Showing 9001 words to 12000 words out of 162126 words
sana'a suna dora musu talla,to yaya lafiyar kura balle tayi hauka,dama can ba tarbiyya yaran suka cika ba balle yanzun da suka zama *'yan talla*,tashin kunya kule kule kulen maza da diban albarka kala kala,tun malam mamuda nayin magana har sai ya saka ido,don bashi da ikon yayi maganar sai gori
kisan hadiza ce ke juya malam mamuda itace mowar mata sakamakon haifar masa namiji da tayi,duk abinda isiyaku ya fada kam baya qarya,sai ya zamanto aminatu baiwar Allah da yaranta sun zama yan kallo cikin gidan,duk da itama huwailar na baqincikin yadda hadiza ke yadda taga dama amma tilas ta bunne cikin zuciyarta don samun damar cin arziqin samun 'yanci a gidan
Amina cire yaranta tayi ta maidasu ta gwamnati,da yan kudaden hannunta tayi masu dukkan abinda ya kamata,ko dama can ita din ba mace ce mai matacciyar zuciya ba,ba'a rabata da 'yan sana'o'i,sune kuwa auka zama marufar asirinta,ita ce kitso,daka,wanki,'yan qulle qullensu kuka daddawa kubewa su lalle ne,da sauransu,da su take samu ake gurgura rayuwar da dadi babu dadi
lokacin da maryamu ta kammala primary taci common entrance G.G.S.C duka wuya ta samu dake qofar famfo,wanda yayi daidai da fitowar manema wa yaransu hadiza wato SHEMA'U,HARIRA FURERA DA RABI,uku yaran huwaila ne daya ce ta hadiza,dukkaninsu basu wuce sha biyu ba sha uku sha hudu,tsabar son aure ne da suka saka aransu ya sasu zama dika dika,ba bata lokaci kuwa aka sa musu ranar aure,malam mamuda ya samu amina da auke kira mama ya sanar mata zai hada ne harda maryamu ya airar da su gaba daya,tunda su gasu qannenta ma sun fidda miji
cikin ladabi da son fahimtarwa tace''amma malam ni a ganina dukkaninsu basu yi girman da za'a aurar da su ba,yanzu haka ita kanta maryamun bata kai sha biuar ba bare su,ba zata fi sha hudu ba gaba daya,ni a nawa ra'ayin malam nafison maryamu tayi karatu,idan ta qara girma tasan ciwon kanta sai a aurar da ita''
wannan abun ya qullata yace indai bata yarda an aurar da ita ba to babu ashi babu duk wani shirgi nasu,bata damu ba don dama can ba wani abu yake musu ba
tofa,wanna ya sake hura wutar tsanar da sukayiwa maryam wanda dama tun suna qanana aka horesu da ita,don ko wasa bata isa ta shiga cikinsu tayi ba,gashi lokacin bata da 'yar uwa don ba'a haifi hindatu ba alokacin,bugu da qari,kyau da Allah ya bata fiye da duk wata yarinya dake cikin gidan,duk da suma Allah ya basu nasu kyan babu laifi saboda mahaifinsu malam mamuda kyakkyawan bafulatani ne
Allah yayi maryam mai hazaqa da qwaqwalwa,tana da matuqar son karatu,haknne yasa bata yadda ta kula kowanne saurayi wanda su kuma suka fassara hakan da cewa girman kai ne kurum don tana ganin ita kyakkyawa ce,cikin zuciharta ita din tasan ba haka bane tunda ba haka take din ba azahirance
maryam doguwar mace ce wadda Allah ya yiwa baiwar diri da structite na jiki duk da tsahonta hakan bai boye kyawun zubinta ba,fara ce amma ba tas ba,idan kaso ma zaka iya kiranta da ja,don irin farin nan ne mai cakude da ja,gashinta sosai irin na fulani mai laushi da santsi,zara zaran gashin ido da na gira da madaidaicin baki,dimple dinta hagu da dama wanda ko magana murmushi tayi sai ya lotsa,hancinta ba mai tsani ba tafe yake da tsohonsa da kuma tudu,idanunta irin idon nan ne da ake cewa oily eyes wanda zakayi tsammanin qwalla ko ruwa ne suka taru cikin qwayar idon,bata da baqin qwayar ido sosai,sanyin muryarta da zaqinta ke dada bayyana kyawun halittar da Allah yayi mata wanda hakan ya ja mata yawan masoya da maqiya ciki harda 'yan gidansu
