Showing 96001 words to 99000 words out of 103202 words

Chapter 33 - ABIN CIKIN ƘWAI

22 Jan 2025

4497

yanzu kaga Jidda ita ce ta yi sanadin rabani da khairat,rabuwa ta har abada wallahi captain zuciyata gab take da bugawa,ina ji ina gani khairat ta yi aurenta,ko kallon arziƙi bai haɗani da ita idan ta ganni ma captain yadda kasan taga wani dodo,Allah kamarin khairat har mamaki ya ke bani"

Ɗan murmushi captain ya yi sannan ya ce"Tabbas Bilal nima da kaina na yadda rayuwa cike take da ƙalubale,Bilal aƙwai wani laifi wanda ka yi wa khairat wanda aduk sanda ta ganka sai taji bata son ko haɗa ido da kai saboda girman laifin da ka yi mata.

Na farko shine ka zargeta da laifin da ba ita ce ta aikata sa ba,na biyu kuma shine rashin binciken da baka yiba alokacin da abin ya faru,wanda Darasin daya kamata ka fuskanta anan shine shi saurin fushi yana haifar da dana sani,don haka shiyasa ya ke da kyau duk abinda zamuyi mu dinga bincike kafin mu aikata,koma koda mutum yana cikin fushi bai kamats ace ya saki matarsa har saki uku ba,ai addini bai ce haka ba Bilal."

Idanuwan Bilal sunyi jawur ya juyo ya ce"Hmm captain baza ka gane abinda naji alokacin ba,duk abinda zan ƙwatanta maka dashi to tabbas ya wuce hakan,ina da matsanancin kishi sosai,musamman ma akan khairat,yarinyar da tun tana cikin mahaifiyarta na ke azabar sonta,amman dubi abinda khairat ta yimin yanzu".

Yana faɗar hakan ya dafe sai tin zuciyarsa ya ce"captain ina jin wani abu acan cikin zuciyata yana yimin yawo,tabbas zuciyata saura kaɗan ta buga,captain ka kaini gida yanzu bazan iya zuwa ba".ya faɗi hakan yana dafe saitin zuciyarsa wanda ya kejinsa kamar zai fito waje,ga wani irin zafi da ya keji acan cikin zuciyar tashi.


Sosai Captain ya tsorata ya koma mazaunin Bilal ɗin ya tuƙa motar cikin gaggawa,asibiti ya kaisa don a halin daya ga Bilal bazai iya kaisa gida ba,shima captain ɗin hawaye ne ke fitowa daga cikin idanuwansa,yana riƙe da hannun Bilal ɗin guda ɗaya,Allah ne dai ya kawosu asibiti lafiya.

Likitocin suka amshesa suma duk hankalinsu a tashe don tuni har ya sume ma,aka shiga dashi emargency.Captain sai hawaye ya ke da sauri ya kira wayar Alhaji Abdullahi mahaifin Aliyu,ya sanar masa duk abinda ke faruwa shima hankalinsa ya tashi sosai,tuni ya sanarwa da ƴan uwansa suka taho tare,amman ba'a gayawa Hajiya kaka ba,harma da mahaifiyar Bilal ɗin bata sani ba.


Sosai hankalinsu ya tashi da jin abibda likita ya faɗa,cewar jininsa ya yi mugun hawa wanda idan ba'a basa abinda ya keso ba komai zai i'ya faruwa,sosai hankalinsu ya tashi to me Bilal ɗin ya keso wanda ba'a yi masa ɗin ba?suka zauna jigum jigum.Baba Usman ya ce"to yaya ko kasan abinda ke damunsa ne?wanda mu bamu sani ba?".

Kaɗa kai Alhaji Abdullahi ya yi sannan ya ce"wallahi Usman ni kai na bazance maka ga abinda ke damun Bilal ba,amman ni dai naga yanzu idan ya dawo sai kaga duk ya rame,ko alokacin ma na tambayesa ko ba shida lafiya ne?amman sai ya ce min babu komai.kasan shi Bilal ba mutum ne me magana ba,ga miskilanci shiyasa ni ban gane konai ba".

Ko da suka ga rashin faɗan rashin lafiyar Bilal zai iya janyo wata matsalar sai suka yanke shawarar kawai gwara su faɗa agida,don haryanxu bai farka ba,wai numfashinsa ne bai koma normal ba.

