Showing 60001 words to 63000 words out of 103202 words
biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:23] Miss Green🍀: *55.. . .56*
. . .har na wuce sai naji muryarsa"ke zo nan"!.ya faƊi hakan cikin haƊe girar sama da ta Ƙasa,wai don kada nace na gansa,haƊe rai na yi sosai kamar ban taƁa dariya ba,na juya shining eyes Ɗina sosai irin yadda Ƴan duniya ke yi,na kallesa irin yadda ya kalleni kallon Ƙasa sannan na yi wuce wata sashe na ba tare da ko waiwayensa na sake yi ba.
sosai abin ya bashi haushi ya wuce fuu kamar kububuwa,ina hangosa ta saman bene,na tun tsire da dariya ina tunanin hali irin na yaya Bilal na wuce ina ce wa hmm zaka shigo hannu sai na gara ka kamar ball,na Ɗauki wayata muka fara chart da anty halisa,dariya sosai ta yi ta ce"kai haba ashe ma mijin na ki bai da wuyar sha'ani?ai so nake sai ya garu sosai sannan mu gana masa azabar da sai yayi kuka saboda haukan sonki".
"hmm anty ni gani nake kamar ba zai soni ba?Saboda yaya Bilal ya tsaneni sosai".na faƊi hakan cikin damuwa,sai kuwa anty halisa ta yi tsaki ta ce"Hmm gaskiya khairat raguwar zuciyarki ta yi yawa,yo idan banda raguwar zuciya ta yaya zakice bazai soki ba?ke fa macece ba namiji ba?kuma kina da qualities Ɗin daya kamata namiji ya soki,to saboda me kuma zaki ce haka?idan har kina son muyi shiri to dole ne sai kin zama mace jaruma ba raguwa ba,don haka ki tashi ki zama gawurtacciyar mace agidanta,ki karƁo mutuncinki da kuma martabarki waƊanda ki kayi watsi dasu,don haka inw me jan kunnenki akan ki kula sosai,kada ki bada kai da wuri ki wana sa yadda ya kamata".
cikin dakiyar zuciya na ce"insha'Allah anty zan zama jajirtacciya kamar yadda ki keso kuma bazan taƁa baki kunya ba".sosai anty halisa ta yi farin ciki muka cigaba da hirarmu.
*****
sosai abinda khairat ta yi masa ya tsaya masa,khairat Ɗin daya sani Ƴar Ƙauye?me nuna masa tsantsar so?yau kuma kallon wani hadarin kaji yaga tana yi mai,kamar an zabure sa haka ya tashi wato allurar soja ta miƘe,indai kuwa baiyi maganin khairat ba yau bai cika soja ba.
ina gama chart Ɗin na kashe wayata baki Ɗaya na tashi na cire after dress Ɗin jikina wacce itama tabi lafiyayyiyar baƘar fatata,na fito farlo na wuce kitchen na Ɗakko indomie Ɗin dana dafa,kawai sai ganin mutum na yi a gabana,wani mugun buguwar zuciya naji,amman kuma sai na daure gudun kada in bada kai na,sai na yi mai kallon Ƙasa yadda na yi masa Ɗazu.
"khairat ni ki kewa wannan kallon ko?".
Na tsinkayo muryarsa Ƙara yimai kallon na yi ya matso inda na ke sosai yana neman taƁa ni,da sauri naja baya kamar naga abin Ƙenkyami na waro ido waje na ce"dont touch me,Kada ka yadda ka taƁani wallahi,ni ba,muharamar ka bace".na faƊi hakan ina turo bakin shawaƁa ta,wanda ya ke yimin mugun kyau Ɗan baki na kamar cunkun fure.
"Khairat ni ki ke cewa ba muharraminki ba?ni ba mijinki bane?".da sauri na zaro ido na ce"Allah ya tsare ni wallahi ni bani da wani aure zaman kai na nake,kuma idan ka Ƙara shigomin sashe wallahi ihun Ɓarawo zan maka.
waro manyan idanuwansa ya yi yana ganin kamar ba khairat ba,khairat me shiru shiru yarinyar da babu ruwanta?to ko dai ba ita bace wani aljanin ne ya shiga jikinta?ga wani mugun turare wanda duk ya tada masa da feeling Ɗinsa,musamman ma akan khairat Ɗin,daman haka take da kayan ado da alatu?sam bai taƁa tunanin hakan daga gare ta ba,don ko agida ma bata fiya fitowa ba tare da hijab ba.
