Showing 39001 words to 42000 words out of 103202 words

Chapter 14 - ABIN CIKIN ƘWAI

22 Jan 2025

4466

ƴan uwansa da sauri.


Kuyi haƙuri gobe da safe zakuji update me yawa.



*Miss green ce*

35🟩36



. . . .kallon mamaki suke ta bin ɗan uwansu dashi sannan Baba Abdullahi,ya ce"lafiya naga duk hankalinka ya tashi?me ya faru me ta faɗa maka?".ya faɗi hakan yana kallon ɗan uwansa.

Wata uwar zufa ya sharɓe sannan ya ce"ta ce wai ko da ta mutu a cika mata burinta na auran Bilal da kuma khairat".ya faɗi hakan yana sunkuyar da kansa.

Murmushi Baba Abdullaho ya yi sannan ya ce"babu komai ai mu bamu i'sa mu tsallake duk wani abu da tace ayi ba,fatan mu dai Allah ubangiji ya tashi kafaɗarta".ya faɗi hakan cikin damuwa sosai don da za'a dawo da ciwon jikinsa da ya fi kowa jin daɗin hakan,don mahaifi yafi gaban wasa.

Baba ƙasim ya ce"ammam kana ganin yaya wannan haɗin ya yi kuwa?kana ganin gashi shi hae mun riga da mun kai masa kuɗi,gashi kuma ta yi maganar khairat?kuma ga abinda ya faru da rayuwae yarinyar?".

murmushi Baba Abdullahi ya yi sannan ya ce"hmm Ƙasim kenan?me ye amfanin gida bai ƙoshi ba akaiwa dawa?ai ko aure ne dashi ba rana aka saka mai ba sai ya aure ta,tunda ba shi ke da kanshi ba mu muka haifesa,kuma zancen abinda ya faru da khairat ni ban yarda ce wa hakan ya faru ba,sannan ko da ma ya faru ɗin dole ne sai ya zauna da ita tunda dau ita ƴar uwarsa ce,idan har bai rufa mata asiri ba waye zai rufa mata?"ina tambayarka ƙasim".?shiru baba ƙasim ya yi don yaga yayan nasu ya ɗau zafi shiyasa ya yi shiru ya sakawa abin albarka kawai,tunda dau bashi da ta cewa don su duk abinda yayansu ya yanke shi suke yi basu taɓa saɓa masa bisa umarninsa ba,yadda kasan mahaifinsu don kunsan ance babban ya uba.
Hajiya inna ta ce"hmm ni wallahi wannan haɗin har zuciyata daɗinsa naji,tun da dai wannan yarinyar ai ƴar uwarsa ce,ai wannan haɗi ya yi daɗi wallahi".ta faɗi hakan zuciyarta fes,don ko yanzu Hajiya kaka ta nunawa matan ƴaƴanta darasi akan sharrin da suke ƙullawa khairat,don haka tasan zuciyoyinsu kamar zasu fashe za ta yi,kowaccs mata agidan so take Bilal ya ce yana son ƴaƴansu amman shi ya yi kunnrn uwar shegu harkokinsa kawai ya ke.

To wannan maganar sosai ta hargitsa ƙwanyar ƴan gidanmu,musamman ma waɗanda daman ba so na suke ba,daga ni har mahaifiyata su mama iklima dukkansu jikinsu ya yi sanyi,wato ita wannan yarinyar duk muguntar da suka yi mata,ƙarshe sai dai ta zamo mata alkhairi,inji masu iya magana suka ce hassada ga mai tabo taki ce.

Daga ni har mahaifiyata babu wanda yasan wannan maganar,saboda tunda mama tazo ko hirar ƴan gidanmu ba ballan tana ma har muji komai.

Yaya Aliyu kuwa yasan komai don Baba Abdullahi ya kirasa ya faɗa masa komai,sannan ya ce kada a sake a gayawa ita khairat ɗin gaya mata kamar zai janyo wata matsalar,sannan suma ƴan gidanmu duk iyayenmu sunja musu kunne sosai akan kada a faɗawa Bilal har sai an ɗaura aure.
****

"yanzu kai mukhtar saboda wannan lalatacciyar yarinyar ka ke kuka?yarinyar da agidannan har ciki ta yi shine don na ce baza ka aure ta ba,shine yanzu zaka sakani agaba kana kuka kamar wani yaro?"To wallahi ka buƊe kunnuwanka da Ƙyau ba zaka auri wannan yarinyar ba irin tsiya irin inyamurai,ni banda ma ubanka da ubanta ciki Ɗaya suke me zaisa ma in haƊa iri dasu,Kaji dai na faƊa maka don ni na tsani haƊa aure irin na kakarku ta haƊa kara da kishiya waje Ɗaya azo ayi ta masifa to ni haƊin nan ba dani ba,don haka ka maida hankalinka,bara'atun ma da ta liƘe maka ta yi ta gama don babu Ƴar da zaka aura ehe kaji dai na faƊa maka".tana faƊar hakan ta yi gaba abinta.

