Showing 36001 words to 39000 words out of 103202 words
na ta ya fito ba,saboda duk iskancinta tana matuƘar jin tsoronsa.
yaya Aliyu da kansa ya shiga kitchen ya dafamin indomie har biyu da Ƙwai wanda yasha su tumatir sai tashin Ƙamshi ya ke,ya dafamin ruwan Ɗumi da madara wadatacciya,har Ɗakin ya kawo min ina ganinshi na yi saurin cire tagumin ina murmushi don naga halin da ya ke shiga idan ya ganni acikin tashin hankali.
da kansa ya dinga bani,na kallesa wasu zafafan hawaye na zubowa acikin idanuwa na,na saka hannuwa na gogesu saboda tausayin yaya Aliyu hannuwansa har kakkarwa suke don ya ciyar dani,shima kana ganinsa zai baka tausayi don ciyar dani ya ke amman jijiyoyin kansa duk atashe.
na kallesa na fara magana murya ta na rawa na riƘe hannuwansa na ce"Yaya aliyu don Allah ka yi haƘuri kaji?wallahi ban san me ya faru da rayuwata ba?ina cikin ruƊu sosai,akan abinda ya faru dan . . . . .saurin rufemin baki ya yi sannan ya ce"shhh kada in ƙara jin kin yi magana,abu ɗaya zaki yi ki faranta min?shine kada in ƙara ganinki acikin damuwa sam,ki manta komai kamar ma ba'ayi ba kinji?".ɗaga masa kai na yi ina ɗan murmushi ya cigaba da bani abincin sai da na cinyesa tsaf daman na ɗakko uwar yunwa,tun jiya rabona da abinci.
maimakon ya ƙeleni ya tafi,sai ya samu waje ya zauna ya dinga bani labari har da na abin dariya,sai gani ina dariya kamar bani ba,daman hakan ya ke buƙata ya tashi ya fita har fita kuma sai ya dawo ya sa ke zama ya ɗauki wayata da ke gefena,ya buɗe ta ya shiga playstore ya buɗemin manhajar arewabook,ya yi murmushi ya ce"yauwa kinga wannan manhajar ina son ki kasance da ita a kullum ammanfa garin karatu kada ki dinga zama ba sallah ko rashin tsafta,duk da dai nasan ƙanwar ta wa aƙwai tsafta."ya faɗi hakan yana murmushi,ya sanya min data har ta wata ɗaya sannan ya bani wayar ya fita.
Yana fita na danna number mamana na kirata bugu ɗaya ta ɗaga,na fashe mata da kuka, sosai ta hau yimin faɗa da nasiha sosai nasiharta ta ratsani na bata haƙuri akan bazan kuma ba,ta bawa mamansu waya wato kakarmu sosai ta yi min nasiha itama tare da ƙwantar min da hankali,sannan ta yi min alƙawarin suna nan zuwa idan matar Aliyu ta haihu,sosai na yi farin ciki don ayadda cikin anty khadija ya ke yau ko gobe ma za ta iya haihu don cikin ya yi girma sosai kamar cikin ƴan biyu.
*****
Tun safe da abin ya faru hajiya kaka baki ɗaya taƙi sakin jikinta,duk wanda ya shigo sai ya ganta ta rafka uban tagumi,tana zaune yanzun ma mero na ta takalarta faɗa amman taƙi koda kula ta,koda aka kawo abinci ma mero ta takurawa kaka wai sai ta ci,amman taƙi ce tun abincin safe ne acikinta,tunanin halinda khairat kawai take ciki take,anya kuwa ba wani abu aka yi wa yarinyar nan ba?i'ta dai ta yarda da khairat yadda ta haƙiƙa ba ta tunanin za ta aika ta irin wannsn ta'asar.
Sallama har sau uku ƴaƴan hajiya kaka sukayi amman bata ma san sunayi ba,Baba usman da Baba auwalu,suma duk sunji abinda ya faru shiyasa suka shigo sashen mahaifiyar tasu don su ƙara jin komai,don dai su har ga Allah basu yarda da abinda aka faɗa ba,don kaf yaran gidannan ta fisu nutsuwa yadda ya kamata,ba tada surutu ko wata fitina ko kuma rawar kai,don haka dole ayi mamakin hakan.
Azabure hajiya kaka ta ɗago tana kallonsu don ta tsorata da shigowarsu,ta tsuke fuska ta ce"ko kuma lafiyarku kuka shigomin ɗaki babu sallama".da faɗanta take musu magana,alamar tana cikin tsananin damuwa da kuma ɓacin rai.