Ganin yaƘi fita ne yasa na ce"mlm don Allah mlm fitarmin a sashe ni na gaji da wannan tsayuwar da ka yi min aka kamar wani sunduƘi".
sosai abin ya bawa Bilal mamaki,sam bai jurar rashin kunya don haka yanxu zai yi maganinta.ban yi tsammani ba kawai sai naji ya janyo ni ya matse min baki na sosai naji zafi na gallara mai cizo,amman ko gezau bai yi ba,na Ƙara gallara mai wani cizon.abinda ban sani ba shine hankalinsa sam baya kan cizon dana yi masa,rigar dana saka irin mai wajen wuya Ɗin nance da sauri na tashi na ture sa gefe,cikin fushi na ce"haba bawan Allah me ye kuma zaka zo kana kallo na".na faƊi hakan cikin shagwaƁa,anan take ya tuno da abinda ya aika ta,da sauri ya fita waje yana gyara zaman bottle Ɗin rigarsa wanda duk a buƊe ya ke.
Yana fita baki Ɗaya na zauna akan babbar kujera wato tree seater,na lumshe idanuwa na fuskar yaya Bilal na yimin gizo sosai,wani irin farin ciki naji azuciyata na danne saitin zuciyata ina jin bugawarta sosai,har hawayen farin ciki sai da na yi saboda tsananin murna da wankewar zuciya,wai yau ne nice ga ni ga yaya Bilal?mutumin da ko inuwa ta bai son gani.kullum sai hantara da kuma zagi?amman yau har shine ya ke kallona kallon cikin ido.
anya ma kuwa xanyi wannan jan ajin da anty halisa ta ce inyi?Kai gaskiya bazan iya ba.mutumin da na ke matuƙar so arayuwata na samesa ai bazan bari inyi wani jan aji ba.garin jan ajin ya tsinke.
Da Sauri na ɗakko wayata na kira anty halisa,cikin zumuɗi tana ɗagawa ta fara tsokana ta da "khairat ta Bilal bada kanki asare kije gida kice ya faɗi."sosai naji wani irin nisha ɗi ya cika zuciyata na ce"hmm anty albishirinki?".
Da sauri ta ce"goro".na ce "fari ko ja"?.da sauri ta ce"fari".duk abinda ya faru sai dana gaya mata,sosai ta taya ni murna sannan ta ce"hmm wa yaga ya masa barni gabas take.ai wallahi wasan ma yanzu aka soma,wannan turaren da ki ke ganinsa ko asiri idan aka yi wa mutum to tabbas alokacin ya ke warware wa,don haka ki kula da saka sa sosai duk wani gurbi na jikinki kibi turaren dashi.kici gaba kuma da addu'ah insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe".godiya na yi mata sosai sannan na kashe wayar na rungume filo a ƙirjina ina tuna ranar da zan ganni gani ga yaya Bilal muna zaman aure na haƙiƙa,yana sona ina sonshi.
***
"Wai ni honey lafiya ƙlau kuwa ka ke? Tun ɗazu naga sai tunani ka ke?wallahi duk ka sanya ni cikin damuwa?".jidda ke faɗan hakan tana shigewa jikinsa.duk abinda take bai ma san tana yi ba.kaf tunaninsa ya tafi ga khairat,sau tari yarinyar yana saka ta acikin munana,amman tabbas yarinyar kyakkyawa ce sosai sai yau ya yadda da hakan.
Ganin tana kiɗanta tana rawar tane yasa jidda ta ce"oh wai ni Bilal wani salon wulaƙancin ka koyo ne?da ina ta yi maka abinda zai sakaka farin ciki amman kai hankalinka yana wani wajen cen daban".?
