Showing 102001 words to 103202 words out of 103202 words
Ta baya na shigo don haka banji shigowarsa ba sai kawai naji ya rungumeni ya ya yi sama dani ya ajjeni akan gado,ya koma farlo ya kunna musu catoon ya kukkule ko ina na gidan,sai masu gadi sojoji har guda biyar sannan ya dawo ɗakin.
Na rufe hannaye na da tafukan hannuna kunya duk ta kamani daga ni sai tawul,murmushi ya yi ya faɗa wanka banɗaki sannan ya fito yana goge ƙwantaccen gashinsa,wanda yanzu ya ƙara kyau da tsantsi.
Ya saka jallabiyarsa sannan ya kalleni ya ce"mamynmu taso muyi sallah mu godewa Allah"murmushi kawai na yi don da haka ya ke kira na,wato mamynmu yadda yara na ke kirana.
Cikin jin kunyarsa na tashi na shiga ban ɗaki na saka rigar bacci me kyau sosai,ruwan pink wacce ta amshi fatata don ayanzu zama a iya kirana da fara,saboda yadda fatar tawa ta ƙara samun cigaba yadda take shan gyara sosai.
Bayan mun idar da sallah mukayi addu'o'i muka shafa ya ɗakko fresh milk da wata banƙararriyar kaza wacce girmanta ma kaɗai da maiƙonta zaisa kaci.sosai naci nasha madarar itama shima yasha daman yanzu na ya little khairat don da kanta ta ya ye kanta,sabawar da aka yi mata da madara,kuma yanzu kununta take sha mai matuƙar ƙarawa yaro lafiya.
Baki ɗaya ya ɗaukeni yana yawo dani kamar a indian film.Hmm ranar fa an yi ƙwanan farin ciki da ƙaunar juna tsakanin khairat da yayan nata Bilal uban ƴaƴanta.
Bayan wasu watanni,ayanzu yaya Bilal ya yi nasarar kama Alhaji Damas biyo bayan tonuwar asirinsa na ayuukan da ya ke yi,sannan su kansu manyan ƙasa sunyi amunna da hakan don suma abin ya shafi yaransu don Alhaji Damas ya ɓata musu yara da basu hodar iblis,ƙarshe har ta yi sanadin kashe ɗan gidan wani babban commisioner,ai kuwa ana kaishi kotu aka yanke masa zaman gidan yari na har abadan.sai dai ya mutu acen biyo bayan laifukan da ya yi wanda ba zai yiwu ya fito ba.
Har yaransa duk an kamasu,har da waɗanda aka kamasu sun kashe wan babban ɗan siyasa kuma shi Damas ɗin ne ya aikasu,ai kuwa ganin hakan ƴan duk yawancin ƴan siyasa suka saka hannu akan kama Damas ɗin saboda ɗauki ɗai ɗai ɗin daya fara yi musu.
Ɗan damas kuwa tuni Aka harbesa a karan battar dasu Bilal suka kai gidzn Daamas ɗin sai dai muce Allah yajiƙan,duk wanda ya mutu.iyayen jidda kuwa har yanzu Bilal bai fasa taimaka musu ba,don ko ba su ba daman shi mutun ne mai tausayi sosai.
*********
bayan shekara goma.
Wata hamshaƙiyar mata na hango tana zaune a babban farlonta,ɗauke da ƙaton cikinta haihuwa ko yau ko gobe.dana duba sai na hango muku ashe khairat ɗin hajiya kaka ce.ta ƙara kyau da cika.
Wani saurayi ne ya shigo wanda bazai wuce shekara sha shida ba,Kyakkyawan gaske me kama da Bilal,ashe irfan ne sai yanzu aka gane ashe duk yafi kama da mahaifinsa,ya zauna kusa da mamansa ya kalli ƙafarta ganin yadda ta kumbura cikin tsananin tausayinta ya tsugunna yana danna mata ƙafar.musmushi khairat ta yi ta shafa kansa ta ce"Allah ya yi muku albarka baki ɗayanku son."da amin ya amsa mata don shi miskilin gaske ne har yafi babansa ma.
Da gudu wata yarinya ta taho me kama da khairat sak,kuma itama ba fara bace kamar su irfan.sai ga Haidar nan ya fito,ya zama ƙato ɗan lukuti shi daman ɗan lukutine,ba kamar su irfan ba.
Ya fara magana cikin haushi ya ce"wallahi da kin tsaya da na zane ki mara kunya,ni sa'anki ne"?.da sauri na kallesa na tambayi ba'asi nan ya ke faɗamin wai wayarsa ya saka chaji shine ta zuba masa ruwa akai.
Haƙuri na basa,sai ga wata kyakkyawar budurwa itama ta shigo iman kenan wacce har ta fara cika budurwa.sanye take cikin kayan islamiyya ta ƙarasa wajen mahaifiyarta ta ce"Mamynmu na tafi islamiyya".murmushi na yi sannan na ce"to iman kada ki manta ki biya ta wajen Anty halisa ki amsomin saƙon nan".murmushi ta yi sannan ta wuce.
