Showing 69001 words to 72000 words out of 103202 words

Chapter 24 - ABIN CIKIN ƘWAI

22 Jan 2025

4474

ke kika ɗauketa ta kika ajjeta a ɓangarenki?ni tun tuni na cire wannan yarinyar daga cikin ƴaƴa na don ba zan zauna da bara gurbi ba". . . tun kafin ya ƙarasa maganarsa Hajiya kaka ta ce"kai Malik faɗi abinda ya kawo ka amman ba wannan ba,tunda dai kai ka kasa gane ce wa sharri akewa ƴarka".ta faɗi hakan tana harararshi.

Yasan sarai halin mahaifiyarsu ba ƙara sauraransa za tayi ba koda ma ya yi magana,sai ya ce"Hajiya daman magana ce akan Yaya Abdullahi,to muna taso mu gaya miki ammsn don Allah kada ki tada hankalinki akan wannan,yanxu haka ma ya fara samun sauƙi".

Da sauri kaka ta fashe da kuka ta ce"Allah sarki ɗana bawan Allah mutum me haƙuri,me yasa kuka ƙi faɗamin abinda ya faru,kuke ta ɓoyemin kuka cemin wai ya yi tafiya ne ta gaggawa?ashe ɗana yana cen babu lafiya"?.sosai suka dinga tausar zuciyarta.

Ina kitchen ina shan sanyayyan ruwan dana fito dashi acikin fridge bayan duk na gama jin abinda mahaifina ya ke faɗa,naji zuciyata tana min suya sosai na ɗaga gorar ruwan swan sai da na shanyesa tsaf sannan na ajje,sai ga Hajiya kaka tana kuka take faɗamin abinda ya faru,sosai jiki na ya yi sanyi donshi Baba Abdullahi babu ruwansu sam da rayuwa da rikicin da ke cikinta,na shafa cikina take naji son cikin ya shige ni,ko don babu komai sai saboda Baba Abdullahi sam bazaiji daɗin hakan daga gare niba,don yana iya bakin ƙoƙarinsa.

A bayan mota muka zauna nida Hajiya kaka sai kuka take ina rarrashinta,a asibitin naga su Rashida har da jidda da Hajiya Ruƙayya,naje na gaisheta ko amsawa bata yiba,Jidda ta zubomin idanuwanta ƙuri tana kallona ganin cikina wanda ya fito sosai,itama hajiya Ruƙayyan sosai ta yi mamakin ganin hakan.


********

Captain Ahmad ya ce"a gaskiya Bilal bazan ɓoye maka ba,ka yi asarar mata irin khairat yarinya mai haƙuri da nutsuwa amman har ka yadda da wannan sharrin da aka yi mata?".wani banzan kallo Bilal ya yiwa captain sannan ya ce"ok kada ma in yadda kenan ko?in kamata da ƙwarto kace min wai ba haka bane?to meye ɗin?".

Captain ya yi murmushin takaici sannan ya ce"a'ah ni gaskiya ban yarda ba,kai meye shaidarka na yadda da hakan"?.ya faɗi hakan yana kallon Bilal.murmushin takaici Bilal ya yi sannan ya ce"eh to ai har masu gadi na tambaya suka shaidamin tunda na yi tafiya take yawo,kaga kuwa dole in yarda".ya faɗi hakan cikin gadara.

"Hmm lallai Admiral da sauranka,kai wato har yanzu baka san mutane ba?suyi maka micijin sari ka noƙe ba".?

Micijin sari ka noƙe sunan novel ɗina sa zan fara bayan na huta.


Ɗakko wayarsa ya yi cikin aljihunsa ya shiga wani vedio ya nunawa Bilal ya ce"wacece wannan?".da sauri Bilal ya ce"jidda ce".captain ya yi ɗan murmushin gefen baki sannan ya ce"wannsn vedio ɗin yafi guda biyar acikin wayata,vedion nan tun sanda ka yi tafiya na ke ɗaukarsa,abin ya juya ne kan khairat amman maganar gaskiya tunda ka yi tafiya na gano jidda na fita kullum daga gidanka,baza kuma ta dawo ba sai dare ya lula,kuma dana matsa da binciken inda take zuwa sai gashi na gano gidan maƙiyinmu Damass take zuwa".