Sosai gidan kowa ya ruɗe da rashin lafiyar Bilal,sai gasu sun cika asibiti kowa hankalinsa atashe Hajiya kaka sai kuka take tana ce wa"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Bilal sai da ka saka wannan damuwar aranka?yanzu gashi nan har ta kaika ga ƙwanciya a asibiti"?.


Baba na ya ce"a'ah umma daman kinsan abinda ke damunsa"?.da sauri ta ce eh ƙwarai nasan abinda ke damunsa saboda ɗiyar wajenka khairat shiyasa duk hakan ta faru,to wallahi tallahi ka faɗawa ƴarka ta fitar min har jika na,tun kafin ranta ya yi masifar ɓaci".

Da sauri baba na ya ce"a'ah Umma kin kullemin kai baki ɗaya?don Allah ki faɗamin wata ɗiya ta ce"?.da sauri ta kallesa sannan ta wurga masa harara ta ce"ban sani ba khairat ƴar wajenka ita na ke nufi,rannan da ta zo da mijinta tana da ciki ya riƙe mata jaka,kamar akanta aka fara ciki shine taga ɗan wajenta Audu Irfan kenan shine ta-yi ta-yi yazo wajenta ya ƙi zuwa,to shine fa daya ƙi zuwa ta ce wai ubansu ne ya zugasa,shine yaje ya gayawa uban nasa yazo,wallahi yarinyar nan khairat babu ko kunyar ƴan uwantaka ta buɗe bakinta ta zagesa tsaf zagi na rashin mutunci.har da ce wa wai ta tsanesa tsana mafi muni.to sai me don ta tsanesa ai muma muna sonsa don haka taje ta ƙarata.tabar ganin mijinta na bani kuɗi to duk ta banzar don ni a'i jika na yafi min wannan farar fatar wacce ke ruɗar ƴarka".


Sosai abin ya yi wa kowa ciwo akan abinda khairat ta yi wa Bilal,Rashida taji nan da nan khairat ta sare mata akai,don ita tun kan yadda take zaginsu irfan ta fake da zaginsu alhali kuma Bilal ɗin take zagi sai taji duk ta sare mata aranta.

Mamana da ke wajen ta sumkuyar da kanta don har zuciyarta ba taji daɗin abinda khairat ɗin ta yi wa Bilal ba,don ko babu komai ai ɗan uwanta ne uban ƴaƴanta,da ya ke ranar da khairat ɗin tazo ranar bikin ƴar gidan Baba Hamza ne kuma an tafi dinner shiyasa ba kowa ne ya san zancen ba,Sai Hajiya kaka uwar ƴan kunne duk da ta tsufa tsam kunnenta na nan daram don ko gulmarta ka yi to babu abinda baza taji ba.


Babu wanda ya kirani ya ce Bilal bai da lafiya hatta mama na bata faɗamin ba,kullum dai idan na buga mata waya zance ta bani su Haidar muyi waya amman irfan sam bai ko kallon inda wayar take,idan ma aka ce masa mamansa ta bugo sai ya ce waishi ba mamansa ba ce.

Ranar dana ji hakan da kunnena ranar na yi kuka sosai,tambayar duniya Shahid ya tambayeni abinda ke faruwa na ce masa babu komai.haka dai ya sakani agaba har na samu naci abinci.sosai Shahid ke kula dani babu abinda na nema na rasa na rayuwa,ko tagumi idan shahid yaga na yi to hankalinsa yanzu zai tashi.



Ammi mahaifiyarsa yanzu ita ke yini a sashe na,saboda taga duk yanda na rame naƙi sakin jiki na kamar da,shima Shahid ɗin yanzu idan ya tafi aiki mai makon da baya dawowa sai maghrib amman yanzu la'asar na yi zai dawo.



Jikin Bilal ya yi sauƙi yanzu,sai dai kowa ya kallesa yasan yana cikin wani hali,ga yaransa wanda yanzu sun koyi wata ƙiwa indai ba shiba basu fiya yadda da kowa ba.hatta abin yanzu yana san ya shafi aikinsa.don daga wajen aikin ma sun aiko masa da saƙo akan yana wasa da aikinsa,uzuri ya bayar akan ce wa bai da lafiya.ai kuwa ba tare da ya watstsake ba ya koma bakin aikinsa.



