Showing 102001 words to 105000 words out of 162126 words

Chapter 35 - ABADAN

yana fadin
''ke hajiya ki iya bakinki,ai dama kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa,bamu da mutumci kamar yadda ke ma baki da shi don babu mai mutumcin dake hada sabgarsa da mu''
''kai yaro dakata a haife na haifeku gaba dayanku,to wallahi duk ba tsoronku nake ba,kudi ne bazan biya ba kuma ku saurari sammacin kotu sai nayi shari'a da kai kam cikin da ka yiwa diyata tun.......''
wani kyakkyawan duka da ya sauka tsakiyar kanta ya haddasa wa qwaqwalwarta daina aiki na wucin gadi,wasu taurari suka kewaye idanunta take ta sulale ta fadi a gun,sai da ta kusa kusan minti biyu sannan jinta ya dawo sai ta kasa bude idanunta,mugu ya tako inda take ya tsaya qerere a samanta yana dubanta
''da niyyar kasheki nazo ke da wancan wawan dan naki qauran mata,amma kunci darajar abinda yake cikin yarki wanda dana ne kuma jikanki,nasan kina jina don ban miki dukan da zaki mutu ba,amma zan baki zabi biyu,ko ki biyani kudina ko kuma na dauke yarki ta zama matarmu,na baki nan da kwana biyar kiyi shawara''


ya juya ya isa inda zubaida take ya dagata ya rungumeta yana shafa cikinta
''kada ki sake ki bari wani abu ya samu cikinan don ina buqatar wanda zai gajeni,duk dan kaza kazan(ya duro ashar) da ya kuma takuraki ki takashi kema yadda ranki keso''ya fada yana sakinta,ga mamakin adnan murmushi yaga tana yiwa mugu har suka juya suka fice daga gidan wanda shigowar mami suka yi kacibus suna ficewa a qasa ita kuma tana shigowa da motarta
bayan ta faka motar cikin mamaki ta fito ta nufi gun security guda uku da su kadai yanzu suka rage a gidan
cikin girmamawa suke gaidata don har yau suna son uwar gijiyar tasu,tambayarsu tayi
''wadan nan mutanen kuma daga ina suka fito''
daya daga cikinsu ne ya amsa mata
''daga cikin gida''fuskarta qunshe da mamaki ta sake tambayarsu
''cikin gida kuma๏ผŸ,gurin wa suka zo๏ผŸ''
wannan karon wani daban ne ya amsa mata
''gun hajiya nene,ai sun dade suna zuwa gunta,ko kin manta ne hajiya,kwanaki ke ta saka kika basu kudin mota''
cike da mamaki ta nuna kanta
''ni๏ผŸni kuma usaini๏ผŸ''
''eh hajiya ke''
ganin sun zuba mata ido sunata kallonta sai ta dauko wani batun
''yanzu ina su samuel da ibrahim''
''hajiya duk an dakatar da sh daga aiki,kuma da aka tambayeki kika ce kin amince,yanzu saura security biyar daga cikin goma sha biyar dake aiki cikin gidannan''


wani mamakin ya sake kamata,jinjina kai ta dinga yi don duka batasan anyi haka ba,ta yaya zata kori su ibrahim bayan sune manya manyan security na gidan tun zamanin alhj abdulkareem mai nasara na da rai,muta ne ne masu amana da cikon alqawari
''ka nemi numbers dinsu ka kira ka kirasu gaba daya kace ina son ganinsu daga yau zuwa gobe,wanda baka samu,contact dinshi ba ka dauki mota ka bishi inda kasan zaka sameshi''
cikin jin dadi yace
''yes madam'' don dukkansu suna fara ganin alamun lallai sauyi ne wata qila yake tunkaro gidan


Har tayi gaba ta dawo
''kada a sake barin wani mutum makamancin wadancan mutanen su shigo gidan nan''
cike da bin umarni suka amsa
waiwayo wa ta sakeyi
''amm...usaini,bama su ba duk baqon da za'ayi ku tabbatar da wane shi kafin shigowarsa gidan nan kamar dai yadda aka saba a daa''nan ma amsa mata sukayi a ladabce kana tayi gaba


idanunta suka kai ga hanyar sashen abdallah,can qasan zuciyarta taji tana son shiga saidai wani abu ya taso ya danneta,haka tana ji tana gani ta sauya akala ta shige bangarensu tana ambaton ya Allahu
har zata shige ta ringa jiyo ihu ihu a bangaren nene,juyawa tayi ta nufi sashen nenen don ganin meke faruwa

