Showing 30001 words to 33000 words out of 162126 words
mamar nata har ta kammala shinkafa da wake da an quli hade da salad tumatir albasa da cocumber,zasu tada sallar kenan hindatu ta shigo,murna kamar ta cinye maryam,cewa tayi itama ba zata zauna ba bari ta fara sallar,ta yada takardun jarrabawarta saman kujera ta fita ta yo alwala
Dari biyar maryam ta fitar ta bawa hindatu da kanta taje ta aiyo musu serdine soyayye suka zauna hankali kwance suna cin abincinsu suna hira,hindatu sai santin maryam take
''wallahi adda maryam kada kiso kiga yadda kika koma,kin zama wata hajiya skin dinki tayi wani freah,qiba ce kawai baki qara ba,kinga kiwa da kin dada qiba tsawon nan naki raguwa ziyi''
dariya ma ta basu mama tace
''to sarkin zance,kiyi a hankali dai kada ki qware''cikin nishadi auka kammala hindatu ta guara gurin ta dawo suka sake bude sabon babin hira,da daidai da daidai take jin matsalolinsu,sai taji dadi jin cewa basu da wata matsala mai yawa,mama tana cikin lemonta sosai don haka sai dan abunda ba'a rasa ba,wanda shina mafi yawa kan karatun hindatu ne
duka albaahinta ta fidso ta damqawa maman tana fadin ta fadi abunda ya dace ayi da su
''um um maryamu,ke din mai hankali ce,na tabbata ko bance komai ba zaki yi duka bunda ya dace din''
tana lissafawa mama abunda takeso tayi din maman na sa mata albarka,ciki harda aiyqn kayan abinci ta ajjiye agidan nasu tunda albaagin nata ya tasamma dubu dari
''hmmm um''hindatu ta fadactana turo baki,maryam ta juya ta dubeta
''ya akayi bakin ki da magana kenan''
''wlh akwai,haka kawai zaki narka albashinki ki siyi abincin gida wanda har wadancan mutanen za'aci,jamila ma da suke qaryar arziqi bata taba siyan gallon din mai ta ajjiye tace kowa yayi amfani da shi ba sai ke da kike nema da guminki,a jikinta kawai zaki ga samunta ita babarta da 'yan dakinsu''
_kumin afuwa kuyo maleji da wannan,a bini bashi_
*mrs muhammad ce ๐*
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ป
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*22
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
murmushi maryam tayi
''akwai bambanci tsakanin jamila da maryama,mama ce mu ta haifemu uwa ta gari,mai nuna mana hanyoyin alkhairai da samun dacewa duniya da lahira,yayin da su kuma inna hadiza ce ta haifesu,kowanne mutum da kika gani yana kyauta ne da abunda yake hannunshi yake kuma da shi na alkahairinsa ko sharri,ma'ana duk abunda mutum yayi miki na sharri to abunda ke hannunsa kenan sharrin,ke kuma kada kice za kiyi amfani da abunda yake hannunki na sharri ki maida masa da martani,nuna masa ke alkhairi ne da ke,kada ki damu da sai wani yayi abu zakiyi,idan kina da dama kiyi din,kuma ki qudurce cewa kinyi ne saboda Allah,to sai kiga koda wanda kika yiwa din bai gani ba baki da haufi don kinyi ne domin Allah kuma ahike bada lada da sakamako''
cikin hikima maruam ta ragewa hindatu haushin da take ji na abunda tayi shirin yi a gidan nasu,har ta rakata super market din dake bayan layinsu ta siyi cartoon na macaroni taliya da couse couse,galoon na manja da man quli,dan madaidaicin buhun shinkafa,ta siyawa mamanta kayan tea complete,har da su cornflakes saboda hindatun
ledar da mami ta bata ta atamfofine guda biyar ciki da sabulai masu tsada sinqi biyu mamanta bawa guda biyu hindatu daya ta ware biyu zata bawa huwaila da hadiza,yara suka samu suka dauko musu kayan hindati na biye da su yayin da maryam tayi gaba
sallamarta atsakar gidan tayi arba da baban nata,cikin fara'a ta nufeshi tana shirin tsugunawa tace