Sai dai fa ƙwana biyu da komawar tasa jikinsa ya ƙara dawowa,yana daurewa don bai san kowa yasan halin da ya ke ciki,ga ciwo na nuƙurƙusarsa amman yana daurewa.


*********

ayanzu mun gama makaranta wacce muka yi shekara fin biyar muna yi,don kowa yasan aikin Lauya yadda ya ke aƙwai cinye shekaru.ya yi dai dai da kasancewa ta shekara ishirin da huɗu a duniya.abin kuɗi sai gashi shahid ya fara cuku cukun nemomin aiki,Allah ya taimake ni aka ɗaukeni a babbar kotu amman bazan fara aiki ba har sai na haihu.


Tun safe ciwo ke nuƙur ƙusa ta amman naƙi in bar kowa ya gane halin da na ke ciki,har dai Ammi ta gano ai kuwa sai ga ciwo daga kaɗan ya zama babba,muka garzaya asibiti,A ruɗe Shahid ya taho asibitin hankalinsa tashe.



Dai dai wannan lokacinne kuma aka kawo Bilal shima ranga-ranga babu lafiya,kowa hankalinsa atashe sai kuka ake.



07068606171



*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨


_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:31] Miss Green🍀: 1001. . . .1002



tashin hankali sai ya zama guda biyu don nima wannan haihuwar har tafi tasu Ƴan huƊu,don har an fara fitar da rai dani,shi kuwa shahid nema ya ke ya fita daga cikin hayyacinsa,ba don ma ammi ba da ba'asan abinda zai faru ba,har an fara haƊa kayan aiki na sunkutu Ƴa ta mace kyakkyawa me tsananin kama da mahaifinta,kyakkyawa ce sosai har tafi mahaifinta ma kyau.


hajiya kaka ma tazo ta yimin barka sai dai fuskarta atamke tsaf,haka ma duk wanda zai zo duba ni sai inga fuskarsa a haƊe sosai na rasa gane kan kowa,kai hatta yaya Aliyu dasu mamana kowa sai inga fuskarsa tamau,abin ya dameni sosai,na rasa wanda zan tambaya gashi nima ban gama warwarewa ba don nasha wuya sosai.

Shahid ne ya shigo shima duk jikinsa ya yi sanyi,yana shigowa ya kalleni sannan ya ce"khairat ya jikin"?.sosai maganarsa ta girgizani don bai taƁa kirana da khairat ba sai dai hayatee,na kallesa sosai Na ce"hubby yau kuma sunana ka ke faƊa"?.na faƊi hakan ina me kallonsa kamar ya yimin laifi.

sunkuyar da kansa ya yi ya Ƙaraso inda jaririyar take ya saka hannu ya Ɗauketa ya rungume ta a Ƙirjinsa hawaye masu zafi suka zubo masa a kuncinsa,a zuciyarsa ya ce Allah sarko Ƴata ashe bazan rayu da mahaifiyarki ba?ashe bazanyi rayuwa da ita me tsayi ba?yanzu me na aikata haka?shin nima ina tunanin zan iya wani auren idan na rabu da khairat?shin ya rayuwar Ƴarsa yaya za ta kasance alhali babu me kula da ita sai mahaifiyarsa zai Ɗorawa wahala.

jin kukan da khairat ta fashe dashi ne ya saka ya juyo da sauri ya ce"khairat lafiya ki ke kuka me aka yi miki?".ya faƊi hakan yana matsowa har ya riƘe hannuna wanda na Ɗora aka ina gunxuma ihu kamar wani ya dake ni.

da sauri na yar da hannunsa gefe na ce"haba na gaji wallahi,yaya kuke so inyi ne?kO cikakkiyar awa Ɗaya banyi da haihuwa ba,amman kowa ya shigo sai inga duk hankalinsa atashe kuma ya Ɗauremin fuska?Haba wannan wani irin rashin tausayi ne?ku faƊamin mana idan wani abune ya faru?"

da sauri ya koma gefe ya ce"khairat babu komai fa haka dai ke ki ka gani,amman babu komai bari inje wajen Ammi sai mu taho tare taje duba wanine ba shida lafiya".yana faƊar hakan ya fita da mugun saurinsa,tuni naji zuciyata ta tsinke na shiga wani irin kuka wanda na kasa gane kansa,na kalli Ƴata wacce kebta shan hannu alamar tana neman abincinta,da ta gaji da shan hannun sai ta fara kuka sosai,nima uwarta ta kuka nake sosai kamar wacce aka aiko mata iyayenta sun mutu duka.


