Showing 51001 words to 54000 words out of 103202 words
ya faƊi hakan yana kallon jidda wacce ta yo tsuru kamar munafuka,tana kallon yadda Bilal duk yana yinsa ya canja jijiyoyin kansa sunsha ta ruƊu-ruƊu.
tana kakkarwar jiki dana baki ta ce"Bilal ka yi haƘuri haƘiƘa banyi maka adalci ba,dana Ɓoye maka komai na rayuwata,amman yau zan gaya maka gaskiyar lamari."
Kasa cewa komai Bilal ya yi zuciyarsa na masa wani irin turiri,ta cigaba"Bilal wata rana baba na ya aikeni shago,naje na yo siyayyata na fito,wasu mutane waƊanda bansan su waye ba,suka Ɗauremin Idanuwa na suka sakani a mota sukayi gaba dani,tun daga ranar Bilal na rasa martaba ta na Ƴa mace,na rasa mutuntaka ta baki Ɗaya,Bilal bayan wannan lokacin nasha wuya sosai don har sai dana Ƙwanta agadon asibiti,an Ɗaukama ko ina da wata cuta ne,ashe babu komai wahalar da nasha awajensu ne."ta faƊi hakan tana shessheƘar kuka.
sosai ta bawa Bilal tausayi,sai dai awani sashe na zuciyarsa sai ya kasa gasgata hakan,gani ya ke kamar ba haka bane?wani sashen na zuciyarsa kuma ya ke tunatae dashi ga barin zargi tsakaninsu don muddin zargi ya shiga to babu aure.
samun kansa ya yi da rungume ta yana Ɗan bubbuga bayanta,har ta yi shiru,sannan ya Ɗaga Ƴar Ƙaramar haɓarta ya ce"jidda ke matata ce,ki daina saka komai aranki game da hakan,insha Allah na yi miki alƘawarin zama da ke da amana,kuma babu mai jin wannan sirrin namu".ya faƊi hakan yana Ɗaga mata gira ta yi masa wani mugun murmushi wanda ita kaƊai ce tasan manufar yin hakan.
tun daga ranar komai ya koma dai-dai,sosai jidda ke jin daƊin Bilal,don yana nuna mata so da Ƙauna,tare da tarairayarta,abinda yafi yi mata daƊi bai wuce yadda Bilal ya watsar da matarsa ba,don haka sai ta Ƙara miƘe Ƙafafuwa,wai ita gata matar so.
****
Rayuwa ta yi min zafi,komai ya tsayamin cak don iya wulaƘanci yaya Bilal ya yimin shi,yau ina Ƙwana huƊu agidansa,amman ko shinge na baizo Ba,ballan tana ma ya duba lafiyata,Ƴan gidanmu cak suka Ɗauke Ƙafarsu babu wanda ya leƘomin.
waya ta dake ringing na Ɗauka Ƴar gidan mama ce Ƙanwar mahaifinmu me suna maryam,na Ɗauka naji muryarta kamar zata yi kuka ta ce"khairat yau dai gani nazo gidanku amman me gadi yaƘi ya barni in shigo,wai hajiya jidda bata bayar da oder in shigo ba,jiya ma baƘi da yawa sunxo amman wallahi ba'a basu damar shigowa ba,wai wannan wani irin abune haka ya ke faruwa".?
jin na yi shiru yasa ta ce"a to nidai babu inda zani,don yanzu na kira hajiya kaka ta ce kada in sake in dawo sai na shiga,to nima Ɗin na yarda da maganar kaka don haka ki fito ayi ta ta Ƙare".ƙit ta kashe wayar ba tare da ta Ƙara magana ba.
abin ya yimin zafi sosai,na ciji leƁena na Ƙasa azuciyata na ce eh lallai jidda tazo da sabon salo,ai kuwa bazai taƁa yiwu a hana Ƴan uwana shigowa gidan ba,tunda duk gidan mijinmu ne.
na saka takalmina soso mai tudu wanda na ajje don sakawa afalo,na fita raina aƁace Na yi hanyar gate Ɗin,a garding Ɗin gidan na hango jidda tana waya,ta kalleni ta zubar sannan ta yi saurin kashe wayar,don daman ta yi hakanne don in hassala,kuma gashi na hassala Ɗin.
ina zuwa na kalli me gadin wanda keda kayan kaki ajikinsa,na ce"meye dalilin Hana Ƴan uwana shigowa Gidan mijina"?.