Sosai mukhtar yaji haushin wannan mummunan zagin da mahaifiyarsa ta kewa sahibarsa khairat,sam ko a mafarki ba zai yarda ce wa khairat za tayi cikin shege ba,sai gashi ana yi mata Ƙazafi da ta yi ciki,tabbas zaiyi amfani da aikinsa na lauya ya tsaya tsayin dafi akan wannan Ƙazafin da aka yi wa baiwar Allah.



******

"yanzu Alhaji Ɗan na wa ne zai auri wannan yarinyar wacce ta zubar da mutuncinta tun awaje har ta Ɗakko ciki,shine ni za'a laƘabawa Ɗana ita saboda anga bai damu da kowa ba".

"Hajiya RuƘayya haƘiƘa zanyi miki abinda baki taƁa zata ba,idan ki ka Ƙara ce wa khairat ta yi ciki?me yasa ku mutane arayuwarku kanku kawai kuka sani?muƘaddara ma hakan ya faru?ita sai aƘi aurenta saboda wannan?mata nawa ne suka yi cikin shege agidan iyayensu har suka haihu kuma hakan bai sa an sakesu ba?sai ita za'a ce baza a aureta ba?no possible ace kuma Ɗan uwanta bazai rufa mata asiri ba?abinda zan gaya miki shine,duk ranar da ki ka Ƙara zagin khairat kisan da ce wa zaki yi nadamar da baki taƁa tunani ba kinji na gaya miki,ruwan ki kiso auren ruwanki kiƘi so?"yana faƊar hakan ya yi fitarsa cikin tsananin fushi.

A tun rayuwar aurensu Abdullahi bai taƁa fushi da ita irin na yau ba,sam bai da faƊa ko hayaniya mutum ne shi mai tsananin haƘuri kafin kaga abinda zai saka shi fushi ana daƊewa,daƁar ta zauna akan kujera wacce take tree seater azuciyarta tana tunanin ta yadda za'ayi wannan auren alhalin ranta bai so.
******

Na fara zuwa makarantar jami'a Ado bayero university kano,ina karantar fannin law(lauya),ban taɓa tunanin zanyi ƙoƙari kamar yadda na ka yi yanzu ba,saboda halin dana tsinci kaina har yanzu babu wanda ya faɗamin zancen aure na da yaya Bilal ko awajensu Rashida ban tsinci zancen ba,ga mama da muke tare itama bata sani ba ko abakin su yaya Salim kuma babu wanda bai san zancen acikinsu ba.

Muna zaune a aji muna ɗaukar lecture,wata ƙawata Salima ta ɗan buge ni kaɗan ta ce"hmm Rahma ga fa mutumin ke nan?wallahi yana matuƙar burgeni sosai,handsome dashi".

Banza na yi mata don ni sam hankalina baya wajensa yana kan wani note dana ke dubawa,ƙamshin turarensa yasa na ɗago don ƙamshin turarensa sak dana yaya Bilal.

Ina ɗagowa muka haɗa ido dashi kyakkyawa ne sosai ba laifi,sai dai ko kaɗan bai kai yaya Bilal ba,na rintse idanuwa na ina jin zuciyata tana ƙuna sosai don tuno da yaya Bilal,na yarda ayanzu a tunanin yaya Bilal akashi ɗari yanzu babu goma aciki saboda yadda mama take ƙoƙari sosai akan in rage tunanin ko da kaɗanne.

Hankalina yana cen kan tunani wanda na ƙwana biyu banyi ba,sosai ya ƙurawa khairat ido kamar zai cinye ta,yarinyar tana matuƙar burgesa sosai yana son mutumin da bai damu da duniya ba,wanda babu ruwanshi da tashin hankali so silent,bai taɓa tunanin zai auri mace mara mutunci irin matarsa ba,ga shegen surutu kamar aku amman kuma bata taɓa ganinshi da gemon arziƙi ba,idan kaga tana wani lallaminshi to tana son yin wani abu da kuɗine to zai ga kalolin tarairaya kala kala.