Ganin haka yasa Baba usman ya fara magana don duk ya fisu sanin kan hajiya kaka ya ce"hmm umma daman hankalinmu ne wallahi duk a tashe,da wata magana da mukaji mara daɗ?shine mukazo muji gaskiyar lamari"?.ya faɗi hakan kansa yana ƙasa don yasan halin mahaifiyarsu maganar da kai ka ke tunaninba komai ba ce to awajenta komai ce.
Ai kuwa sai ta ce"yau naji ikon Allah?to su guntsi fesin matan na ku da suka faɗa muku basu gaya muku komai ba?sai ni kuka zo kuka tsare kuke son in gaya muku?to bari in gaya muku, khairat dai ban yarda da abinda ya faru da ita ba,wata ƙulalliyar aka ƙulla mata don haka yanzu inason ku tashi kuje ku samu munfukan matan na ku,ku ce inji ni na ce"sharri aka yi mata kunji"?.
dukkansu sunkuyar da kawunansu suka yi,suna son ƙwantar mata da hankali i'ta kuma taƙi yarda da hakan don sun san da ƙer idan baza ta yi rashin lafiya ba,don yadda take son khairat akaf cikin jikokinta,wai don khairat ɗin sunanta taci.
Babu yadda suka iya haka suka fice don taƙi basu damar magana,hankalin hajiya kaka bai ƙara tashi ba sai da ta aiki mero kai mata abincin dare aka ce bata nan,anan ne hankalinta ya tashi sosai ta tafi ɓangarensu khairat ai kuwa taci karo da mama iklima tana jin abinda hajiya kaka take faɗa sai kuwa ta ce"hmm ni fa lamarin yarinyar nan mamaki ya ke bani,yarinya sai kace shaiɗan".
azafafe hajiya kaka ta juyo ta ce"akanki wallahi idan shaiɗanun yara ne kina nan dasu,amnan wallahi ba akan khairat ba,ke ni fa wallahi ban ma yard daku ba?yadda kuka tsani yarinyar nan zaku iya yi mata komai don daman ba sonta ku ke ba?amman babu komai Allah yana tare da i'ta,don shi Allah ba azzalumin bawansa bane.
[04/09, 18:40] Ummu Maher(Miss Green): Sosai mama iklima ta tsorata sa jin hakan sai dai idan hajiya kaka tasan wata bata wata ba,za tayi maganin shegen akun bakinta.
***
"Hajiya daman fa ke ca ki ke son wannan yarinyar amman ni daman cen na tsane ta wallahi,tsana mafi muni arayuwata,yanzu ai gashinan ta fito da halinta afili,sai ku gane halinta a'i".
Ce war Bilal wanda ya ke danna computer ɗinsa,hajiya Ruƙayya ta yi mamako sosai sai dai ɗan adam ba abin yarda bane musamman ma yaran yanzu,sai dai kawai addu'ah.
Wasa-wasa sai ga hajiya kaka ta fara ciwo don ko iya magana ma bata yi,sosai abin ya taɓa ƴaƴanta sunyi kuka har sun gaji kuma kullum magani ake amman shiru.
Yaya Aliyu da kansa yazo ya samu Babanmu ya faɗa masa ina wajensa,amman buɗar bakinsa sai ce wa ya yi"ni fa na cire ta daga cikin ƴaƴana idan taso ma ta shiga uwa duniya wannan bai shafeni ba,tunda haka ta zaɓa".sosai maganat ta daki zuciyar yaya Aliyu amman ya daure kawai,don mahaifi ya wuce gaban wasa.
Yaya Aliyu san bai gaya min ciwon hajiya kaka ba,sai abakin Rashida naji wacce ks kawomin ziyara akai-akai,ita ma ta yi baƙin ciki,ta yi kuka abisa ƙazafin da aka yi min a kullum bani haƙuri take don haka yanzu damuwata ƙadance akan ta da,yaya salim ma yana yawan zuwa,maher ƙanina da ke skull shima ya dawo yaji duk abinda aka yi min,kai tsaye ya ce ƙarya ne sharri ne,kuma asannu sai ya tona musu asiri.
Abinda ya ƙara saka rayuwata acikin garari bai wuce kai kuɗin yaya Bilal da saka ranarsa da jidda da aka yi ba,naci kuka har na godewa Allah,wato ni tawa ƙaddarar kenan?kamar wadda ba tada sa'a a rayuwarta?haka dai na dinga sambatuna ni kaɗai a ɗaki,daman idan na gama aiki na sai in shiga ɗaki in ɗakko wayata in ta karatu a arewabook don ina jin daɗin manhajar anan naci karo da wani littafi wanda miss green ta rubuta silar fyaɗe sosai littafin ya ɗaukemin hankali don kusan abinda ya faru dani shine ya faru da yarinyar cikin littafin,anyi mata fyaɗe amman bata san waye ba?anan naji hankalina ya daɗa ƙwanciya don yarinyar cikin book ɗin ta yi haƙuri sosai ƙarshe kuma komai ya zama labari.