Cikin girma mawa ya ce"hajiya ki yi haƘuri jiya me gidan ya yi tafiya kuma bai bani apointment akan wani zai shigo ba,ya bani umarni akan duk wanda zai shigo in kira hajiya jidda idan ta yadda sai mutum ya shigo."
kallon jidda na yi wadda ke nufo inda muke.tana sanye da wani shegen takalmi mai mugun tsayi,ga wani uban glass afuskarta no respect.taɗan janye glass ɗin kaɗan sannan ta ce"obinna duk wanda bazai bi dokar mai gidan ba.ka ƙyalesa kada ka kuma wata magana,ka koma bakin aikinka".
Ta faɗi hakan tana mana wani kallon banza,Maryam ta ce"hmm idan kunsan wata baku san wata ba".sai ta danna wayarta ta kira hajiya kaka tana shaida mata abinda ya faru.
Kai tsaye Hajiya kaka ta shiga ɓangarensu Bilal.ta yi sa'a kuwa Baba Abdullahi yana nan suna hira da matarsa.hajiya Ruƙayya na ganinta ta gimtse fuskarta don tasan ba alheri ya kawo hajiya kaka ba.
Hajiya kaka ta nisa ta ce"Ruƙayya zo ki dake ni ba murtuke fuska ya kamata ki yi ba?uwar rashin ɗa'a.yanzu gashinan kin koyawa ɗanki Bilal ya wulaƙanta ƴan gidansu,saboda shima yanzu ya yi gida ko?to wallahi ko awata uwa duniya ya ke ki kirasa ki faɗa masa wallahi ya yi maza yabar maryam ta shiga gidan nan idan ba haka ba.masifar akanki zata ƙare,yo idan ma ba rainin hankali ba tayaya za'ace a hana ƴan uwan mutum shiga gidan ɗan uwansa?a ina aka taɓa yin hakan?ko ke ƴan uwanki sun taɓa zuwa nan aka hanasu shigowa?to wallahi ahir ɗinki daga ke har ɗan naki mara kunya".
sunkuyar da kai hajiya Ruƙayya ta yi,Baba Abdullahi ransa yakai ƙololuwar tashi,ya nisa ya ce"Ruƙayya yaushe Bilal ɗin ya yi tafiya?ashe shi yanzu idan zaiyi tafiya haka kawai ya ke yinta?saboda ya zama babba ko?babu saka albarkar iyaye?."
"wallahi nima bansan ya yi tafiya ba?amman ka yi haƙuri".
Number Bilal ɗin ya kira,ya ɗaga yana tsaka da aiki bayan sun gaisa ne ya rufesa da faɗa sosai,ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,Bilal ya yi shiru kawai yana jin faɗan mahaifinsa,ya basa haƙuri ya kashe wayar ya kira obinna ya bada umarnin maryam ta shiga.
Maryam na shiga ta kalli jidda ta ce"to uwar mata yanzu ma ai sai ki hanani shiga?uwar iyayi mai son raba kan ƴan uwa".
Ta faɗi hakan tana hararar jidda ɗin.jidda ta yi ƴar dariya ta harɗe hannayenta a ƙirji tana wa maryam ɗin kallon rainin hankali ta ce"hmm kin bani dariya wallahi,ai ta banzar tunda ita dai wacce take cikin gidan ba tada wannan matsayin da zata bada doka da order aji,don haka ni baku burgeni ba".
Ta faɗi hakan tana nuna halin ko in kula,har maryam ta yi gaba sai kuma ta dawo ta ce"hmm jidda ma ki ke kowa?to idan ban mayar miki ba kice ni ba jikar hajiya kaka bace?kema da ki ke wani fiffigewa wai ke gaki star awajen miji ko?to wallahi kiji tsoron Allah don duk matar da ta saka ido ana wulaƙanta ƴa mace tana jin daɗi to wallahi wataran itama sai an wulaƙantata wataran itama,don haka ki guji ɓacin rana".
Dariya sosai Jidda ta yi ta ce"oho dai tsabar rashin zuciya ya ce baya so amman sai da aka liƙa masa."ta faɗi hakan tana tin tsirewa dariyar muguntar ta faɗamin magana.
Har na yi gaba sai kuma na dawo,na kalleta idanuwa na suka cika ɓam,da hawaye ban yarda sun zubomin ba na wuce sashe na.na barsu ita da maryam suna ɗauki ba daɗi.