Yana cikin tunanin monitor ɗin ajin ya shigo yana ta yi mai magana amman baiji ba,hankalinsa yana kan kallon khairat sai da monitor ɗin yaɗan buga desk ɗin sannan ya dawo cikin hankalinsa,duk kunya ta ishesa khairat ɗin ma hankalinta na cen tunani bata ma san wainar da ake toyawa ba,Salima sai dariya take ƙasa-ƙasa taɗan bangaji khairat ɗin sannan itama ta dawo cikin nutsuwarta,duk ɗagowarta sai sun haɗa ido dashi ta takura sosai tana addu'ar ya fita ko ta huta da wannan kallon.
Ina dawowa daga makaranta naga yaya Aliyu da yaya Salim harda maher muka gaisa dasu hankalina na kan mama don ban jiyo muryar ta ba,ina zuwa falon naji tsit babu sai ƙarar tv dake kunne,abin ya bani mamaki don nasan mama afalo take zama gabana ya yanke ya faɗi,to ina mama taje?babu mai bani amsa don haka kai tsaye na shige ɗakinta wanda take ƙwana da ita da kakarsu.

Sosai ta yi mamaki gani babu kowa,sai taji kanta har ya fara sara mata tabbas uwa ta dabance tunda mamana tazo bata taɓa barina ni kaɗai na yi tunanina ba,hankalinta na kai na tana bani labarai kala-kala ni kuma inyi ta dariya.

Ina cikin wannan halin suka shigo,sai naji duk haushinsu na ke ji kamar su suka suga mama ta tafi,ana cikin hakan Anty khadija ma ta fito,ta wani kalleni ta watsar Khairat na hannunta.

Yaya Aliyu ya ce"khairat sai kiga mama ta tafi ko?ki yi haƙuri lil sis bata son ki sani ne shiyasa ta tafi amman ta ce zata dawo ƙwanan nan."waau hawaye ne suka fara zubomin ina kukan na ce"wayyo mamana!yanzu waye zai dinga rarrashina ?mamana tana da lokaci na,bata son in shiga wani hali".sai na fashe da kuka kamar ƴar yarinya.

Yaya Salim ya ce"haba khairat kamar wata ƴar yarinya insha Allah mu zamu dinga rarrashinki kamar mama tananan".ya faɗi hakan yana ɗago haɓata wadda ta gama jiƙewa da ruwan hawaye.

Cire hannunsa na yi daga kan haɓata na ce"a'ah yaya Salim ba zaku iya kula dani kamar mama ba,ku mazane dole ko ta wajen ƙwanciya bacci zamu rabu,amman mamana har baci muke tare da ita,ni dai wajen mamana kawai zan koma".

Na faɗi hakan ina kukan shagwaɓa Maher ya ce"kai anty khairat jibe kifa ƙatuwa dake kina wani kuka harda shgwaɓa ni idan na kula ma harda majina".?ya faɗi hakan cikin sigar zolaya.

Da gudu na tashi na fara dukansa yana karewa da fillon kujerar,ni kuma ina kuka ina dukansa,su Yaya Aliyu sai dariya suke Anty khadija ta kallemu ta watsar sannan ta tashi tsaye ta ce"hmm irin wannan taɓara har ina haka,anbi duk an sangarta yarinya kamar wata ƴar baby".?

Sosai yayannin na wa suke ta mana dariya,babu wanda baiji abinda anty khadija ta faɗa ba dukkansu dai sunji haushin maganar amman a fili kamae basuji ba suka barta kamar wata mahaukaciya,ba taso yin shirunsa ba don abin ya bata haushi yadda ko albarkacin gaisuwa bata ciba amatsayin matar yayansu kuma Ƴar uwarsu.
****


Sosai hankalin Bilal ya tashi jijiyoyin kansa duk sun tashi ruɗu-ruɗu haka za lika idanuwansa sunyi jawur kamar gauta ya ce"yanzu mama ni za'a haɗa da wannan mahaukaciyar yarinyar wacce na tsana arayuwata?yanzu abinda Baba zaiyi min kenan?is no possible hakan ya faru bazan taɓa iya auren wannan yarinyar ba,wallahi dana aureta gwara in auri mahaukaciya wacce ke yawo bola-bola insan abinda na aura,yarinyar da ta gama gantalinta atiti,to wallahi ba umarnin kaka ba ko umarnin meye ne ni bazan aure taba".

"don Allah Bilal idan har ka isa kana ganin kai wuyanka ya isa yanka kanka ɗaya damu da kuma mahaifiyarmu?to don Allah kada ka aureta?sakarai kawai wanda bai san inda ya ks mishi ciwo ba".ya faɗi hakan yana matsowa inda Bilal ɗin ya ke.

