Showing 18001 words to 21000 words out of 162126 words
bata qananen kudade bace,sumar kanshi cike take kuma akwance luf ba tsayayya tamu irin ta hausawa ba,tafi kama data jaruman fina finan india ko larabawa,sai abunda ke saqale bayan kunnenshi guda daya wanda take gani gurin masu aikin tsaro,saidai wannan mai azabar kyau ne haka nan shima baqi ne
har suka kammala wucewa tana tsaye a gun,ita kanta batasan me ya tsaida ta din ba,sai daga bisani ta saki ajiyar zuciya hade da sakin labulen ta koma ciki ta lalubo hijabinta ta zura ta tayar da sallah don wasu guraren har sun idar
mami na tsaye qofar sashenta harde da hannayenta,duk yawan 'yan rakiyar abdallah bai hanata gano yaron nata ba,yayin da murmushin farin ciki yaqi bacewa fuskarta,daga hannun hagun falon kuma haj nene ce tsaye ita da zahariyya,idonsu tsaye car kan abdallah da zubaida wadda a yanzu ta bar bin bayanshi ta nufo inda suke tsaye
zahariyya ce ta tabe baki''don Allah nene dubeta,aikin banza shegiyar yarinya kawai mahaukaciya,wai har wani murna take da dawowar abdallah,don Allah ki barni da ita nene wallahi sai na gyara zamanta''
dafa kafadar zahariyyan tayi tana wani murmushi da na kasa fassara shi''um...um,kinga matsalarki kenan zahariyya gaggawa,idan bakiti wasa ba zaki bata mana plan,ki bar zubaida tayi yadda take so loka ci ne fa,kuma ke kanki kinsan nasan me nake yi koοΌ''
''to amma nene wallahi idan ba muyi taka tsantsan ba zata zame mana matsala''
''ita din ubanta,ni na haifeta ko ita ta haifeni,ki rabu da ita dai a yanzu,akwai lokaci kamar yadda na gaya miki''
''ko tazo kada ki mata maganar''nenen ta fada da sauri ganin zubaidar ta kusa cimmasu,dama mutanen dake falin ne suka hanata isowa da wuri
har isha'i maryam na jiyo sauran hayaniyar jama'a,don haka tana idar da sallar isha'in tayi rigingine abunta bisa gado,kusan goma saura tunanin mamanta ya fado mata,layin hindatu ta shiga nema saboda muryan maman da takeson ji,saidai tayi rashin sa'a is switched off,tsaki taja cikin rashin jin dadi a ranta tana raya cewa da ta dauki albashinta na farko cikin abunda zata yi harda siyawa maman ta waya sabuwa da kuma power bank mai aiki da hasken rana
tana tsaka da tunane tunanen nata taji an turo qofar dakin,mami ce wannan karon cikin kwalliyar atamfa super mai kalan blue maidan turuwa,abunka da fara sai tayi tas
''a'ah maryamu kwanciya akayiοΌ''
''eh wallahi mami''ta amsa mata tana mai miqrwa daga kwanciyar da tayi tana maida daurin dankwalinta da ya zame
''a'ah,yi kwamciyarki abinki,ai kinsha aiki bsna tasheki ba''
tana saka slipper dinta dake bakin gado wanda mami ta bata take amfani da shi tsakanin edroom din zuwa parlour zuwa kitchen
''ba komai mami me kije buqata''
tana shirin amsa mata wayarta ta dau ringing
ta kara a kunnenta kai tsaye tace
''ya akayi abdallah''
cikin kwantar da murya yace
''mami yunwa nakeji,wayyo cikina mami''
dariya tayi
''kajimin shi don Allah,yaron goye ne kai,ka soma ci gani nan fitowa na shigo in taho da maryam ne don muci abincin tunda tare muke ci bayan baka''
''wace hakaοΌ''
''sabuwar mai girki kuma diyata''
''ayyah mami,ayyah....,nikam nasan kin rage ji da ni,banda haka daga dawowata mami yau inason musha hirarmu mu biyu kuma saiki yo gayya,nidai mami ki taho ke daya abinki kamar yadda muka saba ko inzo in taho dake''
''naji ya isa sarkin qorafi,kada ka shigo mana daki gani nan fitowa''
''thank you my mammy,ki sauri na qagu ki fito''