haka aka sha bikin yan uwan nata su hudu yayin da ita kuma ta duqufa karatunta,maryam badai qwaqwalwa ba,hakan ne ma yasa bata samu cikas ko ksdan a karatunta ba,cikin nasara komai ke tafiyar mata,janye jiki da masoyanta sukayi a lokacin bai dameta ba don dama bata buqatar wani damuwa karatunta ne kawai damuwarta,cikin nasara ta shige B U K inda anan ta samu shaidar degree dinta kan fannin girke girke
ba jimawa,da kammalawa kuwa ta samu aiki da wani katafaren gurin cin abinci da shirya bukukuwa ,wanda cikin qanqanin lokaco ta samu matsayi mai girma na shugabantar dukka masu girka wani abunda za'aci ko a gurin ko kuma aka basu kwangilar yi na biki,qwazo himma gaskiya da amana su suka jawa maryamua wannan matsayin wanda hatta da wadda ta kafa gurin *HAJIYA ATIKA ABUBAKAR BAFFA* ke qaunarta
ta bangaren 'yan uwanta kuwa saidai ace Allah ya rufa asiri kawai domin dukkaninsu cikin shekara guda babu wadda bata da tabon saki wanda tsantsar rashin tarbiyyarsu ya hanasu zaman arziqi da mazajensu,a haka dai ake gurgurawa har kawo wannan lokaci,hankalin maryamu bai fara tashi ba sai da aka zo auren qannanta zagaye na biyu wato *azara* *shamsiyya* da *maraqisiyya*,tsantsar gori habaici da baqar magana idan da tana tsiro a lokacin to da tuni ta yiwa maryam,sai Alla ya halicceta mai haquri da kawaici hakanne yasa bata fiya zafafawa kan lamuransu ba,idan suna yi dauke kanta take kamar yadda tun usuli ta tashi taga mamanta nayi
samuwar aikinta ya taimaka qwarai wajen kyautatuwar rayuwarsu,wanda alfanun ilimin da ta gani ya sata jajircewa da tsayawa qanwarta daya tilo don ganin itama ta amfana,duk lokacin da ta daki albashinta bata fasa siyan wani muhimmin abu ta kaiwa mahaifinta ko ta ciri kidin tsaba ta bashi,babu kuma wani jin nauyi zaisa hannunshi ya amsa da sunan ai yarshi ce,haka rayuwar maryamu ta taso cikin tsangwamar *'yan uba* wanda har yau ita take gani ba kuma tasan ranar qarewarta ba
_*WANNAN KENAN*_
*Mrs muhammad ce*π
πππβπ»βπ»βπ»
[9/17, 12:50 PM] 80k: πππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ *ABADAN*πΊπΊ
πππππππ
πΊππΊππΊ
πΊππΊπ
πΊππΊ
πΊπ
π
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πππππππ
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊππΊ
ππΊππΊππΊ
ππΊππΊπ
ππΊππΊ
πΊππΊ
πΊπ
πΊ
βΆ8β£
Cike da tawakkali da yarda da qaddara ta miqa dukkan lamarinta ga Allah,a yanzu kam ta sanya jabir ne kawai cikin addu'o'inta kamar yadda raliya ta shawarceta,domin tausayinsa ne fal cikin zuciyarta,tana ji a cikin zuciyarta ta sanadinta ne ya afka wannan qaddarar
abu guda ne ta kasa tinsa komawa walwalarta da aikinta tamkar,yadda take yi a da duk da yadda take son aikin,ta barwa ranta cewa ta ajjiye aikin zata kuma jira har lokscin da ubangiji zai musanya mata da da wani mijin ko da baikai jabir dinta ba
π²ππ²ππ²π
misalin biyar da rabi ne na yammaci,zaune take a rumfar tasu wadda ta sha mopping tayi fes,dai qamshin turaren tsinke take,mamanta na dakin babansu tana gyarawa don ita ta amshi girki,don sam bata lamunce don ranar girkinta bane ta tura yaranta su share dakin baban nasu ba kamar yafda taga su huwaila nayi tsabar ganda,yayin da hindatu ke makarantar islamiyya
sanye take da maroon din material dinkin doguwar riga da yake ma'abociyar son dogayen riguna ne ko don tsahon da take da shi,yatsunta sunyi kyau da jan lallen da tadan qunsa iya yatsu,a lokaci irin wannan idan bata da abinda duka zatayi,taka duqufa wajen research din girke girke a daga sashukan dake watso kalolin abinci na qasashe daban daban,kadan kadan hankalinta ke rabuwa gida biyu,wani lokaci yayi tsakar gida da yaran inna hadiza keta faman ta'adi cikin falon gyatumar tasu da hayaniya na 'yan fadace fadace atsakaninsu kuma babu wanda ya isa yace zai tsawatar musu