''baba,barka da warhaka''yayin da shi kuma ya tareta cikin hade fuska ba kuma tare da amsa gaisuwar ta ba yana fadin fadi
''lafiya ,ya akayi me kika zo yi๏ผ''
''ya salam,taya za'a raba mjtum da gidan mahaifinshi koda kuwa aure yayi ballantana ita da bata yi aurenba๏ผ''take zantawa ita da zuciyarta
''zuwa nayi na gaidaku baba,kusan wata guda ban ganku ba''
''amma dai maryamu ina cewa.....''maganar tasa ta katse lokacin da yara suka soma ahigo da kayan suna ajjiyewa
''yaya,kai,wannan kuma daga ina๏ผ''
''siyayyar adda maryam ce''hindatu ta bashi amsa lokacin da take sallamar yaran da naira goma goma ladan dako
''uwarta ta siyowa kenan๏ผ''baban ya fada yana duban kayan
''a'ah baba,na dukka gida ne,ga wannan baba a sa mana albarka''ta ce tana ciro naira dubu biyar ta miqa masa
washe baki ya shiga yi
''ah,lallai haihuwa mai rana,maryamu dukka haka,basuyi yawa ba๏ผ''
mirmushi ta danyi zuciyarta fal mamaki
''basuyi ba baba''
''ah lallai wannan gidan aiki ya karbeki,to Allah yayi albarka ya bada miji na gari''ya fada yana irga kudin fuska qunshe da fara'a
ko banza taji dadin addu'ar da yayi mata,tunda dai uba uba ne ba'a canzawa tuwo suna,sai take jin ranta yana mata dadi
ina wuta inna hadiza ta saka maryam,qememe taqi karbar atamfar da ta bata din ai ita tafi qarfin atamfa wallahi,su yanzu atamfa saidai su bayar,ita kuwa huwaila hannu ta saka ta amshe kayarta tana tunanin gobe idan Allah ya kaimu taje kasuwar bakin rimi ta saida barta ko dubu biyar suka bata ta rage son tuni bokan uwani suka soma tatsarta,ita kuwa hindatu ta kalmashe tace gaba ta kaita,
''aikin banza aikin wofi,wa ma yasan daga inda kudin suka fito,an tura yarinya yawon karuwanci tana samo kudi tana kawo muku kuna karbewa an fake da gidan aiki aka kaita,a dai juri zuwa rafi da tulu diban ruwa wata rana zai fashe,ke kuma na dawo gareki munafuka makwadaiciya,an baki abu kinsa hannu kin karbe,to ni nafi qarfin atamfa wlh ehe''
''Allah ko๏ผ,Allah sarki,mu gani a qasa mana wai inji kare ance ana suna a gidansu,idan akwai uwar makwadaita ta duniya to kece kakarta,kwadayin ne ya sakk cusa 'yarki inda bata da gurin zama,kuma da sannu unguli zata koma gidanta na tsamiya''ta yaue labulen dakibta ta shige tabar inna hadiza na ci gaba da babatu da sharrence sharrance kala kala
lokacin da maryam ke sallama da mama tana shirin ficewa daga tsakar gidansu zuwa soron jamila ta danno kai zuwa,ta cake ado cikin wata yar ubansun shadda dinkin riga da skert na rashib arziqi,qam rigar ta kamata har boobs dinta na yowa sama,babu zancan mayafi sam atattare da ita sai daurin zamanin nan da ake kira ture kaga tsiya,waya take tana taku cikin isa da qasaita tamkar wata diyar qaruna
''yanzun nan na fito daga gidan mu hadu kawai a ni'ima guest palace din,amma fa gaskiya wannan karon bazan kuna ba gida zan koma,ok sai na iso''daidai lokacib da ta kammala wayar,bangazar kafadar maryam din tayi sannan ta juyo a wulaqance ta qare mata kallo,wata mahaukaciyar dariya ta saki tana ci gaba da kallonta
''sannu adda maryam,ana nan ana fama ko,ko da yake dai....''ta fada tana kuma kallonta daga sama har qasa
''ba laifi naga kin dan canza,ko an fara bin kwalta ne๏ผ''
waniabu ne ya tokarewa maryam dim maqoshi,rainin hankalin ya fara isarta dukan ya mata yawa,tayi mata uwarta ta mata,batasan lokacin da ta daga hannu ta zabga mata mari ba,ba ita kadai ba hatta da hindatu tayi mamaki,tsawon shekarun da suka dauka bata taba gwada yiwa wata cikin maraina wayon ta haka ba
''kan can uba,kut,me nayi miki,ko ko tsabar baqin ciki da qyashi ne...''