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

A hankali ta qarasa shigowa cikin dakin hannunta dauke da tray dake jere da kwanukan abinci a kansa,gabanshi ta qarasa ta ajjiye tray din,wanda har ta shigo ta ajjiye din yana zaune kan wheel chair dinshi kanshi a duqe a qasa,shi kadai ahi da Allahn sa yasan abinda yake ji cikin qirjinsa,wani irin zafi radadi da quna,da zai iya yana kin fiddo da zuciyarshi zaiyi waje ya huta irin azabar da yake ji,bai taba sanin so da kishi masifa bane sai yau,baiyi tsammanin son da yake mata har yayi irin wanann girman ba,ya sani cewa yana ganin qimarta fiye da duk yadda yake ganin qimar wata diya mace a duniya idan ka dauke maminsa,tana da wani girma na daban a idaniyarsa da zuciyarsa ma baki daya,wannan ne karo na farko da tunda yazo duniya kishinsa kan wata diya mace ya motsa,shi kansa baiyi zaton kishinsa ya kai haka ba,duk da agefe guda qoqarin goge firman laifin da ta yi masa yake ta faman yi saidai ina zuciyar taqi aminta,idanuwan su gaza daina hango masa maryamunsa tsaye da wani


batasan gurin da ya tsaya ba tare suka taho daga rafin malam dogo amma sai gashi har ta shigo gidan sukayi sallar magariba da isha bai shigowa ba,sai bayan isha'i ya shigo bai kuma tsaya ba kanshi tsaye ya shigo dakin dama kuma bai tadda inna wuro ba a tsakar gida ta ahiga daki dauko kayan kadinta


Jikinta gaba daya a sanyaye take,wani saahen na zuciyarta na ganin wane laifi tayi ba ita ta kira ahmad ba kuma ta riga da ta gaya masa tare suke,Allah kuma shaida ne bada wani abu ta kula shi ba,gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu
wannan tunanin ya qarfafa mata gwiwa tana tsaye a gabanshin tace
''abdallah''
''abdallah''shiru taji tamkar ba da shi take ba
''abdallah ga abincinka,ina ka tsaya na ahigo inna wuro tana tambayata inda ka tsaya sai qarya na mata,me yake damunka ne๏ผŸ''
shiru nan ma taji
''na zuba maka tuwo ne inna ta.....''
dagowar da yayi ya sanyata ja da baya zuciyarta na bugun uku uku,wani irin birkicewa ta ga idanunshi sunyi,wani matsanancin tashin hankali take hangowa qarar cikin idanunshi,farar fuskarshi ta hada ja kamar wanda aka mammara


Ga mamakinta sai taga ya saki murmushi yana fadin
''na gode da abinci,amma bazan iya ci ba''ya maida kansa qas kamar yadda tazo ta taras da shi,ajiyar zuciya ta sauke cikin,mutuwar jiki ta sake dawowa gabanshi ta duqa tana mai janyo kwanunkan
''dazun da rana baka ci abinci ba,bazai yiwu yanzun ma kace ba zaka ci ba''ta fara zuba masa kana ta miqa masa


Sake kallonta yayi,wannan karon raunin dake tattare da idanun abdallahn yafi na dazu,ita kanta sai da abun ya taba ta,irin raunin da ko sanda lalura ta sameshi bata gani,cikin idanunshi ba,murmushin ya kuma yi kana yace
''haqiqa Allah na iua jarabtar bawanshi ta kowanne fanni da yaga dama,ban yarda cewa ni abdallah cikakken maraya bane sai yau,na rasa mahaifina na rasa soyayyar mahaifiyata haka na rasa soyayyar macen da na riga nayi amanna cewa zata zauna da ni a duk yadda nake ko kuma nazo mata,saidai tunani na ashe kuskure ne๏ผŸ,duk da bai kamata naga laifinki ba maryam baki rufeni ba,kin gayamin baki sona bani kike so ba amma na gaza cika miki muradinki na rabuwa da alaqaqai abdallah,baqinciki na daya maryam igiyar aure na da aka hau kan martabarta aka tuburbudawa qasa,na yaba miki kuma ina kan yaba miki kan namijin qoqarin da kika yi kike kuma kan yi na bawa,rayuwata kariya,haqiqa bani da abunda zan iya biyanki da shi,na miki kuma alqawarin da zarar na samu lafiya zan cika miki burinki na rabuwa da ni,kici gaba da yimin alfarma zama da ni kada wasu su fuskanci wani abu,na miki alqawarin daina saki yimin duk wata wahala,kidai ci gaba da zama da ni din har na samu lpy idan da rabon haka ni kuma na baki 'yancinki da kike da muradi''