cikin haka ta jiyo sallamar inna hadizar,abu na farko da ya biyo bayan sallamarta shine ashar da ta dura wanda har sai da maryamu tayi ta'awizi cikin zuciyarta
''kaga tsinannun yara shegu,ke balaraba da na bar muku dakin a bude shine kuka maida min shi sansanin fada da kokaye kokaye,kuma saboda tsabar baqincikin Allah yayi maka arziqi a rasa mai tsawatrwa uaran salon su fasa ma abu kosu lalata ma su jawo maka asara,dadin abun ma yanzu kana da arziqin da zaka gyara''
sarai mama tasan da ita take amma kasancewar ko da can ma da jini ajika ba kula shirginta take ba yasa yanzun ma tayi mata dif,saiga huwaila ta fito daga wanka takalleta
''a'a,ina kuma kikajeοΌ''
''yo ina kuwa zanje da ya wuce gidan doyar albarka jamila''ta fada tana shirin shigewa dakinta
sakwatoto huwailan tayi
''amma inace baki tafi ba don wanna wanka da nayi na shirin zuwa ne,tunda munyi tare zamu je''
''kiji hiwaila da wani zance,don,lawai zaka girin naka sai ka jawo bareοΌ''binta wadda tare suka je da innar tata ta maidawa huwaila raddi
''kinga ba dake nake ba 'yar ayi jikar na saba''
''a'a,dakata don ta fadi gaskiyarta,kada kiyi haushin kaza huce kan dami''inji onna hadiza cikin salon tare mata
''au bayanta kike goyo kenanοΌ''
''qwarao,yo akan meοΌ''
baqinciki ya,hanata cewa komai sai qwafa kawai da ta ja ta shige dakinta
qarar wayarta ce ta sata dawowa daga diniyar da su inna jadizan suka shigar da ita,a kullum kwanan duniya sake gasgata zancan raliya takegame da abinda ya faru tsakaninta da jabir,jikinta a sanyaye tabi wayar da kallo ,da kamar ba zata daga ba amma ganin sunan *mama* ya sata babu jinkiri ta daga,cike da,girmamawa take gaidata
''babu abinda zaki cemin maryamu,wa yafi qarfin qaddara a rayuwaοΌ,abun nan ya riga ya wuce addu'a ce kawai mafita,amma anyi anyi ki koma gun aikinki kinqi,na tambayi haj rabi ko wani laifin aka miki sunce babu komai,ko an miki wani abu ne agunοΌ''
cike da girmamawa tace ''babu abinda aka yimin mama wallahi''
''to shikenan,indai da gaske haka ne kizo gobe gida ki sameni da la'asar,da akwai aikin da aka samu kuma gaskiya a iya hasashena babu wadda ta dace da aikin sai ke,don na yaba qwarai da tarbiyya gaskiya da riqon amanarki''
ba zata iya musu da mama ba wato hajiya atika abubakar,banda haka da wata ce zqta ce mata ta gode bata buqata,amma girmanta da qaunar da take gwada mata ta wuce haka a gurinta don haka tace
''to mama,na gode Allah ya saka da alkhairi insha Allahh goben ina hanya''
''to shikenan a gaida mutan gidan''
''zasu ji insha Allah''
ta sauke wayar tana jin wani abu na dan taba zuciyarta,mama da bata kima da shigowa ba tace ''ke da wayeοΌ''
ajiuar zuciya ta saki
''haj atika ce,wai tana nemana gobe''
''to Allah yasa lafiya,ko zancan komawarki ne gurin aikinοΌ''
''a'a,tace wani aiki ne ya samu,amma sai naje goben zanji''
''Allah ya rufa asiri ''ta fada maman tana ficewa dauke da wankakken zanin gado da rigar filo
murmushi maryam tayi tana jinjina kai,wato miji da mata sai Allah,maman ta tana burgeta matuqa,bilhaqqi take kula da mijinta,bata duba komai sai zatin Allah da kalmar nan ta *aure bautar ubangiji*
ππ²ππ²ππ²
washegari ta shirya tsaf cikin atamfa dinkin riga da skert yaluwa sosai tayi,mata kyau ta qara haske da rama,hakan sai ya sake fidda tsayinta,kasancewar lahadi ce yasa ta nemi rakiyar hindatu ko zata ji dadin tafiyar,don ita kanta bata son tafiya ita kadai,gani take kamar idan ta fita nuna ta za'a dinga yi,tsawon watanni kusan biyar amma tunda abin ya faru baifi sau biyi ta fita ba zuwa uku shima sai dare