Sosai maganar da jidda ta faɗamin take bin dukkan gaɓɓan jikina,na ƙwanta akan ɗaya daga kujerun farlona na saki kuka mai ƙarfi,tabbas na cancanci Jidda ta yi min gori,yau ƙwanana huɗu amman ko albarkacin haƙƙina da ke kansa ai ya kamata ya saukemin,amman madadin rashin hakan gashinan matarsa na wulaƙanta ni.
"Haba Khairat yanzu don wannan banzar ta faɗa miko magana shine ki ke kuka?ai kuwa matuƙar zaki dinga yi mata kuka to kuwa ta samu lagon ƙuntata miki agidan aurenki,ki zama jajirtacciya agidanki,nasan kina da dauriya amman ki ƙara daurewa kinji".ta faɗi hakan tana sharemin hawaye na.
Nan dai muka shiga hira take cemin gobe za'a kawomin gara ba'a gama haɗawa bane,na ce mata babu komai.
Ta ce"yanzu ma daga asibiti na ke naje dubo Rashida,kinsan tun bayan bikinku ba tada lafiya".ta faɗi hakan cikin damuwa.
Nima cikin damuwar na ce"innalillahi ashe haryanzu jikinne?shiyasa dana buga mata waya naji shiru?tun shekaran jiya na ke kira amman switch up".na faɗi hakan cikin damuwa.
Maryam ta ce"ke dai bari ɓari ta yi wallahi ciki wata huɗu".da sauri na saki salati tsabar tausayi kamar zanyi kuka,na ce"yanzu ya jikin na ta?".maryam ta ce"ai da sauƙi ma yanzu don wallahi ranar da tayi ɓarin da mukaje baki ga ba abin tausayi,ko magana bata iyawa sai dai idanu,don ta zubar da jini sosai ai yanzu da sauƙi".
Tuni jikina ya hau tsuma na idanuwa na suka kawo ruwa,don komai idan aka saka Rashida aciki mai mahimmaci ne,tun muna ƙanana idan ɗayanmu ba shida lafiya to zaka samemu cikin wani hali.
Maryam ce ta dinga rarrashina,amman duk da haka ban daina kukan ba,tunanin halin da Rashida take ciki shine yafi tsayamin,na ce"insha Allah zanje in duba ta fatanmu dai Allah ya bata lafiya me ɗorewa,na faɗi hakan muryata na rawa.
***
Har washe gari jikina duk babu daɗi,na kira wayar yaya Aliyu mijin Rashida yafi sau 5 amman bai ɗaga kiran ba,ƙarshe dai na haƙura.
Na fito daga wanka kenan na jiyo ƙarar tsayuwar mota,jikina yana rawa na leƙo na hango Yaya Bilal yana fitowa daga cikin motar,kayan da ya sanya sunyi matuƙar amsarsa,kyaunsa ya ƙara fitowa sosai,hawaye masu zafi suka fara ambaliya acikin idaniyata na saka hannuna na goge,ban gama ida abinda na ke ba na hango Jidda ta fito daga sashenta taci uban riga da wando english wears ya yi matuƙar kamata,ta rungume Yaya Bilal shima ya rungumeta sosai,kamar wani zai ƙwace ta,tuni wani abu ya tsayamin azuciyata kamar wani mashi ko kuma guduma,tsananin kishi na yakai ƙarshe da sauri na saki labulen,ya yinda shi kuma ya ɗauki jidda kamar ƴar tsana suka yi ɓangaren Bilal ɗin.
Na ƙwanta akan gado na hau aukin kuka,wanda ayanzu ya zamarmin kamar wani abinci,ina da komai a store ɗina,don tun kafin a kawo min gara ya ajjewa kowaccenmu abinci,fridge ma cike ya ke da abubuwa na more rayuwa,ni dai mijine ya zamarmin wahala don tunda muka yi aure ban ƙara sakashi a ido na ba sai yau.
Ina cikin wannan yanayin naji ana buga ƙofar ɓangare na,jiki na duk babu ƙwari nazo na buɗe,wanda na gani atsaye ne yasa ni waro idanuwa na waje.. .✍🏿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:22] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*
📃LITTAFI NA 2
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
*Matso kiji👂🏻*
Ki dinga tsarki da kanimfari musamman ma idan bayan kin gama al'ada yana cuko da gaban mace sosai sannan ya matseki ciki da kuma wajenki.
49. . . .50
. .. ."Yaya Salim kaine?".Na faɗi hakan ina matsa masa,na gaishesa ya ce"ai ba ni kaɗai bane ma dasu mama ne harda Hajiya kaka".buɗe idanuwa na yi murna ta isheni ƴar damuwata naji ta kau.