"Jidda!".da ƙarfi Bilal ya faɗi sunanta sannan ya ce"ki shiga hankalinki sam ni ba lusarin namiji bane,wanda mace za ta yi ta faɗa masa magana yadda take so ya kyale taba,ki shiga tai tayinki".ya faɗi hakan yana nuna ta da yatsa,tasan halin Bilal ƙwarai da gaske,idan zuciyarsa ta hau yana iya aika tawa mutum ba dai dai ba,ta zauna kan kujera tana rufe bakinta da ƙarfi ta firfirto da idanuwanta waje,ba komai yasa ta yin hakan ba,bai wuce yadda Bilal ya yi mata ba,a iya saninta Bilal bai taɓa koda yi mata kallon banza ba,ko da ma ace ita ce da laifi to shine ke bata haƙuri.
****
"Wai Aliyu me yasa kullum ka ke yimin wulaƙanci duk akan matarka Maryam?idan ka gaji dani ne ka sake ni mana?amman irin wannan cin fuska da me ya yi kama?".khadija ce ke faɗin hakan tana kuka.
Ya kalle ta sosai cikin nutsuwa ya fara mata magana"khadija ban tsane ki ba?ina sonki sosai kamar yadda na keson Maryam,harma fiye da ita saboda ke ƴar uwa ta ce,duk da babu hadisin daya zo akan idan kana da ƴar uwa ka aure ta,kafi sonta akan waccen saboda ita wannan ƴar uwarka ce,amman ki sani Khadija an halacci zuciya abisa son wanda ya ke kyautata mata,sannan kuma tana ƙin duk wanda ya ke munana mata,to kinga abinda ya ke tsakaninki da Maryam kenan".
"Ai daman nasan haka zaka ce ita tafi kyautata maka,ni dana ke gutsirar naman jikinka ina nama dashi ai sai ka yi ta zagina,tunda wannan matar taka ta shanye min miji".ta faɗi hakan tana kuka.
Aliyu mutum ne mai sanyin hali sosai,matuƙar mace tasan kan na miji da gudu zata iya dashi,don sam bai da zafi sosai sai dai idan ka ƙure shi,Salim ne ɗan zafin kai irinsu Bilal.
A hankali ya ƙaraso har gabanta,wani wari ya bugesa kamar ya toshe hanci,amman sanin hakan zai ƙara janyo wani hargitsin sai ya share,ya tsugunna agabanta ya kamo hannuwanta duka biyu ya manna musu wani irin hot kiss,tuni jikin Khadija ya yi mugun sanyi don yadda ya yi mata kiss ɗin.
Ya kalle ta sosai ya kashe mata ido ɗaya,ai tuni khadija ta sallama masa,ya yi murmushin cin nasara sannan ya ce"ummu khairat ina alfahari dake sosai,inason ki yi min wasu alƙawarurruka har guda biyar?".
Da sauri ta ce"insha Allah zan riƙe maka alƙawari mijina,Abban Khairat".ta faɗi hakan ita ma tana kashe masa ido ɗaya.
Yauwa alƙawari na farko shine,kada ki dinga saka damuwar Maryam akanki har ta yi miki illa don kin san halin da ki ke ciki yanzu,ɗan cikinki yana buƙatar kulawarki sosai don haka don Allah ki daina damuwa.sannan abu na biyu ina son ki kasance mai tsafta da kula da kanki da ƴarki khairat,abu na uku ina son ki dinga tausasa zancenki wajen yi min magana,sannan abu na huɗu ki dinga yimin girki kullum a ƙalla sau biyu matuƙar ina sashenki,sannan abu na biyar ina son ki dinga riƙe min sirrina,tare da yimin ƙwalliya da kula dani".
Ya faɗi hakan yana yi mata mugun smile ɗinsa mai tafiya da ita,ta hango asalin kama da mahaifinta akan fuskar Aliyunta,ta magantu ta ce"insha Allah mijina daga yau zaka same ni a mai kula da kai,ta yadda zaka yi alfahari da ni."
Sosai Aliyu yaji farin ciki ya mamayesa,ya rungume ta sosai,da kansa ranar ya yi mata wanka fes suka haɗu suka yi aikin ɓangarenta dashi,zuciyarta fal farin ciki.
Maryam ma da ta gama aikinta nan ɗin tazo,sai dai khadija taƘi bada fuskar yin hakan,kuma ranar Aliyu a ɓangaren maryam ɗin ya ke,sai bayan magrib sannan ya shigo,Maryam ta amshe sa kamar wani abu ma bai faru ba,ya kalle ta sosai ganin kawai dauriya take,ammsn sauran kaɗan ta fashe da kuka.