babu dadewa suka isa gidan maman,a falon qasa aka saukesu mintina biyar aka haura da su samanta wanda ba kowa take kaiwa ba,cike da fara'a ta tarbi maryam din,ita dai ranta yanason maryam din,natsuwarta na burgeta,
kayan ciye ciye ta sa aka kawo misi ta dan basu lokaci kadan sannan ta dawo
''maryam''abinda ta fara cewa kenan
''kamar yadda jiya na shaida miki a waya aiki ne ya samu,yayi shige da na gurina amma yana da bambanci domin wannan a gida zaki dinga yinshi,zaki samu albashi mai tsoka fiye da na gurina''
ta,dubeta da aily eyes dinta''mama wanne irin aiki ne a gidaοΌ''
''kinsan marigayi *alhaji abdulkareem mai nasara*οΌ''
sai da tadan shiga tunani sannan tace
''eh ina jin sunanshi mama''
''yauwa,kinga sanannen mutum ne kuma fitace tun kafin rasuwarshi,yaro daya Allah ya basu wato *Abdallah*duk da cewa yana da wata matar amma Allah abi bata haihuwa da shi ba,saidai ya riqe mata nata uaran da ta taba haifa awani gidan mata ne su biyu da nimiji daya yanzu haka duka suna tare a gidan duk da rasuwan shi alhj abdulkareem din hakan baisa sun raba mazauni ba,mamanshi na matuqar sonshi da kaffa kaffa da lamuranshi,duk da haka ana farautar rayuwarsa don kusan sau biyu kenan ana zuba poising abincinshi,ta rasa daga ina matsalar take,kuma duk lokacin da hakan ya faru idan aka tashi binncike sai a samu da hannun kukunshi,hakan yasa take canza masa kuku kala kala,amma har yau babu wanda hankalinta ya kwanta da shi
abdallah shine shugaban jami'an tsaro na farin kaya wato *S S*na nijeria gaba daya,wanda aikinsa kansa na buqatar ya zamo cikin kulawa da tsaro na musamman
bata da lokacin zama agida kasancewarta cikakkiyar likita kan fannin matsalolin da suka shafi mata,wannan ne yasa ta bayar da cigiyar amintacce ko amintacciya wanda ya qware kota qware afannin girki,to qawarta aminiya ta ce hakan ne yasa ta bani cigiya ni kuma naga ke kika fi cancanta da wanna aikin maryam,ina fatan kin fahimceni abunda kuma ya shige miki duhu kina iya tambaya ta''
shiru tayi domin tana jin abun da kamar wuya,sam bata ji ya kwanta mata ba aikin,tamkar aikatau zata tayi,kenan tunda aikin dafa abinci zata gidan wasuοΌ,anya kuwa zata iya amsar tayin maman,amma tana jin nauyinta ,ba zatq kallon tsabar qwayar idonta tace mata a'a kai tsaye ba,kusan minti biyi sannan ta ajjiye numfashi
''ina ganin mama zanje na sanar da maga batana tukun,idan yaso duk abinda suka yanke akai zan sanar miki''
''yayi kyau,hakan dai dai ne maryam,wannan shike dada nunamin hankalinki da kaifin tunaninki,amma ina fatan bazaki watsa min qasa a ido ba''
''insha Allahu''
ta fada ka a qasa''
a haka sula rqbu bayan ta baiwa hindatu dubu daya tace ta siyi kayan kwalliya
cikin mota hindatu ta isheta da karadin wallahi yaya maryam ki amshi aikin nan
murmushi kawai tayi
''yarin ya ce ke hindatu har yau baki da hangen nesa''
''to,ya maryam meye aibu a cikiοΌ''
bata amsa mata ba sakamakon jin ringing din wayarta da tayi ta soma kiciniyar cirota dqga aljihun jakar,raliya ce mai kiran
''hello ummin fadil''
''na'am mommyn fadil kina ina neοΌ''
''kin ganni a hanya na dawo ne a wata unguwa''
''yauwa don Allah ina son ganin ki ne ya za'ayiοΌ''
''babu damuwa bari kawai na qaraso''
''yauwa ta gurina''
dariya ta bata tace ''sai na qaraso''ta maida wayar jaka sannan ta yiwa mai adaidaita bayanin inda zai juya da su''
ππ²ππ²ππ²
''daga ina kuke da yammacin nan neοΌ''raliya ta tambayi maryam sanda take dire musu drinks
''hmmm,wallahi kinga haj atika ce tayi kira na,wai ta samamin aiki gidan marigayi abdul kareem mai nasara''