Na rungume Hajiya kaka ina ce wa"i miss u so much my Hajiya kaka".itama rungumeni ta yi tana tsokana ta,wai tunda na yi aure ko kiranta awaya banyi ba.
Sosai mukasha hira ananne ma ake hirar zancen rashin lafiyar Rashida,na ce"Hajiya kaka inason zuwa in duba ta".
"A'ah ƴar nan ba'a haka daga aure sai kuma ki fara fita?yanzu ma daga gidan mero muke,itama ta saka min kuka wai sai ta biyoni munzo nan,to shine fa naja mata kunne akan baza ta bini ba,sokon mijinta gashinan gabanki Salim ko kallon ƙurar zancenmu baiyi ba,daga baya ma ya fito waje shine na biyosa na ce sai ya kawoni gidanki,amman gidan Rashida muka fara zuwa tunda yafi kusa da gida."
dariya na yi na ce"Allah sarki Mero ai ita ga ta ga gida ma babu nisa tunda bayan gidanmu ne,Amman hajiya kaka ya ki ka jikin Rashidan?".
"Ah wallahi jikinta da sauƙi sosai,ai da ya ke ma an sallamota da wuri,ita kuma haka Allah ya tsara mata to ubangiji Allah ya bada na aike".dukkanmu da amin muka amsa aka cigaba da hira,Hajiya kakanta leƙa taga garar da aka kawomin ta ce"ah gara wallahi ta yi,wannan dai idan ba rabawa biyu zaki yi ki bawa waccen figigiyar ba ai har sai ayi shekara ma".ta faɗi haka tana dariya.
Har ƙofar sashena na rakosu mama ta ce"to khairat muyi banƙwana gobe insha Allah zan wuce gida,Allah ya bada zaman lafiya".na amsa da amin hawaye na fitowa daga cikin idaniya ta.
"Au yay naji ɗan jakar uba,au yanzu don Allah Bilalu kana cikin gidannan?Amman har muka gama zaman daɓaro baka shigo ba?saboda kana wajen wannan ƙwailar matar taka?a to ahir ɗinka idan aka shiga haƙƙin jikata,don ina jiye maka tashi da ƙonannan jiki".
Ta faɗi hakan tana harar jidda wacce ko kunyar idon hajiya kaka bai hanata ɗafewa jikin Yaya Bilal ba,shine ma yaji kunya ya ture ta gefe ɗaya ya durƙusa har ƙasa yana gaidasu mama,Hajiya kaka ta ce"ah to ni dai na faɗa maka,ka biyewa mace ka faɗa wuta tsundum wallahi,kuma duk ihunka Ruƙayya da Abdu baza su fito da kai ba".Ta daɗi hakan tana yin gaba abinta.
Bayansu Hajiya kaka sun tafi da daddare na yi wanka na mai kyau da sabulun da mama ta haɗomin na gyaran fata,na ɗakko qur'ani ina karantawa sai naji zuciyata kamar an wanke min ita fes.
Na ɗakko wayata na buga wayar Rashida naci sa'a ta ɗaga,da sauri ta ce"ah lallai amaryar yayana kin manta dani ko?da tuni yanzu ina barzahu,amman ko kizo ki dubani ko?".
Duk alokaci ɗaya ta sakomin waɗannan tambayoyin na ce"ayya Rashida kinfi ƙarfin haka awaje na,nima shekaran jiya da maryam tazo shine take faɗamin abinda ya faru har kuka sai da na yi wallahi".
Nan dai muka cigaba da hirarmu ta aminai,ta ce"kin buga number maryam kuwa".?
Na bata amsa"eh na buga ita ma akashe shiyasa duk naji kamar na rabu da wani abu mai muhimmanci arayuwata,me ya faru da wayar na ta"?.
"Hmm kinsan fa washe garin ranar da aka kaita sukayi faɗa da Khadija shine ta fasa mata wayar,bata tsaya anan ba ta shiga ɓangarenta duk ta rugurguza kayan wuta masu amfani da kayan kitchen ɗinta,Hmm kedai bari khairat jiya dai Khadija agida ta wuni,don yaya Aliyu ce wa yayi ta koma ta gyara tarbiyyarta sannan ta dawo,ina faɗa miki da ya ke yaya Aliyu ɗan duniya ne,kayan daya canjawa khadija na kayan wuta da kuma kayan kitchen su ya ɗiba ya bawa maryam".tana kaiwa nan ta rintsire da dariya.