Da ya ke yasan kan abinsa tuni ya bi da ita yadda ya keso.kafin wani ɗan lokaci ta saki jikinta sosai suka faɗa hirarsu gwanin sha'awa.
*****
To fa tun daga wannan ranar ne na buɗe shafi salo salo,sai na lura yana guest ɗinsa yana shan iska zanzo in wuce wata,ina shawagi na ko kallonsa banyi,sai in fake da motsa jiki,ai kuwa sosai ya ke shagala da wannan ɗin,amman girman kai ya saka shi wani jan aji.
Yauma kamar kullum na fito daga ni sai tree quater ɗin wando baƙi,wanda yabi jikina irin me bin jiki ɗin nan,sannsn na saka wata riga t shart wanda ta ɗameni sosai na ɗakko ruwan gora mai ɗan sanyi,na ƙulle gashin kaina ma'ana na saka ribom ai kuwa ba ƙaramin kyau hakan ya ƙaramin ba,da ya ka irin gashina mai taushi ne wanda ake kiransa roba roba,kuma sai ya yi kamar na yi doughnut ɗinsa ya yi cukus,kamar black american,na saka konbus ɗina mai kyau,irin na mata na fito abina ina ɗan gudu kaɗan,ai baki ɗaya ya shagala da kallona ina kallonsa,na cigaba da bubbuɗawa kamar yadda na saba yi masa.
Sai ga jidda nan ta fito,ganin abinda ke faruwa yasa ta kusa daskarewa awajen,ta kalleni taga harkar gabana na ke,ta kalli mijinta taga shi kuma aikin kallo na ya ke.
Kawai ganinta na yi agabana tana wani muzurai cikin fushi ta ce"dalla malama koma ɓangarenki zaki fito kina wani muskutawa,kina neman ki haukata mutum".
Dariya sosai na yi kamar na mayar da ita mahaukaciya sannan na ce"oh ikon Allah jidda ki ke kowa?don Allah ki matsa daga kusa dani banda lokacinki,saboda ni dai ina da abinyi,kuma don Allah kiɗan matsa don wallahi wari ki ke kamar mushe?". . .✍🏿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:24] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*
📃LITTAFI NA 2
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
*Matso kiji*👂🏻
Kada ki kasance mai yawan yiwa mijinki musu wallahi yin hakan yana dakushe ki a wajen mijinki don haka a kiyaye,ba da faƊa ko fushi miji ya ke saka ya soki ba,A'ah da rarrashi da kissa ake mallake miji.
-------------------------
59. . . . .60
. . .bai ajje ni a ko'ina ba sai kan kyakkyawan gadonsa,da sauri na tashi cikin tsiwa na ce"haba mlm saboda me zaka wani ɗauke ni kamar ƴar tsana?don Allah ni ka daina shiga harka ta".
Murmushi ya yi irin na gefen baki sannan ya ce"a'ah nifa ban shiga harkarki ba,kece ki ke shiga harka ta ni yanzu ma fitar min a ɗaki na".wani kallo na aika masa sannan na yi hanyar waje na saka hannuna da niyyar buɗe ɗakin,amman naji kamar an rufe ƙofar,ƙarar mukulli naji alamar mukullin yana hannunsa,na juyo na harɗe hannuwa na a ƙirji,ina yi masa kallon ba kada wayo.
Don nima in nuna masa na iya rainin hankalin sai nazo na zauna abakin gado,na harɗe ƙafafuwana waje ɗaya,shima yadda na yi hakan ya yi sannan ya ce"khairat"!.cikin voice ɗinsa mai daɗi.
A hankali na juyo na kallesa sannan ya ce"haƙiƙa kafin a sami mace kamarki za'a daɗe ba'a sami mace irinki ba,Khairat na kasance mai cutarki da kuma shiga haƙƙinki,amman baki taɓa buɗe baki kin cemin kina son haƙƙinki ba,don Allah ina neman yafiyarki,idan har ban nemi yafiyarki bazan taɓa gamawa lafiya ba don Allah ki yafemin".
