Showing 138001 words to 141000 words out of 162126 words
yunwa,cikin muryar kuka tace
''naji amma pls ka barni,da underwears dina''duk da mood din da ya shiga sai da ta bashi dariya
''a garinku kika taba gani anyi wanka da underwears๏ผ....''
''please...''tayi saurin katseshi,shiru ya danyi kamar bazaice komai ba kana daga bisani ya saki ajiyar zuciya
''alright,amma fa gaskiya kin tauyeni maryam''
kusan dai abdallah rabin wanka yayi,fatar ta kadai ta tsone masa ido,sai sheqi santsi da qyalli take,ai a ranar ya bawa idonshi abinci sosai,gyaran da tasha gun haj laila ya gama rikitashi,kusan awanni hiyu suka kwashe cikin bayin yana bawa idonshi haqqinsa,duk da bai tabata ko kadan ba don ya fuskanci a tsure take sosai
Da ido tabi kayan baccin,abdallah dan garari ne qarshe,bata da daman musa masa tunda itama ya mata alfarma,kuma da sharadin zai mata abinda take gudun indai ta kuma yi masa musu,don haka ta karba ta koma toilet ta saka su,ta kalli kanta a madubi ba shakka ba qaramin kyau suka yi mata ba,saidai kunya ta lullubeta,dukka hannayenta da singalalin qafartava waje yake,haka nan ana iya hango saman qirjinta sabida net ne mai kama da code lace a gun,ba yadda ta iya haka ta fito tana rabe rabe,sai Allah ya taimaketa ya tayar da sallah lokacin da ta fito din,tayi hamdala ta haye gado taja tattausan bargon dake kai ta lulllube jikinta tana satar kallonshi,cikin nutsuwa yake sallarshi da cika qa'idoji sharudda da dokokinta,kallo daya zaka masa ka tabbatar ya samu ilimin addinin islama bada wasa ba,hakan na daya dah cikin abinda yasa take sake ganin qimar mami take sake qaunatar shi kansa abdallan,don ada ta yiwa 'ya'yan masu kidi kudin goro,saboda yawancinsu idan iyayenka nada arziqi mulki ko sarauta nasu damuwa da zuwa islamiyya,gani suke sunfi qarfinta,amma kuma ai baka fi qarfin shiga wuta ba ko๏ผ
don kaje gaban Allah kace rashin sani ne ya saka aikata ba daidai ba sam ba hujja bace a gun Allah,tunda ga makarantu na addini nan ko ina
Ganin yana niyyar sallamewa ya sata maida idonta ta gimtse don kada ya kamata tana satar kallonshi,murmushi yayi don tuni jikinsa ya bashi kallonsa takeyi,baice komai ba har ya kammala da dukka addu'o'insa kana ya miqe ya isa gadon yana jan bargon gami da cewa
''malama mai,baccin qarya a tashi a bani,abinci naci''da sauri ta damqe bargon bayan ta bude idonta,sai da ya tuntsire da dariya ganin yadda ta haqiqance wai ita bacci take amma daga jin anja bargo har ta zabure ta miqe,ya sakar mata bargon ya koma gefan madubi ya zauna bayan ya harde hannayensa ya zuba mata ido yaga ta yadda zata tashi,ai kam kasa tashin tayi qarshe sai ta yayimi bargon ta yafashi ta cukuikuye kana ta soma yunqurin tashi
''nikam a haka nakeson ki tashi''ya fadi yana boue dariyanshi,marairaice tayi
''amma fa babu mayafi kuma yakayan yan gajeru ne''
girarsa ya daga
''yes,haka nakeson in ganki,ko kinfison naje na kalli wasu๏ผ''ya fada yana dage gira.