dariya ma ya bata,abdallah kenan,ko yaushe idan yana gabanta daukan kanshi yake kamar qaramin yaro
sai da ta dan kalli maryam ta gefan ido dake zaune gefan gado kanta a qasa tana fatan bata ji ba,ta riga da taji amma sai ta nuna kanar bata ji din ba saboda bata ji komai a ranta ba don itama batason ta shiga tsakanin wannan uwa da dan masu azabar shaquwa
''kinci abincinki e maryam''
''sai anjima,amma dai na shigo da shi''
''to shikenan ki kwanta ki huta,Allah ya huta gajiya,sai gobe idan Allah ya kaimu''
''to mami''
har ta kusa ficewa maryam din tace
''a cewa ya Abdallah ina masa barka da zuwa''
murmushi mamin ta saki don har cikin ranta taji dadin kulawar da maryam din ta nuna kan tsoka daya a miyanta
''zaiji insha Allah''
ta fice bayan ta ja mata qofar
kayanta ta cire ta sauya na bacci ta ja abincinta ta danci sannan ta kwanta baki daya
Qarfe takwas a kitchen tayi mata,tana cikin hade haden abinda zata tanadar musu na bre fast taji an shigo kitchen da sallama,ta waiwayo tana amsawa,mace ce wadda a qiyasce zata doshi shekaru hamsin,ta qaraso kusa da maryam,a ladabce maryam din ta gaidata,itama ta amsa mata cikin fara'a sannan ta dora da cewa,ni suna na uwani,ma'aikaciyar haj bintu ce,naje hutu na ne da take bani na shekara sai yau na dawo,kin ganni da wuri koοΌ,qauyen mu ba mai nisa bane shi yasa na fito dacwuri gasji Allah ysa na iso da wuri,ni daga qauyen sumaila nake''
murmushi maryam tayi jin cewa suna da maqwaftaka da qauyukansu
''sannu baaba,ni kuma suna na maryam sabuwar ma'aikaciyar data dauka ce saboda kula da girkin yaronta,ni a cikin gari nake saidai asakin mu yan qauyen gaya ne''
cikin jimami da 'yar fara'a tace''Allah sarki kice maqota ne mu,kingawadancan ma'aikatan hajiyan maha'inta ne,da su aka hada baki aka zubawa yaron nan guba wallahi,Allah ne yayi da sauran shan ruwansa a gaba,don Allah mero ki riqe amanar hajiya saboda mutuniyar kirki ce''
dariya baba uwani ta bata jin ta ambaceta da mero
''insha Allahu baba,Allah ya bamu ikon riqe amana''hira baban ta shiga zubawa maryam tana maida mata labarin yadda lamarin ya auku,taso ta karbi wani abin ta taya maryam din amma ta qiya don hirar ma kadai da take mata tana debe mata kewa da sata jin qwarin gwiwar aikin,da haka har ta kammala hada fried plaitain with sauce,ta dafa tea da ya wadatu da kayan qamshi lemon grass,kimba da ginger,ta jada da coconut flour pancakes saboda tea din
da yake ba mai yawa tayi ba duka kadan kadan ne daidaisu hakan ne ya bata damar kammalawa da wuri,ta zubawa bab uwani tana ci tana santi maryam na dariya,cikin haka mami ta shigo suka gaisa itama ta shiga dariyar santin da baaba uwani take bayan ta yi mata sannu da isowa,itama tayi mata barka da dawowar abdallah gida,mami tace ta bar baaba uwani ta gyara kitchen din ta wanke kwanukan don dama aikinta ne
cikin kitchen din ta barsu ta shiga dakinta ta gyarashi kana ta shige wanka bayan ta wadati shi da freshner,koda ta fito karyawa tayi ta kuma kwanciya,babu dadewa kuwa bacci ya sureta,sai sha biyu da rabi ta farka,agogo ta duba da hanzari ta shiga toilet ta wanke bakinta da fuskarta ta zura hijabinta dan zuwa saman mamin ta tambayeta a dora girkin rana ne
*mrs muhammad ce*π
ππππβπ»βπ»βπ»
[9/17, 12:51 PM] 80k: πππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ *ABADAN*πΊπΊ
πππππππ
πΊππΊππΊ
πΊππΊπ
πΊππΊ
πΊπ
π
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πππππππ
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊππΊ
