Showing 150001 words to 153000 words out of 162126 words

Chapter 51 - ABADAN

sama musu uba wanda bai dace da su ba,wadan nan yaran haqiqa jarabta ce Allah ya hadamu da ita ko ince hukunci ne tun a gidan duniya da Allah yayi mana kan bijirewa umarninsa da mukayi,hanya daya ya kamata mubi wadda zamu nunawa Allah mun karbi jarrabawarsa shine mu ruqe 'ya'yan,muyi musu kyakkyawar tarbiyya,don Allah don annabi kada mu barsu su lalace su zama kamar yadda ubansu yake,kada mu bari tarbiyyarsu ta gurbace kamar yadda ta ubansu take,kada mu bari su zama guba cikin al'umma,don Allah muyi iya yinmu kan rayuwarsu,yadda malam ya mutu kawai izina ce a garemu baki daya,kada mu bari wataran su zama silar da za'a la'ancesu a la'ance mu koda ta Allah ta kasance akanmu''
babu wadda jikinta bai mutu ba,haka suka mata godiya kowacce idanunta shabe ahabe da hawaye zuciyarta cike fal da nadama da dana sani tana kada kan yayanta saboda yadda warin cikin gidan ke fitowa waje tana kama hanyarta


A haka duka suka fashe saura ita da habiba,hannunta habiba ta kama tana fadin
''mu tafi zahariyya,nikam sai yadda Allah yayi dani,bani da kudin da zasu isheni naje har abuja,amma zan fara da zuwa katsina inda dangina suke,daga can nasan zasu maida ni gida''haka suka kama hanya suna tafe suna kuka,idan ka,gansu sai ka tsammaci,mahaukatane suka gudo daga gidan gajiyayyu


Da qyar habiba ta samu mai motar daya yadda zai kaita katsina bayan ya mata tambayoyi ya tabbatar ba mahaukaciya bace sabida dauda da yadda take buga tsami,don sai sukai sati basuyi wanka ba haka gashi ba suturar arziqi garesu ba,haka al'adar gidan malam ko ince boka na hayi take,shima driver din a boot ya saka ta bayan ya lafta mata kaya don kada passingers su ganta ko suji doyi su fasa shiga



Da qyar ta qarasa jikin get din gidan ta dinga bugawa,ibrahim daya daga cikin security din shi ya fara bude yar qaramar qofar gidan yana cewa waye,turus yayi ganin mace mai siffar mahaukata tsaye a gabansa,baki ta waahe jajayen haqoranta suka bayyana tana fadin
''yauwa ibarahim,sannu ashe ka dawo aiki''kai kawai ya gyada mata
''eh na dawo''
''nene na tana ciki kuwa''rai ya hade mata kana ya girgiza kai
''bata nan''
''to mami fa,hajiya bintu''
''tana ciki''sai ta fara qoqarin shigewa tana fadin
''alhamdulillah''tsawa ya daka mata kana ya tsaidata
''hala irin mahaukatan nan ne da ke gudowa daga turu ko''
sai ta dubeshi
''haba ibrahim,na kama sunanka din,na kama na nene,na kama na mami kuma kace min mahaukaciya,zahariyya ce fa,zahariyyan nene''cike da mamaki ya zuba mata ido,yakai a qalla kusan minti goma yana qare mata kallo kafin ya ganota ta hanyar idanunta,tab aikam ko giyar wake yasha bazai barta ta shiga ba,mutanen da suka so hallaka iyayen gidansa mutane na gari,haka kawai ta dawo ta sake wargaza zaman lafiyar gidan bayan sun samu nutsuwa da kwanciyar hankali,yarinyar da bata da mutunci,bazai iya tuna sau nawa tasanya hannu ta tsinka masa mari ba a matsayinsa na soja,ko ranar da zasu sallameshi ita da uwarta bai manta irin zagin,cinmituncin da suka dinga dura masa ba,wata yazo qarshe amma da suka tashi korarsa hanashi salary din watan sukayi,wanda hakan ya zama sanadiyyar rasa danshi(hmmm,ka shuka alkhairi dai sai kaga da kyau)



murna ta fxatonta zaice ta shiga sai taga ya hado gurar sama data qasa ya hadeta gu guda
''wallahi ko cewa akayi idan baki shiga ba mutuwa zakiyi saudai ki mutu,na baki minti biyar kibar qofar gidan nan,don duka ahlin nene yanzu basa cikin gidan nan,sun shiga duniya,kema gwara kici gaba da bin sahunsu''yaja qofar ya rufe,zubewa tayi a gun tana kuka haiqan don tasan bata da wani gata kuwa