''kika ci gaba da magana ina mai tabbatar miki zaki kwashi haqoranki a qasa,banza jahila dabba wadda batasan inda yake mata ciwo ba''
tsit tayi da bakinta don taga irin bacin ran da bata taba gani cikin idanun maryama ba,gaskiyar hausawa dake cewa wargi ma guri shika samu
daga haka bata dada ba ta mewayeta tayi wucewarta,dadi kam tamkar maryama ta taka rawa saboda farinciki,mama ma wannan karon bata ce uffan ba,don tsan yau da gobe tafi qarfin wasa,fitarta waje babu inda idanunta suka kai sai kan jabir dake zaune mazaunin direba,idanunshi qur bisa qofar gidan tamkar dama an sanar da shi maryam din na fitowa,mamaki da tausayi suka cika maryam,jabir ne wannan,jabir ne ya koma haka,ina gayu davtsaftar jabir suka tafi๏ผ,me yake faruwa da jabir me ya sameshi๏ผ,mamakinta bai sake daduwa ba sai da taga ya dauke kansa daga gareta tamkar ma bai taba saninta ba
cikin matuqar sanyin jiki take takawa har ta isa bakin titi ta tari napep tayi gida
lokacin da ta isa gidan tuni anyi sallar magariba duhu ya riga ya shigo,ba haka taso ba taso ne ta koma da wuri ta dora musu dinner din,saidai lokacin ya riga ya qwace mata,kitchen din ta nufa kai ysaye bata ko doshi dakinta ba,mami,ce gaban gas din tana ta hidimar hada abincin,yayin da kuna dan shagwabar nata ke tayata da dauko wannan dauko wancan
''idan banda rigimar abdallah don Allah ina kai ina girki๏ผ,nace ka...''sallamar maryam ta katseta
''sannu mami da gida,har kin dawo๏ผ''ta fada tana ahirin amsar aikin daga hannunta
''yauwa maryamu ya kika barosu๏ผ''
lafiya mami suna gaidaki๏ผ''
''kinga maruamu barmin nayi yau dai daya ki huta kema,nima na wasa qwaqwalwata ko๏ผ''mami ta fada tana hanata aikin da take qoqarib karba
''ayyah,mami da wuri ma naso na dawo lokaci ne ya qwace min''
tsaki abdallah ya ja hadi da barin miqo albasar da yakewa mami ya koma ya zauna
''ki bata mami aikinta ne,idan baki bata ba ma acikin albashinta na wani watan''
yau ranta abace yake tana jinta daidai da duk wanda ya taba tane,hakan ne yasa ta maida masa raddi
''babu damuwa,mami ina jinta ne tamkar mama na ne saboda haka babu ciniki tsakaninmu,ko ba kudi qimar shekarunta sun biya in mata aiki''
baki ya tabe kamar mace
''gaskiya ne naga kina amsar albashinki,ai da,sai kice kin yafe''
murmushi tayi cikin gatse,sanann cikin qasa da murya ta yadda mami da ta tafi sink wanke albasa ba zata ji ba
''kada ka manta haifata akayi yadda akayi yadda aka haifeka,aiki nake kamar yadda kake wa qasarka aiki da albashi ake biyanka,am not a servant,ciniki kuma ko tsakanin da,da uwa halas ne''
tofa baki yasan me zai fada tuni fuskar 'yan maza ta sake hadewa
a zafafe yayi niyyar maida raddi saidai isowar mami gun ya katse masa hanzarinsa,tilas ya hadiye abunda ya qunso
''zan zuba miki albasar maryamu kafin nan ki shiga daki kin ajjiye kayan hannunki kin sauya kaya ko๏ผ''
