Showing 12001 words to 15000 words out of 103202 words
ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[23/09, 16:16] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
*GAWURTATTU 5*
---------------------
masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.
SIRRINMU👂🏻*
Manzon Allah (s.A.W)ya yi mana jan kunne ga idan zamuyi magana mufaɗe da tausashen harshe,idan kuma ba zaka iya hakan ba to ka yi shiru ko,faɗi alkhairi ko ka yi shiru🤫
-------
Team
*GAWURTATTU 5*
11🟩12
. . . .rarrashinsu Baba na kawai malaman ke yi don sun san wannan wani maudu'u'i ne na daban,babu wani mutum da zaiso ƴaƴan da ya haifa na cikinsa su zamo suna da irin wannan halin na neman mata ba tare daya shiga wani hali ba,duk zuciyoyinsu sam babu daɗi.
Bai san sanda ya cire belt ɗinsa ya hau jibgarsu ba,zuciyarsa kamar za ta fito saboda zafi,wai yau ƙannensa ne acikin wannan halin?ai kuwa rufe idanuwansa ya yi yana ta jibgarsu malaman na ta bashi haƙuri amman ko ta kansu ma bai bi ba,duk wanda kuma ya yi gangancin saka hannunsa wajen cetonsu to fa dashi za'a haɗa,har ita big girl ɗin da sauran muƙarrabanta duk ya haɗesu ya jigba,su Baba kuwa suna gefe basu da niyyar hanashi,sai da ya jibga don kansa sannan ya barsu.
a ranar muka koma gida dukanmu,ni dai jikina haryanzu bai daina ciwo ba,alokacin da muka shigo cikin gidan na hango Hajiya kaka suj fito ita da Hajiya Inna ƙawarta kuma aminiyarta da alama ma unguwa zasu je.
Muna fitowa daga cikij motar kowa da guntun ciwonsa ajikinsa Rashida ce kawai babu ciwo,da sauri naga Hajiya kaka ta yi gefe tana salati kamar ta ga abin tsoro.
Bata iya magana ba har muka ƙaraso kowannenmu yana tangaɗi kamar zai faɗi,Hajiya kaka ta ce"ikon Allah sai kallo wannan wani irin dukane haka duk jikinku ya toye kamar an ƙona ku?ni dai yau naga abinda ya isheni". ta ɗora hannunta aka xa ta saka kuka Hajiya Inna ta ce"haba Hajiyata mu fasa tafiyarnan kawai yau dai gidannan ba lafiya ba"?.da sauri Hajiya kaka ta ce"yo ina kuwa lafiya jikokina duk an farfasa musu jikkunansu wallahi idan ma malamanne sukayi musu dukan ƙatti to wallahi aikinsu ya ƙare a nigeria,Allah da a ƙasar umanne da tuni sai dai wasu da tuni sunsha harbi".ita dai Hajiya Inna jan hannun aminiyarta ta tayi don tasan halinta yanzu sai ta tsaya tayi ta sunbatu kuma ba tare da ta tambayi ba'asi ba ta ɗorawa wani laifi.
Kai tsaye ɓangaren Hajiya kaka mukayi dukkanmu bayan mun zauna sai ga ta kamar an jeho ta ta ce"to wallahi Allah bazamu yarda da fasawa jikokina jiki ba,an gaya musu tsintosu mukayi ko kuwa?to wallahi ahir ɗinsu".dukkansu sunkuyar da kansu sukayi musamman ma waɗanda suka san sunyi laifin su Nadiya kenan,duk bakunansu a kumbure wasu kuma idanuwansu.
"Ikon Allah ku kuma me ye na wani sunkuyar da kai kamar munafukai?".babu wanda ya amsa mata acikinsu Yaya Bilal daya gama harzuƙa musamman kalaman kaka ya ce"loook Hajiya kaka ba abinda ki ke tunani bane?waɗannan yaran ni da kaina na yi musu wannan dukan"?.da sauri Hajiya kakanta juyo tana kallon Bilal kamar dai yaune ta fara ganinsa.