ππΊππΊππΊ
ππΊππΊπ
ππΊππΊ
πΊππΊ
πΊπ
πΊ
βΆ1β£5β£
A qofar falon ta tsaya tayi knocking,daga can ciki taji mamin na tambayar wane,ta amsa mata sannan ta mata izinin ta shigo
A bedroom ta tarad da ita tana gyaran wadrob dinta
''sannu da aiki mami''
''yauwa maryam,sannu''
''mami ai da kin kirani na miki aikin''
''haba,kina bacci maryam ya zan tada ke''
''mami dama cewa nayi me za'a dora,naga rana tana ta yi''
tana zuba wasu kayan cikin sif din tace
''indai don ta Abdallah ne rabu da shi,don ko breal fast din ma baici ba,yana can yana yawon bacci,na yi da shi ua tashi ma ko laruawar ne yayi ya koma kinga yaqi,baqi sai ziwa suke masa sannu da dawowa amma kinga yaqi fitowa wai ramuwar bacci yake,saidai kawai ki dan dafa wani abun ba mai hawa ba saboda ke da baba uwani,ga baqi kuma don nasan yau ba za'a rasa baqi ba''
''to,mami''ta amsa tana shirin juyawa ta fice
''tsaya ki dan taya ni hira,ai yayi wuri a dora shi yanzu mamin ta dakatar da ita tana murmushi
kadan kadan suke hirar tasu har soma taya mamin aikin,tana shirya kayan ta miqa mata ita kuma ta zuba acikin drower din
Bata shirya kallon qofar dakin ba amma tilas tayi hakan,sallama akayi cikin wata murya mai cike da dadi da kwarjini wadda ke bayyana cikar haiba da halittar mamallakinta,second daya da yin sallamar qamshi ya baibaye dakin gadon mamin duk da cewa an dan turo qofar ne kadan an kuma boye a bayan qofar daga waje ba'a kai ga shigowa ba
hannun wanda ya bude qofar mai daure da agogon rolex ne kawai da barin jikinsa zaka hango
''mami na shigo ko na komaοΌ''
''taya zance abdallah ka koma,bismallah qaraso''ta bashi amsa tana kallon qofar fuskarta qunshe da murmushi
ya qarasa turo qofar a hankali ya bada wata 'yar qara kadan,ya sako farar qafarsa mai dauke da zara zaran yatsuda maau qunshe da gargasa saman kowannensu,sanye yake da shadda fara qal babbar riga da 'yar ciki da wandonta,baqar hula ce zanna ahannunsa wanda da alama yana tafe ne yana mata kari bai qara sa ba ya iso dakin,fuska cike da qayataccen murmushi yake fadin
''nayi zaton kinyi fishi saboda banyi break ba''
''banyi fushi ba amma banji dadi ba''
''Allah ya bako yawan rai mami na,nima banso nayi missing daddadane n break fast ba,saboda na tabbata zaiyi dadi kamar abincin jiya''
''to ai ga mai girkin nan,sai ka mata sannu''ta fada tana nuna maryam wadda ke,daskare gu guda,kallo daya ta masa ta kasa yin na biyu,ba don komai ba sai wani kwarjini da cika ido da taga yayi mata,duk kyawun mami da take gani aahe nafila ne,wannan tabbas idan da mace ne saidai a hanata fita zuwa ko ina saboda fitar ba qaramin hadari bace tattare da ita da ssauran mutane
ya dan dubeta a fisge atill,kanta na duqe yace
''sannu fa''
ba tare da ta dago ba tace
''ina wuniοΌ''
''lafiya''
ya amsa yana diban mami
''uhm,sai ina kuma''
yana ci gaba da karin hularsa yace
''masallaci mami,kin manta yau juma'a''
''haka ne,ka ci wani babban riga kamar gaske''
''kamar ranar daurin aure na ko mami''ya fada yana qarasawa bakin mirror yana dai daita hular a kanshi
''gafara can,mutumin da ya kasa fidda mace shike zancan ranar aurenshi,kaci gaba dai da zama a tuzurunka har a rasa mai aurenka''
murmushi ya fidda mai dan sauti ya dukin turaten mamin yana sake fesawa
''haba mami,ba irinmu kerasa macen aire ba ko shekara sittin sukayi a duniya,ki kwantar da hankalinki ina nan ina duba miki,kinsan sai na zaba na darje''
''garin ruwan ido kuma fa...''