''to,mami na gode''maryam ta fadi gami da juyawa ta bar kitchen din,abdallah ya bita da kallon zaki san koni waye,yayin da ta daga kafadu alamun dake nuna masa am ready
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k: ๐๐๐๐๐๐๐
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ *ABADAN*๐บ๐บ
๐บ๐๐บ๐๐บ
๐บ๐๐บ๐
๐บ๐๐บ
๐บ๐
๐
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐๐๐๐๐๐๐
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐๐บ๐๐บ๐๐บ
๐๐บ๐๐บ๐
๐๐บ๐๐บ
๐บ๐๐บ
๐บ๐
๐บ โถ2โฃ3โฃ
*_an karbo daga abu hurairah Allah ya qara yadda da shi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace: kalmomi guda biyu,masu sauqi akan harshe,mafiya soyuwa agurin ubangij,masu nauyi akan mizanin auna ayyuka SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI,SUBHANALLAHIL AZIM_*
su biyu cikin falon misalin qarfe goma na dare,mami na bisa computer dinta tana tsara wata saminer da zasu gabatar yayin da maryam ke zaune gefanta tana tayata hira
''abdallah shiru bai dawo ba,halan yau aiki ne ya tasaahi gaba''cewar mami lokacin da take ci gaba da typing
''da alama''maryam tace
mami tadan bar abunda take ta juyo da hanklainta ga maryam
''wai ni kam maryam meye matakin karatunki ne๏ผ''
murmushi ta danyi
''degre ce''
''ta daya ko ta biyu๏ผ''
dan bude baki tayi alamun mamaki
''a'ah mami,ta dayan dai''
''mai zai hana in maida ke makaranta ki samu wata degree din kan fannin kasuwanci๏ผ,na fuskanci kina da amfani matuqa atattare da mu,sa'annan ina buqatar mai kula da kamfanonin abdallah mai amana kamar ke,kamfanoni wadanda ya gada da kuma wadanda ya bude daga baya,ya kike gani maryam zaki iya๏ผ''
shiru ta danyi cikin shakku,bata son ta fiya zura kanta cikin harkokin masu hannu da shuni, tana gudun wulaqanci,duk da tayi amanna cewa mami sam ba haka take ba,ta yarda da karamci da kuma son jama'a irin nata,to amma shi uban tafiyar fa wanda sam tasu batazo daya ba๏ผ
''yaya ne maryam naji kinyi shiru ko baki da sha'awa๏ผ''
girgiza kanta tayi
''a'ah mami,duka abunda kika yanke mami dai dai ne,amma zanso na fara sanar da baba da mama naji me zasu ce akai''
''gaskiyarki,wannan dai dai ne,amma duk da haka ki fara hada min takardunki nasan bazasu qi ba,babu wanda zaiqi ilimi wa dansa,ina da qawa a jami'ar b u k sanate ce so insha Allau babu matsala''
''to mami na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma''
''no maryam,diya ta nayiwa kinga babu buqatar godiya''gyada kai tayi fuskarta qunshe da murmushi
sallamar nene ce ta maida hankalinsu bakin qofar,nenen ce kiwa cikin doguwar riga mai zubin buba mai taushi saidai wannan nada hannaye gajeru da alamu shigar barci ce tayi
''maraba da nene''
''yauwa...mami''ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon dake,daura da inda mami da maryam din ke zaune,a mutunce suka gaisa
''zuwa nayi na diba yarona abdallah kwana biyu banjin duriyarsa''nene ta fada tana murmushi
mami ta rufe computer tana cewa