Alhaji Abdullahi ya kalli Hajiya Ruƙayya sannan ya ce"ke kuma na gode da abinda ki ka yimin?amman ki sani daga ks har ɗanki babu wanda ya isa ya juyani akan wannan maganar,ƙanina ma Malik daya ƙalubalanci abin yanzu sama-sama na ke dashi kai bama shi ba koda mahaifiyarta ce ta nuna ba taso to bata isa,a ƙarshe ina ƙara jan hankalinku da ku kula sosai da abinda zaije ya dawo matuƙar kuka nuna min isa".


Yana faɗar hakan ya wuce fuuu abinsa,Hajiya Ruƙayya ta kalli ɗan na ta sannan ta ce"my son mahaifinka mutunne mai kafiya akan abu,muddin yasa abu a gabansa to sai ya ci masa,don haka ka yi haƙuri kawai amman fa idan ka aureta ni na sakaka ka gana mata azabar da zai sa da ƙafarta tabar gidan,kuma sannan ban yarda ka kusance ta ko d sau Ɗaya ba.




*Miss green ce*


Hmm ku kasance da wanman littafi mai suna Abin cikin ƙwai aƙwai babbar tafiya nan gaba,mai cike da ƙalubale,ban tausayi,ban dariya,da sauransu ku dai ku kasance da ummu maher miss green,sannan aƙwai alƙawarin dana yi muku na koyar da girke-girke insha Allah ban manta ba sai anan gaba.

*A C Ƙ*

MISS GREEN

*37⬜38*


. . .da sauri Bilal ya ce"Allah ya tsareni da ko shiga ɗakinta don ban san abinda zan tarar ba,na tsani wannan yarinyar tsana mafi muni arayuwata,zan cigaba da addu'ah da kuma lallaɓa Baba Allah yasa kada in auri wannan annobar".yana faɗar hakan ya yi waje abinsa cikin zafin zuciya da kuma ƙuna.

bai san adadin rashin son ta da ya ke acikin zuciyarsa ba,ko son kallonta bai yi balle kuma har ya zauna inuwa Ɗaya da'ita bai fatan hakan ta faru don matuƘar hakan ya faru to tabbas aƘwai babbar matsala agaba.



*****

Ina yawan jin faɗuwar gaba,na rasa me ke janyo min hakan,na kasance acikin ruɗu sosai,ban san wanda zai rarrashe ni ba,shiri na ke sosai don yau so na ke zanje gidan Rashida don mun ƙwana biyu bamu haɗu ba,wata atamfa ta na ɗakko ɗinkin riga da siket atamfar holland ce ja yellow da ratsin ja,sosai na yi kyau acikin atamfar kamar ka ɗaukeni,haka kawai naji inason yin ƙwalliya na shafa hoda da janbaki ja amman maroon sai ƙwalli da maskara,wow gaskiya na yi ƙyau sosai daman gani da shape irin na coco cola sai na yi wani ƙyau kamar kasace ni,na yi park ɗin gashina a baya daman gani da tsayin gashi amman kuma kamar roba haka ya ke,na yi ɗaurina ture kaga tsiya.na yafa mayafi na ja amman da followers yellow kaɗan,na ɗauko dogon takalmina high hill,sosai na yi kyau kamar zarah acikin wata,na ɗauki wayata da ƴar fos ɗina suma suk red ne.ina fitowa muka haɗe da Anty khadija afalo,ta kalleni sama da ƙasa ta ce"ke kuma sai ina?".Tambayar ce taban mamaki don bata saba ganina ina gantali ba.


Na ce"daman zanje gidan Rashida ne mun daɗe bamu haɗu ba",taɓe baki ta yi sannan ta ce"oky amman kin san dai baki gama aikinki ba ko?".Ta jeho min wannan tambayar ta rainin hankali,sosai tambayar ta bani mamaki don nasan dai tun safe na gama komai harda wankin kayan khairat,to kuma wani aiki ne zanyi?.

"Ki ka tsaya kina kallona ko kin gama aikinne?".kasa magana na yi saboda ban san me zance mata ba,ni ba mutumce mai musu ba ko jayayya ma ban iya ba sai dai ka gaji ka yi shiru.