da sauri ya tare ta
''wayyo mami....yi shiru don Allah,you will be suprise in sha Allah''
''hmmm,Allah yasa....maryam ina zuwaοΌ''ta tambaheta ganin ta miqe
''zanje ne na dora girkin mami''
''abdallah maka lunch neοΌ''
''kai kuci kayanku kawai mami ni zan wuce gidan baffa mu gaisa''
''to yayi kyau,ka gaishe min su da kyau,muje maryam nima saukar zanyi,kada a shigo a yita nema na''
tare suka sauko dukansu abdallah na gaba,mami na bayansa maryam na binsu a baya
''banza a banza kawai,maras kunyar qarya,gidan da kike taqama da shi ina cewa 'yar karo ce ke''
surutan wata matashiya kenan lokacin da take shigowa falon,matashiya ce 'yar zamani wadda shigarta kadai ta isa nuna maka hakan,sanye take da fitted gown wadda tabi lafiyar jikinta,kanta daure da roses sai swagger dinta mai sarqa rataye a kafadarta,takalmin qafarta kuwa kai kace sama take shirin tabowa saboda tsininsa,fuskarta tasha fente fenten kwalliyar zamani
''a'ah salma,ke da wa kuma,hali zanen dutse''inji mami da ta tsaya tana kallonta
''ni da waccar agolan gidan taku mana,duk randa nazo gidan nan sai ta nemi raina min hankali,wallahi abdallah ka ja mata kunne ni ba sa'arta bace,ni na hana ka sota da zata dinga neman huce haushinta akaina,ina ruwan biri da gada,nafsi nafsi kawai''
kafadunshi ya daga yana ware hannayenshiπ€·π»ββ
''ina ruwan abdallah ya taku,kina da baki kema fa''ya fada cikin ko in kula
ta yamutse fuska
''baka fa da kirki wani lokacin wallahi,watsamin to qasa a ido,mami kina jinsa ko''
murmushi tayi
''bismillahi Allah,ai kun fara kuma kenan''
ya dubi mama
''manta da ita mami,ni zan wuce masallaci''
''ni matsalata da kai waqanci wlh,ka sani fa sarai saboda kai na zo,shine zaka wani fita''ta fadi mishi tana kallonshi bayan ta zauna tana sabule cogen qafafunta
''sai na fasa sallar juma'a saboda sarauniyar matan duniya ta zo''ya fada yana yin gaba abinsa
''a'a,ni bance ba amma sai yaushe zaka dawoοΌ''
''qarfe biyar,bit ban tabbas ina iya wuce hakan,idan zaki iya jira na fine''
''ina jira sai ka dawo''
ba tare da ya amsata ba ya qarasa ficewa
maryam na kichen take jiyo su
tunda ta shiga kitchen din bata fito ba sai da ta kammala girkin,lokacin da ya fito mami bata falon sai baquwar da taji an kira salma dake kwance dai dai kan three sitter,kanta ta dago tabi maryam da kallo,hada idon da sukayi bak sata dauke idonta ba
''sannu maryam,kada dai ace har kin kammalaοΌ''
inji mami dake saukowa daga saman bene
''eh na gama mami''ta amsa mata bayan ta tsagaita daha tafiyar da takeyi
''sannunki''ta amsa mata sannan ta juya don shigewa dakinta,tana jiyota tana tambayar mamin wace itaοΌsaidai bata ji amsar da mamin ta bata ba
kiran da mamin ta yi mata ne ya sake fito da ita tun bayan shigarta dakin wanda wanka kawai taui ta saiya kayanta tayi salla,biyi taga 'yan matam sun zama,saidai iya wannan sanhe take da riga da wando wadanda suka bayuana surarta,inda Allah ya taqaita siririya ce sosai,
tadan dauke kanta zuwa sashen da mamin ke zaune
''gani mami''
''yauwa maryam,baki fito kinci abincinki ba,ga baqi yau agodan amma kin zauna a daki''
''mami na qoshi ne sai anjima''
''to zauna muyo hira,bana son kina zaman dakin nan ke daya,na gaya miki nafison ki dinga jin a ranki ke diya ta ce,wannan sunanta salma 'yar qanwata ce,waccan kuma sunanta saddiqa ita kuma 'yar yaya na ce,dukansu sunzo yoma abdallah sannu da zuwa''
''sannunku''ta fada cikin sassanyar muryarta
amsawar ganin dama suka mata tamkar wadanda aka tilasta,wanda hakan sam bai,mata dadi ba,har taji zamansun ma guri daya babu marching,don sam bata son wulaqanci,maca ce ita mai karamci shi yasa ako yaushe take tsammanin karamci daga gurin duk wanda zata mu'amaleshi
''am...mami da wai kitchen zan koma in dora abincin dare''
''baki gajiya maryam,a qa'ida ai kin gama girkinki na yau tunda sau biyu ne a rana ko''
kanta na aqasa tayi murmushi
''ba aikinta kenan ba,ki barta mana mami''inji saddiqa wadda ta dora qafa daya kan daya tana danne danne waya da bai wuce tana charting ne