Nima dariyar na ke na ce"hmm Rashida kema fa ki danki da makamanciyar irin wannan matsalar,ki daina dariya".
"Hmm a fahimtarki hakanne,amman a fahim tana ba haka bane,da zaki yi ƙwana ɗaya agidana da sai kinci dariya har cikinki ya ƙulle,abinda baki sani ba shine Yaya Aliyu dai da ki ka sani mijina,agaban Nadiya yana nuna kamar yana sonta ne ko kuma tsoronta,amman wallahi ko ɗaya babu haka,ahi dai yana yi ne saboda fita hakkinta,kuma wallahi son da Nadiya ke yimai ya fi nasa yawa nesa ba kusa ba,don haka ki daina zaton ko aƙwai wani abu,in ma asiri zasuyi to ni na fisu har awajen Allah,don ni zuciyata awanke take fes,babu wani abu acikinta kinga kuwa ƙarshe kansu zai koma".
Gyaɗa kai na yi kawai don ni a fahimtar tawa ko wani abin suka yiwa Rashida,don tsaf nasan Mama iklima cikinta da wajenta,basu da tsoron Allah ko ɗaya,su dai kansu kawai suka sani da kuma ƴaƴansu.
****
Wayar dana ajje ce ta fara ruri,na ɗauka na saka a kunne ba tare dana duba ba,saboda wanke salad ɗin dana ke a kitchen,muryar Zuhra ce ta karaɗe min kunnuwa,ƙawata ce a Bayero university muka haɗu,wajen zamanmu ɗaya da kuma wata Zainab,ganin suma duk masu hankaline yasa na yi ƙawance dasu.
"Ah lallai ya yi amarya agidanta,kina more amarci wallahi,kai muma dai Allah ya nuna mana ranar aurenmu,amman kash nasan Dadyna bazai taɓa aurar dani yanzu ba,kin san burinsa akaina wai har sai na cika lauya sannan zai aurar dani,wallahi abin nan yana damuna,gashi kuma ni ina son auren".
Ɗan murmushi kawai na yi,tausayin Zuhra duk ya cika ni,Allah sarki ita tana ganin kamar duk wata mace idan ta yi aure shikkenan ba tada wata damuwa?ko kuma kawai morewarta take?ita dai gata nan kamar wata sunduƙi agida,yau sati ɗaya cif amman babu ita babu miji,naji wani abu kamar mashi ya daki ƙirjina,saboda jin tashin motar Yaya Bilal,na ɗan zuge labulen kitchen ɗin ina hangosa,shi da ƴar ganan goshin sane wato Jidda.
"Kina jina kuwa amarsu"?.
Da sauri na dawo cikin hayyaci na sannan na ce"zuhra abinda ba keso dake,ki ƙara haƙuri komai lokaci ne,haka zali ka shima aure lokaci ne dashi,don haka ki cigaba da addu'ar Allah dai ya baki miji nagari,ba auren ba samun miji nagari ayanzu shine ya yi ƙaranci acikin al'umma."
"Ba komai khairat ina jin daɗin shawararki gare ni,Allah ya baku zaman lafiya tare da danƙwan soyayya me ƙarfi musamman ma shi mijin".dariya kawai na yi don ba nida wata amsar da zan bata,don na fitar azuciyata ce wa na cire tsammanin wai wataran Yaya Bilal zai soni kamar yadda na ke sonshi.
"Yauwa gobe ne fa hutunki zai ƙare amarsu don wallahi nida zee munyi matuƙar missing ɗinki sosai,mutuminki ma sir Deen sai tambayarki ya ke muka ce masa ai kin riga da kinyi aure,wallahi ina baki labarin har kuka sai da muka laɓe mukaga yana yi,kai ni da zee munga abin mamaki."
"Hmm"
kawai na ce don ni yanzu ban ma san yadda za'ayi da makarantar ba.
ina gama cin abincin na tashi na fita duk jikina asanyaye,sun daɗe da dawowa don haka kai tsaye na wuce sashen Jidda,suna zaune afalo suna kallo Jidda ta jingina da kafaɗar Yaya Bilal na yi sallama na shiga.
Gabana ya bada wani rassss,kaɗan ya rage zuciyata ta buga,dukkansu wani kallo suka bini dashi,cikin sarƙewar murya na fara gaishesa,wani banzan kallo ya yi min sannan