Da sauri Bilal ya kalli captain yana jin kamar zai sume saboda tsoron abinda yaji daga wajen captain.. . . . .




MAGANCE KAUSHIN KAFARKI

Kaushin fata abu ne da ke addabar fatar mutum musamman a lokacin sanyi. Akwai abubuwan da ke sanya kaushin fata kamar yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai mayuka da dama wadanda ake sayar da su domin magance matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsalolin, fata sai ku karanta abubuwan da na lissafo muku. 

MATAKAI:

· 1)- A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a barshi na tsawon mintuna biyar zuwa goma kafin a shiga wanka a kullum.

2)- A kasance ana diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.

 3)- Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki sai a bari na tsawon mintuna goma sha biyar sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada us din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga cikin jiki.

•4)- A kasance ana amfani da man kwa-kwa a fatar jiki. A daura man kwa-kwa a wuta ya danyi dumi sannan a mulke fatar jiki kaf dashi na tsawon mintuna talatin kafin a shiga wanka a kwanta. A kasance yin hakan a kullum.

•5)- Shan madara kofi daya kafin a kwanta bacci a kullum yana taimakawa fata sosai.

•6)- A kasance ana shafa man kadanya a jiki bayan anyi wanka da daddare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gabadaya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.

 

7)- A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi.

8)- Lemun tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar dake da gautsi a jiki sannan yana sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matsa ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon mintuna uku sannan a wanke


9)- Ayi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a maka duka a jiki yawan amfani da ababe dayawa a fata yana haifar da kuraje a fata.



*By*
*dr mata ummu maher(miss green)*
*don neman ƙarin bayani*
07068606171

*MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨


Instagram links👇

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/


Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


MISS
GREEN CE
[23/09, 16:29] Miss Green🍀: *🏮ABIN CIKIN ƘWAI🏮*


littafi na 3


*by✍🏿*
Ummu maher(miss green)🍀


Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Sirrinki👂🏻🌈*

Ƴar uwa ki kasance mai yawan yiwa mijinki da ƴaƴanki addu'ah da al'ummar musulmi baki ɗaya,don ita addu'ah makamar mumuni ce.
------------------------------

73. . . . . .74


. . . ."Hajiya zuciyata ciwo take min agame da abinda Khairat ta yi min,hajiya sai yanzu na tabbatar da abinda ki ke faɗamin a game da khairat,hajiya ki yafe min don Allah."ya faɗi hakan yana fashe wa da kuka sosai.

Hajiya Ruƙayya ta ce"Bilal kenan tunda har ta yi agidan ubanta agidanka ne baza ta yi ba?ai shiyasa na faɗa maka wannan yarinyar ba macen aure ba ce,amman saboda kai yaro ne shiyasa wannan kakar taka ta cuce ka,insha Allah sai Allah ya saka maka."ta faɗi hakan tana share mishi hawayen fuskarsa.


******

a hankali na farka na buɗe idanuwa na waɗanda suka yimin girma sosai,na fashe da kuka tuno abinda ya faru da sauri Rashida ta matso inda na ke,ta rungumeni itama tana kukan Yaya Aliyu yana tsaye yana kallonmu shima yana goge hawayen fuskarsa,na kallesu su duka ahmad ma yana wajen commisioner of police na ce"nasan bakunanku cike suke da tambaya ta ba'asin abinda ya faru?amman ni da Kai na zan faƊa muku duk abinda ya faru".

Su Dukansu suka zubomin idanuwa suna kallona,na share hawayen fuska ta na basu labarin duk abinda ya faru,dukkansu salati suka saka yaya Aliyu ya ce"tabbas Bilal zaiyi nadamar wannan Abinda ya yi miki khairat,ki yi haƘuri Ƙaddararki kenan".kuka na fashe dashi na ce"wallahi yaya Aliyu ayanzu na tsani Bilal tsana mafi muni arayuwata,koda ma ace bai sake ni ba toni tabbas xan saki kaina kuma babu tantama jidda ce ta haƊamin wannan sharrin,na barta da Allah shine zai sakamin".sai na fashe da wani irin matsanancin kuka me cin rai.

