dana saka kayan na yi ƙwalliyata simple na ɗaura ɗan ƙwali na akan ƙwantaccen gashina wanda yasha saloon sai tashin ƙamshi ya ke.

Rashida ta shigo tana dariyar tsokana ta ce"to Alƙawarin Allah ya cika an ɗaura auren Rahama da kuma Bilal".

Wani irin faɗuwar gaba naji,yanzu shikkenan an ɗaura aure na da Yaya Bilal?yanzu shikkenan na zama matarsa?mun zama abu ɗaya?tuni hawaye suka fara ƙwaranyo min kamar an buɗe bakin fanfo. . .✍🏿

07068606171



*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨


_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:21] Miss Green🍀: 45. . . . 46


Rashida ce ta share min hawayen ta juyo da fuska ta tana kallona sosai ta ce"Khairat wannan kukan da ki ke ya yi yawa,don Allah ki daina kinji"?.Ta faɗi hakan tana kallon cikin idanuwa na,a hankali na ce"to na daina sis Don Allah ki yafemin kinji".

Dariya ta yi sannan ta ce"a haba matar yaya ai bata laifi,yanzu dai tashi mu fita waje ana ta hotuna bakyanan,waccen rasai ɗin matar yayanki mero tana cen gindin camera ana ɗaukar hoto,abin dariya Yaya Salim yaƙi fitowa yana cen wajen abokansa,wai kunya ya keji kada araina sa don ya auri mero".


ta faɗi hakan tana jan hannuna,murmushi kawai na yi mukazo muka wuce ta kusa dasu Hajiya Kaka ta ce"yauwa Rashida fita da ita,don ni na gaji da zaman ta aɗakin nan".

"Cikin shagwaɓa na ce"au yanzu Hajiya kaka har kin gaji dani ko"?.murmushi ta yi sannsn ta ce"haba Me sunana yaya za'ayi in gaji dake?ai hakan ma bazai yiwu ba".

Hotuna sosai aka yi mana,mamana da ƴan uwanta duk sunzo an ɗaukemu hotuna,da yaya Salim da Yaya Aliyu da autanmu maher duk an ɗaukemu hoto gwanin sha'awa.
Duk abinda muke yi a idon su Hajiya Iklima,ta ciji laɓenta har sai da taga jini ya fito,Anty kishiyarta ta zaro idanuwa waje ta ce"ikon Allah Iklima jini fa na ke gani abakinki"?.ta faɗi hakan da mamaki.

"Hmm Za kiga abinda ma yafi jini abakina,matuƙar ina ganin matar nan da ƴaƴanta sai inji kamar zan mutu saboda baƙin ciki,a duk duniya babu halittar dana tsana irin Zulaiha da kuma ƴaƴanta musamman waccen baƙar ƴartata,na tsanesu tsana mafi muni arayuwata".

"Ai ba ke kaɗai ki ka tsanesu ba,nima na tsanesu wallahi,duk wani iyaye na Zulaiha yanzu ai ya zama tarihi,wai ita wadda miji keso ta dinga wani iyawa,yanzu ina iyawartata take?kinga kuwa ai ko yanzu ɗan koli yaci riba wallahi".Anty ta faɗi hakan tana hararar mama wacce ma bata san wainar da ake toyawa ba,da Rana aka kira masu kiɗan ƙwarya sosai suka ƙware wajen sana'arsu,aka sakamu a tsakiya nida mero,ai tuni amarya mero ta ware ta zage tana ta muskuta mazaunai kamar ba amarya ba,ina ta taɓa ta wai kada ta yi amman ina rawar take ta yi,ko ajikinta.

Hajiya kaka sai liƙi take ta mana,musamnan ma ni,atarihi babu wani bikinda Hajiya kaka ta taɓa kashe kuɗi irin bikina,ta kashe kuɗi ba na wasa ba,har tausayi ta bani.

Ana cikin wannan kiɗanne na zagaye a hankali na fita na koma ɗakin Hajiya kaka na dinga cin kukana idanuwa na sukayi jawur kamar gauta.