Hakanan taji maganar ta daki zuciyarta sosai,tayi yinqurin duban qwayar idanunsa saidai ta kasa tilas tayi maganar tana kallan wani gurin daban
''yanzu me nayi maka haka da kake gayamin wadan nan maganganun,duka mai ya taso da su๏ผŸidan maganar ahmad kake ni babu komai tsakani na da shi hasalima zuwa yayi ku gaisa''
ambatar sunanshi shi ya dago hasalar da yaketa qoqarin dannewa,cikin tsawa yace
''ahmad yake ko watever ba ruwa na da shi,ba maganarsa muke ba anan,magan ce tsakanin na da ke,don kin kula shi kun saba har kunsan juna wannan tsakaninku ne,igiyar aure na nada qima da mutunci a wajena tunda na biya sadaki,ni ba ragon namiji bane tun fil'azar jarabtar da Allah yayimin bazata zama silar zamowa na rago ba,kin cancanci kiyi hakan don a yanzun kinfi qarfin abdallah nakasashshe,sai cikakken namiji mai lafiya ba irina ba,saidai ki sani,har yanzu igiya ta na kanki so kiyi respecting dinta,sannan a hakan na tabbata nima akwai masu sona wadanda zasu iya zama da ni duk yadda nake''
sai ta qarasa gigicewa baki daya,kamar zata shide da jin fassarar da ya mata,kanshi tayo gaba daya tuni idanunta sun fara fidda ruwan hawaye,da sauri ya dakatar da ita
''kada ki cemin komai,bana buqatar naji komai''daga haka ya danna gefan keken ya soma yunqurin ficewa daga dakin,wani irin kuka ta saki ta fada saman katifa bai dakata ba har ya fice daga dakin


tana iya jiyoshi shi da inna wuro suna hirarsu abinsu tamkar babu komai cikin zuciyarsa,yayi qoqari matuqa wajen kawar da duk wata damuwa da yake jin tana taso masa
''bawan Allah in sha Allahu jibi tsoho alhaji zai dawo daga qasa mai tsarki,da izinin Allah kasa rqn warkewarka nan kusa''a fuska ya nuna jin dadinsa sosai,amma farincikin da yake sa ran ji duk lokacin da aka gaya masa tsoho alhaji zai dawo sam baiji shi ba,bai san dalili ba,amma yana zaton hakan baya rasa nasaba da abinda zuciyarsa ke gaya masa na cewa yana warkewa rabuwarsa da maryam tazo


Shigowar musatafa kenan abdallah ya maida shi yace yake ya kira masa mairo,babu jinkiri ya fice kuwa,ya dubi inna wuro yana fadin
''sam yarinyar nan ta daina shigowa inna ko ta miki wani laifi ne๏ผŸ''
kai ta kada
''a'ah a'ah,ni,babu abinda ya hadamu,abinda na lura kawai tana wasan buya ne da maryamu,ban sani ba ko ita ta yiwa laifin''karon farko amsar dalilin wasan buyab ya fado zuciyarsa,tana kwancen ta jiyosu batasan dalili ba sai taji ruwan hawayenta ya dadu ta sake qunshe kanta cikin filo hawayen na sauka qamshin turaren abdallah da ya kama katifar na ratsa qofofin hancinta,cikin sakanni ya haifar mata da wani baqon yanayi cikin zuciya da gangar jikinta



duban inna wuro yayi yace
''inna''
''na'am bawan Allah''ta amsa masa bayan ta dubeshi tana ci gaba da kadin
''magana nakeson muyi da ke inna ta fahimta''sai ta ajjiye abinda takeyi din tq bashi dukkan hankalinta''uhmmm ina saurarenka''
''inna na daukeki tamkar kakata haka nake jinki had zuciyata akwai maganar da nakeson gaya miki tuntini''sai ya matsa gefan kekensa take ya qara matsawa da shi gaban innar kadan sanann cikin qasa da murya ya fara mata maganar



lokacin da taji sallamad meron sai da taji wata faduwar gaba,haka siddan ta kasa zama sai ta miqe ta yaye labulen window din dakin,shi abdallah yake fuskanta don haka ta sake lafewa sosai don kada ya hangota