Ina cikin karanta book ɗin na jiyo nishin anty khadija sosai hankalina ya tashi na fito farlo,na ganta durƙushe jikin dining table ta riƙe bayanta da hannu ɗaya,da sauri na isa inda take ina ta rafko mata sannu,na yi saurin kiran yaya Aliyu awaya,shima cikin tashin hankali ya taho.
*Miss green ce*
[23/09, 16:20] Miss Green🍀: 33🟫34
. . . .muna zuwa kai tsaye labour room aka kaita duk ta galabaita sosai,sa ƙer take nishi duk hankalinmu atashe muka zauna a reception ɗin bayan sun shigar da i'ta ɗakin ƴan haihuwa.
Na kalli yaya Aliyu wanda duk a ruɗe ya ke na ce"bro ka kira mutanen gida mana susan halin da ake ciki?".girgiza min kai kawai ya yi alamar baya buƙatar hakan.
Munfi awa biyu a zaune sannan likitab ta fito ta ce"ta kasa haihuwa da kanta suna tunanin ma operation za'ayi mata,likitan ta tambayi mijinta?yaya Aliyu ya bisu zuwa wani office.
Data na da ke kunne naji saƙonni na ta shigowa,sunan Rashida da na gani ne yasa ni duba saƙon na ta,anan na ke gaya mata abinda ke faruwa,na ce"Rashida ni naso ya faɗawa mutanen gida don baki gani ba wallahi ta sha wahala sosai".
"Ai gwara kada ya gaya musu,kin san dai yanzu a halin da ake ciki,ni bana son su ganki ma tunda su basu yarda da ƙaddara ba,kuma abinsu babu bincike,yanzu hajiya kaka ma tana cen rai a hannun Allah kuma nasan duk sanadin wannan abin ne".
wata irin muguwar faɗuwar gaba naji ina hawaye na ce"Rashida kina son ki ce min hajiya kaka ce tace babu lafiya?innalillahi yanzu a gida take ko a asibiti?kuma me ya janyo ciwon na ta?".
Duk alokaci ɗaya na rattabo mata waɗannan tambayoyin?ganin hankalina ya tashi sosai yasa ta fara ƙwantarmin da hankali sannan ta ce"khairat kada kice zakije gidanmu ki ƙelesu aƙwai lokacin zuwan,Hajiya kaka addu'arki take buƙata ba wai kuka ba,idan ki ka yi mata addu'ah ko a i'na take Allah zai amsa,don Allah khairat kada ki ɗaga hankalinki kinji don Allah".
Muna cikin wayar mijinta yaya Aliyu ya amshi wayar ya ce"khairat kada ki ɗaga hankalinki babu abinda zai faru da hajiya kaka kinji".goge hawayen fuska ta na yi ina jin kaina ya yi min wani iri kamar zai tsage gida biyu.
A haka har yaya Aliyu ya dawo ya sameni ganina riƙe da kaina wanda ke barazanar rabewa gida biyu ya ce"khairat me ya ke damunki?kanki ne ke ciwo".?duk babu amsa don haka ya saka bayan hannunsa kan goshina yaji mugun zafi kamar wuta,yana cirw hannuna daga kan goshina sai yaji na tafi luuuuu.
Sosai ya tsorata ya fara girgiza ni yana kiran sunana,amman ina sai na yi sharaf a hannunsa,wani irin salati ya saka da gudu ya ɗaukeni kamar ƴar tsana yana ihu yana kiran likitocin.
Da sauri likitocin suka bayyana,suka sakani a gadon marasa lafiya suka yi wani ɗako dani,yaya Aliyu fa ya zama kamar wani mahaukaci sabon kamu,ga matarsa tana labour ga ƙanwarsa babu lafiya,ya rasa awani bigire zai kira wannan ƙaddarar ya ɗaga hannayensa biyu sama yana ce wa"ya Allah ina roƙonka don tsarkin sunayenka tsarkaka Allah ubangiji ya bawa waɗannan bayin na ka lafiya ƙanwata da kuma matata.
Da ƙer likitoci suka dai-daita numfashi na amman ina wani stage wanda addu'ah kawai na ke buƙata,waya ta dana ajje i'ta ce ta fara ringing yaya Aliyu ya ɗauka yaga an saka mamana,shahada ya yi kawai ya ɗauka ya kara a kunnensa hawaye na fitowa daga cikin idanuwansa.