Sai ta hade rai ta cuno baki kishin ya motsa,miqewa tayi ta sauka daga kan gadon sai ta tsinci kanta da sauya taku,binta yayi da kallo kamar ya hadiyeta haka yake ji har ta fice a dakin ya kasa dauke idonsa daga hanyar,ba kyau na fuska kawai Allah ya mata baiwa da shi ba har diri na jiki duka ta samu,shikam Allah ya zaba ya bashi bashi da abinda zaice da ya wuce alhamdulillah
Cooler ce mai dauke da friede rice da coleslow,sai farfesun hanta daban,kusan tare suka ci abincin saidai shi ya dinga bata tana karba cike da kunya
''kunyarki tayi yawa maryam,amma.....na kusa tsige miki ita''haka ya fada yana wane kashe mata idanu
cikin jikinsa ya janyota bayan ya kashe wutar dakin yana sansanar qamshin jikinta,wani qamshi yake ji na tashi a jikinta da bai taba jin irinsa ba,sai da ya gama sansana iya son ranshi kana ya hautsinota suka dawo fuskantar juna
''hira nakeso muyi irin ta ma'aurata my dear na''ya fadi bayan ya hade tafukan hannunsu cikin juna,sai ta sunne kanta a qirjinsa tana murmushi,batasan haka zama da masoyi yake da,dadi ba,sai,yanzu ta sake tabbatarwa tabbas a baya batasan farincikin zuci ba sai yanzu
''maryam''ya kira sunanta tamkar mai rada,bai jira amsarta ba ya dora
''gobe ne zamu shiga wata rayuwa,rayuwa ce da bamu taba sanin ya take ba sai a labari,rayuwa ce da bamu taba dandana irinta ba sai a mafarki,zama zamuyi na dindin din,ina son don Allah maryam ki riqe amana ta,ina sonki da yawa ina qaunarki fiye da yadda kike hasashe ko zato,zuciyata bata taba dandanar soyayya wata diya mace ba baya ga mami na sai akanki,kinsan gausawa sunce zo mu zauna zo mu saba,ni yarima ke sarauniya,inason mu gina masarauta mai cike da ni'ima nutsuwa da kwanciyar hankali,ina so matata ta kasance tamkar qawata,qanwata,yayata mahaifiyata mahaifina da kuma 'yata ta yadda ta kowanne bangare daga cikin mutanen nan da na lissafa zata iya taka rawa a gurbinsu''ya zarce da gaya mata ra'ayinsa da qa'idarsa me yakeso da abinda bayaso,ya kammala yana maida numfashi yayin da maryam tayi shiru har yanzu kanta na kwance a qirjinsa
Babu shakka abdallah mutum me mai sauqin ra'ayi da hali qwarai da gaske,tasha jin ana fadan halayen masu sunan,sai yau ta sake tabbatarwa hakan suke,yau din da Allah ya hadata zaman aure da mai irin sunan,wata qila sun samu tabarrakin sunan da ya zamto babu sunan da Allah yafi so irin abdullahi sai abdur rahman,dama ya bata ta fadi nata dukkan ra'ayin yaci mata alwashin kiyayewa shima,saboda zaman tare kowa,nada haqqin akan dan uwansa,bawai shi kadai ke da haqi ko keson kyautatawa ba,Allah ya fada cikin qur'aninsa mai girma cikin suratul baqara''walahunna mislul lazi alaihinna bilma'aruf,suna da(su mata)kwatakwamcin abinda ke kansu na kyautatawa(akan mazansu,ma'ana yadda zata kyautata maka kaima akwai kawatankwacin hakan a kanka)
itakam kasa fada tayi sai da ya matsanta mata kan haqqinta itama ta fadi din
''qaunarka kawai abdul idan ka bani ya isheni rayuwa,ka soni har mutuwarmu,ka riqe amana ta,kada ko tozarta qaunar da nake maka''
''har *ABADA* har *ABADAN* maryam banjin akwai abinda zai sa na tozarta tukuicin qaunar da kika yimin,idan dai wanan ne matsalarki ki goge shi daga babin matsala daga ciki kundin rayuwarki''ya fada yana shafa gashin kanta da ya sauka har kafadarta
wani irin bacci sukayi mai cike da qauna da tsantsar bege cike da shauqin juna
๐๐๐๐๐๐๐
Da safe sai guduwa tayi don ta fuskanci abdallah na son sake tsareta wai tayi wanka ta shirya anan,ita kuwa batason abinda zaisa mami ta gane bata kwana a dakinta ba,duk da tasan babu ruwan mamin ba nunawa zatayi ba ama abun da kunya tusa gaban suruki
shigarta waitin parlour din taci kark da kibrin yana fitowa daga sashen nasu,ta sake kallon agogo qarfe shida saura na safe,da,sauri ya qaraso gareta