Ayanxu ƴaƴan khairat 8 ne ga cikin na 9.bayan ƴan huɗu sai Little khairat wacce yanzu ke masar ta koma wajen mahaifinta tun tuni,don tun tana shekara biyar ya ɗauketa.da ƙer aka samu shahid ya yi aure ya auri wata balarabiya mace me kirki kuwa don tare suke zuwarmin da little khairat.amman har yanzu Allah bai basu haihuwa ba.shiyasa ya ke masifar son little khairat.
Bayan little khairat ta haifi twins,Maryam da Hafiz amman ana kiransu Maher da Amira.sai kuma ƙaramarsu me kama da khairat sak itace sarkin ɓarna.
Sai na tara yanzu zata haifa,babban ɗan gidan captain Khalil wato ibrahim wanda yanzu ya ke da shekara ishirin da huɗu shine ke son iman,don ya dage sosai shi khairat ya keso,kuma alhmdh yarone me hankali yana da nutsuwa kuma yana da aikin yi.don yanzu har mahaifinsa ya samo masa aiki a babban asibiti lilitan mata wato ghanychology.
Ina zaune naji jiniyar mota ta tsaya,irfan da ke min tausa ya riƙe hannuna muka tashi,Arman na hango da mahaifinsa.wanda mahaifin nasa yaje ya ɗakkosa a makarantar sojoji da ke kaduna. Shi daman tun tasowarsa ya keson aikin mahaifinsa wato soja.
Da sauri yazo ya zo ya rungomeni yana murnar ganina.ina ta murnar ganin ɗana,Yaya Bilal wanda yaci wankan shadda kamar wanda be fara manyanta ba.don haryanzu shekararsa arba'in da baƙwai.don haka har yanzu kamar saurayi na ke ganin abina,don gaskiya jikin yaya Bilal me kyau ne,kullum sai inga kamar ana ƙara masa kyau.
Haɗamu ya yi dukkanmu ya rungumemu,mu duka iman ce kawai bata nan tana skull cikin farin ciki na kalli iyalina ina jin wani irin mugun daɗi har cikin rai na.
Adaren ranar na haihu ɗa namiji me kama da yaya Bilal,bayan anyi suna ina zaune ina shafa mai ya shigo,ya ajjemin wata takadda kan cinyata.na kallesa cikin tsoro.amman na daure na buɗe.da sauri na tashi na rungumesa.ya biyamina hajji harda umra nida yarana baki ɗaya.daman kuma su Mamana da baba Abdullahi suma zasuje.
Na rungumesa na ce"Allah na gode maka daka bani miji nagari abin son kowacce mace.na gode mijina Allah ya albarkaci dukiyarka.ya albarkaci yaranmu dana al'ummar musulmi baki ɗaya."
Bai bari na ƙarasa ba ya yi kan faffaɗan gadonmu me kyau.muna dariya cikin nishaɗi.
*Alhamdulillahi*
Hmmmm laifin daɗi ƙarewa anan na kawo ƙarshen wannan littafi nawa,me suna ABIN CIKIN ƘWAI.gaskiya ni kai na dana rubuta littafin naji daƊinsa sosai,saboda wasu darussa dani kai na dana Ƙaru,don labarin na gaske.
Fatana Allah ubangiji yasa mu amfana da abinda ke cikinsa,abinda na rubuta dai dai Allah ya bamu ladan baki Ɗaya,akasin haka kuma Allah ya yafe mana baki Ɗaya.
HaƘiƘa babu abinda zan ce wa ubangiji sai godiya,saboda yadda kuka nunamin soyayya da Ƙauna Allah yabar zmnci amin.
dafatan zaku biyoni asabon littafi na,wanda har sai yafi abin cikin Ƙwai haƊuwa,don shi labarin ba na mutum Ɗaya bane,labarin xai zamo kamar drama don zai zamo akan mutum uku ne,waƊanda suka sha gwagwarmayar rayuwa.
SUNAN LITTAFIN👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*MICIJIN SARI KA NOƘE*
DUK WANDA YASAN KARIN MAGANA YASAN ABINDA LITTAFIN YA KE MAGANA AKAI.KU DAI KU BIYONI DON JIN YADDA ZATA KAYA.
*KU KASANCE DA GAWURTATTU BIYAR INSHA ALLAH SUN SHIRYA TSAF DON DAWO MUKU DA SABBIN LITTAFINSU,AMMAN SAI MUN HUTA NAN DA ƊAN WANI LOKACI.
*TAKU HAR KULLUM*
*ummu maher(miss green)*
don Allah duk wanda ya karanta littafin nan yaji daɗinsa,ya yimin addu'ah akan Allah yacikamin burina.
Ilove u too all.