"Haba khairat me yasa ki ke ajje wayarki ne ki tafi wani wajen ina ta kiranki baki ɗaga ba"?.hankalin yaya Aliyu ne ya ƙara tashi ya ce"a'aaa mama ni ne Aliyu ne".
Gaban mama ne ya faɗi sosai ta ce"a'a to ina khairat ɗin"?.
Kasa haɗa kalma ɗaya ya yi wacce mama baza ta gane komai ba,ya yi dauriya ya ce"eh daman na shigo ne yanzu ta ajjs wayar a farlo i'ta kuma tana maƙontanmu nan".
Ajiyar zuciya mama ta yi sannan ta ce"to ka aika mata da wayar inason muyi magana da ita ne"?.
Jikinsa ne ya yi sanyi sosai da jin abinda mahaifiyarsu ta faɗa bakinsa yana rawa ya ce"am daman mama ni yanzu zan koma da gaggawa ne na kai khadija asibiti labour take".ya faɗi hakan yana jin bai ƙyauta ba ƙaryar da ya yi wa mahaifiyar tasu.
"Ayya to Allah ya sauketa lafiya,to nima ina kan hanya insha Allah daman suprise na yi muku,ni da mama muna kan hanya".
Gabansa ne ya yi mummunar faɗuwa da ƙer ya aro dauriya suka yi sallama,ya leƙa khairat wadda aka saka mata oxigien saboda numfashinta da ya ke tafiya ba dai dai ba.
Wasu hawaye ne suka zubo masa yasa bayan hannunsa ya goge,ya samu kan wani benci ya zauna yana kallon kyakkyawar fuskar ƙanwarsa wadda ke kan screen ɗin wayarta,ya shafa fuskarta a hankali yana kuka ya ce"sister Allah ya baki lafiya,Allah ya tona asirin waɗannan mugayen mutunen waɗanda sukayi silar rashin lafiyarki,da kuma silar mutuwar auren mahafiyarmu."
fashewa da wani matsanancin kuka ya yi,yana jin zuciyarsa na yi masa zafi sosai,yana zaune yana kukan wata nurse ta fito cikin farin ciki ta ce"congrat munyi nasarar cirowa matarka babynta mace yanzu haka uwar na ɗakin hutu,babyn kuma tana nan."
Bin nurse ɗin ya yi har ɗakin ya hango kyakkyawar babynsa sai wulga fararen hannayenta take fafare ƙal,kamanninta da khadija kamar ta yi ka ki komai iri ɗaya.
A hankali yaje ya ɗauki ƴarsa ya sumbaci goshinta sannan ya yi mata huɗuba,da sunan khairat wato Rahama.
Har yanzu khairat bata dawo dai dai ba,khadija kuwa tuni ta warware kamar ba wadda aka yi wa operation ba,ƴan uwa har sun fara zuwa,sai dai ko sau ɗaya Aliyu bai gaya musu rashin lafiyar khairat ba,ya tashi ya tafi wajen ƴar uwarsa,har yanzu bata san inda kanta ya ke ba.
Ya yi kuka har ya gaji,Salim da maher zuwansu kenan Aliyu ke shaida musu abinda ke faruwa da ƴar uwarsu,da gudu suka ɗunguma zuwa ɗakin da aka ƙwantar dani,dukkansu sun ruɗe sai kuka suke yaya Aliyu yana ta basu baki shima yana share hawayen da ya cika masa ƙwarmin idanuwansa.
Ko zuwa wajen khadijan basu yi ba suka zauna kowannensu ya riƙe hannun khairat suna ta tofa mata addu'o i.
*****
Aranar mama ta sauka ita da mahaifiyar ta,asibitin suka fara sauka kai tsaye ɗakin da khairat take ya ƙwatanta musu,kasa ƙarasa shigowa mama ta yi ta kasa magana bakinta sai rawa ya ke,a hankali ta ƙarasa wajen khairat ta rungume ƴarta a ƙirjinta tana wani irin kuka mai tsuma rai,yanzu ƴar ta ce ta dawo haka?baki ɗaya ta canja kamanni acikin awanni,yarinya ƙarama amman Allah ya jarabce ta da ƙalubale kala kala.
Mahaifiyar mama i'ta ke rarrashin mamanmu su yaya Salim ɗin ma kuka suke sosai,sun kasa rarrashin mama don basu san ma me zasu ce mata ba,don suma neman masu rarrashin suke.