ana cikin wannan halin ne anty hakisa tazo,da sauri ta Ƙaraso cikin Ɗakin tana ce wa"subhanalillahi khairat me ya faru haka?ga yarinya na ta kuka alamar tana neman mama kuka kinƘi bata?".ta saka hannunta cikin gadon babyn ta Ɗakko ta tana Ɗan girgiza ta,ta zauna ta ajjemin ita akan cinya ta tace"khairat yi haƙuri ku bata tasha kinji?koma menene ya faru bai kamata ki yiwa Ƴarki ta cikinki haka ba,ki bata tasha sannan sai muyi magana".

Sai shashsheƘar kuka ba ke harda majina ta kalleni kawai,tana jin tausayina har cikin ranta,a hankali na ke shayar da ita jaririyar ta riƘe babban Ɗan yatsana tana kuma kallon cikin idona sosai,ina kallon yarinyar sai naji zuciyata ta fara sanyi tabbas ƳaƳa rahama ne arayuwa,Allah ubangiji ya bawa duk wanda basu haihu ba,ya basu masu albarka wanda za'ayi alfahari dasu aduniya da lahira.

sai da tasha ta Ƙoshi sosai sannan anty halisa ta amsheta ta sakata a kafaƊarta har ta yi gyatsa,sannan ta kalleni sosai ta fara yimin nasiha sannan ta ce"khairat yanzu fa daga dubo baban Ƴan huƊu na ke".da sauri na kalleta sannan na ce"me ya same shi kuma?daman ba shida lafiya ne?".

Na faƊi hakan zuciyata na bugawa sosai,ganin na shiga wani hali ne yasa ta gane ce wa ban san ba shida lafiya ba ta ce"khairat come down,kinga yanzu kin haihu fa kina buƘatar ki samu kulawa sosai don haka kada ki Ɗaga hankalinki don Allah ciwon fa yanzu da sauƘi".

da sauri na miƘe na ce"haba anty halisa ni fa ba yarinya bace kamar da,kowa fa ya shigo fuskarsa babu daƊi,ni nasan aƘwai abinda ake Ɓoyemin."Na faƊi hakan cikin kuka na tashi tsaye ina jin wani irin jiri yana Ɗiba ta,ga uwar yunwa da na keji wacce ta gama cika min ciki na ce"anty halisa don Allah zo muje ki nunamin Ɗakin da aka Ƙwantar dashi"?.

da sauri ta ce"a'ah fa khairat bazan iya rakaki ba gaskiya,kinga ba kida lafiya kuma bayan haka mijinki ma fa yana cen yanzu na baro sa acen,kinga ai babu daƊi ki dai bari ki samu lafiya sai kije".da sauri na Ƙarasa kusa da ita ina kuka na ce"don Allah anty halisa ki rakani in duba sa,zuciyata ji na ke tamkar zata fito don Allah".

sosai take kallona cikin mamaki,wato khairat micijin sari ka noƘe ce,wato duk tsanar da take ce wa ta yiwa yaya Bilal ashe duk Ƙarya ne?to idan ba Ƙarya ba me yasa ta damu don ba shida lafiya?.


ganin khairat Ɗin ta dage ne yasa ta ce"to khairat muje".ta Ɗakko min jaririyar muka fito,ina dafe bango ina tafiya jirin yana Ɗiba na amman a haka har muka isa Ɗakin,duk naji jikina ya Ƙara yin sanyi sosai.


da mutane sosai a Ɗakin duk suka zubomin ido mamaki Ƙwance kan fuskarsu har da shahid a Ɗakin,da ammi mahaifiyarsa da kuma mama har dasu yaya Aliyu,ga hajiya kaka a gefe su Rashida,sai maryam wacce bata fi wata biyu da haihuwa ba,ta haifi Ɗanta na miji,me sunan yaya Bilal.


saurin dafe jikin bango na yi ina waro ido waje,ganin yaya Bilal Ƙwance kamar matacce an saka mishi abin shan numfashi ya yi wani irin fari fauu ga kuma ramar da ya yi,an saka masa kaya ruwan skye blue irin na marasa lafiya.