Rashida ta rungumeni tana kuka ta xe"ki daina kuka khairat insha Allah sai Allah ya saka miki."Ta faƊi hakan tana kuka,ahmad ya kalleni sosai tausayina duk ya cika zuciyarsa ya ce"Khairat nima dai haƘurin zan baki saboda duk wanda ya sanki yasan halinki don haka inason ki share hawayenki,insha Allah nan ba da daɗewa ba gaskiya za tayi halinta,don shi ramin ƙarya ƙurarre ne,ita kuma ƙarya fure take bata ƴaƴa".

Sosai suka dinga ƙwantarmin da hankali har naji zuciyata ta ɗan samu salama,sai da aka yimin ɗori a hannuna don na samu gocewar ƙashi.ban san yaya aka yiba yanzu so ya koma ƙi nidai na tsinci kaina da mugun ƙin yaya Bilal,ni gani nake duk abinda aka ce masa na yi ai shi me yin bincike ne ba kawai ya hau kai ya xauna ba.don haka insha Allsh zan nuna masa khairat ɗin daya sani adacen baya to ayanxu ba ita bace.zanyi kuma duk yadda zanyi wajen gano duk wanda ya yimin wannsn sharrin.

Yaya Aliyu yana ɓaremin ayaba ya ce"khairat tun acen baya munyi kuskure sanda abin nan ya faru kafin ki yi aure,har na barki ki ka zauna agidana ba tare da kin zauna agidanmu ba,saboda tsoron wani abu da zai biyo baya,kinga sai aga kamar bamu da gaskiya ne amman yanzu insha Allah gidanmu zaki je,don gidan ubanki ne,duk wanda zai yi miki gori ya yi miki,nidai na baki goyon bayan duk wanda ya yi miki kada ki barshi kema ki rama kinji"?.

Ɗaga kaina na yi sannan na ce"gaskiya ne Yaya Aliyu awannan karon na saka tsoro araina da tunanin abinda mutane zasu iya faɗa akai na amman yanzu kome za suyi sai dai suyi amman agidan ubana zan zauna,babu kuma wani tsoron da zanyi tunda dai nasan abinda ake zargina akanshi sam ban aika tashi ba" .

Ahmad yana jinmu sai kuwa ya ce"khairat su mutane daman idan kace zakaji tsoron su to sunfi son hakan,gwara ka dage ka amshi ƴancinka wanda ka rasa awajensu.ki nuna musu cewa kefa yanzu an daina cutarki ki bari,za kiga kowa yana jin tsoron haɗa hanya da ke."

Sosai naji daɗin shawarar daya bani,Rashida ma ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce"haka ne khairat duk abinda suka gaya miki,amman gaskiya Yaya Bilal bai kyautawa kansa ba,amman ni nasan aƙwai ranar nadama".murmushi kawai na yi sai naji zuciyata duk ta wanke.

Na ce"insha Allah zanyi ta bincike har sai na gano duk wanda ya shiryamin wannan ƙulalliyar".murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce"khairat kenan ki barsu da Allag yafi ki rama da kanki don ramawar zai zamo kamar kin raina hukuncin Allah ne,abinda na keso da ke shine ki nutsu sosai ki dage da addu'ah babu dare babu rana,wallahi khairat na baki wasu ƴan ƙwanaki ƙalilan sai kin bani labarin abinda zai faru,don haka ki manta da wannan abin."

Murmushi na yi najin daɗin shawarar Ahmad na ce"babu komai insha Allah yaya Ahmad zanbi shawararka kuma zanyi duk yadda kace inyi".murmushi ya yi sannan ya ce"good girl yanzu na hangi Khairat ɗina".da sauri na kallesa jin abinda ya faɗa shi kuma sai naga ya yi murmushi tare da tashi tsaye ya sanya hannuwansa biyu cikin aljihunsa sannan ya ce"to ni zan tafi yanzu saboda ayyukan dana bari a office,Khairat Allah ya baki lafiya,ni zan tafi".