''yauwa dama ke nake nema na rasa yadda zanyi na ganki''da mamaki kan fuskarta ta kalleshi
''lafiya๏ผ''
sai ya hau sosa kai
''ah...mero...mero ke nemanki,tana daki''
mamaki ya cikata saidai bata ce komai ba ta nufi bangaren nasu
gabanta ne ya dunga faduwa ganin meron nafa rusa uban kuka,duk da ita kanta ta tsorata amma sai ta danne ta qarasa inda take,sai kuwa ta sake qara sautin kukan nata,take ta gane abinda ya faru da ita,bata iya cewa komai ba ta taimaka mata tare da koya mata wasu dabarun data fusknaci meron bata sani ba,ta tausaya mata tsoro ya sake cikata,jikinta duk yayi sanyi saidai bata nunawa meron ba din kada ta karya mata gwiwa,haushin labaran ya kamata,me yasa sam su,basu da haquri,atleast ai ya bari yan uwanta su koma
Kukan mero yaqi qarewa,zama tayi ta dinga mata bayani sannu a hankali ta fahimceta,ta samu ta daina kukan bayan digon bayani data mata,duk da ita ma ba sanin wani abun tayi ba ga kunya na yadda zata mata bayanin,bata kai ga tafiya ba kiran abdallah ya shigo wayar ta,da sallama tare da sanyin jiki
''shine kika gudu ko๏ผ,idan kin gama da maryar labaran din kicewa mami na fita amma bazan jima ba zan dawo,shima gashi nan muna tare ki gayawa amaryar tasa''kunya ta cikata
kada dai ace ya sani abdallan,kamar kuwa ya san me take tunanin yace
''ba wani,abu yace da ni ba,nina fuskanta da kaina,naga kuma yana buqatar training,so kada kunya ta ta qaran miki akan ta da''ya qaraahe maganar yana dariya ciki ciki
A sanyaye ta sauke wayar a kunnanta,ji take ma kamar ita yakewa dariyar,ta dubi mero dake kwance hajaran majaran ta miqe
''maigidan naki sun fita da abdallah,zan je mu gaisa da su mami,amma dole ki dinga qarfafa jikinki kada ki nunawa su inna wani abu kin fahimta''kai ta gyada mata ta yi mata godiya ta fice
Tuni har sun tashi,kasancewar mutumin qauye ya saba da tashin wuri,baya malalacin baccin nan na bayan sallar asuba,Allah ya taimaketa mami bata fito ba,don haka anutse suka dinga gaisawa daga bisani ta shige dakin da inna wuro take.
*mrs muhammad [truncated by WhatsApp]
[3:19pm, 10/12/2017] Huguma๐: ๐๐๐๐๐๐
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ *ABADAN*๐บ
๐๐๐๐๐๐
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐๐บ๐๐บ
๐๐บ๐
๐บ๐
๐
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐บ๐๐บ๐๐บ๐
๐บ๐๐บ๐
๐บ๐๐บ
๐๐บ
๐
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐ก
*_home of expert and perfect writers_*
โถ6โฃ3โฃ
*Daga jabir dan Abdullahi R A yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa ''((idan mutum zai shiga gidansa sai ya ambaci sunan Allah yayin shigar tasa da yayin ci abincinsa,sai shaidan yace:baku da abinci baku da gurin kwana(a cikin gidan),idan kuma ya shiga ba tare da ya ambaci sunan Allah ba yayin shigar tasa sai shaidan yace:kun samu gurin kwana,idan bai ambaci sunan Allah ba yayi da zaici abinci sai yace(shi shaidan din):kun samu gurin kwana da abinci))*
Tana dakin suna ta hirarsu da inna wuro mami ya shigo dauke,da kwando wanda ta zuba kayan breakfast a ciki na inna wuron,da sauri maryam ta tashi ta amsheta kamta aduqe tana gaidata,ta amsa mata asakekamar kuma ba aurukarta ba yadda dai sjka saba,zama tayi itama aka soma hirar da ita duk da maryam taja bakinta ta tsuke,saboda kunyar mamin,sai ta tsugunna tana hadawa inna wuro tea.
''ni inna wuro dama zamanki kikahi wlh damu,da kiwa,naji dadi sosai''inji mami,kama bakinta inna wuron tayi
''rufani ki saya ni bintu,ina ni ina zaman maraya,wannan ao saiku,dubi fa don Allah wai wannan ruwan ahine karin safenku,ina kuwa zakuyi qwari''ta fada tana nuna tea din dake hannun maryam tana figita mata,dariya ta basu,baki daya,kai imna wuro nanu dama,duk yadda mami taso ta yadda tayi zamanta aje a taho mata da tsoho alhajinta sam ta qiya.