Na ce"to idan na dawo ma zan ƙarasa aikin".na faɗi hakan inawa little khairat kiss akumatu na yi tafiya ta ko hangenta banyi ba.taɓe baki ta yi sannan ta kalli ƴar ta khairat ta ce"oh ke dai Allah yasa kada ki yo wannan mai mummunan halin,kawai an tashi an laƙabawa yarinya sunan wannan mara mutuncin,ga sunan ubana dana uwata ba'a saka ba sai na wannan banɗararriyar."ta faɗi hakan tana bawa Khairat mama.
***


Tun akan hanya wani ya ke ta bina amman ko kallon ƙurarsa banyi ba,ya yi parking ɗin rantsatsiyar motarsa a gabana.na juyar da kaina gefe na tsaya ina kallon ikon Allah,wani mutumine ya fito daga cikin motar sanye da glass ya ce"Hajiya oga ne ya ke son yin magana sa ke".kallon tsaf na yi masa sannan na ce"ok kawai ya ganni a hanya sai ya ce wani zai yi magana dani to ka ce masa bazan tsaya ɗin ba".na yi wuce wa ta.

Daga gidan Yaya Aliyu naira ɗari ne zai kaika gidan Rashida na shiga keke napep na yi gaba abuna,sai dai tunda na shiga motar na hango wannan motar abaya tana bina har zuwa ƙofar gidan Rashida.

Na rasa me zance saboda haushi,na fito da kuɗin na bashi cikin fushi na shiga gidan,ko waiwayensa ban ƙara yi ba,a farlo na same ta tana cin abinci da gudu ta taho ta tarbeni tana ce wa"kai sis na ji daɗin zuwanki".har muka zauna Rashida bata sake ni ba kamar wani zai ƙwaceni.

Na ce"ni don Allah sakeni bayan ma ko zuwa inda na ke biki yi ba?Yau watanku uku da aure amman kin manta da zamana".dariya i'tama ta yi sannan ta ce"hmm ai gidanku bazan iya zuwansa ba,saboda anty khadija sam bana shiri da ita don ni bana son rainin hankali da kuma wayo".na ce"hmm".kawai ba tare dana ƙara ce wa komai ba.

Na ce"wai ni Rashida ya naga kin ƙara wani fari ne da cika idanuwa?".Dariya ta yi sannan ta ce"hmm ai nan da 7 month zaku zo suna".

Rungume ta na yi ina dariya na ce"ah ki ce mun kusa zama manya?".

Ta ce"ni kuwa ya naga ko ɗan gyaran amare baki fara ba?ai wallahi Khairat baki da mutunci ace zaki auri yaya na amman sai a duniya na ke ji"?.

Kallonta na yi ƙuri na kasa ce wa komai,mamako da kuma ruɗu suka cika ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwata,na ce"hmm wai Rashida me yasa ki ka fiye wasa ne?Ta yaya za'a ce za'ayi biki na amman baki sani ba?"a'i kema kin san ba zai taɓa yiwu ba".na faɗi hakan ina kallonta.
Sosai mamaki ya game ƙwaƙwalwar Rashida ta ce"wai kina nufin baki san za'ayi aurenki nan da sati biyu masu zuwa ba?".Ta faɗi hakan tana kallona.

Da sauri na tashi tsaye na ce"haba Rashida kada ki sanya zuciyata ta buga da waɗannan kalaman na ki maras tushe?Don Allah ki faɗamin abinda ke faruwa"?.

Ɗan huras da numfashi ta yi sannan ta ce"hmm khairat nasan za kifi kowa farin ciki dajin wanda zaki aura,Yaya Bilak shine wanda zaki aura,har an kai kuɗi da komai tun wata uku da suka wuce".sosai na waro idanuwa duka waje na ce"Wai Rashida kin tabbatar abinda ki ke faɗamin gaskiya ne kuwa"?.Kallon banza ta yi min sannan ta ce"ai kin san na saba yi miki haka"?.

Rasa tudun da fawa na yi na ce"lallai Rashida ni mai sa'ace kiga duk tsayin shekarun dana yi da dakon bawan Allahn nan azuciyata ashe nan kusa zan aureshi".na faɗi hakan ina rungume da filo a ƙirjina,Rashida ta ce"ah to kinga mune manyan ƙawaye kuma ƙannan miji ba?".Ta faɗi hakan tana kai min dukan tsokana.

Sai dai tun yanzu na fara tunanin wani irin zama zamuyi da Yaya Bilal?Yadda ya tsaneni kamar mutuwarsa?lallai aƙwai babbar matsala a wannan rikitattan zaman na mu.

Ranar dai na yi yinin jin daɗi,Rashida ta ce"baki tambayeni mutuniyarki Nadiya ba"?.murmushi na yi sannan na ce"hmm Rashida ni fa yanzu gwara inyi nesa dasu don zama dasu ba alkhairi ne arayuwa ba,kina ganin dai halin dana fa ɗa saboda su,ni tunani na ma kada Yaya Bilal ya zargeni akan hakan kinga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login