minti biyar na cika ibrahim ya sake leqowa ya sameta zaune,baice uffan ba ya fara qoqarin ciro bindigarsa yana saitata a kanta
''bari na kasheki kinga an rage iri''habawa,kamar ba mai ciki ba haka ta dinga fella gudu har ta fita babban titi,tsayawa tayi tana haki da waige waigen ko ya biyo sahunta,daidai lokacin da motar gida mahaukata ke zagaye tana kame tababbun masu rangwamen gata dake yawo kan titi suna kaisu gidan mahaukata din basu magani bisa umarnin gwamnati,cikin sa'a kuwa suka hangota,ba bata lokaci suka mata tara tara suka damqeta suka cusata cikin motar,ihu take tanason ta subuce musu fadi take
''wallahi niba mahaukaciyya bace da hankalina,gidanmu naje aka biyoni da bindiga shiyasa na gudi titi''wannan surutan nata suka qara musu amanna kan mahaukaciya ce

🍂🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Cikin kwanakin kusan babu abinda yake damunta illa kewar abdallahn ta kawai



Kewarsa take gaba dayansa bawai wani abu daban ba,don kusan bayan kowacce awa uku zai kirata ya debe mata kewa da daddadar muryarsa,mamar kowanne lokaci yauma suna maqale a waya tana kwance ta gama shirin bacci
''baby,anya kuwa zan iya cika kwana goma nan kuwa,na hisham zan baro na taho?''a shagwabe tace masa
''sabida me?,ka barshi kawai ka qarasa din''
''baby na gaza jurewa wlh,kewarki na son kasheni,bansan kuskure na tafka da na tafi ba baqarami ba sai yanzu,kuma yadda nakeji na tabbata kema haka kike ji''
''wata qila ma na fika''ta fada a hankali,kamar ya taka rawa haka yaji saboda farinciki,son da maryam ke nuna masa irin wanda yake fatan samu ne daga macen aurensa,bashakka shikam dan gatan mami da maryamu ne
sai da suka raba dare suna musayar zafafan kalaman qauna kafin suyi sallam


Da wannan damar mami itama tayi amfani ta samo mata masu koya mota har gida matar ke zuwa tana koyawa maryamun,a haka lubabatu ta nace har itama ta fara koya,cikin sati guda sai gashi maryamun ta fara qwarewa,matar kam jinjina mata tayi don lallai kam na qaramar basira take da ita ba

🍂🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Tun jiya abdallah ya sanar da ita suna hanya in sha Allahu,saboda tsabad murna adaren kasa komawa bacci tayi,zama tayi ta dinga lissafe lissafen abubuwan da zasuyi a gidan gobe,tunda ba zasu shigo ba sai kusan magariba,har yace da yasan haka zata masa taqi komawa bacci da bazai gaya mata ba


A parlour dinta ta samu baaba uwani da lubabatu sun gama breakfast suna zaune suna hirarsu abinsu,gu ta samu ta zauna da yawancin lokuta bata fitowa da wuri sai sun gama shan hirarsu da abdallah tayi wanka sannan ta fito ta karya,cikin girmamawa ta gaida baaba uwani suka gaisa da lubabatu sannan ta sanar musu isowar abdallan
''to alhmdlh,Allah ya iso da su lafiya''inji baaba uwani cikin farinciki,ba tare da bata lokaci ba suka soma yan sabgogin da duk ya kamata suyi din,duk da gidan amarya dama ba wani abu yaje da buqatar a sauya masa ba,amaryar ma irin maryam ami tsafata kula da tattali
lubabatu ke ce mata
''babu wani dan gyara ne haka adda da zakiyi?''batasan sanda ta harareta ba don sarai ta fuskanci me take nufi
''halan wannan karon so kuke abdallah ya kaini kushewa ba asibiti ba''ta fada a zuciyarta,a fili kuwa cewa tayi
''uhhmmm,baku fa da kunya sosai yaran yanzun''dariya lubabtu tayi tana toshe bakinta tare da cewa
''Allah ya bawa adda haquri''