Tsakar dare na fara ɗan motsa ɗan ya tsana yaya Salim da ke gefena ya ɗaga fuskarsa da sauri don bai san sanda bacci ma ya ɗaukesa ba,mama da ke kan sallaya ta tashi da sauri sukayo kaina su duka,kakarmu,yaya Aliyu,mama,yaya Salim,maher.dukkansu suka rufu akaina suna yimin sannu.
Murna da farin ciki suka cika zuƙatan waɗannan family,hawaye na fitows daga fuska ta na ce"mama na".da sauri ta amsa tana shafa fuskata i'tama kuma tana hawayen.
Na fara samun sauƙi sosai don ƙwanana uku suka sallameni,ita ma anty khadija an sallame ta muka wuce gida baki ɗaya,sai dai tun a asibitin sai da yaya Aliyu da khadija suka hau sama suka faɗo,don muraran ta nuna bata son mu koma gidanta,yaya Aliyu ya ce ai kuwa bata isa ba sai dai ita tabar gidan don duk duniya bashi da kamar mahaifiyarsa da kuma ƙannansa musamnan khairat wacce take mace.
****
"Oga mun gano yarinyar da wannan ɗan matsiyaciyar ya ke so,mu kashe ta ne ko kuma mu barta?".ce war ɗaya daga cikin yaran Alhaji Damas,baƙi ƙirin dashi kamar zunubi.
Sassanyan lemo Alhaji Damas yasha sannan ya ce"ni bana taɓa yin abuna ba tare da ba yi wa mutum mai kankat ba,ba zaku kashe ta amman zaku yi mata ƙanin mutuwa ta yadda zai san ce wa ni dashi ba ɗaya bane,ta yaro ƙyau take ba ta ƙarko."ya faɗi hakan yana miƙewa tsaye yaran nasa suka bishi abaya.yana saƙa mummunar ƙuduri akan Jidda wacce ta kasance budurwa ga Bilal.
Zama na da mahaifiyata yasa yanzu na ɗan fara sakin jikina,ga shi ko da wasa bata bari na in zauna ni kaɗai saboda abinda likita ya ce kada a barni ni kaɗai saboda b.p ɗina ya hau sosai,kuma duk ta silar tunanin.
Ranar suna Yaya Aliyu ya ce baza ayi suna ba,saboda yasan abinda hakan zai kawo,barka ma kawai da ƴan gidansu sukazo sai da akaso ayi faɗa,wai mama tazo ta zauna gidan ɗanta wai ta ƙwaso tsohuwarta inyamura sun taho tare.
Wannan magana ta tsayawa mama sosai,a take mutuwar aurenta ta dawo mata sabuwa fil,hawaye masu zafi suka zubo mata,lallai su mama iklima sun cuce amman babu komai kansu suka cuta don har awajen Allah ta fisu tunda dai ita bata taɓa cutar dasu ba.
****
Hajiya Inna ta kalli ƙawarta hajiya kaka ta ce"yanzu Ramatu haka zamu yi ta zama kina tare da wannan ciwon da aka rasa gane kansa,kullum abu ƙara gaba ya ke ni wallahi gani na ke ma kamar a mafarki".ta faɗi hakan cikin damuwa.
Mero da ke gefen Hajiya kaka tana ɗan yi mata tausa,itama duk shirmenta yanzi ta ajjesa a gefe tunda hajiya kaka ba lafiya.
Alokacin su Baba Abdullahi suka shigo,Baba Bashir,Baba auwalu Baba ƙasim, suka zauna suna gaishe da hajiya inna ta amsa itama tana musu ya mai jiki,suka amsa mata da sauƙi sannan hajiya inna ta ce"a'ah lafiya na ganku ku dukanku kunsha manyan kaya haka?".
Baba Auwalu ne ya ce"ai shi yaya Abdullahi ba tare muka fita dashi ba,yanzu dai shigowa ne dai muka haɗu dashi to shine ya ce daman zaizo duba umma ne,amman mu mun kai kuɗin Bilal ne har da saka ranarsa."
"Ikon Allah to Allah ya sanya alkhairi".
Suka amsa da amin suna kallon mahaifiyar tasu wacce ke kallansu itama har zuciyarta tana jin daɗin ganin kan ƴaƴanta a haɗe.
Bakinta ya fara motsi alamar tana son yin magana,mero ce ta lura da hakan ta ce"la kaka nason yin magana".ta faɗi hakan da farin ciki don ta damu da ciwon hajiya kaka.
A hankali Baba Ƙasim ya saka kunnensa dai-dai bakin Hajiya kaka,jin abinda take faɗa ne yasa ya kalli