Fashewa ta yi da kuka ta ce"to wallahi Allah Ya isansu mugu mai jinin fulani,mai Ƙirar samu dawa kawai wato abin ma mugunta ne ko?ai gashi ka daki waƊannan amman baka daki waccen Ƴar jakar ubarba mai Ƙira irin ta ka".ta nuna Rashida ita kuwa ta murguƊa mata baki".kaka ta harzuƘa za ta Ƙara magana Baba na ya dakatar da kaka wajen ce wa"umma waƊannan yaran sun zubar mana da mutuncinmu a gari,waƊannan yaran da ki ke ganinsu Ƴan neman mata ne".
Hajiya kaka bata fuskanci abinda baba ya faƊa ba ta ce"a'ah malik to idan basuyi abota da mata ba to daku zasuyi?"Ganin kaka bata fuskanci abinda suke nufi ba yaya Bilal ya daka musu tsawa ya ce"i'm talking to u ku faɗa mata abinda kukayi ko kuma yanzu in ƙara yi muku wata sabuwar tafkar".ana cikin hakan iyayensu mata suka shigo su dukansu saboda an gaya musu abinda ke faruwa.
Suka zazzauna kowaccensu ji take kamar ta haɗiye zuciya ta mutu saboda an daki ƴar ta,kuma zuwansu ya yi dai dai da fara bada labarin tun kaisu makaranta har zuwa iyanzu da sukayi abinda sukayi.
Sosai iyayensu suka fara salati masu kuka na yi masu zagin ƴaƴansu suma sunayi,amman mama kishiyar mama da sauri cikin kuka ta ce"wallahi wannan ƙarya akewa su Nadiya idan hakanne me yasa su waɗance munafukan ba'a dakesu ba aka fake da dukan waɗannan tunda sune marasa galihu".wata uwar harara baba na ya bita dashi sannan ya ce"wallahi idan kika ƙara magana awajennan to abakin aurenki".yana faɗin hakan ya juyawarsa kamar ba shine ya yi maganar ba.
Sosai abin ya ƙular da mama ta cigaba da kukanta wai yanzu akan wannan shaiɗaniyar yarinyar aka kuburawa ƴarta idanu har haka.
Jagwab kaka ta zauna kamar zaman ƴan bori ta ce"yau na shiga ɗaka ban fito ba,me zan gani haka acikin jikokina aka samu waɗannan masu halin mutanen annnabi luɗu?ya Allah idan mafarki na ke Allah yasa in farka."
"kaka wannan maganar fa ta zama dole ayi meeting akanta,insha Allah yanxu kowa zai tashi ya je ya huta gobe za'ayi meeting insha Allah".cewar Baba Abdullahi mahaifin yaya Bilal.
Kaka ta ce"Allah sarki ABIN CIKIN ƘWAI,so sukayi su lalata miki rayuwarki amman Allah ya fisu Allah kuma ba azzalumin bawansa bane,ni duk da haka ma sai na kaiki asibiti inji ko sun taɓa miki rayuwarki masu rayuwar dabbobi kawai".tana faɗar hakan ta ja hannuna muka shiga ƙuryarta kunya duk ta isheni wai za ta saka a dubanu gasu Baba duk a wajen.
dukkansu suka tashi jikinsu duk a sanyaye Hajiya Inna ta shigo ta kalleni ta ce"oh sannu ƴar nan Allah yabi miki haƙƙinki,Allah kuma ya shiryar dasu gaskiya,don wannan sam ba halin ƴan mutunci bane,wannan halin ƴan akuya ne."
caraf kaka ta amshe tana ƙwalla ta ce"ni fa abin nan ya bani mamaki wallahi yo me ye abin so ajikin mace da mace idan ba rashin mutunci ba?ni fa anya ma kuwa waɗannan yaran basu shaye shaye?na ga abin na su ya zarce hankali sun kama ƴar uwarsu sun ciccijeta haka kamar ƴaƴan mayu?Allah badon jikokina bane wallahi da sai igiya ta yi saura don bazan yarda ba,idan ita waccar sokuwar inyamurar uwar ta ki ta yi shiru to ni wallahi ba zan yarda ba don ni ba sallamammiya ba ce".