''ba komai mami,ai ba wani qa'ida tsakanin mu,kuma ko ba haka bama ai kinga baqi aka yi,kuma aikin ya abdallah nake,tunda aikinsa nake kinga ba laifi na giwa wadanda suka zo gunshi abinci''
sosai ta burge mamin,tana son mutum mai sauqin kai,wanda ta fuskanci halin maryam ne
yayin da salma da,saddiqa suka dago kai suka kalleta,salma ta kasa shiru
''hmmmm,lallaikam,dadin abun ma biyanka ake ba''
sai abun ya bawa maryam din mamaki,to meye kuma hadin kaska da kifi,me haka kuma,me tayi mata,gaza bawa kanta amsa taui don ita dai yasan yau ta fara ganin salma,babu kuma abunda ya hadata da su balle tace ko ta mata wani abun ne
''salma,bana so fa irin wadan nan halayyar naki kin sani sarai ko''mami ta fada cikin dan hade gira
''yi haquri mami,nima ba wani abu nake nufi ba''
''jeki maryam ki hutar da kanki kiyi iya cikin abdallah kawai,shima din kiyi simple kada ki dauka da wuya''
''to''
ta gada sanna ta miqe ta shige kitchen dinmami ta nita da kallo,yanayin yarinyar na burgeta,sanyi sauqin kai da kawaic yakanah da danne abu cikin rai
*mrs muhammad ce*π
πππβπ»βπ»βπ»
[9/17, 12:51 PM] 80k: πππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ *ABADAN*πΊπΊ
πππππππ
πΊππΊππΊ
πΊππΊπ
πΊππΊ
πΊπ
π
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πππππππ
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊππΊ
ππΊππΊππΊ
ππΊππΊπ
ππΊππΊ
πΊππΊ
πΊπ
πΊ
βΆ1β£6β£
jallop din couse couse ta hada mishi wadda ta wadata da carrot grean beans da piece,sai qoda da hanta a madadin nama,qamshin curry da tyme kadai ke tashi a ciki,yayi shar gwanin sha'awa,sannan ta hada banana apple anda strawberry juice,baaba uwani ta barwa gyaran gun ta wuce ta shirya dining,duk suna zube a falon kowacce da abinda take,ko saahen da 'yar uwarta ke zaune bai isheta kallo ba tamkar ba 'yan uwa ba,taji dadi da bata tadda mamin cikin falon ba don haka tana kammalawa ta ahige daki don ko alama bata buqatar zama acikinsu
mutum ce ita mai jan mutuncinta da gudun wulaqanci,
har magariba abdallah bai shigo ba hakanan basu fasa jiransa ba,ana kirayen kirayen sallar isha'i sannan salma fa fara hada tarkacenta tana yima mami sallama,bata kai ga fita ba abdallah ya shigo
sanye yake da jeans baqi da red din t.shirt hannayensa soke cikin aljihun wandonsa,kan sa yasha gyara sai qyalli yake sumar ta masa kyau sosai,ma'abocin qamshi ne hakan yasa turare ke masa rakiya duk ta inda zai gifta
duk yadda salma ta dauki zafi ganinshin da tayi sai taji sakayau tamkar ma bai mata komai ba,ta saki ajiyar zuciya wadda har sai da ta fito fili
''a'ah,yaushe ka shigo gidanοΌ''inji mami
''b fore isha,na shigo nayi wanka ne zan fita sallar isha ne waccar yarinyar ta tsaidani zubaida take ko''
dukansu babu wadda bata shaqa ba,mami ce ma ta dan tare masu don ba dadi
''amma dai kasan ana jiranka tun dazu ko''
ya karuar da wuya yana kallon mami
''hakan ne yasa ma na shigo yanzu mami,don nasan kaskar nan na jirana''
kasa magana mamin tayi salma ko da tasan cewa da ita yake wani abu ya tokare mata wuya,tuni qwalla ta ciko mata ido,cikin rawar murya tace
''abdallah ni kake cewa kaska''
yayo wani dan qaramin murmushi irin na gefan bakin nan
''mene don ance miki kaska,ita ba halittar Allah bace kamar yadda kike''
kai ta girgiza tare da cewa
''na gode abdallah''
fuu ta zagayeshi ta wuce
mami ta soma kiranta tare da yunqurin binta,da sauri ya sha gaban mamin yana murmushi
''qyaleta don Allah mami,indai salma ce zata dawo''
harararshi ta danyi
''saboda ka saba mata haka ko,to saddiqa na daki saura itama ka wulaqanta tan kaji abdallah''yarfe hannu hayi cikin gajiyawa
''again mamiοΌ''kafin ta bashi amsa saiga saddiqar ta fito tana sakin hannu rigarta wanda ta tattareshi saboda alwalar data daura
bakinta a waahe take fadin
''oyo yo ya abdallah''hannu ya dan daga mata
''ππΌqanwa,yaushe ke kuma kika zoοΌ''
murmushi ta saki hade da kashe ido daya cikin sigar son jan hankali
''cikin awa ta