A hankali mama ta ƙaraso inda na ke,ta ɗago fuskata sosai ta sharemin hawaye na sannan ta ce"khairat aƙwai abubuwa da yawa da ya kamata in faɗa miki amatsayi na,na mahaifiyarki duk wata uwa tagari tana yi wa ƴarta da nasiha da tabi mijinta,ta yi masa biyayya,yi na yi bari na bari sannan aƙwai wasu abubuwan da ya kamata in faɗa miki na farko shine,kada ki sake mijinki yaji wari ko wani bashi ajikinki,ki kasance mai tsarkake jikinki ki zamo kullum cikin tsafta,yin hakan zai ƙara kusanta ki da mijinki sannan tsafta na ɗaya daga cikin ginshiƙin aure,matuƙar mace ƙazama ce to za kiga babu inda auren ya ke kaiwa,kullum cikin faɗace2 da kai ƙara,abu na biyu kuma shine ki kasance mai kula masa da dukiyarsa wala yana nan wala baya nan,ke dai ki zamo mai saka idanu akan kula da dukiyarsa,sannan ki rintse idaniyarki akan kuɗinsa,duk yawan kuɗin da zai ajje kada ki ɗaukar masa,khairat nasan halinki nasan baki taɓa yin hakan ba amman ki kiyaye hakan.ladabi da kuma biyayya indai ya baki umarni ko menene ki yi,indai har bai take addini ba to ina mai jan hankalinki ki yi sa,iya girki nasan ke gwana ce akan hakan amman yanzu tunda miji zaki yiwa to tabbas ya kamata ki ƙara ƙwazo sosai ta yadda zaki yi fice aduniyar girki.

Khairat idan har na ce zan zaunar dake inyi ta yi miki magana akan aure to tabbas zamu ƙwana ban gama ba,sai dai ince Allah ubangiji ya baku xaman lafiya me ɗorewa.
Tana faɗar hakan ta rungume ni tana kuka sosai,nima kukan na ke a haka Rashida ta shigo ta samemu,itama ta taya mu kukan,babu mai rarrashin wani.

Mama ta ce"khairat wannan envelope da kika bani wanda wannan bawan Allahn ya baki,jiya na buɗesa naga kuɗi ne aciki har dubu ɗari,to shine na wuce kasuwa na siyo miki wasu abubuwan,banso na yi amfani dashi ba amman Aliyu ya tabbatar min da mutumin arziƙine,sannan yau daya zo ɗaurin aure ya baki ƙyautar mota guda,amman mahaifinki ce wa yayi ba za'a amsa ba,amayar masa amman motar tana gidan Aliyu,za'a siyar a siya miki wani abin mai amfani."

Na yi mamakin Ahmad sosai kamar bai san daɗin kuɗi ba?irin wannan zubar da kuɗi haka?nan dai mama ta sakani agaba na shiga banɗaki ta zubamin wani abu mai ƙamshi acikin ruwan,na shiga na yi wanka ƙamshi duk ya baɗe ɗakin,ina fitowa ta bani wata zuma mai kauri tace insha,babu musu na ɗaga kaina nasha,sannan ta bani wasu abubuwan ta koyamin yadda zanyi amfani dasu koda bayan aure idan ina da buƙata.


Yadda ake haɗa zumar mata.

*Zuma*
*citta*
*kanunfari*
*minanas*
*Riɗi*
*sassaƙen ɓaure*
*sassaƙen gamji*
*ƙwaƙwa*

Ki samu zumarki mai ƙyau,sai ki samu sassaƙen ɓaure amman bayan kin dakashi ya yi luƙui kin tankaɗeshi,sai ki ɗora zumar akan wuta kiɗan ƙara ruwa kaɗan,sai ki zuba garin minanas da kuma garin ɓauren da kika daka,sai gamji shima kamar garin ɓaure,chokali biyu biyu zaji zuba,ya danganta da yawan zumarki don ba'a son ya cika kauri da yawa,sai ki zuba garin citta,da kuma garin kanumfari,sai kiɗan soya ƙwaƙwa daban daman kun riga da kin soyata ƙananu sai ki zuba aciki,riɗinki ma ki zuba bayan kin wankeshi kin busar dashi sosai.sai ki rage wuta kina juyawa kaɗan kaɗan,shi wannan haɗin ba'a son ki cika masa wuta.

Za kiji yana ƙamshi to alamar ya yi kenan,sai ki sauke ki samu ƙwalbarki mai ƙyau ki zuba aciki,ki dinga shan chokali 2 da safe biyu da yamma.