''amma dai inna ai kya zauna har a raka mairamun taki nata gidan anjima ko,ku gano nata dakin''maryam dake gefe gabanta ya fadi,sai walwalarta ta ragu,tsoro ne fal ranta
''nan fa daya,nifa yau sai qauyen ni'ima bintu''da qyar tasha kanta amma fa saidai a rakata taje ta gano don babu faahi yau zata koma,ta bar tsohonta shi kadai a gida(hmm,mata irin na da kenan masu iya tattala miji da bin umarni)
''kema sai ki zauna ki karya don hajja laila ta iso yau takeso itama ta koma audan din,tana can gun takwararki ana mata gyaran jiki da qunshi,sai kije can ki samesu don nan ba zaku sake na saboda mutane''kamar an dira mata dutse haka taji ta amsa da ''to''
''sannunki bintu,ke dai kin zama uwar kowa kenan,kin kama kowa kin riqe kamar yadda hausawa suke cewa da na kowa ne,arziqinki na kowa ne,Allah ya albarkaci rayuwarki data yaranki,da za'a samu ire irenki cikin al'umma su wadata da an bar kukan yunwa qunci da talauci,Allah ya jiqan mai gidanki''inji inna wuro
''ameen ameen inna,ai shi arziqi da Allah ya baiwa dan adam tamkar ka dauki wani abu ne mallakinka ka baiwa,wani kace ya amfana ya kuma amfanar da wasu,muma aro Allah ya bamu da rabon mu aciki da rabon wasu,ma'ana ka ci ka ciyar da wasu,ruwanka ka ci kai kadai ka tashi ran qiyama cikin wahala,don Allah na narka dukiyar ne ya dinga maka azaba da ita,abinda ka bayar shine rabonka don shi zaka taras a cikin littafinka ranar gobe qiyama,wanda kaci kuma banza ne don na wani ka yiwa ba bare a rubuta maka ladar ka ciyar da dukiyarka ga wani,kai kanka baka da tanbas din dawwama cikin dukiuar,wataran Allah na iya karbe kayansa ya baiwa wanda yaa dama,ko ka muti kabar zuriya to baka aikata alkhairi na wa kake zaton zai kula maka da su๏ผ''
''wannan haka yake binta,Allah kasa mu dace''inji inna wuro,maryam na gefe tana jinsu ita kanta addu'a takewa mamin cikin zuciyarta,ko bata taba mata komai ba ta haifa mata *GWARZON MIJI DAYA TAMKAR DA DUBU ABDULLAHI BAWAN ALLAH*,bare babu irin halaccin da bata mata ba,mami mutum ce wadda samun kamarta zaiyi wuya
ruwan shayin kawai ta sha taji cikinta gaba daya ya cushe don haka ta fice tabarsu adakin,dakinta ta koma tayi wanka ta saka baqar doguwar riga don kada kayan ta su baci garin lalle,can ta tars da haj laila tana hada lallen qunshi,tuni mero an shige cikin dilka da kurkum ga bayaga halawa da aka sha.
Ita kanta kasa gajiya tayi da sabawa fatarta sabulu saboda wani irin santsi da taji tana yi na ban mamaki,itakam dama ko ba'a gama gyaran jkkin nan ba a yau zata cewa haj laila abarta haka,tana kallon yadda mero keta fama ina ga ita,fitowarta kenan haj lailan ta miqa mata wani anu cikin cup sai qamshin citta da kanunfari yake tace
''shanye diyata''haushi ma kamata yayi bata ce komai ba tayi kurba uku ta faki idonta ta fita da shi da niyyar zubarwa
cikin garden na gidan ta shiga ta daga zqta fara zubarwa taji an riqe hannunta,a hankali ta dago kanta sai suka hada ido,sanye yake cikin suit baqi da ja saidai yar saman ya cireta tana singalalin hannunshi,da alamu har ya dawo daga fitar da yace mata zaiyi
sai da ya mashe mata ido daya sannan yace
''shigowata kenan naga wani haske ya cika gidan nan,ina waiwayawa naga ashe kece,shine na biyoki ina fata banyi laifi ba''ya fadi maganar yana qoqarin amshe cup din daga hannunta,tana qoqarin boyewa ta bashi amsa
''um um,ko daya bakayi laifi ba''
ganin yana qoqarin maida abin babba yana son ya rungumeta yasa ta sakar masa cup din a sauqaqe,sai ya leqa ciki yana fadin
''hala wanann abun dadi ne mami ta baki ko,Allah yayi da rabo na kenan nasha๏ผ''ya tambayeta yana kallonta,wani irin kyau yaga tana fitarwa,tambayar kawai yayi amma bai gane me yake fada
da sauri ta girgiza masa kai
''a'ah,kada kasha''
''why๏ผ,muba muta ne bane''yayi tambayar yana dan zaro ido gami da dage gira.