''abdallah na nan qalau aiki ne ya sashi gaba,da wuri yake fita kuma bai shigowa da wuri,yanzun na zancanshi muka gama da maryam''
ta juya ta dubi maryam sai a lokacin ta gaidatakanta na sunkuye a qasa,sam batason kallon idanun natar,haka nan sai taji fargaba ta kamata,second talatin idanunta na kan maryam din tana saqa a kanta kafin ta dauke kabta ta maida ga mami
''lafiyanshi dai qalau ko๏ผ''
''lafiya qalau yake''mami ta bata amsa cikin jin dadin tambayar tata,wadda har ga Allah tayi tsammanin ta mata ita ne da zuciya daya
ta miqe tsaye tana cewa
''tiw,ni zan wuce dama abunda na shigo naki kenan,sai da safenku''
''Allah ya bamu alkhairi nene an gode ki gaidamin su zubaidan kwana biyu ma bata leqo min ba,zahariyya dama sai wani abun ya kawota''murmushin yaqe nenen tayi cijin zuciyarta tana cewa
''bintu ki guji ranar gamuwar mu dake,gamon mu dake bazai ma rayuwarki daidai ba''
''abdallah na bani kunya wlh,dubi yadda baiwar Allahn nan ke sonshi take damuwa da shi,amma shi bashi da abun wulaqantawa sai diyarta,idan baiyi wasa ba na kusa masa auren dole''
'yar qaramar dariya ce ta subucewa maryam
''ai mami ba'a yiwa namiji auren dole''
itama dariyar ta tayata
''to za'a fara kan abdallah''
mintina ashirin basu cika da fitar nene ba abdallan ya shigo,ya sauya shiga ba wadda ya fita da ita bace,indai mami taga hakan to a gajiye ya dawo ya fara shiga sashensa yayi wanka ne
kan table maryam ke serving nashi yayin da shi da mami ke hira jifa jifa,ta kammala tana shirin sauka ta basu guri taji yace
''ke...mene wannan din๏ผ''ya fada yana nuna abincin da ido,kafin ta bashi amsa mami ta karbe zancan
''dambun shinkafa ne mana''
ya bata fuska kamar yadda yara keyi ya dubi mami
''gaskiya mami ni bazanci wani abu dambu ba''maryam ta kalli farantin don sake gano aibun dake tattare da dambun da ta bata lokaci a kitchen tana girkawa,dambun shinkafa ne da aka masa hadin vegtables sosai saboda ta sonshi da son gayayyaki,cabbage ne carrot zogale green beans harda gyada da wadatacciyar albasa sai dafaffen nama data yankashi qananu ta zuba a ciki,mamaki tayi cikin zuciyarta duk da bata nuna ba kan fuskarta,ta lura tsirfar da ya tsuro da ita kenan cikin yan kwanakin nan
''amma kaifa dazun kace shi kake sha'awar ci ayi maka๏ผ''
''am sorry mami na,dambu ayanzu is too heavy na cishi na kwanta ai sai ya kashe miki ni''
dariya ma ya bata,bata zaci konai ba don yaune ya fara wa marya din a gaban idonta
''is ok,maryam yi haquri kinji taimaka ki sama mishi wani abun mai sauqi da sauri''
''no mami,ni zan zaba akwai abunda nake sha'awar ci''
''uhmm''ta fadi tana kallonshi
''sakwara nakeso miyan agushi''bata fuska mami tayi
''kai lokaci fa ya qure gaskiya ba zata girka ma sakwara a yanzu ba saidai ka barwa gobe''
''tunda kin roqa mata shikenan tamin jallop din supaghetti with serdine''bai qarasa ba ma ta sauka tayi kitchen