Lubabatun ke mata zancan girki dane dame za'ayi?,sam ba wanda ta yadda ta bawa girkin don tace da kanta zatayi,sabida wannan ne karo na farko da zata yiwa mijinta girki cikin gidan aurensu,abinci ta tsara zata masa kala uku baya ga kala kalar farfesu shima uku,sai drinks don haka tun sha biyun ta fara ragewa don kada lokaci ya qure mata


zuwa la'asar ta kammala komai sai miya da bata qarasa ba guda biyu su din ma suna kan wuta saura kadan su kammala dahuwa,tana falo tana dan hutawa saiga baaba uwani dauke da yar jakarta,cikin mamaki maryam ta dubeta
''a'ah,baaba ne zakiyi da jaka da ranar nan?''
''gida mana meramu,zan koma gidan hajiya,tunda yau abdullahi zai dawo ko''
''haba baaba,ai kwa bari sai gobe tunda baku san zai dawo din na sai dazu da safe fa''bakinta ta kama
''rufamin asiri meramu,haba don rashin hankali sai in zqune muku gotai gotai,hajiya ma ta riga da ta aiko direba,ya iso ma yana waje yana jira na''tana mita ta miqe ta haura sama ta daukowa baban atamfa mai kyau turmi daya,sinqin sabulu da turare sai plate din takalmi guda daya,godiya sosai baaban ta dinga mata har ta sata jin kunya,hijabinta ta zura saboda umarnin abdallah na sanya hijabi ta rakata har bakin get suna yiwa juna godiya


Tana dawowa ciki saiga lubabatu itamq da nata kayan,hararata tayi tace
''wallahi baki isa ba,kada ma kice min tafiya zakiyi,ku barni ni kadai bayan sai magariba zasu shigo''dariya hindatu tayi
''wallahi ya hisham ne yace da naji zaku dawo na bar muku gidanku,idan kuma na zauna duk abinda nq gani nina jawowa kaina,kai take gyadawa
''shi hisham din ya gaya miki haka?,to babu inda zaki kuma zai shigo tamu ni da shi''haka ta tare hindatun ta hanata tafiya



qarfe shida ta fito daga wanka ana ta shiye shiryen kiran sallah magariba,duk bayan mintina sai ta duba wayarta ko zata ga kira ko saqon abdallah amma shiru,a haka ya qarasa gaban madubi ta tsara kwalliya mai cike da tsari bayan ta mulke jikinta da nau'in turaruka kala daban daban,gaban sif dinta taje ta bude cike da tnanin wacce shiga zata yi ma,ta jima tana nazari kafin daga bisani ta fidda wata gown mai bala'in kyau,ashe ce wadda aka mata ado da jajayen dutsina daga gin breast din da kuma furanni,ta gyara gashinta tayi masa kanta daurin V shafe da jan dankwali,fashion ta saka na jajayen sutsina take ta fito gaba daya kamar wadda aka sauya


Babban hijabi ta saka zata tada salla kenan taji knocking ta tambayi waye lubabatu ce tace ta jirata sallah zatayi tana fitowa,tana idarwa ta sake duba lokaci gari har ya dan fara duhu,ta cire hijabin ta sake gyara daurin nata kana ta fito falon,burner ta kunna dake lunguna na gidan duka ta sake sa turaren wuta daidai lokacin da lubabaatu ke fitowa da shirin ta na tafiya,mutuwar tsaye lubabatun tayi
''adda maryam!,kinganki kuwa,shan kyau irin wanann daukar magana haka?''dariya lubabatu ta bata ta dinga darawa,da qyar ta tsata suka fara sallama,ta tambaueta ta me takeso ta bata
''kome kika bani adda maryam yayi,ni ko zaman ma da nayi gidan nan ai ya isheni,ac din da nasha ta kwana goma bakiga har na canza ba,ga kuma babban kamu nayi ya hisham...''
''munafukai,ai dama daga yadda naga kuna wani kallin juna elh ma san da walakin kuma bari yazo sai na tsigaleshi''da sauri lubabatu ta rufe mata baki
''don Allah kada ki masa maganar,bai furta da bakinsa ba,yace kawai dai zamiyi maganar idan ya dawi zaizo gidanmu''hannunta ta cire daga bakinta
''ni kinga kada ki goge min janbakin tun kan wanda aka sa donshi ya gani''ta fada tana dariya kana ta shiga ta dauko mata itama atamfa saidai ita ta hada mata da kayan kwalliya