Sai kawai taga ya dangwalo ya tsotsa
''hmmmm,gaskiya da dadi''ya fada yana kaiwa bakinsa,kafin ta qwace har ya kurba,ta karbe kana ta zubar
''na gaya maka mazq baku sha,idan poising ne kuma fa๏ผ''
sai taga ya saki murmushi mai fidda sauti kana ya harde hannunsa a qirji
''sai abun ya zama abun alfahari a gareni,masoyiya ta bawa masoyinta guba sabida tsabar qauna,kuma zaqinta zanji dear na,ballantana ma na sani ke din ba zaki iya ba,saboda wasu ma da suka yi yunqurin bani naci kin kawar da hakan,ko kin manta har asibiti kika je aka tabbatar miki da irin nau'inta da kuma qarfinta๏ผ''
ido ta zaro,wai abdallah aljanine ko kuwa yana da su ne๏ผ
murmushi ya kuma yi,ta bude bakinta da niyyar yin magana,sai yayi azamar qarasowa gabanta,yasanya tafin hannunshi ya rufe labbanta yana kallon qwayar idonta tare da cewa
''yi shiru da bakinki,ki adana duk wasu tqmbayoyi da kike da,su,wannan hiran na daya dagq cikin hirarrakin da na tsara mana,cikin gidan mu na qauna,a kan gadon soyayya,a kuma qirjin masoyi''ya qaraahe maganar yana kashe mata ido.
kunya ta kamata sai ta zame bakinta tana murmushi ya sake matsowa kusa da ita yana yin qasa da murya saitin kunnenta
''ina fata kin tanadarmin salo salo na soyayya da,qauna wadda zaki shayar da ni,kinsan abdallah dan soyayya ne,yana son soyayya musamman ga matarsa''ya fada yana qoqarin janta jikinsa,gabanta ya shiga faduwa,ta faki idonsa ta zille tayi hanyar fita,baiyi yinqurin binta ba don ya tabbatqr da mutane a wajen amma sai ya matso uadda zata iya jinsa ya biyo bayanta
''ki gama zulle zullenki yarinya,awa,nawa,ne ya rage๏ผ''hakan da ya fada sai ua sata tsayawa ta juyo ta dubeshi idonta har ya cika da qwalla,dariya ya sa mata tayi hanzarin ficewa daga gun.
Zuwa la'asar gaba daya hajja laila ta gama da kyawunta,tamkar buga qunshin akayi aka dayeshi,banu kuskure ko daya aciki,ja ne amma har saman hannu da saman qafa,abinka da fara ya fito kuwa yayi marun,kyau kam basai an fadeshi ba ya gama yi,tuni yan kawo mero sun tafi don yaci ace ma zuwa la'asar din sun kai gida,saukowarta kenan daga saman mami dauke da wata leda wadda wani arnen codenet ne a ciki da aka fidda wa dinki na garari,kudadr mamin ta saka masu yawa ta siyawa maryam din sabida wannan rana,sallama akayi aka shigo falon qasan,raliya ce janye da hannun fadil(yaronta)sai hindatu da lubabatu da kulu,baaba huwaila da hajiya atika.
Cikin dakinta suka shiga ita da raaliya hindatu lubabatu da kulu,baaba hadiza da hajiya atika kuwa suna sama gun mami,mami ce tasa duka suka zo don yi mata rakiya,hira suka dinga yi wanda zuwansun ya rage mata fargaba sosai,lubabatu da kulu nata kallen kallen gidan mami don yau ne zuwansu na farko,sun tabbatar cewa Allah ya yiwa adda maryam din baiwa ba qarama ba.
Raaliya ce ta shiryata tsaf cikin codenet din orange da yellow,kana ta dora mata alkyabba da mamin ta hadota cikin kayan,yellow ce mai ratsin fari,fadar irin kyawun da tayi ma bata baki ne,su kansu tsayawa sukayi kallonta,kai tsaye gin mami suka fara zuwa kana suka fice suka barta ita da ita,kallonta mamin take cike da farinciki,burinta kam ya gama cika a yau,hannu ta miqawa maryam din ba musu ta bata,gefeanta ta zaunar da ita kana tace
''maryam,da farko abinda zan fara cewa dake shine kiyi haquri,don babu wani abu da ya wuce haquri da mace zata riqe wanda zai,zame mata jagora kuma madogarar gidan aure,haquri maryam shine komai a rayuwa,kiyi haquri a duk yanayin da zaki tsinci kanki a gidan aurenki,duk wata mace da kika gani zaune gidan aurenta wallahi ba za'a rasa wata matsala da take fuskanta ba komai qanqantarta,ta wata ne tafi ta wata,qila wadda kikewa hangen ta haye ta huta da zata buda miki cikinta wallahi saikin tayata kokawa,komai dadinki da mimi wataran sai kun samu