wani irin kuka na fashe dashi tuni na tsugunna Ƙasa da rarrafe na Ƙarasa bakin gadon,saboda Ƙafufuwa baza su iya kaini wajensa ba,na ce"Yaya Bilal anya kuwa kai ne?me ya faru da kai?wani irin ciwo ne wannan?".duk ni kaƊai ke sambatu na kamar mahaukaciya sabon kamu,babu wanda ya cemin Ƙala,sai ma harara da wasu ke bina dashi.

ban ma san na riƘe hannunsa ba sai yanzu na Ƙara ƘamƘame hannunsa na ce"don Allah yaya Bilal ka tashi,idan ka mutu nima tabbas zan iya mutuwa,da kai na saba yaya Bilal tun ina Ƙarama ta ka nuna min so,ka nunamin Ƙauna,haƘiƘa banyi maka adalci ba".

Da sauri shahid ya tashi ya fita waje,duk zuciyarsa babu daƊi wani irin kishi yaji ya turniƘe masa Ƙirjinsa,ya zauna kan wani benci ya saki kuka kamar Ƙaramin yaro,mutane sai wuce wa suke suna kallonsa yana son khairat da duka zuciyarsa yana jin ciwon rabuwa da ita,amman ya zama dole ya yi hakan don ayanzu ya gano ce wa ba Ƙaramin so khairat ke yi wa tsohon mijinta ba.


Yana zama ammi ta biyo bayansa don ganin halin da Ɗanta ke ciki,itama duk zuciyarta babu daƊi ko kaƊan,ta ce"shahid ka yi haƘuri ka ka baiwa Allah lamarinsa,sam banji daƊin hukuncin daka Ɗauka akan aurenka da khairat ba,ka sani shi Allah yana tsara lamarinsa yadda yaso,khairat suruka ce ta gari a azamana da ita dana yi,bata taƁa yimin wani abu da raina zai Ɓaci ba,kullum ƘoƘarinta shine ya za'ayi ta kyautatamin,don haka ni sam banji daƊin wannan abinda ka aikata ba."


Murmushi shahid ya yi wanda masu iya magana suka ce yafi kuka ciwo ya ce"Ammi ki daina magana ki yi shiru,saboda ni kaƊai nasan halin da nake ciki xuciyata tana yimin zafi sosai akan wannan sakin da na yi wa khairat,wanda ita kanta bata san na yi mata ba,ammi jiya fa dana shiga wannan bawan Allahn kiran sunan khairat kawai ya ke,sannan ciwon zuciya ya kamasa saboda Ƙaunar khairat da ya ke yi,Ammi ina da imani ina kuma da tausayi bazanso nima ayimin hakan ba,ni nasan nima zan iya shiga wannan halin akan Ƙaunar khairat,amman babu komai zan karƁi Ƙaddarata insha'Allah".

ya rungume mahaifiyarsa yana kuka me tsuma zuciyar me sauraro,shahid kiran sunan Allah kawai ya ke yi,halisa ta fito daga cikin Ɗakin da jaririyar a hannunta ta tsaya a tsaye tana kallon shahid wanda ke Ƙwance kan cinyar mahaifiyarsa yana kuka kamar Ƙaramin yaro.

sosai ya bata tausayi ta matso a hankali inda suke ta fara magana cikin harshen turanci ta ce"shahid ka yi haƘuri ka fauwalawa Allah komai,amman banji daƊin sakin da ka yiwa matarka khairat ba,don ba'a wasa da aure".

a hankali shahid ya tashi daga kan cinyar ammi ya ƙarasa wajen halisa ya amshi ƴarsa.wacce ke ta baccinta hankali ƙwance.me kama dashi sosai ya zauna yana kallon ƴarsa cike da so da ƙaunarta.sai yanzu ma ya tuno bai yi mata huɗu ba ba.wasu hawaye suka zubo masa ya share su tuno da halin da yarinyar zata kasance na rashin mahaifiya akusa da ita.shi da yarasa mahaifinsa ma ya damu sosai balle kuma mahaifiya.gashi nigeria ba wajen zaman bane dole zai koma masar.ko england tunda dai shi ɗan asalin ƙasar england ɗin ne.


yana gama raɗa mata sunan Ammi ta amshe ta.tana manna mata kiss a goshinta na jin daɗin ganin jikarta ƴar shahid gudan jininta.lallai wannan yarinya zata sha gata.ya ce"Ammi na raɗa mata suna da Rahma(khairat)taci sunan mahaifiyarta.


07068606171



*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login