''inason in bada doguwar riga ki kaiwa binta amma ina tsoron halinsu,ni ko ganinsu a gida ma banayi anya ma kuwa suna nan''
dariya lubabtu ta sheqe da ita
''wallahi sunana,ai yanzu ko nawa za'a basu su miki rashin arziqi ba zasuyi ba,bakisan ya abdallah ne yasa aka debe su aka rufe ba suka kwana aka tsoratasu kan rashin mutuncin da suke miki keda mama?da suka dawo wallahi ko qofar dakin maman ma daina bi sukayi bare su kallshi,kuma da amincewata yasa akayi hakan,dama iskancinsu ya ishemu,yanzu kuwa idan kinji suna rashin mutunci a gidan uwarsu data koya musu suke saukewa''ta qarashe maganar tana cin dariya abinta
mamaki ne ya kamamaryam,a gaida abdallah,shikam halinshi ne idan dai zaiyi abun alkhairi ba wanda yakr gayawa saidai idaniyarka ta gane maka ko a baka labari,qimarsa ta sake daduwa cikin idonta,babu shakka duk wanda zaiga qimar mahaifanka ya tsare maka mutuncinsu ya girmamasu ya gama maka komai koda kuwa yankan naman juna kuke kai da shi,har harabar gidan ta rakata itama bayan ta sa driver ya dauketa zuwa gida


tsuru ta dawo tayi cikin falon tana ta duba lokaci,qarar wayarta taja hankalinta,dagawa tayi da sauri ganin sunan abdallah ne
''hello baby,kimin afuwa bazan samu danar dawowar yau ba,wani muhimmin abu ya tsaidamu,amma din Allah kada ranki ya baci,ki leqo yanzu compound na aiko wani yaro zai kawo miki saqo,idan bai iso ba ki jirashi a nan don bana so ya shigo min gida''kafin tace komai ya katse wayar,galala tayi da waya a hannunta ta rasa nayi ma,jikinta ba qwari ta zari hijabinta data tuna yace ta fito yayo aike


har tsakiyan gidan ta fito bataga kowa ba don haka ta tsaya nan wajen minti goma tana jira taga ko zai iso,ganin tsaiwar tayi yawa yasa ta yanke shawara komawa falo ta zauna bakin window ta jirashi a nan tunda tana iya ganin harabar gidan daga nan,jikinta ba qwari haka zuciyarta babu dadi tana rungume da hannayenta a qirji kanta a qasa har ta iso qofar falon



Cak taji anyi sama da ita baki dayanta,a tsorace ta soma laluben fuskar mutumin saidai tun kafin takai ga tozali dashi turatensa ya gaya mata *ABDULLAHINKI NE*,falon ya shige da ita wanda suna shigar wasu qwayaye masu launin ja da fari suka kama a take rubutun *AM BACK I LOVE YOU* ya bayyana,murmushi ya subuce mata bayan da suka hada ido,shima mayar mata da martani yayi kana suka zube kan kujera ya hau aika mata da saqonnin kewarta da yayi,da qyar ta lallabashi yayi wanka yayi sallar isha'i,kadan yaci abincin don baki daya hankalinsa na kanta,tana cikin gyaran gun da suka ci abincin taji baki daya an sungumeta bai sauketa ko ina ba sai bedroom dinshi wanda ayau suka fara amfani da shi


Rikice mata yayi kamar wancan karon sai hakan ya tsoratata,shima kuma ahankali sai ya dinga qoqarin daidaita nutsuwarshi ganin ta fara tsorata,cikin salo da qwarewa na namijin da yasan abinda yakeyi ya dinga tafi da ita,tamkar wani corse yayi a tafiyan tashi,saidai ba wani corse tsabar iya soyayya ne da tattalin mace,wata duniya ya jefasu wadda basu taba koda tunanin akwaita ba,soyayya ta gani zallah madararta daga gun abdallahn nata,soyayya ya gwada mata mai sanyi da tsayawa a rai,duk wahalar da take zaton shanta sai abun yazo mata da sauqi,duk da ba laifi ta dan jigata amma bai yi wani yawa ba


Tunda suka fito daga toilet yake zaune daure da towel,duk inda tabi idanuwansa na kanta,shi kadai yasan me yake ji game da ita cikin zuciyarsa,gaba daya ya hanata sakewa da mayen kallonshi,ga kunyarsa dake nuqurqusata,maganganun da ya dinga gaya mata kawai dazun idan ta tuna sai ta rasa inda zata saka kanta saboda kunya,sarai tasan ita yake kallo amma taqi kallonshi,sai da ta gama sharce gashinta ta saka hand drayer ta busar kana ta zo zata giftashi don ta dauki ribbom dinta dake kan gadon ta daure gashinta,baki daya ya janyota ta fada jikinsa ya dorata saman cinyarsa,cikin kunnenra yake rada mata
''baby Allah yayi miki albarka,banu shakka kin cika alqawarin,ki shayar da ni mamaki,ke din yar aljanna ce Allah baby kamar yadda kike yar baiwa''boye kanta ta dinga yi cikin gashin qirjinsa,yasa hannu ya sake maida mata gashin kanta baya
''amma baby yauma kamar nayi hurting dinki ko?''ya tambayeta a tausashe cikin tausayawa,kai ta gaya masa
''kadan ne ba yawa,kuma ba damuwa a haka ake daina jin zafin baki daya,zan dinga shiga ruwan dumi ne kawai''kissing nata yayi a goshi kana yace
''Allah ya miki albarka,ya bamu zuriyya ta gari,qarasa shiryawa ki rakani naga mami na,bazan iya kwana ban ganta ba''murna ta kamata sosai don itama tayi missing nata,duk da kunya na taba can qasan ranta