Murmushi na yi sannan na ce"na gode Yaya Ahmad Allah ubangiji yabar zumunci".ya amsa da amin suka yi sallama da Yaya Aliyu sannan ya tafi,har ya tafi kallonsa na ke sai naji Yaya Aliyu ya yi magana sannan na juyo.




******

da wata baƙuwar number aka kirasa ya ɗaga,kai tsaye yaji muryar Alhaji Damas yana ce wa"kai ƙaramin ɗan rainin hankali,ka sani koda ka ceci wannan yaran to baka isa ka ceci mahaifinka ba,wanda ayanzu yana kan hanyar dawowa gida,amman kuma ƙarshe bazai dawo gidan ba,sunyi sallana bye bye".ya faɗi maganar cikin salon dabanci.

Da ƙarfin gaske Bilal ya kira sunansa sannan ya ce"kai mutumin banza la'anannen Allah,har kana da wani iko wanda ya wuce ikon Allah ka sani na bawa Allah ajiyar mahaifina shine zai karemin shi,don haka don Allah idan kaso ka kasheshi ko yanxu,komai yana tafiya ne da ikon Allah ba da ikon wani chan ba.don haka ka yi duk abinda ka yi niyya".yana faɗar hakan ya kashe wayar hankalinsa a mugun tashe.

Jidda da ke kallonsa ta taso cikin salo nason mantar dashi komai ta matso kusa dashi sosai zata taɓa sa,da sauri ya ɗaga mata hannu alamar bai buƙatar hakan,ta mayar da wani malulun haushi daya turniƙe mata xuciyarta cikin fushi ta fara magana"ai daman tunda wannan tsinanniyar ta gama da kai dole ka dinga yimin duk wulaƙancin da kaga dama,babu komai insha Allah kaima za kaga ƙarshenka,don Allah baya barin azzalumi irinka"..

Da sauri Bilal ya miƙe ya ce"ke!jidda kada ki ƙara kirana da azzalumi idan kuma har ki ka kuskura ki ka ƙara kirana da wata kalma da bata yimin ba,to tabbas zanyi miki duk abinda bakya tunani".da sauri ta ce"to se me idan ka yimin?rashin mutunci ai ka gajeshi ne wajen wannan munafukar kakar taka". . .wani mugun mari ya wanka mata wanda har sai da taga hasken wucewar wasu taurari ta ɗauke wuta lokaci ɗaya saboda marin ba ƙaramin shigarta ya yi ba,ya ce"ki shiga hankalinki jidda kinga duk zagin da zaki yimin ki yishi a iya ni kaɗai amman ki ka sake kika saka wannan kakar tawa to tabbas zan miki abinda sai kinyi nadamar faɗar duk wata mummunar maganarki,domin ita dai wannan kakar tawa da ki ke ganinta,ina matuƙar ji da ita aciki n rayuwata,yadda na kejo da iyaye na to ita fiye da hakan na ɗauke ta,don haka matuƙar ki ka ƙara zaginta to wallahi abakin aurenki".


Sosai abin ya bawa jidda mamaki kamar wani wanda aka yiwa asiri ta kasa gane kansa ko kaɗan,tabbas ashe da sauran rina a kaba,ya zama dole shima ta yi maganinsa kamar yadda ta yi maganin matarsa,ta yadda sai yadda ta yi dashi ya zama mijin tace hatta ita kakar tashi ma sai ya manta da ita.


Tuni ya fice ya figi motarsa da mugun gudu,masu gadin sai mamakin ogansu suke don sunga gudun ya yi yawa,tun a mota ya kira Captain ringing ɗaya ya ɗauka,ko gaisuwar Bilal bai bari sunyi ba,ya faɗa masa duk abinda Damas yace masa yanzu awaya.Captaim ya ce insha Allah yanzu zanyi shiri in taho,insha Allah ƙarshen Damas yazo.