haƙuri Hajiya kaka ta fara ba ta ta ce"ki yi haƙuri waɗannan yaran addu'a zamuyi ta yi musu Allah ya shiryesu,kuma daman inason in gaya miki kada ki yadda ƴaƴanki su mayar da yarannan makaranta don ƙara lalacewa zasuyi,kuma sannan su fito da miji ayi musu aure ko hankalin kowa ya huta".
da sauri kaka ta ce"kai Inna gaskiya ƙwaƙwakwarki tana ja wallahi,ke daman tun muna yara kina da ja,su Hansai basuyi asarar kuɗin tara ba".dariya Hajiya Inna ta yi sannan ta ce"to ai kinga gwara ayi musu auren kowa ya huta,ko kuma ma idan sukace muku basu da mazajen auren ga ƴan uwansu maza nan sun cika gida taf sai a harhaɗasu kawai kowa ya huta."
Sosai kaka ta yi murna da shawarar ƙawatarta Hajiya Inna,suka cigaba da tsara abubuwansu ni kuma na fito waje don tafiya sashenmu ƙafata ta yi tsami sosai jan ƙafar kawai na ke,ƙamshin turaren yaya Bilal naji naji wani irin mugun shauƙi har cikin raina ban ankara ba na ji an bangajeni an wuce na buɗe idanuwa da ƙer,Yaya Bilal ya wuce ko kallon inda na ke baiyi ba ballanta na ma in saka ran zaiyi min magana,wasu zafafan hawaye ne suka fara ƙwaranyo min,son maso wani ƙoshin wahala tun ina ƙarama ta na ke dakon son yaya Bilal har girma na amman shi ko ajikinsa idan ya ganni ma yadda kasan yaga kashi haka ya ke nunawa.
Allah ya yiwa yaya Bilal halitta mai ƙyau da tsari kaf ƴan gidanmu babu wanda ya kai koda ƙwatansa a komai,ga ilimi,addini,ƙyau,kuɗi,nasaba.duk ta haɗa waɗannan abubuwan duk jikokun gidanmu farare ne yawancinsu amman ni ba fara ba ce,amman kuma baza'a kirani da baƙa cen ba,ina da ƙira mai ƙyau kuma ina da ƙyau dai dai gwargwado,ina da ilimi,tarbiyya,nasaba,da sauransu.
Ina cikin wannan tunanin na shiga sashenmu kai tsaye na wuce sashen baccinmu daman kowa da ɗakin baccinsa amman yau ina shiga naga Nadiya a ɗakin baccina ta fito daga ita sai tawul ta fito daga banɗaki tana jan ƙafarta da ƙer wata uwar harara ta bugamin sannan ta fita daga ɗakin ban kula taba na shige ɗakina na ƙwanta a hankali duk jikina yana yimin wani irin mugun ciwo wasu zafafan hawaye suka zubomin tuno da abinda ya faru dani.
Ina cikin wannan halin mama ta shigo ɗakin ta ce"a'ah khairat daman kina nan?ina ta tunanin shiga ɗakin kaka ashe kin shigo?tashi muje yayanki Bilal ya kirawo dr xai duba lafiyarki."har zuciyata na ji wani irin sanyi mai daɗi wai yaya Bilal ya kirawo likita?to ko dai shima ya fara sonane ban sani ba?ina cikin tunanin mama ta ƙarayimin magana na tashi na fita Yaya Bilak na hango ya wani kame a kujera ya yi ƙyau a cikin jallabiyarsa ƴar asalin larabawa,wata irin kunya ce ta baibaye ko ina na jikina a hankali na isa wajen na gaishesu amman Yaya Bilal ko kallo na baiyi ba.naji babu ɗadi a raina amman ban nuna hakan ko a fuska ba.
Allura ya ce zaiyi min ta kashe zafin ciwo,rau rau na yi da idanuwa kamar zanyi kuka naƙi in tsaya ayimin wata uwar tsawa yaya Bilal ya yi min jikina yana kakkarwa na tsaya akayimin ina kuka.tsaki naji yaja sannan ya yi ficewarsa tare da ce wa"dr maher ka sameni a waje".da to ya amsa likitan ya kalleni sosai ya ce"sannu crazy girl".ban amsa masa ba na cigaba da matsar ƙwalla ta,ya ajjemin magungunan da kuma allurar da ba'a gama min ba.mama ta yi masa godiya ya tafi.