Kallonsa na yi sosai ina mai mamakin maganarsa na ce"Yaya Bilal nifa baka yimin komai ba,ban kuma ce ka yimin ba,Allah ya yafe mana baki ɗaya,yanzu dai buɗemin ƙofa in fita saboda bacci na keji".
Na faɗi hakan cikun shagwaɓa wacce ta zamomin ji,matsowa ya yi har inda na ke ya tsugunna agabana,ya ɗago haɓata sosai ya kalleni cikin ido sannan ya ce"Khairar nasan abinda na yi miki da zafi da kuma ciwo,amman don Allah ki yafemin,na rasa me ya shiga ƙwaƙwalwata alokaci ɗaya naji na tsaneki,alhalin baki yimin komai ba,khairat ni na nuna miki sona tun kina ƙarama kuma na tafi na barki dashi,shiyasa har ki ka girma da sona. . ."
Da sauri na ce"wa ni?a'ah nifa bance inasonka ba,idan ma ka taɓa jin hakan to ƙarya ne,amman ni bance inasonka ba,don Allah ka barni in tafi".na faɗi hakan ina tashi tsaye.
Ji na yi kawai ya sureni baki ɗaya,ya ƙara ajjeni akan gadon,muzurai sosai na fara yi don na riga dana saka acikun zuciyata bazan sakko kamar yadda ya ke soba,ya shige banɗaki abinsa sai gashi ya fito daga shi sai tawul,ya kalleni sosai na kauda kaina gefe,don baki ɗaya naji zuciyata ta ƙarye akan Yaya Bilal,sam bazan iya wani fushi dashi ba,amman dana tuno nema wa kaina ƴanci na ke sai na share sa.
Ban san lokacin da na ya ƙaraso inda na ke ba ya ce"maza ki tashi kije ki yi alwala kizo muyi Sallar nafila,mugodewa Allah daya nuna mana wannan ranar,khairat ɗin Yaya Bilal ta auri Bilal ɗinta".
Harararsa na yi sannan na ce"wacce rana kuma ka ke magana akanta?ai ni tuni na manta da wata ranar aure,wata na ɗai ɗai har biyu agidan nan amman kace wai intashi inyi alwala?Yaya Bilal yanzu duk kamanta cutar da ka yi min?ka auro ni amman ka mayar dani kamar me aikin gidanka,sai da ka gama cin amarci da amaryarka sannan yanzu kace wai zaka dawo guna?wallahi bazai yiwu ba,bazan yarda ka rainamin wayo har haka ba,ka koma cen wajen matarka wacce ka keso bani khairat wacce ka tsana ba,don haka don Allah ga hanya ka fitarmin a sashe na".na faɗi hakan cikin dauriya kuma fa da zai fita ɗin da bansan halin da zan tsinci kaina ba,dauriya ce kawai.
Murmushin nan nasa ya yimin mai tsayawa azuciya sannan ya ƙaraso inda na ke,ya ce"khairat bazan gaji da roƙarki yafiya ba,ki yafemin don Allah ban san nima me yasa na yi miki hakan ba,amman wallahi tallahi da zaki huda zuciyata ayanzu da babu abinda xaki gani sai son khairat,fal acikinsa,Khairat ki fahimce ni,ni nasan kina sona kamar yadda na ke sonki".
"Hmm a taka fahimtar ko?har ka ke ganin ce wa inasonka ne?to ayanzu ban sonka,khairar ɗin da ka sani ada cen baya to ayanzu ni ba ita bace,don haka ku fita daga idanuwa na kai da matarka,kuma ka gaya mata ta fita daga harka ta".
Sosai naji ya janyo ni har muna jin numfashin juna,ya kalleni sosai sannan ya ce"ƙarya ki ke khairat ina ganin sona acikin waɗannan idanuwanki na ki,sona bazai taɓa gogewa acikin zuciyarki ba khairat,tun baki san menene so ba na koyar da ke,don haka ke ƴar makarantata ce".
Shagala sosai na yi da kallon fuskarsa abinda ban taɓa samin damar yi a arayuwata ba,sosai ya dinga yimin wani abu wanda na ke neman shagala,ai da sauri na yi gefe ina mayar da numfashi,don har yanzu ina nan