Kai tsaye gidan Damas ɗin ya wuce,hatta gate ɗin wanda ya ke buɗe alamar yana nuna yanzu aka shigo ba'a kai ga rufesa ba,tuni Bilal ya ɓurma gidan da matsanancin kudu,masu gadin suka taho da sauri zasu rufe gate ɗin amman tuni Bilal ya shige ciki,Damas yana zaune a babbar fadarsa ya ɗaga kai ganin Bilal ya shigo da motarsa har Kusa da babban falonsa.

Ya yi wata muguwar dariya irinta basawa,ya kalli Mahaifin Bilal ya ce"oh Allah sarki Alhaji ka godewa Allah ɗanka yana sonka sosai,tunda gashi har yaxo don kaucewa muguntata."Alhaji Abdullahi ya yi dariya sannan ya ce"haba bawan Allah ai duk ɗan halak ba ɗan shege ba yana don iyayensa,don haka kada ka yi mamaki don ka gansa,abinda yafi haka ma zai iyayi indai har akai na ne". . .ko kafin ya gama maganar har Bilal ya diro Falon.

Alhaji Damas ya saka wata mahaukaciyar dariya ya ce"hhhhh Bilal kenan ta yaro kyau take bata ƙarko,don haka yanzu zan nuna maka isa ta akan mahaifinka,tuni ya yi wani fito sai ga wani mutum ya fito daga bayan mahaifin Bilal ya caka masa wuƙa.da wani irin mugun gudu Bilal ya taho Wasu majiya ƙarfi suka rirriƙe Bilal.

Bilal ya ce"don Allah kada ku kashemin mahaifina wallahi ba shifa laifi akan komai".dariya sosai Alhaji Damas ya yi,dai dai lokacin kuma Captain ya bayyana da wasu ma'aikatsn suji sunfi mutum hamsin.wata irin sufa Bilal ya yi,ya hanɓare wannan wuƙar ta hannun wannan mutumin,tuni Alhaji Abdullahi ya faɗo kan ɗan nasa Bilal ya tare mahaifinsa yana kuka,don a ƙa ida idan abu ya faru da mutum irin haka to kada a yadda ta faɗi ƙasa ataresa da sauri,yin hakan zai sauƙaƙa masa komai.

Captain yana shigowa ya saki uwar wuta shida sojojin da suka shigo ko ta ina sun saki wuta,ana ta ɗauki babu daɗi tsakanin Su captain da kuma yaran Alhaji Damas,Yana ganin haka tuni ya danna layar ɓatansa ya ɓace batt awajen,Captain ya daki iskar wajen yana jin haushin rashin kama Damas.

Kai tsaye Bilal asibiti ya yi da mahaifinsa yana kuka sosai,jini sai malala ya ke ajikin Alhaji Abdullahi,Bilal ya kasa gayawa kowa abinda ya faru gudun kada hankalinsu ya tashi,Bilal ya nuna takaddar shaidar aikinsa..da sauri suka amshi mahaifin Bilal saboda sanin waye Bilal ɗin,aka fara taimakon gaggawa.

Ya samu waje ya zauna cikin ɗaya daga cikin kujerun da aka ajje awajen don zama,ya riƙe kansa wanda ya ke shirin tsage masa gida biyu,saboda masifar da ya ke ciki,ga sakin da ya yiwa Khairat har yanzu yana jin abin aransa. ga kuma kamata da ya yi da ƙwarto,bayan haka kuma ga abinda ya faru da mahaifinsa.



********

kai tsaye sashen Hajiya kaka muka yi nida Yaya Aliyu,da kayana wanda Rashida ta ɗebomin agidan Bilal wanda akan wannan kayan sai da akaso faɗa da Jidda wai Rashida baza ta shiga ba,ai kuwa ta bangaje ta,ta shige ta ɗebo kayan.

Muna zuwa Hajiya kaka ta miƙe tana ce wa"a'ah Abin cikin ƙwai lafiya nags hannunki harda bandeji"?.Yaya Aliyu ya ce"ba tada lafiya ne kaka".muka samu waje muka zauna da ƙer na zauna saboda hannun nawa,gashi ƙasan mara ta yanzu wanda ya yimin kamar dutse kuma ina jin wajen

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login