Mama ta ruƙo hannuwa a hankali muka fara tafiya sai ga Hajiya kishiyar mama ta fito daga kitchen ta ce"hmm ayi dai duk a gama wai ke uwarki ta koya miki munafunci ko?to duk kuyi a sannu in dai munafurci ne na iya shi har na dameku ba dai ƴaƴanmu kika ɓatawa suna ba?hmm kijira na ki ɓatancin don kare ma bazai shinshina ba,shegiya ƴar inyamurai kawa".tana faɗar hakan ta yi shigewarta ta barmu anan tsaye tunani ya cika zuciyoyinmu,muka haɗa idanu da mama na bata ce komai ba ta kaini har ɗakina sannan ta bani magani ta tafi.
"Ƴar halak yanzu na je tunaninki?".dariya Rashida ta yi sannan ta ce"Allah sarki Khairat ya jikin na ki?".ɗan murmushi na yi wanda yafi kuka ciwo na ce"da sauƙi Rashida".
"Hmm gaskiya Khairat idan da zaki yarda da kin koma ɓangarenmu sai mu dinga ƙwana tare don ban yarda da zamanki a ɗaki ke kaɗai ba,ni fa waɗannan munafukan har yanzu ban yadda dasu ba,don wallahi zasu iya aikin tumasancinsu a gidannan don haka ni zanje in samu mama in faɗa mata komai".
Ruƙo hannunta na yi na ce"kada kije Rashida kin san halin mama da gudun zuciya ba za ta taɓa yadda ba,don haka ki barta kawai Allah zai kareni daga sharrinsu".taɓe baki Rashida ta yi ta ce"to ni yanzu me zance Allah dai ya tsareki daga sharrinsu".nan muka cigaba da hirarmu.
****
Washe gari da safe har ɗaki mama ta kawomin abin kari bakina ya kumbura sosai ta ce"Khairat kafin kici abincin nan sai na gasa miki bakinnan don ya kumbura sosai".mama da kanta ta gasa min bakin muna cikin wannan halin naji muryar hajiya kaka tana ta tujara a babban farlonmu,na kalli mama itama ta kalleni sannan ta ce"kaka ce ki fita ku gaisa".ina shirin tashi sai ga tabta shigo ta ce"wayyo Allah na me zan gani Khairat?kai amman waɗannan yara sun cika marasa mutunci,shiyasa yanzu ina shigowa waccen munafukar ta taho wai za ta gaisheni ko kallon iskarta ma banyi ba na yi tahowa ta,shegiya sadakar yalla".
tana ta sababinta bance mata ƙala ba mama ma bata komai ba sai kuwa kaka ta ce"hmm ai ke Khairat sallamammiyar uwa kika samu tunda duk abinda za'ayi miki sai dai ta yi shiru ta yi zugudum kamar buhun lalle".ta harai mama da sauri mama ta fita don zamanta awajen ba alkhairi zai janyo ba don haka ta fita don tsahon shekarun da ta yi da kaka tasan halinta tsaf.
"Ke ba fa zaki zauna a wannan sallamamman sashen na ku ba,ɓangarena zaki koma don na ga aƙwai masu halin awakai a gidanku,don haka ki tashi yanzu yanzu ba sai anjima ba mu tafi don bazan lamunci halin masu laluben mata ƴan uwansu ba,kada Allah ya turo mala'ikunsa su rushe mana gidan duka tunda saɓon Allah ake a gidan".
kallon kaka na yi rau rau da idanu na ce"a'ah ni dai kaka babu inda zanje wannan sashen na ki mutum yaje ki yi ta yimai masifa abu kaɗan ki zageni".galala Hajiya kaka ta yi tana kallon Khairat ta ce"eh lalla ai barewa ba tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba eh halin Malik ki ka yi tsaf na taurin kai to wallahi ko zaki yi kashin jini yasin sai kin bini sallamammiya kawai".tana faɗar hakan ta fito.
A farlo suka haɗu da Nadiya da iman suna kallo a tv da sauri kaka ta murza idanuwanta ta ce"yo ikon Allah khairatu zo ki ganemin waɗannan masu halin mutanen annabi luɗi sunyi rashe rashe suna kallo,ko uban waye ya basu damar zama suna kallo?su da sukayi wannan mummunan laifi".