Hmm ni dai bazance komai ba,sai an gwada akan san na ƙwarai.
*****


"Ai Bilal ba sai ka nunamin ce wa baka son yarinyar nan ba?ƙarfe nawa yanzu?ɗaga kanka ka duba agogo?".a hankali ya ɗaga kansa ya duba agogon ƙarfe 10 na dare,ya sauke kansa sannan ya ce"kai Hajiya kaka gaskiya kina takuramin wallahi,yanzu me ki ke son inyi miki?".

sheƙeƙe ta kallesa sannan ta ce"ungo Ruƙayya zaka yi min"?.ta faɗi hakan tana harararshi,ga dai mata nan ka bari agidanku ka ƙi ka kawo motocin da za'a kaita gidanka,mero wacce zata zauna agidannan tun biyar akazo aka ɗauketa,amman kai shine zaka gaya min maganar banza ko"?.

"Haba grany!ba fa ita kaɗai ce matata ba,ga Jidda nan,amman ita babu wanda ya damu,sai ita ƴar gwal,kuma ni zanje in ɗauko jidda da kaina,ita kuma xan aiko azo a ɗauketa,shikkenan?".

Ya faɗi hakan yana ɗagawa Hajiya kaka gira,ta ce"ai wallahi kuwa baka isa ba Bilal,wato ma har ka ke cemin ita wannan figigiyar matar taka kai za kaje ka ɗakkota,ita kuma wannan za'ka aiko a ɗauketa ko?to ban yarda ba,sai dai ita ka tura a ɗakkota wallahi,kuma ni zan kaita har ɗakinta".

Ta faɗi hakan tana shiga ɓangarenta,daman mama ta sakani na canja kayana,wata haɗaɗɗiyar lifaya mai ƙyau,fara ƙal da ratsin kore na yafa ta har kaina na rufe ruf,hajiya kaka ta janyo hannuna mama tana ta rarrashina,muka fito waje.

Yana tsaye inda kaka ta barsa,ya hangota ya juya kai abinsa,azuciyarsa yana ce wa yarinyar da aka haifeta agabana na raineta sannan yanzu acw wai ita ce matata?wannan ma ai janyowa mutum raini ne.ya shiga cikin motar ya tayar da ita abaya muka zauna nida hajiya kaka,sai ƴar uwar mamana guda ɗaya.


Karatun qur'anine ke tashi acikin motar,ga ƙamshin freshner ya cika motar mai sanyin daɗi,har mukaje kuka na ke,duk haushi ya cika sa a fili ya ce"wannan ai dole mutum yasha pain reliep".Hajiya kaka na jinsa ta hararesa ta baya.

Abakin kyakkyawan ɓangare na aka saukeni,ɓangare uku ne agidan,ɗaya nawa,ɗaya na jidda ɗaya na me gidan,ɓangare na ya yi kyau sosai,ko sisin mahaifina babu aciki Baba Abdullahi shi ya yi rawa ya yi tsaki,kayan da aka sakamin ko su Rashida dasu ke matsayin ƴaƴansa bai yi musu shi ba.har kayan kitchen bawan Allahn nan shine ya yi,ya bawa ƙannansa su Aisha suka siyo masu matuƙar kyau.


Koda zamu shiga sashen nawa hajiya kaka ta ce"ki yi bismillah kafin ki shiga Allah ya kareki daga sharrin duk wani mai sharri".

Da ƙafar dama na shiga gabana yana dukan uku uku,shikkenan ta faru ta ƙare yau dai Allah ya kawoni gidan da za'a gasa ni kamar yadda na nema,jikina duk ya yi sanyi sosai.

Sai asannan aka dinga kawo mutane aka cika gida ɓam,Jidda kuwa ta cika ta yi ɓam,don ta kirasa amman bai gani ba wayarsa na silent,sai sannan ya duba ya gani,tuni jidda tafi awa agidan,don Babanta ya ce akawo ta tunda masu ɗaukarta basu zo ba,a sabuwar motar Jidda ɗin aka kawota,sabuwa dal sai sheƙi take.


Shigowar saƙo wayarsa ne yasa ya duba alokacin yana shirin zuwa ya ɗauko jidda,da sauri ya kalli sashen jidda ɗin sannan ya kalli wajen motocin gidan,sosai abin ya basa mamaki me yasa bata jira yazo da kansa ya ɗauketa ba,wani kishi ya tokare masa ƙirjinsa,yanzu haka wasu mazan duk sun kalle masa matarsa.