Tare da mustafa suka shigo,tana ido biyu da abadallah ta fara sussunne kai cikin duqunqunan nan hijabinta,inna wuron ce ta dubeta
''au,to kuma meye hakan,wa kike kunya ne๏ผŸkinga bani na kiraki ba dama tunda kin gujeni kinga mai kiran naki''
gaban abdallah tazo ta zauna kana ta gaida shi
''bani amsawa tunda bamusan laifin da muka yi miki ba kika gujemu''
qara dunqule kanta tayi guri guda wani dadi ya rikito mata kamar ta tashi tayi rawa
''ni dai babu komai''haka ta fada,abdallahn ne ke janta da hira abunka da gwanar surutu tuni ta saki jikinta suka fada hirarsu,daga bisani maryam taga inna wuro ta tattre kayanta ta shige daki ta barsu


qasa qasa suka koma magan ta yadda bzata iya jiyosu ba,sai fuskar mero da ta gani ta fadada ta fara'a tana sake boye kanta,ji tayi ta soma jin juwa juwa sabida haka ta saki labulen ta koma kan sofa tana dafe da qirjinta
''kada ki jawomina bunda bazan iya ba,kada kimin irin wannan rashin adalcin,ki rabu da abdallah bai dace da ni ba,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,abdallah ba mate dina bane''abibda ta ringa fada kenan qasa qasa wani hawaye mai zafi na bin kuncinta


tun tana duba agogo har ta haqura,sai da ya buga qarfe sha daya daidai har ya dora da mintina sannan ta sake jiyo muryarsu
''ki tabbatar gobe tare zamu fita rafi dake kinyi alqawari๏ผŸ''kai ta gyada kamin tace
''eh nayi alqawari''
shima kan ya jinjina
''to shikenan sai da safe goodnight sweet dream''duk da bata fuskanci mai yace ba sai ta saki dariya tana waiwayensa har ta fice


ya janye idonsa yana sauke ajiyar zuciya,har yazu nauyi da zafin da yake ji a qirjinsa yana nan babu ainda ya ragu duk da faman turereniya da yake masa amma sam ya gaza cimma nasara,cike da kasala ya danna madannin tafiya keken ya nufi dakin da shi cikin wani rin yanayi na jin kadaici da zazzafar qauna




*mrs muhammad ce*๐Ÿ‘‘



๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ
[8:50pm, 9/30/2017] Huguma๐Ÿ‘‘: [3:02pm, 9/30/2017] Huguma๐Ÿ‘‘: ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*

5โƒฃ1โƒฃ






*_Allah S W A yana fada cikim alqur'aninsa mai girma''haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu abubuwan tambayane (ranar alqiyama)_*


*_cikin wata surar kuma yana cewa''ku cika alqawari lallai alqawari abin tambaya ne (ranar qiyama)_*


Da sauri sauri mami ke tafiya har ta isa ga sashen nenen,nenen ta taras kwance male male tana zabga ihu saboda tashi data kasa yi,zubaida da danan na durqushe kanta suna qoqarin dagota
ta qarasa gabansu tana shirin taba nenen tana tambayarsu
''me ya sameta,lafiya๏ผŸ''zubaida ta bude baki dom bata amsa,da sauri nene ta sake saka wani ihun tana fadin
''wayyo Allah na,kada ku kulata,kada kuyi mata magana''
itadai zubaida da batasan me hakan yake mufi ba tayi zaton ko qwaqwalwar nenen ce ta samu matsala
''wallahi faduwa tayi ne,bamusan me ya sameta ba''ta bawa mami amsa da haka don batasan me zata ce mata ba


idanu adnan ya zq
aro don yasan babu shakka a yau dai asirin jikin mami ya gama karyewa don sun qetara sharadinsa
''Allah ya tsine miki dai albarka zubaida,haihuwarki bata qare ki da komai ba,kin sake jawo mana wata asafar,kin karya mana asiri''nenen ta fada hawaye shabe shabe,kallon rashin fahimta mami da zubaida ke mata,tuni adanna ya juya ya fice mami ta bishi da kallo


ta dawo da kallonta ga zubaida zata mata magana ifanunta ya sauka kan cikinta sai ta kasa magana ta tsaya kawai ta zuba mata idanu,udon zubaidan ya cika da qwalla don kusan duk gidan babu wanda take ganin mutumci mituncinsa kamar mamin,babu wanda yace komai nenen ta sake sakin ihu
''adnan kaje ka duba min yata zahariyya,kada su hallakamin ita''cikin tashin hankali,mami ta kalli zubaida
''kamata mu kaita sama na mata allurar barci ko zata dawo hayyacinta''
''wallahi bintu kada ki sake kice zakimin allurar bacci,lafiyatq qalau,jikina ne kawai yayi nauyin kuma zai warke,na tsaneki wallahi bintu taurin ran danki abdullahi duk shi ya jawo mana wann masifar da muke ciki''