Da sauri su Nadiya suka kalli kaka sukayi wuƙi wuƙi da idanuwansu,don sun san kakarsu aƙwai tonon asiri suka haɗa baki wajen ce wa"hajiya kaka ina wuni".zaro idanu kaka ta yi sannan ta ce"oh ni ina ganin rashin hankali a gidannan ke Nadiya don ubanki sadakar yalla ce ta raɗamin wannan sunan Hajiya?ke kuma imani fulanin daji ce ta raɗamin ko kuwa?".da sauri suka haɗa idanu don mamakin zagin da kaka ta yi musu,ganin mamakin zagin da ta yi musu suke ta ce"to wannan kallon da kuke min munafukai nima ƙwaƙwuleni zakuyi?kamar yadda kuka yi wa ƴar uwarku khairat?to wallahi ahir ɗinku don ni na fi ƙarfin maitarku,kuma bari Malik ɗin ya dawo duk sai an kori masu aikin gidannan ku koma masu yi mana aiki,tunda rashin aikin yi ne yasa kuke saƙule ƴaƴan mutane".
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*miss green ce*
[23/09, 16:17] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------
*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------
masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.
*Sirrinmu*
mata mu kasance masu tsafta,ladabi,biyayya,haƙuri,juriya.domin shi namiji ba ta ƙarfi ake samunsa ta lallami da lumana.Allah yasa mu dace amin.
----------------------------------
15⬜16
. . . .Ina ƙwance duk abin duniya ya isheni tun jiya Yaya Bilal ya i'so gidan amman tsoron fita na ke don bana son abinda zai janyo mana tashin hankali dashi don matuƙar yazo to fa tabbas sai an ɗebi ƴan kallo,shi yasa ma na rufawa kaina asiri na yi zamana a ɗakin,ina jin tafiyar mama ta taho na yi saurin lulluɓa da bargon don bana son ta aikeni gun kaka don yau ita ce da girki.
"Khairat!Khairat!! Mama ta fara tashi na, na buɗe idanuwa na gaisheta sannan ta ce"kalli garin mana rana ta fito sosai amman kina cikin ɗaki kina bacci?yanxu Khairat kin lalace da bacci wallahi da tun kafin in tashi zaki shiga kitchen ki girkamin abinci?amman yanzu sai na tashi da kaina na yi sannan kuma ki ƙi tashi da wuri?ni dai gidan miji na ke jiye miki don wannan salon da ki ka ɗauka ba mai ɓullewa ba ne?yanzu ki tashi ki kaiwa kaka abinci don ya zama ready".tana faɗar hakan ta fita nasan halin mama ba ta san jira don haka na tashi da sauri na shiga ba yi na yi brush sannan na wanke fuskata,daman na yi sallah tun asuba gabana yana ta faɗuwa don bana son na haɗu da Yaya B,don nasan ko ban kulasa ba dole ne na yi laifi,don idan na gaishesa ma ba ya amsawa ko kallon inuwa ta bayayi,ni na rasa wannan wacce irin tsana ce haka?.
ina fitowa farlon na iske Amira ƙanwar su iman tana homework,da murmushinta ta juyo ta ce"la Anty daman ke na ke jira ki tashi wallahi".murmushi na yi mata sannan na ce"to little sis me kuma ya faru?".shagwaɓe fuska ta yi sannan ta ce"assignment aka bani kuma wallahi na kasa yi guda 3,ne na yi ɗaya sauran ban iya ba,kuma na bawa su Anty iman sunce wai baza su iya ba aikin na da wahala"?.
"To Meeraty bari dai yanzu in kaiwa Kaka abinci in dawo sai in yi miki kinji?"da to ta amsamin ni kuma na wuce don kai aiken kaka.inason Amira don kaf cikin ƴan uwanta ta fita zakka ita kaɗai ce take sona acikinsu sauran duk sunbi layin iyayensu mata.
Tun daga ne sa na ke jiyo ƙamshin turarensa gabana yana ta faɗuwa na tsaya cak sai da na karanta