sai taga fuskar raliyan ta sauya ta dan tsuketa
''ba zaki koma wani aiki ba,aure zakiyi maryam''ta gada kai tsaye tana kallon maryam din
ba tare,da kawo komai cikin zuciyarta ba tayi murmushi
''banda abinki qawata ba sai Allah ya kawo mijin baοΌ''ta fada cikin rashin kulawa
''Allah ya kawomiki miji maryam''sai da taji qirjinta ya wani irin buga
''mijiοΌ,wa ya gaya miki,qarya ne ni babu mijin da na samu''
matsowa tayi sosai ta kama hannayen ta
''maryam kin amince da ni kin kuma yarda da amincin dake tsakaninmuοΌ''
''me ya kawo wannan tambayar kuma raliyaοΌ''ta tambayeta cikin yanayi na shiga duhu
''maryam so nake ki auri nasir mijina''
a hagunce take kallon raliyan,jo tayi lamar ta doka mata guduma atsakiyar ka,gani take kamar ba'a hayyacinta take ba''raliya,me kika sha yau,ko baki da lafiyaοΌ''
murmushi tayi
''nasan zaki fadi haka maryam,amma ras nake,kuma nasan me nake,cewa nayi mijina nake so ki aura nasir''
''shi ya aiko ki lo ke kika aiko kankiοΌ''ta tambaueta tana mata kallon ba a hayyacinta take ba
''ni na aiko kaina tare da amincewarsa''
zame hannayenta tayi ta miqe
''idan kin warke kya kirani muyi maganar da kika rani domin ita,don dai wannan ban daukeshi da muhimmanci ba''
kamo hannunta tayi
''zauna maryam,wallahi a hayyacina nake,kuma lafiyata lau''
wani kallo ta watsa mata''sake ni raliya,ni 'yar halak ce kuma nasan halacci na kuma yi imani da akwaishi,idan haka kike to ni ba haka nake ba,idan kuma nasir din ne ya saka ki to ki gaya masa ni maryam 'yar halak ce''ta zame hannuwanta ta fice yayin da raliya ta bita tana qwala mata kira amma ko waiwayota bata yi ba,hindatu dake farfajiyar gidan tana waya itama wucewar maryam din ta gani sai binta tayi a baya
kuka zata yi ne ko ihuοΌme kuma yake shirin faruwa da itaοΌme yasa guguwar rayuwa ke walagigi da itaοΌ,yau wai amiyarta ke gaya mata ta auri mijinta,ta ina ta yaya ma zata iya auren mijin raliya ko su biyu ne suka rage a duniya,ko da suka ke gida mama kasa gane kanta tayi,don tunda ta shigo gidan dakinta ta wuce kai tsaye,cikin damuwa maman ke tambauar hindatu me ya faru da maryam din
''ni dai mama da mukaje gidan hajiya lafiya lau muka fito,kuma iki ta samar mata gida alhj abdulkareem mai nasara,amma dai mun biya gidan anty raliya,to nidaiina waje bansan me suka tattauna ba naga dai ta fito da sauri ma biyo bayanta''
''alhj abdulkareem mai nasaraοΌ''mama ta maimata sunan don ba boyayyen mutum bane,mai arziqi ne na gani a fada wanda akayi qiyason duka nigeria babu wanda ya kama qafarshi
''to Allah ya kayuta,indai raliyance ai ba'a ashiga tsakaninsu,idan kuma aikin ne ma zamuji,qyaleta hindatu,nasqn zata min maganar da kanta''don shaquwar dake tsakaninsu yasa maryam bata boyema maman tata duka damuwarta
*mrs muhammad ce*π
πππβπ»βπ»βπ»βπ»
[9/17, 12:50 PM] 80k: πππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ *ABADAN*πΊπΊ
πππππππ
πΊππΊππΊ
πΊππΊπ
πΊππΊ
πΊπ
π
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πππππππ
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊππΊ
ππΊππΊππΊ
ππΊππΊπ
ππΊππΊ
πΊππΊ
πΊπ
πΊ
βΆ9β£
kwana guda da yini daya bata ce da maman tata komai ba,itama zuba mata idon tayi bata tambayeta ba
kwana na biyun ne qarfe uku taji sallamar raliya,tana kwanve can cikin dakinsu saman katifarta,don yanzu zaman daki da kwanciya kuma ta aira wanda hakan baya rasa nasaba da yawan tunanin da take fama da shi,sai da gabanta ya fadi lokacin da tqji suna gaisawa da mama ta fadi mata tana cikin dakin
jawo dankwalinta tayi tana dauraqa tare da qoqarin yashi duka a lokaci daya,raliya ta iso bakin katifar ta zauna bayan ta shimfide