kiran sunan abdullahi ya sanya gabanta faduwa har sai data kirq sunan Allah,haka suka kinkimeta da qyar suka iya haurawa da ita saboda azanar nauyinta,mamin ta yi mata allurar barcin,tana ta surutanta da su basu fahimvi komai ba ciki saboda basu san me ta qulla ba da haka bacci yayi awon gaba da ita


Ta fito daga sashen nene ta nufi sashenta tana dafe da kanta don tun sanda ta kira sunan abdullahi kanta yake mata ciwo,suna take ta nanatawa cikin zuciyarta
ta qarasa bedroom dinta ta shiga tayi wanka ta daura alwala ta bada faralin sallah,har yaznu ciwon kan uaqi saukar mata don haka ta balli magani ta sha ta kwanta,babu jimawa nannauyan bacci ya dauketa


Yana zaune kan kekensa yayi kyau cikin jallabiyya fara sol,fuskarshi qunshe da murmushi yana kallonta,itama shi take kallo,a hankali ya fara tahowa gabanshi tana miqa masa hamnu saidai duk sanda ta kusa zuwa dab da shi keken da yake kai sai yayo baya da shi taga ya mata nisa


Sai ta fara binsa da gudu keken na sake tafiya da shi saidai yana fuskantarta fuskarsa kuma dauke da murmushi,sai da sukayi tafiya mai nisa kana keken ya tsaya cak,sai taji an,dafa kafadarta da sauri ta waiwayo,maryam ta gani tsaye kusa da ita tana murmushi,ta nude bakinta zata kira sunanta bat taga sun bace mata gaba dayansu,dube dube ta dinga yi amma ta nemesu sama ko qasa ta rasa,wani rami ta gani a gabanta ta tafi a hankali ta keqa sai ta hangosu ciki suna zaune,ji tayi luuu ta tafi itama zata fada ciki


firgigit ta farka tana ambton sunan Allah gami da dafe kanta dake sara mata kamar zai tsage gida biyu,tafi minti talatin a haka sannan taji sannu a hankali ciwon kan yana raguwa yana raguwa har ta daina kinsa gaba daya,sai ta jita sawai kamar wadda aka kunce daga sarqa
''abdallah,maryam''ta fada a hankali



Kamar wadda aka tsikara ta dago da kanta ta miqe da sauri ta sanya hijabinta ta fito,hanyar sashen abdallahn ta nufa kanta tsaye tana tafiya wasu abubuwan da suka faru suna fado mata tamkar mutumin da yayi mafarki yake tuna abunda ya faru,kallo daya ta yiwa sashen nasa jikinta ya gaya mata ba lafiya ba,qofar na nan a lallauye yadda su muugu suka yi mata ranar da suka zo nemansa,jikinta babu qwari ta shiga ciki ta dinfa duba ko,ina da ina ta,iya qurar da bangaren yayi kawai ya isheta amsar cewa gidan ya dade babu mai rai a cikinsa,hotunan abdallahn ta dinga bi tana kalla bata ankara ba kuka ya subuce mata,zaman dirshan tayi saman carfet hawaye masu dumi suka shiga turereniyar fita daga idanunta


''ina ka shiga abdallah,ina ka tafi ka barni''abinda ta donga fada kenan a hankali cikin kukanta
mafarkin da tayi dazun ya dinga dawo mata tar kamar a lokacin takeyinsa,babu shakka ta tabbatar abdallah da maryam duk inda suke suna da buqatarta,suna da kwadayin ganinta
maganganun nene suka sako kai suma
kada kuyi mata magana,shikenan kun karya min asiri
asiri๏ผŸ
asiri wanne iri take nufi,wa aka yiwa asiri kuma akan ne ya karye๏ผŸduka daga shigowarta gidan a tau tunaninta ke ta mata shawagi,mutanen da ta gani sun fita daga gidan kamar ta taba ganinsu cikin gidan,cikin wani dare cikin kuma wata rayuwa data yi a baya,rayuwar data dinga jinta kamar rayuwar cikin mafarki,cikin rayuwar ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login