Kai tsaye sai da ya fara shiga sashensa ya ajje wasu abubuwan sannan ya shiga wajen jiddarsa,yana shiga ɗakin na ta ya hangota kan gadonta babu ko lulluɓin idanuwanta sun kumbura saboda kuka,ta fara harararsa,ya matso inda take ya kalleta sannan ya ce"haba my jidda ki yi min uzuri don Allah". . .


tun kafin ya ƙarasa ta ce"don Allah kada ka ƙarasa faɗar abinda ka yi niyya,idan banda rashin adalci shine ita kaje ka ɗaukota ni kuma ka barni ni kaɗai ko?wannan shine alƙawarin da ka ce za kayi min?".

riƙe hannayenta ya yi wanda suka sha lalle ya ce"jidda kece matar da na keso,ta yaya ki ke tunanin rashin adalci daga wajena?ko kaɗan bazan taɓa haɗaki da wata mace ba,u are my one and only".ya faɗi hakan yana sumbatar goshinta,tuni ta washe bakinta don arayuwarta tana matuƙar son Bilal,amman idan ta tuno da wani abu sai taji duk ranta ya yi masifar ɓaci.


Ina rungume ƙirjin Hajiya kaka sai rarrashina take,Rashida ta ce"hmm wallahi Hajiya kaka duk kinfi son khairat, ni fa har yanzu ko gida na ma bako sani ba".ta faɗi hakan cikin shagwaɓa.

Sai kuwa Hajiya kaka ta ce"Allah sarki dukkanku ina sonku amman a gaskiya ita khairat ina tausayinta ne sosai,sam ita bata ƙwatar kanta kamar yadda ku keyi,haƙurinta ya yi yawa gaskiya,shiyasa na ke tausayinta balle yanzu kuma za ta zauna da wannan miskilin sai yadda hali ya yi.to wallahi daman ina faɗa miki duk abinda ya yi miki ki rama,kada ki zauna kina wani jin kunyarsa yasa miki hawan ruwa ya barki anan."

Hajiya inna wadda zuwanta kenan ta ce"khairat ki ka biyewa Ramatu kaiki za tayi ta baro,don haka ki yiwa mijinki biyayya iya bakin iyawa,yi na yi bari na bari kinji".

"To ai ni cewa na yi kada tayi masa biyayyar?Allah hajiya Inna ki dinga kyautata zato".

"A'a to Ramatu tsakaninki da Allah banyi gaskiya ba?so ki ke ƙwana biyu a sako miki ita kome?,ah to adinga sara ana duban bakin gatari dai".

Nan dai suka dinga yimin nasiha sannan suka tafi har su Rashida,har ta tafi sai kuma ta dawo ta rungumeni tana share hawaye ta faɗamin wani abu a kunne,dariya na yo itama ta yi sannan suka tafi suka barni da kewa ni kaɗai kamar mayya.


Na ya ye mayafin fuskata ina kallon ɗakin,naji wani hawaye yana fita acikin idanuwa na..oh ko wata irin rayuwa zanyi a wannan gidan?mijin da baiso na?wani irin ƙalubale zan fuskanta?Allah kaɗai yasan abinda zan gani,na rintse idanuwa kuka yaci ƙarfina,ina tuno lokacin da na ke neman yafiyar mahaifina,ko kallona baiyi ba,ƙarshe ma ya tashi yabar wajen". . .✍🏿

07068606171



*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨


_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:21] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*


📃LITTAFI NA 2

UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*addu'ar samun lfy ga ko wani irin ciwo*

an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ɗauka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ƙasa sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka;

"bismillahir turbati ardina biriqati ba'dina yashfa Taqimuna bi'izni rabbina".



47. . . .48


. . . .Nasha kuka na sosai kamar ma bazan daina ba,na tashi na shiga banɗaki Na ɗaura alwala sannan na shimfiƊa sallaya na tayar da sallah,na yi isha'i da kuma shafa'i da wuturi Na Ɗaga hannaye na sama ina kuka ina addu'ar Allah yasa yaya Bilal wataran yaso ni kamar yadda na kesonshi,Allah kuma yasa albarka acikin auranmu.

na shafa addu'ar na tashi na Ƙwanta na Ɗaga idanuwa na sama ina tuno da wasu abubuwa,waƊanda suka wanzu arayuwata,gashi haryanxu ban samu sauƘinsu ba.

Babu zancen zuwan ango,don tun ina yaudarar kaina wai ina tunanin zaizo har naji shiru babu shi babu labarinsa,na rintse idanuwa na hawaye yana fitowa.


***
"Jidda ki faƊamin abinda ya faru da rayuwarki?Jidda ni fa ba yaro bane balle kice ko yau ne aka haifeni?nasan komai ayadda ya ke duk dani ba mazinaci bane amman ki sani shekaruna sun kai in san hakan,kada ki Ɓoye min komai,na yi miki alƘawarin indai ki ka faƊamin gaskiya,bazan taƁa zarginki ba".

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login