girki ba baqonta bane cikin minti ashirin ta kammala ta,tun kafin ta fito qamshi ya soma cika qofofin hancin abdallah amma sai ya dake
''mami,dazu munyi waya da abida,ta ce nan da kwana uku zata zo nijeria''
farinciki sosai maryam ta gani fuskar mami
''masha Allah,gaskiya ta kyauta qwarai kuwa da gaske,kaga ta baka kubya kai da kaqi zuwa''
''to mami me zanje na mata''
''any way dai tunda tace zata zo magaba ta qare,fata na idan tazo din wannan karon konai ya daidaita,canki cankar da kake tayi wa muta ne ta qare''
''haka nake fata,na soma gajiya da qulafucinsu naci da rashin zuciya,inason nima na huta mami na samu peace of mind''
kafadarshi mamin ta buga''ja'iri sai yanzu kasan da hakan...am maryam''
''na'am''
''insha Allahu nan da kwanaki uku zamuyi baquwa abida diyar ambassador muhammad mukhtar kuma idan tazo zata dan zauna da mu na wani dan lokaci,so ya kamata kinga na sanar miki haqqinki ne sa'an nan daura da dakinki zata zauna kinga ke zaki karbi baquncin,ina son kuma a sake tanadin sabbin girki,duk na san ban da matsala dake,ke din ba baya bace''ta qarashe maganar cikin sigar zolaya tana murmushi wa maryam din
murmushin ta maida mata
''insha Allahu mami babu damuwa''
''mami a maida abincin nan kawai kitchen nina qoshi ma''inji abdallah bayan ya gana jagulashi da cokali
harararshi tayi
''baki isa ba ko zaka ci kayi amanshi sai ka ci,maryam tafiyarki kije ki kwanta Allah ya bamu alkhairi,gobe insha Allahu zamu tattauna''sallama ta yi mata tayi shigewarta yayin da mamin ta ja plate din ta soma nado taliyar cikin pork tana cusawa abdallah,shikam ya bude ciki ya dinga diba,dama yana so kasuwa kawai yake kaiwa
''almiri ashe kana ci din kenan shegen girman kai yasa kace baka ci''mami ta fada tana dubanshi
dariya ya qyalqyale da ita ya kanne ido daya
''so nake dama mami ta bani da kanta nasan sai yafi dadi''
''Allah ya shirya min kai abdallah''ta fadi tana murmushi
๐๐๐๐๐๐
tafiya take bata ko ganin gabanta saboda takaici da baqinciki,wai sai yaushe ne burinsu zai cika kan abdallah๏ผ,sai yaushe zasu samu nasarar kau da abdallah daga doron duniya,da wannan tunani ta samu da qyar ta maida kanta bangarensu
adnan da zahariyya dake dakon zaman jiranta cike da buri da fatan jin daddadan labari suka taso
''yaya nene๏ผ,anyi nasara kuwa๏ผ,rashin ganin nashi nada nasaba da aikin mu kuwa๏ผ''saida ta fada jabar saman kujera kafin tace
''mun sake fadu wannan karon ma babu nasara,rashin nasarar kuma yafi na kowanne lokaci''
adnan ya sake matsowa gabanta
''yaci dinne bai mutu ba๏ผ''
''ina ma yakai ga cin,ai ko ci baiyi ba,kuma hakan baya rasa nasaba da wannan tsinanniyar mai girkin da na rasa inda bintu ta samota,yarinya sai shegen kwarjini''
''oh shit๏ผ''adnan ya fada bayan ya dunqule hannunshi ya daki tafin hannunsa,zahariyta kuwa kasa magana tayi face bin sahun uwarta da tayi ta fada saman kujera
a sukwane ya koma shina ya zauna bayan yayi qasa da