Har ta miqe ya kuma riqo hannunta
''baby kin kashe jiki da yawa,ko zaki iya taimakin na shirya?''girarta daya t dage masa kana ta kashe ido
''why not my''
kai ya girgiza fuskqrsa qunshe da murmushi
''lallai a shirye kike baby,get ready for d second round idan muka dawo,irin wannan kashe ido haka''hannu tasa ta rufe tafin fuskarta kana ta janyo wani dan towel din ta fara tsane masa jiki da shi,sai da ta gama shiryashi tsaf kana shima ya shiryata cikin wata doguwar riga mai hade da hijabi

*********

Dadi gun mami kamar ta goyesu haka ta dinga ji,cooler uku ta yiwa mamin na duk abinda ta dafa wa abdallan,kusan awa daya suna hirarau tare daga baya ta tasgi don basu guri su gana su biyu,don tsakanin da da uwa akwai sirri(qalubalenmu mata,sai kuje gaida uwar miji keda mai gida ki musu qifi qifi a tsakiya idan kika san uwar miji mai kawaici wadda ba zata iya ce miki ki matsa ki basu guri su gana ba,ke kuma ba hankali,na minti goma ba zaki iya matsawa ki basu guri ba,ta yiwuwu akwai maganar da alokacin takeso suyi da danta,don Allah mata mu gyara,koke ya yiwa haka keda mahaifiyarki ai bazakiji dadi ba)
mamin ce ta tambayeta ina zuwa
''zanje mu gaisa da mero ne''
''to...to,bata kuwa dade da barin nan din ba,sai da na korata ma tukun''tana murmushi ta sulale ta fice


Fes ta taras da meron da bangarenta,bisa dukkan alamu training na mami ne,tayi kyau da ita ta fara gogewa,haka nan fatarta ta qara kyau,kallo ta tarar da su sunayi ita da labaran din,suka gaisa sai ya miqe ya fice ya basu guri,murna mero ta dinga yi sosai ta dauko wannan ta kawowa maryam,ta rakito wancan ta bata har sai data ce ya isa,sun dan jima suna hira tana sake wayar mata da kai kan wasu abubuwan da tasan ta fita waye wa akansu,sai da ta kusa awa guda sannan labaran ya shigo yace mai gida na magana zasu wuce,kamar kada ta tafi haka mero taji tace amma zata zo itama taga gidan takwaranta,dariya tayi tace shikenan sai tazo din


A waiting parlour ta taddasu tsaye da mami,sai data rakasu har bakin mota,abdallah ya dubi mamin
''badai wata matsala ko mami zamanku da su labaran''murmushi tayi
''wallahi ko kadan,basu da matsala kam,ina jin dadin zama da alhamdulillahi''ya gyada kansa yace
''masha Allahu,mami sai da safe,muna ta missing dinki mami''murmushi tayi
''gwara ai kusan gurma ya kamaku da haka zaku saba ai''ta dube maryam da kanta ke qasa tace
''diyata ku gaida gida tinda qarfi da yaji sai kinyi surukuta da ni bayan nace ni bana surukutar,ki kula da kanki,kaima ka kulamin da ita,Allah yayi muku albarka''ameen suka amsa baki daya


Sai daya tsaya da ita a hanya ya mata siyayyar kayan maqulashe,qememe yace tayi zamanta a motar basai ta fito ba
''zan iya hadiyar zuciya fa idan kika fito wani ya kalleki,ke Allah zan iya mutuwa maryam a kanki,kishi ne da ni sosai,qaunarki ce tamin yawa,ba qaramin kamu ta yimin ba fa''dariya ta qyalqyale da ita''anya my kishin nan naka bai yawa ba''
ido ya zaro
''waya gaya miki?,bakisan yadda sahabbai keda kishi bane?,duk kishin nan nawa baikai nasu ba,kuma ma ai dole na kasance mai kishi saboda annabi muhammad S,A,W,yace maras

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login